Free chapter · Read without an account

SIX DAYS OF SILENCE

by Jiddaah Barkum · ZAYD ARMAAN

ZAYD ARMAAN

CHAPTER 115

SIX DAYS OF SILENCE

JIDDAAH BARKUM

———

Raihana ta ji wani irin faɗuwar gaba, ta rasa gane kan waɗannan abubuwa da suke faruwa da ita, how on earth? Ta yaya za a ce wannan ita ce uwar kishiyarta, amma tana nuna mata irin wannan kulawa? Ta yaya za ta zama mai kirki haka ba tare da ta nuna mata ƙiyayya ko wani irin bambanci ba? A tunaninta, ya kamata ta ji wani irin tsoron kusantar Hajiya Hauwa, musamman saboda alaƙar da ke tsakaninta da Seeyama, amma abin da take gani a yanzu ya sa ta kasa fahimtar komai, this is different, ta san akwai mutanen da suke da kirki, amma wannan kulawar ta Hajiya Hauwa ta zo mata ne a lokacin da ba ta zata ba, yes is normal ace halin ta ba daya da na yar’ta ba but wnn abun ya kai ayi questioning, a hankali ta ɗago kanta, ta ɗan canja yanayin fuskarta, ba wai ta hade rai bane amma kuma ba murmushi ko daya a fuskarta, “Zan dafaa da kaina yanzu,” ta fada a hankali, Hajiya Hauwa ta ɗan ji jikinta ya saki ganin yadda fuskar Raihana ta canja, “Good girl,” ta faɗa cikin murmushi, tana shirin ƙara yin magana, amma kafin ta buɗe baki, sai idanunta suka sauka a kan Zayd wanda ya fara takowa cikin parlour ɗin a hankali, yana tafiya ne cikin nutsuwarsa, hannu ɗaya a cikin aljihun wandonsa, fuskarsa babu alamar murmushi, idanunsa kuwa suna kallonsu kai tsaye, baya ko kiftawa, Hajiya Hauwa ta ɗan yi shiru na daƙiƙa kaamr batayi tsammanin ganin sa ba, amma kasancewarta gogaggiyar maace sai kawai ta yi dariya a hankali, tana janye hannunta daga kafaɗar Raihana, “Ai gwara da ka shigo, son,” Zayd ya ci gaba da takowa, bai ce komai ba, Hajiya Hauwa ta gyara tsayuwarta, sannan ta ci gaba da magana cikin yanayin na mai damuwa da abin da ke faruwa, “Dole sai ka saka ido a kan Raihana, zama take ba ta breakfast da wuri, kuma ai karin safe shi ne abinci, idan ba sa ido ka yi ba, gaskiya akwai damuwa,” ta ɗan juya ta kalli Raihana, wadda ta sunkuyar da kanta tana wasa da gefen hijab ɗinta, “Don na fahimci kamar abinci bai dame ta ba, kuma mu dai a san ba ahalin yunwa ba ne, wannan ai sai danginta su ga ta canja, a ɗauka wani abu ake mata ta qare haka” Zayd bai ce komai ba, ya ƙaraso ya zauna, still staring at them both with his usual unreadable expression, ganin haka, Hajiya Hauwa ma ta zauna, ta fuskance shi, Zayd ya fara gaisheta, fuskarsa har yanzu a tsare, ganin sun fara gaishe-gaishe, sai Raihana ta yi maza, ta sulale ta bar su a wajen, ta shige kitchen, ba don za ta ci wani abu ba, sai dai kawai ta kauce wa zaman falon da take ganin a yanzu kasancewarta a ciki ya zama kamar wata lalura, especially with Zayd sitting right there, staring at them without saying much, ta shiga kitchen ɗin, ta jingina da counter, tana sauke ajiyar zuciya.

Ba ta ma san dalilin da ya sa kasancewarsa a wajen yake sa ta kasa zama cikin nutsuwa ba, abin da ta sani kawai shi ne, ba ta son ta zauna a falon tana jin kamar duk wani motsinta yana ƙarƙashin idanunsa, bayan wucewarta, Hajiya Hauwa ta miƙe tsaye tana ɗaukar jakarta, sai ta juya ta dubi Sadiya, wadda take tsaye a gefe, ta rabe kamar munafuka, tana riƙe da ledar kayanta, “Gata nan, na kawo ta, ita ce mai taimakon Raihana, dama da muka yi magana, na yi muku alƙawari, so here she is,” sai ta juya gaba ɗaya ta fuskanci Sadiya, tana ɗan ɗaga gira, “Ke, ba ki iya gaisuwa ba ne? Sai faman raba idanuwa kike a wajen?” Sadiya ta firgita kaɗan, ta matso da sauri, “Ina kwana,” ta faɗa, tana zubawa Zayd ido, shi kuwa bai ko kalleta ba, kawai ya amsa cikin sanyin murya, “Lafiya,” sai ya mayar da kallonsa kan Hajiya Hauwa, ya zuba mata idanunsa, kafin ya yi magana cikin nutsuwa, “I think she doesn’t need the maid now,” Hajiya Hauwa ta zaro ido, tana kallonsa kamar ba ta tabbatar da abin da kunnuwanta suka ji ba, “Eh? Me ya sa za ka ce ba ta buƙatar yarinya, kuma yanzu?” Zayd bai nuna wata damuwa da mamakinta ba, ya ɗan jingina da kujerar, sannan ya yi bayani cikin nutsuwarsa, “Za ta koma school ne, kuma yini take yi a can, so kinga, zai zama of no value ace ta bar yarinya a gida ita kuma ba ta nan, zamanta a gidan zai zama sai da dare, so, the girl won’t feel comfortable staying here alone all day,” Hajiya Hauwa ta zuba masa ido, ba ta ko kiftawa, tana sauraron bayaninsa, bayan ɗan lokaci sai ta sauke ajiyar zuciya, “Ai sai nake ganin haka ma ya fi, tunda idan ta dawo gıdan dai, aƙalla ta samu wanda za ta dinga zama da ita a gidan musamman idan ka tafi sabgogin ka kuma kafa dai ba ita kadai bace wasu lokutan kuma baka wajenta kafa bazata zauna cikin loneliness ba, kuma gashi idan ta dawo school a gajiye yaushe za ta fara house chores a yanayın stress din school, ga kula da miji, ga hidimar karatu? Abin zai mata yawa,” ta girgiza kai a hankali, kamar yanzu take sake tunanin yadda rayuwar Raihana za ta kasance idan ta koma makaranta, “Besides, ba wai an kawo Sadiya ne don a ƙara mata nauyi ba, an kawo ta ne don ta taimaka mata,” Zayd ya saurare ta cikin shiru, fuskarsa har yanzu a tsare, Hajiya Hauwa ta ɗan karkata kanta, tana kallonsa da murmushi, “Ka ga dai, son, sometimes mutum yana tunanin abu daga gefe ɗaya ne kawai, amma idan ka duba ta wani angle, sai ka ga akwai amfani a ciki,” Zayd bai yi saurin amsawa ba, ya ɗan mayar da kansa gefe, yana kallon hanyar kitchen ɗin da Raihana ta bi, sai ya sake mayar da kallonsa kan Hajiya Hauwa, “We’ll see, Mommy,” ya faɗa a taƙaice, cikin calm voice ɗinsa, ba tare da ya ƙara wani bayani ba, Hajiya Hauwa ta yi murmushi kawai, tana ganin kamar aƙalla sun fahimci juna, sai Hajiya Hauwa ta ɗora da sauri, kamar ta tuna wani abu, “Kuma idan kana tunanin kada a bar Sadiya ita kaɗai ne idan Raihana ta tafi makaranta, sai ta riƙa zuwa wajen Seeyama ta zauna da Rabi har Raihana ta dawo, ba shi ke nan ba? Ai wannan shi ne amfanin mata biyun su riƙa taimaka wa juna,” Zayd ya yi shiru, yana sauraron ta, bai ce komai ba, sai kawai ya jinjina kansa a hankali, “It’s fine, Mommy,” “Good!” ta faɗa, tana washe baki cike da gamsuwa, “Let me take my leave, and don’t forget to keep watching over Raihana, ka riƙa tabbatar da cewa tana cin abinci, please, okay?” “Okay,” ya amsa a taƙaice, Hajiya Hauwa ta yi murmushi, sannan ta yi masa sallama kafin ta juya ta nufi ƙofa, Zayd ya bi ta da kallo har ta fita, sannan idanunsa suka tsaya kan ƙofar na ɗan lokaci bayan ta rufe, sai ya sauke ajiyar zuciya a hankali, ya mayar da kansa gefe, yana tunanin wani abu da bai bayyana a fuskarsa ba, ba tare da ya kalli inda yarinyar take ba, ya miƙe tsaye, kai tsaye ya nufi kitchen ɗin, a hankali ya tura ƙofar, Raihana, wadda take jingine da kitchen island, ta firgita, da sauri ta juyo, idanunta suka sauka a kansa, nan take idanunsu suka haɗu, da sauri ta janye nata, ta fara wasa da fingers ɗinta, zuciyarta kuwa ta fara bugawa da wani irin sauri, kamar tana son tserewa daga ƙirjinta, Zayd ya zuba mata ido, yana kare mata kallo kamar mai binciken halittar jikinta, fuskarsa a tsare take, babu alamar abin da yake tunani, Raihana kuwa, tana jin nauyin idanunsa a kanta, ta rasa abin da ya kamata ta yi, ta kasa ɗago kanta ta kalle shi, sai ta ci gaba da wasa da yatsunta, tana ƙoƙarin ɓoye tashin hankalin da take ji, bayan ɗan lokaci, sai ya bude baki sannan ya yi magana a hankali, “Ga yarinyar nan a falo, ki je ki ba ta wajen zama,” Raihana ta dan kalleshi nan idanunsu suka hadu ta janye nata da sauri tana jinjina masa kai alamar taji abinda yace, Zayd bai ce komai ba, ya ci gaba da kallonta na wasu daƙiƙu, sannan ya juya ya fice abinsa, kai tsaye zuwa masallacin da ya fito da niyyar zuwa tun farko, Raihana ta tsaya cak, that’s it? Ta ɗauka ko ya zo ne don ya ga ko tana cin abinci, ko kuma zai tambaye ta dalilin da ya sa har yanzu take zaune ba tare da ta karya ba, amma babu ko ɗaya daga cikin waɗannan, kawai ya gaya mata ta ba yarinyar wajen zama, sannan ya fita, ta yi jimmmm, tana kallon ƙofar da ya bi, a hankali ta sauke hannayenta, amma ƙafafunta sun riga sun sake yin sanyi, ta lumshe idanunta, tana ƙoƙarin danne wani irin yanayi da ya fara cunkushe mata zuciya, why does it hurt this much? Ba ta san abin da take tsammani daga gare shi ba, amma ta san cewa wannan ɗan lokacin da ya tsaya yana kallonta ya sa ta yi tunanin wataƙila ya zo ne saboda ita, wataƙila ya lura ba ta ci komai ba, wataƙila zai tambaye ta ko tana lafiya, amma a ƙarshe, sai ta gane cewa ta sake sa ran wani abu daga gare shi, alhali shi bai ma nuna mata cewa yana tunanin hakan ba, ta buɗe idanunta a hankali, tana kallon inda yake tsaye a lokacin da ya shigo, zuciyarta ta cunkushe da wani irin yanayi mara daɗin ambato, ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta jingina da kitchen island ɗin sosai, tana ƙoƙarin kwantar da hankalinta, haka aka ci gaba da kwana, har kwanaki shida suka shuɗe, kwanakin Seeyama ma sun ƙare, amma har zuwa wannan lokacin, ba ta samu abin da take so daga Zayd ba, duk wani yunƙurinta na neman kusantarsa ya zama kamar bata lokaci ne kawai, domin Zayd ya ci gaba da zama cikin irin halinsa na rashin nuna damuwa da ita, baya ce mata ci kanki iyakacinsa da ita duuk asubar duniya zaiyi mata knocking assalah shikenan sai wata asubar, tun bayan abin da ya faru a daren nan, Seeyama ta fara jin wani irin shakku a duk lokacin da ta ga Zayd, ba ta sake samun ƙarfin halin yin abin da take so a gabansa kamar da ba, ko da yana zaune a falo idan tazo ta zauna amma baya kallon inda take abinda ne gabansa kawai yakeyi sai ta ji jikinta ya ɗan yi sanyi, tana tunanin ko ya gano wani abu game da abin da ta yi masa, Zayd kuwa, kamar ba ya son ya ba ta damar yin wata magana da shi, yana yin abin da ya ga dama, idan kuma ya yi magana da ita, sai ta kasance a taƙaice, bai sake nuna mata irin kusancin da ta saba gani a baya ba, wannan shi ne abin da ya fi damun Seeyama, ta rasa yadda za ta fassara shirunsa, wani lokacin tana ganin kamar ya san abin da ta yi, wani lokacin kuma sai ta ji kamar yana ƙoƙarin kauce mata ne kawai, amma duk da tsoron da take ji, har yanzu ba ta daina kai wa Safina kukanta ba, kusan kullum sai ta nemi Safina ta ba ta labarin abin da ke faruwa a gidan, tana ƙara nuna mata yadda Zayd ya canja mata, amma Safina ma ta fara gajiya da wannan batu, ta sha gaya mata su koma wajen mutumin nn, ta bi abin da ya ce, amma Seeyama ta ƙi amincewa da sharadin da aka ɗora mata, yanzu kuma tana so Safina ta ci gaba da nemo mata wata mafita, Safina kuwa ba ta sake ɓoye mata haushinta ba, ta faɗa mata cewa tun farko ta ba ta shawara, amma ta ƙi saurara, kuma ba ita ce ta jawo mata wannan matsalar ba, duk da haka, Seeyama tana nn akan bakar ta, a wajenta, babu abin da zai sa ta bayar da kanta ga wani mutum, ba za ta taɓa yarda da wannan sharadin ba, kuma ta dage cewa idan ba Zayd ba, to babu wani namiji da zai taɓa samun wannan damar a wurinta, Safina ta gaji da maimaita magana iri ɗaya, a ƙarshe, sai ta faɗa mata kai tsaye cewa kada ta sake kiranta da matsalolin da ta ƙi bin shawarar da aka ba ta a kansu, Seeyama ta ji haushi sosai, amma ba ta da wani zaɓi illa ta yi shiru, duk da haka, zuciyarta ba ta samu nutsuwa ba, domin har yanzu tana son samun abin da take nema daga Zayd, amma ba ta san yadda za ta yi ba, ita ma dai Raihana, hakan take haka rayuwarta ta kasance a cikin waɗannan kwanaki shida, da asuba, Zayd ne yake zuwa ya tashe ta domin sallah, wani lokaci yana ƙwanƙwasa ƙofar ne kawai, wani lokacin kuma idan ya ga ta yi jinkiri, sai ya kira sunanta a taƙaice kafin ya wuce, bayan nan, ba ya sake bi ta kanta, ko da sun haɗu a cikin gida, Zayd ba ya ce mata kala idan ta gaishe shi zaice lafiya shikenan sannan ya ci gaba da harkokinsa, babu tambayar ko ta ci abinci, babu tambayar ko tana lafiya, balle ya tsaya ya kula da yanayinta kamar yadda ta yi tsammani zai yi, da dare kuwa, wani lokacin yana zuwa ya duba ta, amma ba ya shiga ɗakinta, yakan tsaya ne a ƙofar, ya tabbatar da cewa ta rufe ƙofar, komai yana kashe, sannan ya juya ya tafi, idan ya ga hasken ɗakinta a kashe, sai ya ɗauka ta riga ta yi barci, wani lokacin ma, Raihana tana jin takun sawunsa a wajen ƙofar, takan buɗe idanunta a hankali, ta saurari motsinsa, amma ba za ta motsa ba, idan kuma taji kaamr zai shigo sai ta yi pretending kamar tana barci, tana jiran ya wuce, wani ɓangare na zuciyarta yana son ya shigo, ko da kuwa zai tsaya na minti ɗaya ne kawai, ta so ya tambaye ta ko tana lafiya, ko ya ce mata wani abu da zai nuna cewa har yanzu yana damuwa da ita, amma duk lokacin da ta ji takun sawunsa yana nisa, sai ta buɗe idanunta a hankali, tana kallon duhun ɗakin, so, that’s all? Ta tambayi kanta, amma ba ta da amsa, a hankali sai ta juya ta kwanta da kyau, tana ƙoƙarin danne tunanin da ya addabe ta, iyakacin abin da ke haɗa su a waɗannan kwanakin shi ne tashe ta sallar asuba da kuma waɗannan ziyara na dare da yake yi ba tare da ya shiga ba, komai ya canja, Zayd ya tattara duk wani abu da ke tsakaninsa da matan sa biyu, ya mayar da shi kamar ba komai ba ne, ya rufe kansa a cikin shirunsa, ya bar su su na ta kokarin fahimtar abin da ya faru tsakaninsu, ita kuma raihana duk da cewa ba ta son ta yarda, ta fara jin zafin wannan nisan nasa fiye da yadda ta zata, amma ba ta san yadda za ta gyara abin da ya lalace ba, kuma mafi muni shi ne, ba ta san ko Zayd ma yana son a gyara shi ba.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol