Free chapter · Read without an account

BENEATH THE CALM

by Jiddaah Barkum · ZAYD ARMAAN

ZAYD ARMAAN

CHAPTER 113

BENEATH THE CALM

JIDDAAH BARKUM

——-

Bayan ɗan lokaci, likitan ya fito daga emergency room ɗin, yana cire glasses dinsa yayin da ya kalli Imraan da Sameer da ke zaune a reception, “You can go in and see him now, he’s awake, but he still needs enough rest, kada ku daɗe kuna damunsa da magana sosai, jikinsa yana buƙatar hutawa,” nan take Imraan ya miƙe tsaye, “Thank you, Doctor, Allah Ya saka da alheri,” likitan ya gyada kai, sannan ya sake ba su wasu ƙarin bayanai kafin ya wuce zuwa wani ɗakin, da jin cewa za su iya shiga su ga Zayd, Raihana wadda take rakube a gefe ta ɗago kanta da sauri, tun da aka shigar da shi cikin emergency room, hankalinta yana can, amma ta kasa samun ƙarfin tambayar likitocin komai, “Ya farka?” ta tambaya a hankali, muryarta cike da fatan jin amsar da take so, Imraan ya juyo gare ta, “Eh, ya farka, Alhamdulillah, come on, mu je mu gan shi,” ta miƙe a hankali, ta bi bayansu tana riƙe da gefen hijab ɗinta, zuciyarta na bugawa, a duk matakin da ta ɗauka zuwa ɗakin Zayd, sai ta ji wani irin farin ciki yana gaurayuwa da tsoro, Alhamdulillah, he’s awake, ta maimaita kalaman a cikin zuciyarta, tana jin kamar wani babban nauyi ya sauka daga ƙirjinta, da suka shiga ɗakin, sai suka tarar da Zayd a kwance a kan gadon asibiti, idanunsa a rufe, fuskarsa a ɗan gajiye, an haɗa shi da na’urorin da ke lura da yanayin jikinsa, yayin da hannunsa ɗaya ke kwance a gefen gadon, Sameer ya ƙarasa kusa da shi da sauri, “Sir, how are you feeling now?” Zayd ya buɗe idanunsa a hankali, ya kalli Sameer na ɗan lokaci kafin ya amsa, “I’m fine,” muryarsa ta fito a raunane, amma har yanzu akwai irin nutsuwar da ya saba da ita, Sameer ya ɗan numfasa, yana jin sauƙin ganin maigidan nasa a farke, “Thank God, Sir, you really scared us tonight,” Imraan ya ƙaraso kusa da gadon shi ma, yana kallon Zayd da wanann kallon nasa na shaqiyanci, “Wallahi, ka ba mu tsoro sosai, ka san yadda na ji lokacin da na gan ka a haka? For a moment, I didn’t even know what to think,” Zayd ya ɗan ɗaga gira, amma bai ce komai ba, Imraan ya girgiza kansa a hankali, “Anyway, Alhamdulillah ka farka, ka dai kwantar da hankalinka ka huta, we’ll talk properly when you’re feeling better,” Zayd ya jinjina kai a hankali, a duk wannan lokacin, Raihana tana tsaye a gefe, kusa da ƙofar ɗakin, ta kasa ko motsawa, idanunta sun makale a kan Zayd, tana nazarin fuskarsa kamar tana son tabbatar da cewa da gaske ya dawo hayyacinsa, ta so ta ƙarasa kusa da shi, ta so ta tambaye shi ko har yanzu cikinsa yana ciwo, ta so ta gaya masa yadda ta ji lokacin da ta same shi a toilet, yadda ta firgita, yadda ta yi tunanin ta rasa shi har abada, amma kalaman da ya yi mata kafin ya suma suka sake dawo mata a rai, ta haɗiye yawu, tana jin wani irin raɗaɗi a zuciyarta, da na sani…… A hankali ta sauke idanunta, tana ƙoƙarin danne hawayen da suka fara taruwa a cikinsu, Imraan ya juyo gare ta, ya lura da yadda take tsaye shiru tun shigowarsu, “To, kin gani ko? Ya farka, alhamdulillah, ki kwantar da hankalinki yanzu,” Raihana ta ɗago kai ta kalle shi, sannan ta gyada kai a hankali, Imraan ya sake kallon Zayd, “Zuwa safe, we’ll come back with Sameer, ka dai huta sosai, Sameer zai fita ya nemo muku abin da za ku iya buƙata kafin safe, sannan ya kawo,” Zayd ya jinjina kai, Imraan ya gyara tsayuwarsa, sannan ya yi masa murmushi, “Alright, rascal, lemme go, sai da safe, we’ll be back,” Zayd ya ɗan kalle shi, “Hmm,” Imraan ya yi dariya a hankali, “Look at you! Har yanzu kana da wannan attitude ɗin naka, even on a hospital bed,” Sameer ya yi murmushi kaɗan, amma Zayd bai nuna wata damuwa ba, ya dai juya kansa kaɗan, yana nuna cewa ya gaji da magana, “Rest, Sir, we’ll see you in the morning,” Sameer ya faɗa cikin ladabi, Zayd ya jinjina kai kawai, Imraan ya sake kallon Raihana, sannan ya yi mata alamar ta kwantar da hankalinta kafin shi da Sameer su fice daga ɗakin, a hankali ƙofar ta rufe, kuma a wannan lokacin… Su biyu ne kaɗai suka rage a ɗakin, Zayd da Raihana, shiru ya mamaye ɗakin, sai sautin na’urorin da ke lura da bugun zuciyarsa kawai ake ji, Raihana ta tsaya a inda take na wasu daƙiƙu, tana kallon Zayd daga nesa, ta yi tunanin ko zai juya ya kalle ta, ko zai tambaye ta wani abu, ko ma ya nuna cewa ya san tana wurin, amma Zayd bai yi ko daya ba, ya rufe idanunsa a hankali, sannan ya juya kansa zuwa ɗayan gefen gadon, yana nuna mata a fili cewa ba ya son yin magana da ita, Raihana ta tsaya cak, kallon bayansa take yi, zuciyarta na mata wani irin ciwo, is he still angry with me? Ta san amsar tambayar, tabbas yana jin haushinta, ta haɗiye yawu, ta ɗauki matakai kaɗan zuwa gadon, tana jin ƙafafunta kamar ba sa son ɗaukar ta, a hankali ta ƙaraso kusa da shi, ta tsaya tana kallon fuskarsa da ya juya daga gare ta, “Sannu…” ta fada cikin sanyin murya, bai amsa ba, ta ɗan sunkuyar da kanta, “Yaya kake ji yanzu? Ciwon ya ɗan ragu?” Zayd bai buɗe idanunsa ba, balle ya nuna yana jin abin da take faɗa, Raihana ta matsa kaɗan, ta gyara gefen bargon da ke jikinsa, tana ƙoƙarin ganin ko akwai wani abu da take iya yi masa, “Please, ka yi ƙoƙarin hutawa, likita ya ce kana buƙatar rest sosai,” har yanzu babu amsa, sai ta ji kamar an ɗora mata wani nauyi a ƙirji, ta san Zayd mutum ne mai wuyar ganewa, kuma idan ya ji haushi ko baya Jin haushin shi dai ba ya saurin bari a gane abin da ke zuciyarsa, amma a wannan lokacin, yadda yake yin watsi da ita ya fi duk wata magana da zai yi mata zafi, “Kayi hakuri…” Sai kuma Ta yi shiru, ta kasa ƙarasa maganar saboda muryarta ta fara rawa, ta so ta ba shi haƙuri, ta so ta bayyana masa cewa a lokacin da ya zo wajenta, ba ta fahimci yadda yake ji ba, kuma ba ta yi tsammanin lamarin zai kai ga haka ba, amma duk da haka, ta san kalaman da ta yi masa sun yi masa zafi, “I’m sorry,” ta furta a hankali, Zayd bai motsa ba, babu ko alamar cewa ya ji ta, Raihana ta ɗan lumshe idanunta, tana jin hawaye sun fara taruwa a cikinsu, shi kam zayd Ya ci gaba da kwanciya yana kallon ɗayan gefen ɗakin, kamar babu wanda yake magana da shi, hawaye ɗaya ya gangaro a kumatunta, ta goge shi da sauri, tana ƙoƙarin danne sauran, amma abin ya gagara, ta ji zuciyarta tana mata nauyi, musamman ganin yadda yake ƙoƙarin nuna mata cewa ba ya son ko jin muryarta, a ƙarshe, ta daina ƙoƙarin tilasta masa ya amsa, a hankali ta ja kujera daga gefen gadon, ta