Free chapter · Read without an account

The Calm Before the Storm

by NorthernAngel · His Rose

Yau sati biyu kenan da tafiyar Yemma, and the estate had never been this peaceful. Two days ago, Amirah da Imaan suka wuce makaranta, Johns Hopkins. Of course, Imaan tayi kuka sosai cewa ba za tafi ba tunda Yemma ba ta nan, amma babu wanda ya bi ta kanta sai Noor da take tayata roƙon Baffa. Shi kuwa Baffa yana sane ya matso da tafiyar tasu saboda ta damesa da koke-koke—har zazzaɓi tayi a satin da Yemma ta tafi—dan haka kawai yayi deciding to send her off early, wanting to completely distance her from her mother’s endless toxicity saboda clearly yana affecting ɗinta. Noor kuwa da ma tun satin tafiyar Yemma ya taka mata birki akan kar ta ƙara zuwan masa da zancen Yemma ko ta zo tana masa kuka; Imaan ma don yarinya ce shi yasa yake lallashinta. Bangaren Zara da Zafar kuwa, lafiya lau kake jinsu. Last weekend ɗinsu ma a beach house ɗinsu suka yi spending ɗinsa, daga su sai su enjoying their own private sanctuary. Zara haka ta sa dangana a ranta game da zuwa engagement party ɗin Brother Obi, wanda ya cika ko’ina a social media kasancewar an elite, high-society party ne ba na wasa ba. cikin wanda suka halarta har da Roman, wanda yanzu ya warke sosai sai ɗan abun da ba a rasa ba game da yanda yake motsa hannun sa. A halin yanzu yana Warri a gidan Daddy Ikenna yake zaune; Vicky ce ta kaisa ta yi introducing ɗinsa a matsayin close friend ɗin Zara sanda take Toronto, har da ƙarin gishiri a kan irin gudunmawar da ya bayar when she was struggling with her mental health. Daddy kuwa, jin haka da kuma ganin yadda gaba ɗaya yaransa—tun daga Vicky, Brother Obi, Sam, har ma da surukarsa Cindy—duk sun saba da shi kuma suna sonsa, tuni ya karɓe shi ya yi welcoming ɗinsa cikin gidansa with open arms. Duk suka sa ya sake sosai, making him feel completely at home. Har Daddy ke gaya masa cewa he’s welcome to stay as long as he likes, kuma shi da kansa zai sa lauyoyinsa su kammala masa long-term residency papers dinsa ba tare da wata matsala ba. Roman sosai ya yi fatan ganin Zara a party ɗinnan, amma ta ce masa ba za ta samu damar zuwa ba. Sosai wannan rayuwar tata ta seclusion and very private take bata mamaki, amma mafi mamakin ma shi ne yadda everyone is cool with it, har iyayenta kamar ba wani abu bane suke nunawa. Shi dai kullum burinsa ya ganta, ya faɗa mata duk abubuwan da suka faru so she truly knows who she's married to. Zara kuwa, tuni ita kam ta cire komai a ranta dangane da event ɗin da bai barta ta je ba, ta ci gaba da sha’aninta tana rayuwarta cikin tsantsar kwanciyar hankali da mijinta da yarta. Har lokacin ba ta san komai game da tafiyar Yemma ba, sai dai kawai wani ɗan zato da take yi sakamakon maganar da ta ji Noor ta faɗa a ranar; tunda ta ga Zafar bai ce mata komai ba, sai ita ma ta yi choosing ta ƙi yi masa maganar tun da ba damuwar ta bace. A ɓangaren Rahama ma, nothing had changed. Tun tafiyar Yemma sau ɗaya ta samu ganin Zafar a office ɗinsa—shima da kyar, da roƙo, da tura masa explicit nudes masu dagula lissafi kafin daga bisani ya ba ta wani ɗan gajeren reply yana cewa ta zo. A ɓangaren Noor da Omar kuwa, sai dai a ce Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Domin kuwa a yanzu, babu abin da Omar ke fuskanta sai koke-koke, maganganu marasa daɗi daga wurin Noor game da tafiyar Yemma. Duk wani bacin rai da fushin da take ji a kan Zafar, a kan Omar take sauke shi—duk da cewa ba directly ba, saboda tana shakkar Omar ɗin kuma tasan halinsa sarai. Sai dai tayi ta zuba maganganun habaici indirectly, tana cewa Allah ya sakawa mahaifiyarta, wai a ce babu babba a gidan, kowa yana gani amma babu wanda zai iya yin “the right thing.” Tuni Omar ya gane cewa abin da take nufi da “right thing” shi ne Zafar ya saki Zara. Amma ko a jikinsa; bai taɓa kulata ko biye mata ba. Shi dai yasan ko a yau auren Zara da Zafar zai zo ƙarshe, hamdala ma zai yi. Kawai dai wannan maganar ba huruminsu bane shi da Muazzam, kuma yana da yaƙinin cewa Zara tana tafiyar da komai lafiya lau—saboda kusan kullum yana shiga gidan kuma yana samunta cikin tsantsar farin ciki da kwanciyar hankali. Mostly, idan Zafar na office, ita kaɗai za ka tarar tana yi wa kanta pampering sessions: inma tana sama hammam ɗinta dan spa, ko ka tarar tana saka hair mask, shafa abubuwa a fuska, ko ana mata massage. Wani lokacin kuma za ka same ta a garden tana shuke-shuken flowers, ko tana zaune ita da yarta suna wasa cikin nishaɗi. Idan kuma Sam na gida ne, to tare za ka gansu suna kallon crime shows, buga PS, ko suna playing chess. In kuma lokacin da Zafar ke gida ne, to a lokacin bratty side ɗinta ke tashi, za ka same su tare suna ta hira tana zuba mai shagwaba cikin tsantsar soyayya. Ga kuma koyon girki da ta ɗaukar wa kanta da yi a yanzu; Sometimes za ka same ta ita kaɗai a kitchen ɗinta tana amfani da wani makeken interactive smart cooking display  da aka yi mounting domin ta, tana yin girkin as AI walks her through the recipes step-by-step har ta gama. Idan ta gama kuma tana saka mutanen gidan su ci su faɗa mata ko ya yi daɗi, sometimes har inviting ɗinsu Muazzam ɗin take suyci dinner ɗin da ta girka a gidan ta. Kallo ɗaya dai za ka mata kasan rayuwa na mata daɗi, tana cikin tsantsar kwanciyar hankali. Wannan shi yasa Omar sam baya bi ta kan Noor, domin yasan ƙanwarsa tana cikin ƙoshin lafiya da jin daɗin rayuwa. Amma shi kansa, zuciyarsa cike take da tsantsar nadama da ɗaci—nadamar auren Noor da ya yi. He should have known better. Noor will forever be her mother’s puppet; har abada ba a canzawa tuwo suna. Kamar mafarki, tun aurensu duk wasu halaye nata ke fitowa fili. Sai yanzu ya ƙara tabbatarwa cewa some things are better left as fantasies, because the moment you try to make them come true, that’s when you realize all that glitters is not gold. He had loved Noor—ya kwallafa ransa a kanta tun yana teenager. Yayi making up mind ɗinsa that she was the one he was going to marry when he was just eighteen, but he realized now that it was all just a childish fantasy. Bayan su girma kuma da suka fara dating, feelings ɗinsa had only prolonged because of their history——that deep, bittersweet thrill of holding onto something forbidden was what kept the spark alive for so long. Wannan underlying guilt, pity, da the self-blame—shine abun da yayi anchoring emotions ɗinsa. Bayan ya rasata kuma he was devastated, he kept chasing that high of wanting someone who was clearly no longer his. But then what? The moment ta zama tashi kuma, sai ya fara ganin komai through a completely different lens. Wannan thrill ɗin ya tafi saboda yanzu, everything was halal. The danger, the risk, the taboo—the very things that fed the fire—were gone. Yanzu, babu abun da ya rage sai raw reality, sai gaskiya, da kuma ɗacinta. Tabbas yana son Noor—he cared about her, but he was definitely no longer in love with her. Yayi moving on tun tuni; all he really needed was closure, kuma auren su ultimately gave him that closure. Yana son ta har yau, amma not enough to be blind to her ugly traits, her self-entitlement, and her selfishness—just like her mother. Su zasu iya treating kowa yanda suke so, amma the moment someone gave them a taste of their own medicine, immediately abun ya zama disrespect, ya zama hatred. Su as long as sun samu abun da suke so, toh basu damu whose feelings got hurt ko kuma whose mental health got ruined in the process ba. A gurinsu, their mother was their god. Yemma entity ce da kowanne ɗan adam is expected to bow down to, no matter how terribly she treated people. Yemma could get away with absolutely everything simply because, a idonsu, ita  wata untouchable figure ce who stood above everyone else in the world. In tayi walking all over you, you were expected to just take it. Baza ma kayi complain ba—no, you could not complain about Yemma simply because Yemma ce ita. Amma the moment ta taka ka, and you took a stand to protect yourself? Suddenly you lacked home training, you were toxic, and you were being utterly disrespectful to her, anan ne kuma zaka ga fushin yayan ta kuma dole a ɗau mataki. Idan akwai abu guda ɗaya da ya fahimta, shine jarabawar Yemma ta farko ba shi da Noor bane. Domin har gobe Yemma na ci gaba da juya kan Noor yadda ta so, she holds an absolute, unshakeable psychological grip over her, kuma har abada Yemma wata ubangiji ce a idon Noor. And the most frustrating part? Ita tsab take tsallake maganar Yemman tayi abun da ranta keso amma idan wani yayi hakan she loses her mind and gets furious, ko da kuwa shima ɗan yemman ne, wato yayanta Zafar. That supreme hypocrisy and double standard is what makes Noor so sickeningly selfish. Ta nan za ka gane cewa cikin ’ya’yan Yemma, babu wanda ya yo halinta irin Noor ɗin—she is her mother’s absolute carbon copy, down to the last toxic trait. So, babban jarabawar Yemma auren Zafar da Zara ne; the ultimate battlefield where her manipulative grip finally met its match. Till this day, Zafar always views Yemma the same as how Noor sees her. Yes, shi can get away with everything,  amma fa bacin ita, akwai wadda idan tayi mata abu ita ma she can get away with it, wato Zara! Yadda Yemma za ta yi wa Zara abu ta ci bulus, haka Zara zata yi mata taci bulus; and he prayed his sister will never find out about this. Because the moment Zara tasan hakan, she wouldn't hold back or cut Yemma any slack at all—so gwara dai hakan da take ɗaga mata ƙafa saboda Zafar, tana hakuri da abubuwan da take mata da zagin iyayen ta da take duk dan ta zauna lqfiya da mijinta. Wannan abun da Noor take, to him it's justified saboda Yemma duk abunta mahaifiyar ta ce—he could almost forgive her fierce, blind loyalty to the woman who birthed her. Amma son kanta na cewa kawai Zafar ya saki Zara shi ke sa tana ƙara fita ransa, crossin that ugly, unforgivable line. Ba wai dan Zara ƙanwarsa bace kawai a’a; it went far beyond family ties. Kawai son kan Noor ɗinne ke masifar rage mata quality a idonsa, stripping away whatever little respect he had left for her. How can a woman be so selfish? How can a woman want to destroy another woman’s happiness just so she could be happy? Allah ya sani, dalili ɗaya ne zai sa sakin Noor will never be an option—shine Baffa. He simply couldn't put that kind of heavy, heart-wrenching burden on the old man, not when Baffa had carried enough weight of his own. Zai ci gaba da haƙuri da halayen nata da ke cigaba da fitowa fili, kamar yadda Baffa ke haƙuri da halayen mahaifiyarta—trapped in the exact same quiet, enduring cycle. Kaddaran su kenan... A ɓangaren Zara da Zafar kuwa, bayan kwana biyar da tafiyar su Imaan school, Baffa ya tafi Umrah—saboda da farko akwai abin da ya tsayar da shi, da tuni ya riga ya tafi. Washe gari bayan tafiyar Baffa, Zafar ya tusa Zara gaba suka yi Dubai tare da shi, Muazzam, da Amrah. Ba ƙaramin gwagwarmaya ya sha da ita ba, domin fir ta ce ba za ta je ba. Wannan ya ba shi mamaki sosai, tunda a baya ita da bakinta ta ce tana missing ƙasar, amma da lokacin tafiya ya yi sai ta ce ba za ta ba, har da cewa sai dai ya fara tafiya ita ta biyo bayansa. Yayi tunani da nazari iri-iri yana son gano dalilin da ya sa take son ya tafi ya barta a gida, amma ya kasa gane kan abin. Abin da kawai zuciyarsa ta ba shi a matsayin amsa shi ne so take taci ƙafar kare yana tafiya. Dan haka without a second thought, ya sa ta gaba ba da son ranta ba, suka wuce Dubai su huɗu. Dalilin ma da yasa bazai iya barin ta ba saboda zasu kwana biyu acan, kar kuma Yemma ta dawo baya nan sai Zaran ita kadai. Zara kuwa, ba ƙaramin ɓata mata rai ya yi ba, domin hakan ya raba ta da plan ɗinta na maganin Rahama; tana ta faman faɗa da fushi yayin da suka nufi can din. Sun yi sati biyu a can, amma ta matsa lamba cewa sai dai su dawo gida. Lokacin da ta ji Baffa yana waya da Zafar cewa zai wuce Algeria in two days, hankalinta ya tashi matuka, ta dage cewa lallai sai ta koma gida. Zuwa lokacin, adjusted age ɗin Jasmine ta cika watanni uku cib-cib. Haka Zafar ya saka su a jirgi suka dawo gida ita da yarta. Nan fa, washe garin dawowar ta, ta fara shirye-shiryen abin da za ta yi domin fidda Rahama a gidan gaba ɗaya—yayinda ita ma Rahamar a nata ɓangaren, suke can suna shirye-shiryen nasu dabarun tare da mahaifiyarta...

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol