Free chapter · Read without an account
08
Kamar yadda indo ta umarce su haka kowannensu ya shiga gida ya kulle, direct kasuwa tayi tana tafe tana wakarta, daidai wajen mai chaji ta tsaya,wani katon dutse tasaka ta balle mabudin, shiga tayi ta dakko wata speaker kunna tatayi ta saka wani kida mara dadin saurare, ta kore, abinka da dan karamin kauye take ko ina wannan karar ta wanzu, tana kara gaba, gida taje ta bude kayanta, wani katon abu naga ta dauka fari tass, rafin dan marka taje, bata bata lokaci ba ta cilla sannan ta tafi, speaker ta dauka taita gantalli, ta hana kowa bacci, ko wane gida tazo wucewa sai taji kukan yaro.Dandali ta koma ta nufi rumfar idi zama tayi ta fara cin breadi, sai da ta koshi ta fito, mai tukubar tsire, kai in takai ce muku labari sai da ta aikatawa mutanen kauyen nan barna mai yawa, sai wajen 3 sannan ta koma ta maida speaker tai gida, tana zuwa ta kwanta ta fara sheka bacci.
Tin aasuba al'ummar kauyen ke tafiya debo ruwan, abin mamaki jan ya ragu dan za a iya sha ma.Indo sai can wajen tara ta tashi, ba sallah ba salati ta fito daga bukkarta, gaban iyalle taje ta zauna,kallonta tayi tace "tashi kije kiyi sallah, ko kallonta batayi ba tace bazanyi ba alkur"an kuma ki bani abinci na, iyalle ce tace shikenan ke da allah ai, zo kije ki kaimini nika, da har zatace bazata ba amma sai tayi tinanin yau garba zai dawo tsabb zai casata shisa ma ta kwammace gara ta kai.Nikan ta dakko ta fito, daga wajen ba inda taje sai nika tana shiga taga wani dan masifan layi, tana shiga ta ture na kowa ta saka na nata a gaba, wata budurwa ce ta mike tafi indo girman jiki, tazo kanta tace'ke indo kinga dai na rigaki dan allah ki bari a nika min, indo bata kula ta ba, mai nikan yana gaam wanda yakeyi ta kwatsa nata akai, a lokacin aka nika mata sannan ta dakko tayo gaba.Fitowarta ne yasa ta hango lantana ta dakko nika, cike da zafin nama ta karasa ta hankade nikan ya zube, kafin ma kayi wani kwakkwaran tinani taji saukar kulli a cikinta, danneta tayi tana kirba, sai huci take kamar wata macijiya, badai ran nan kin gudu ba, bara yanzu naje na samo wukar, tashi tayi ta shige gida, da kyar lantana ta mike ta fara kokarin ceton rayuwarta.Koda ta fito bata ganta ba hakan yasa ta kara maj sai gidan su salame, salame ta juya baya tana wanke wanke taji saukar icce, juyowa tayi cike da masifa, idanunta ne suka sauka akan na indo, cike da jin tsoro yasa ta fara jan baya, amma ina kafin tai motsi indo ta cafki wuyanta ta fara dukanta,sai da ta jigata ta sannan ta fito tana huci.Hango fadawan mai gari tayi, take ta kwala musu kira tace nasan ni kuke nema muje, basu san taya akai ta sani ba, dan haka suka tafi, tafiya sukeyi a kofar gidan mai gari ta tsaya, idanunta idanun malam iliya, ai tana ganinsa tasha jinin jikinta, dan haka ta tsaya tana raba ido.Malam iliya ne yace "mai gari kayi sheda daga yau na sallami indo daga makaranta ta, bana buqatar ta kara zuwa domin indo ta zame min jaraba, ina iyawa da kowa amma banda indo, dan haka a nema mata wani malamin amma badai ni ba yallabai, mai gari ne ya kalli indo yace" kinji dai me ya fada miki ko, mai makon tayi magana sai murguda baki tayi tana kunkuni.Koda ta koma gida garba ne zaune akan tabarmar kabar da iyalle ta shinfida masa, gefe ta samu ta rakube kamar wata ta kirki, kallonsa take ganinsa da litattafai, pen, biro, uniform, takalmi, zaro ido tayi tana fadin shikenan na shiga 3 yanzu kawu garba sai ya kaini wannan makarantaar, tinaninta ya katse da fadin"ke ki tabbatar yau baki fita ba domin gibe da sassafe zamu wuce zuwa dutsinma, saboda naga alamun lamarinki har da jahilci,tashi yayi ya tafi ya bar wajen.