zauna a kai, sannan, ta yi tagumi, tana kallon bayansa da ya juya daga gare ta, ta kasa cewa komai, Zayd kuwa yana kwance shiru, idanunsa a rufe, yana sane da kasancewarta a ɗakin, ya ji muryarta, ya ji yadda ta nemi ya yi haƙuri, amma duk da haka bai juya ya kalle ta ba, haushin da yake ji bai bar shi ya nuna mata ko da ɗan tausayinsa ba, a tunaninsa, idan har ta kasa sauraronsa lokacin da ya je wajenta yana neman taimako, me ya sa shi kuma zai yi saurin yafe mata yanzu? Ya sake juya kansa kaɗan zuwa ɗayan gefen, yana ƙoƙarin samun nutsuwa, Raihana ta kalli bayansa, hawaye na zuba mata a hankali, ta yi tagumin nata, tana jin kamar tana zaune ita kaɗai a cikin ɗakin duk da kasancewarta kusa da shi, a wannan daren, ba ta bukaci Zayd ya yi mata magana mai daɗi ba, ba ta bukaci ya yi mata murmushi ba, abin da kawai take so shi ne ya kalle ta, ko da na daƙiƙa ɗaya ne, ta tabbatar cewa duk da haushin da yake ji, har yanzu yana iya kallonta kamar yadda ya saba, amma Zayd bai juya ba, kuma a cikin shiru mai nauyi na ɗakin asibitin, Raihana ta ci gaba da zama a kujerar, tana kallon bayansa, tana jin hawayenta suna gangarowa a hankali, yayin da shi kuma yake ƙoƙarin nuna mata cewa a wannan karon, ba zai zama mai saurin sassauta zuciyarsa a gare ta ba, a takaice dai, sai da Zayd ya kwana a asibiti, washegari aka yi discharging dinsa bayan likitoci sun tabbatar da cewa jikinsa ya fara dawowa normal, sai dai har yanzu yana jin weakness a jikinsa, saboda haka aka ba shi shawarar ya huta sosai, a tsawon lokacin da suka kwana a asibitin, Zayd bai ko kalli inuwar Raihana ba, balle ya saurare ta, tun tana ƙoƙarin yi masa magana, tana ba shi haƙuri da ƙoƙarin bayyana damuwarta, har ta gaji ta zuba masa idanu kawai, duk yadda ta so ta samu damar yin magana da shi, Zayd ya ƙi ba ta ko da ƙaramin opportunity ne, da safe, Sameer da Imraan ne suka zo suka ɗauke shi suka mayar da shi gida, a lokacin, jikinsa ya ɗan samu sauƙi, sai dai weakness ɗin bai gama barinsa ba, amma duk da haka, ko kallon part ɗin Raihana bai yi ba, kai tsaye ya wuce part ɗin Seeyama, kamar babu wata Raihana a gidan, Raihana ta bishi da kallo har ya ɓace daga ganinta, nan take ta ji wani irin ciwo ya tokare mata zuciya, hawaye suka cika mata idanu, Ya Allah, har yaushe zai ci gaba da yi min haka? Ta gaji da ƙoƙarin neman attention ɗinsa, gaskiya ba ta son abin da ke faruwa a tsakaninsu, amma kuma ba ta san yadda za ta gyara shi ba, wannan sharen da yake yi mata, da wannan shirun da ya ƙi karya wa, sun fi ma ta ya buɗe baki ya gaya mata komai a fili, ko da abin da zai faɗa zai ɓata mata rai ne, at least, ta san inda ta dosa, amma wannan ignoring ɗin nasa yana kashe mata zuciya a hankali, ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, ta goge hawayen da suka gangaro mata, sannan ta juya ta nufi part ɗinta cikin sanyin jiki, kamar wadda aka cire wa wani abu mai muhimmanci daga rayuwarta, a ɓangaren Seeyama kuwa, tana zaune tana cin abinci lokacin da ta ji an buɗe ƙofar part ɗin, da sauri ta ɗago kai, ta miƙe tsaye tana kallon ƙofar, da idanunta suka haɗu da na Zayd, gabanta ya faɗi sosai, ta haɗiye yawu da ƙyar, hannunta ya tsaya a iska yayin da ta ji wani irin tsoro da mugun shakkarshi yana ratsata, tun lokacin da ta ga an ɗauke shi a sume, hankalinta bai taɓa kwanciya ba, yanzu kuwa ganinsa a gabanta, cikin ƙoshin lafiya duk da ɗan weakness ɗin da ke tattare da shi, ya sa ta rasa yadda za ta yi, ta buɗe baki da niyyar magana, “Babe, ni—” Amma kafin ta samu damar kammala maganar, ya wuce ta ba tare da ya ko kalle ta ba, kai tsaye ya shige bedroom ɗinsa, ya ja ƙofar ya rufe, Seeyama ta tsaya cak a inda take, bakinta a buɗe, a hankali ta sauke hannunta, ta koma ta zauna a kan kujera, tana kallon ƙofar ɗakin kamar za ta buɗe a kowane lokaci, ta kasa ci gaba da cin abincin, cokalin da ke hannunta ta ajiye, zuciyarta na bugawa da sauri, ta san Zayd, ta san irin shiru nasa idan ya fusata, kuma ta san idan ya yanke shawarar ɗaukar mataki, ba lallai ne ya fara ihu ko ya yi barazana ba, wani irin sanyi ya ratsa jikinta, me zai yi min? Ya gano abin da na yi ne? Ko kuwa yana jiran lokacin da zai fuskance ni? Ta dafe hannayenta biyu, tana ƙoƙarin kwantar da hankalinta, amma hakan ya gagara, abin da ta fi tsoro shi ne rashin sanin abin da ke cikin zuciyar Zayd a yanzu, domin a wannan karon, ba ta san irin hukuncin da zai ɗauka a kanta ba, kuma wannan rashin sani ɗin ya fi komai tsoratar da ita, a dai-dai lokacin da Seeyama ke zaune cikin fargaba, wayarta ta fara ringing, ta ɗauko wayar, ganin Mommy ce ke kiranta ya sa ta miƙe da sauri ta shige bedroom ɗinta kafin ta ɗaga kiran, fuskarta a haɗe ta amsa wayar, ba tare da ta fara gaisuwa ko tambayar ya uwar ta take ba, “Hello,” Mommy Hauwa ko a jikinta, kamar ba ta lura da rashin tarbar da aka yi mata ba, kai tsaye ta shiga maganar da ta kira saboda ita, “Yanzu kin ji rabin shirun? Maimakon ki kira ki tambayi dalilin da ya sa ban kawo miki Rabi ba, tunda na gaya miki washegari zan kawo ta, sai kika yi mana banza kika watsar da mu, to, ga mu nan muna shiri, zan kawo ta yanzu, dama zazzaɓi ta yi ne, sai yanzu ta ji daidai, in Sha Allahu, cikin minti talatin za mu iso,” Seeyama ta hade rai kamar mommy na gabanta, sannan ta dafe goshinta cikin ɓacin rai, “Mommy, ni fa na fasa! Na ma gaya wa babe cewa ba na so, zan yi komai da kaina kamar yadda kowace mace take yi a gidanta, ai naga ba ni kaɗai kike so ki kawo wa yarinya ba, Mommy, don haka na fasa, ke ma sai ki fasa kawo mata, mu duka mu rasa, kowacce ta zage ta yi nata!” Ta faɗi maganar cikin ko in kula, kamar wadda ba ta ganin laifin abin da ta faɗa, a ɗaya ɓangaren wayar, Mommy Hauwa ta yi shiru na ɗan lokaci, ba don ta rasa abin da za ta ce ba, sai don ta kasa yarda da yadda ’yarta ke magana da ita, “Seeyama, kin san da wa kike magana kuwa?” ta tambaya cikin nutsuwa, amma muryarta ta sauya, Seeyama ta juya idanu, “Toh mommy me nace? Ai nasan kece,” “Good, tunda kin sani, ina so ki tuna cewa ni mahaifiyarki ce, ba ƙawarki ba, ba zan zauna ina sauraron wannan rashin manners ɗin naki ba, na gaya miki zan kawo Rabi, kuma na riga na yi magana da ita, ba ke za ki sa ni na karya alkawarin da na ɗauka ba saboda kawai kin tashi da wani mood ɗin daban,” “Amma Mommy—” “Dallah ni rufemin baki!” Mommy ta katse ta, “Kin yi tunanin abin da kika faɗa kuwa? Kin ce saboda ina son kawo yarinya ga Raihana, shi ya sa ke ma ba ki buƙatar taimako? To, me ya hana ki tunanin hakan tun farko? Me ya sa sai yanzu kika tuna da hakan bayan a gaban raihana da mijinku nace san kawo sai yanzu zakice wani kin fasa ?” Seeyama ta yi shiru, tana cizon leɓenta saboda ɓacin rai, Mommy ta ci gaba, “Raihana ma sabuwar amarya ce a gidan, idan tana buƙatar taimako, za a taimaka mata, ke ma idan kina buƙatar taimako, za a taimaka miki, ba gasar da ke tsakaninku ba ce, Seeyama! Amma idan kin zaɓi ki ƙi taimakon da aka shirya miki saboda kawai ba ke kaɗai za a taimaka wa ba, wannan zaɓinki ne,” Seeyama ta ja dogon numfashi, amma maimakon ta yi shiru, sai ta sake magana cikin ɓacin rai, “To, ni dai na ce na fasa, ba na buƙatar kowa ya zo ya yi min komai!” “Fine,” Mommy ta amsa a taƙaice, “Amma ki sani, ba zan yarda ki yi amfani da wannan halin naki wajen ɓata wa kowa rai ba, zan kawo Rabi kamar yadda na tsara, idan tazo ki kashe ta,” da haka ta katse kiran, Seeyama ta zuba wa wayar ido, numfashinta yana fita da ƙarfi, ta jefar da wayar a kan gado, sannan ta zauna tana dafe kanta, komai ya fara haɗuwa a kanta, Zayd yana cikin wani irin fushi da ba ta san yadda za ta fuskance shi ba, Mommy kuma ta ƙi sauraron ta, yanzu ga batun Rabi da ba ta so ta zo, amma duk da haka Mommy ta dage a kan za ta kawo ta, ta ciji leɓenta, idanunta suka yi jajir, “Ni dai banida sa’a” ta fada tana Jin kamar ta fashe da kuka, Arman Mansion kuwa, Ummie ce tsaye a gaban mirror, wayarta manne a kunnenta tana magana da Anty Mariya, amma daga kallon fuskarta, za ka fahimci cewa akwai abin da yake damunta, ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, sannan ta girgiza kai, “To, Mariya, ya zan yi? Ba zan sa Zayd ya hana ’yar uwar ubansa abin da ta ce za ta yi ba, kuma ni, kina tunanin zan kira Raihana in ce mata ta faɗa wa mijinta cewa ba ta so? Girma na ne ko mutuncina ne hakan? Wallahi, abin nan ya daure min kai, amma kamar yadda Suhaila ta faɗa, kawai sai na ga kamar Hauwa tana da wani abu a ranta, me ya sa za ta kai wa Raihana yar aiki, ba Seeyama kaɗai ba? Abin ya daure min kai sosai,” kawai dan ba zaka zauna a gaban yaro kana nuna halin mutum ba,” Anty Mariya ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ce, “Toh, ni Ummie, zan je gidan, zan yi wa Raihana hannunka mai sanda a kan yarinyar da za a kawo, a kawo ta ɗin, amma ta iya takunta da ita, ta kula da motsinta, amma ba za a ce a zuba ido kawai ba, bayan ba ta san halin Hauwa ba, kada ta ɗauka cewa za ta yi komai da zuciya ɗaya, ta je ta saki jiki da ko ma wa za a kawo, sai daga baya a fara zantuka marasa daɗi da za su dagawa kowa hankali,” Ummie ta yi shiru, tana kallon kanta a madubin, kamar tana nazarin kalaman kanwarta, a hankali ta ce, “Kina ganin haka zai yi, Mariya?” Anty Mariya ta yi caraf, “Toh, Ummie, me kike ganin mafita? Tunda kin hana a tunkari Hauwa a faɗa mata ba a so, ni sanyin nan naki yana bani mamaki! Har inda za a cuce ki, shiru kike yi? Ni wallahi, da ni ce ke, da ta ga abin al’ajabi!” Ummie ta yi murmushi mara ƙarfi, ta girgiza kai, “Kin san ni, Mariya, ba na son rigima, musamman a cikin gidan Zayd, ina so komai ya tafi cikin mutunci, amma wannan lamarin na Hauwa, gaskiya akwai abin da bai kwanta min a rai ba.”

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol