Free chapter · Read without an account
09
Tin fitar garba ba wanda tayiwa magana sai tashi tayi ta tafi dakinta, zama tayi tana tinanin meye mafita, domin batason wannan makarantar, kuma tasan saboda wannan gantalin nata ne yasa za a kaita, ganin bata da wata mafita ne yasa ta mike tace "bara naje na karasa aikina dan wallahi habi sai jikinki ya gaya maki, fitatayi tana tsallenta.Direct gidan su dije taje, tana shiga ta hango suna cin nama, ai wani tsalle tayi ta sako hannu, ci takeyi amma fadi takeyi" amma tsabar rashin mutunci dije kuna cin wannan dadin shi ne kika ki kirana, yanzu da ni ce da tini na nemoki, shegiya kawai, "wai dije a ina kika samo wannan naman, dariya tayi tace a dakin lawan saboda kinsan aljanu sun masa duka.Mikewa tayi tsamm ta nufi bakin kofar dakin, ba wani excuse ta danna kai tana muzurai, wasu kwanika ne guda 3, zama tayi tana baje baki yayin da lawan ke kallonta a fusace, ko kallonsa batayi ba ta fara kokarin aikin budewa, daya naman data baro ne, daya kuma garau garau sai ruwa, ba abinda ya fito daga bakinta sai "Alhamdulillah amma dai lawan ka koshi da wannan abincin naka shisa kakeso na maka aiki, lawan kasa magana yayi ya tsaya yana kallonta.Kofar gidan mai gari ne taff da mutane, kowa yana tofa albarkacin bakinsa kuma ba komai bane maganar tasu sai indo,ita wadda akeyin maganar dominta ma bata wajen bare tasan ma da ita akeyi, garba ne ya mike yace "to jama'a ku saurara dik wannan jawabin ba akan indo bane to insha allahu nan da gobe war haka tana makaranta, domin kuwa zata koma makarantar kwana ta baku waje ku huta, kowa na wajen ba abinda yake fadi sai Alhamdulillah, kara ma haka.Mai gari ne ya katsesu yace "to ku sani dai wallahi dik mai so ya rabu da indo lafiya to ya zama tabbas ya bata wani abin, idan ba haka ba wallahi kunsan sauran, liman ne ya kallesa da mamaki yace" amma me gari yadai me ya faru, murmushi mai gari yayi yace "bazaka gane ba liman wallahi aljanun indo su suka targadi ni kwanaki, kowa na wajen shiru yayi domin kuwa idan haka ne tabbas indo nada aljanu masu karfi.Da wannan shawarar aka watse akan gobe karfe 8 na safe kowa zai je domin suyi sallama da indo.Indo sai wajen karfe 9 ta isa kofar gidan habi, kallon gidan tayi tace "shegiya wato ke ga aljana, ai wallahi yau sai kin tumurmusu, idsn kuma ba haka ba ina nan dake sai na dauki fansa, kokarin tura kofar take amma gam taki motsi, kasantuwar an saka mata kyaure mai kwari, tsalle tayi ta dare katangar ta shige gidan, a hankali kamar wata barauniya, shiga take sai da tazo dai dai kofar dakin sannan ta tsaya.Shiga dakin tayi tana murmushin samun nasara,habi ta tarar tana ta sharar bacci, da dsriyar mugunta tace "shisa na baro wancan sokon mijin naki a wajen zaman majalissa,daure fuskarta tayi sannan ta dankara mata wani kulli a gadon baya, firgigit ta mike tana sosa wajen, tana kalle kalle, mata ta gani zaune a kan gado.Indo ce ta ce ai sai nayi maganinki, tashi tayi tsaye, ta fita can kuma ta dawo da ruwan sanyi a bukiti,dagashi tayi ta juye akan gadon take dakin ya jike, maimakon ta tafi aa sai da ta cika dakin da ruwa, sannan ta sami habi, wata leda naga ta zaro sai kuma ta bude, wani abu ta fito dashi a dunkule, habi bata ankara ba ta tura mata a baki, sannan ta fito kullota tayi ta inda tabi ta nan ta koma.
Gida ta tafi tana shiga taci karo da garba yana mitar ina indo, sadaf sadaf ta fice domin tasan gamonsu da garba ba kyau, ganin ta shi ma yasaka shi yin shiru yana hira da inna, tinda ta shiga bukkarta, ba abinda takeyi sai bincike, kafin wani lokaci kuma ta debo tulin kudade, zama tayi ta shirya su, sai tayi dariya lokacin amfaninku ya zo."Amma kuma ya kamata ace na tafi da wani abu na musamman, zama tayi a gadon sai da taji batajin motsin kowa, sannan ta fito,ta rasa ya zatayi domin tanason guzuri, kasan cewar makotansu ana siyar da gurasa ne yasa ta haurawa, wani katon buhu ta ciko da gurasa, sannan ta dawo tana dariya.