Free chapter · Read without an account
THE UNEXPECTED INVITATION
ZAYD ARMAAN
CHAPTER 116
THE UNEXPECTED INVITATION
JIDDAAH BARKUM
———-
A yammacin da zai bar part din seeyama, Zayd yana zaune a falon part ɗin,sanye yaje da white shirt sai jogger trouser laptop ɗinsa a buɗe a kan cinyarsa, wasu takardu kuma a warwatse a kan ƙaramin teburin gabansa, idanunsa suna bin rubuce-rubucen da ke kan screen ɗin, hannunsa yana aiki a hankali, lokaci-lokaci yana ɗaukar wata takarda ya duba abin da ke ciki kafin ya mayar da ita gefe, fuskarsa a tsare take kamar yadda ta saba, hankalinsa kuwa ya karkata ne gaba ɗaya kan aikin da yake yi, daga ɗakinta, Seeyama ta fito sanye da wata doguwar maroon Yasmeen abaya wadda ta yi mata kyau sosai, kasancewarta doguwa ya ƙara fito da kyawun rigar, yayin da ta ɗaura dankwalin abayar a kanta cikin tsari, wayarta tana hannunta ɗaya, ɗayan hannunta kuma yana riƙe da gefen rigarta yayin da take takowa a hankali zuwa inda Zayd yake, ta tsaya a gefen kujerar da yake zaune, tana kallonsa na wasu daƙiƙu, Zayd ya ji motsin zuwanta, amma bai nuna ko alamar ya lura da ita ba, ya ci gaba da kallon laptop ɗinsa kamar babu wanda yake tsaye a gabansa, Seeyama ta haɗiye yawu a hankali, ta runtse idanunta na ɗan lokaci, tana tattara ƙarfin halin da take buƙata kafin ta buɗe bakinta, “Babe…” Ta kira shi cikin sanyin murya, Zayd ya ɗago kansa ya kalleta, fuskarsa babu wani canji, bai amsa kiran ba, bai kuma tambaye ta abin da take so ba, kawai ya tsaya yana kallonta, kamar yana jiran ta faɗi abin da ya kawo ta, Seeyama ta saki gefen rigarta da take riƙe da shi, ta ɗan matsar da wayarta a hannunta, sannan ta yi magana a hankali, “Don Allah, ka yi haƙuri, ka ba ni dama in yi magana da kai, just ten minutes, please,” Zayd bai ce komai ba, shirun nasa ya sa ta ƙara jin tashin hankali a zuciyarta, ta ɗan matso kaɗan, tana ƙoƙarin ganin ko za ta iya samun wata alama daga fuskarsa, amma abin da ta gani bai ba ta wani tabbaci ba, “Please,” ta sake faɗa, wannan karon muryarta ta ɗan yi rauni, “I just want to talk to you, ba zan ɗauke maka lokaci mai yawa ba, wallahi,” Zayd ya mayar da idanunsa kan laptop ɗinsa, ya danna wasu abubuwa kafin ya yi magana cikin sanyin muryarsa, “I’m listening,” Seeyama ta yi shiru na ɗan lokaci, domin ba haka take tsammanin zai amsa mata ba, ta ɗauka wataƙila zai kore ta ko kuma ya gaya mata ba shi da lokaci, amma yanzu da ya ce yana sauraron ta, sai ta rasa ta inda za ta fara, ta ɗan gyara tsayuwarta, ta sauke numfashi a hankali, “Na san kana fushi da ni,” ta fara magana, tana kallon fuskarsa, “And I know things haven’t been the same between us lately, amma ka ba ni dama in yi maka bayani, please,” Zayd ya ɗago kansa a hankali, ya zuba mata idanunsa, “Bayani a kan me?” Tambayar ta fito cikin nutsuwa, amma akwai wani irin sanyi a cikinta da ya sa ta kasa amsawa nan take, ta lumshe idanunta na ɗan lokaci kafin ta sake buɗe su, “Game da yadda kake min, babe, ka daina magana da ni kamar yadda ka saba, ko da muna wuri ɗaya, sai na ji kamar ba ka ma san ina wurin ba, I don’t even know what I did to deserve this kind of treatment,” Zayd ya ɗan karkata kansa, yana kallonta ba tare da ya katse ta ba, Seeyama ta ɗan matsa hannunta a hannun kujerar, sannan ta ci gaba da magana cikin sanyin murya, “Na yi kewarka, wallahi na yi kewarka sosai, I miss talking to you, I miss the way things used to be between us,” ta tsaya, tana kallon fuskarsa, kamar tana jiran ya ce wani abu da zai rage mata nauyin da ke zuciyarta, amma Zayd bai yi magana ba, ya mayar da hankalinsa kan takardun da ke gabansa, ya ɗauki ɗaya daga cikinsu ya fara dubawa, kamar maganganunta ba su shafe shi ba, Seeyama ta ji wani abu ya tokare mata maƙogwaro, “Babe, are you even listening to me?” Zayd ya ɗago kansa a hankali, “Kin ce kina son yin magana da ni, na ba ki damar yin hakan, me kuma kike so in yi?” Ta buɗe bakinta, amma babu magana da ta fito nan take, a karo na farko cikin waɗannan kwanaki shida, ta fahimci cewa samun Zayd ya saurare ta ba yana nufin ta samu kusancinsa ba ne, yana zaune a gabanta, yana kallonta, amma zuciyarsa kamar tana wani wuri daban, ta sauke idanunta a hankali, “Nothing,” ta amsa cikin raunin murya, “I just want things to go back to normal,” Zayd ya kalleta na wasu daƙiƙu, sannan ya mayar da idanunsa kan laptop ɗinsa, “Things don’t always go back to the way they were,” ta ji kamar kalaman sun sauka a zuciyarta da wani irin nauyi, ta ɗan girgiza kanta, tana ƙoƙarin ɓoye yadda maganar ta taɓa ta, “But why? What changed?” Zayd ya yi shiru, a hankali ya rufe wani file da yake dubawa, sannan ya ɗago kansa ya kalleta kai tsaye, “Ke ya kamata ki san abin da ya canja,” Seeyama ta tsaya cak, zuciyarta ta buga da sauri, yayin da tunaninta ya koma kan daren da ta haɗa masa fura da nono, shin ya gano abin da ta yi ne? Ta haɗiye yawu, tana ƙoƙarin kada fuskarta ta nuna tsoron da ta ji, “Me kake nufi da haka, babe?” Zayd bai amsa tambayar ba, ya tsaya yana kallonta cikin nutsuwa, fuskarsa babu wata alama da za ta taimaka mata wajen fahimtar abin da yake tunani, sai ya mayar da laptop ɗin da ke kan cinyarsa kan teburin, ya tattara wasu takardu ya daidaita su, snn ya juyo gareta, “Seeyama, idan kin gama abin da za ki faɗa, ina da aiki da zan yi,” ta ji zuciyarta ta ƙara nauyi, ta zo ne da niyyar samun damar yin magana da shi, wataƙila ta fahimci dalilin da ya sa ya canja, amma duk da cewa tana tsaye a gabansa, har yanzu tana jin kamar tana magana ne da wani mutum da ba ta taɓa sani ba, ta kalli fuskarsa a hankali, “Babe, please… don’t shut me out like this,” Zayd ya ɗago kansa, idanunsa suka sauka a kanta, “Then give me a reason not to,” Seeyama ta kasa magana, a hankali ta janye hannunta daga gefen kujerar, ta matse wayarta a tafin hannunta, tana jin kamar duk kalaman da ta shirya faɗa masa sun ɓace daga kanta, Zayd kuwa ya mayar da hankalinsa kan aikinsa, kamar dai wannan tattaunawar ba ta da wani muhimmanci a gare shi.
Seeyama ta tsaya tana kallonsa, amma wannan karon ta kasa sake ɓoye abin da ke damunta, idanunta sun fara cika da hawaye, ta runtse su na ɗan lokaci kafin ta sake buɗe su, tana ƙoƙarin samun ƙarfin halin faɗin abin da ta daɗe tana gudun faɗa, “Na saka maganin ne a cikin nonon, babe…” Ta faɗa cikin sanyin murya, kalamanta suna fita ɗaya bayan ɗaya, Zayd ya ɗago kansa daga kan takardun da yake dubawa, fuskarsa ba ta canja ba, Seeyama ta haɗiye yawu, hawaye suka fara gangarowa daga idanunta, “Amma wallahi, ba da niyyar cutar da kai na yi ba, I didn’t mean to hurt you, ka yi haƙuri, please,” ya ci gaba da kallonta cikin shiru, ba tare da ya katse ta ba, “I am just obsessed with you,” ta faɗa, muryarta tana rawa, “Ka fahimce ni, wallahi, I love you so much, har wani lokacin ma ban san abin da nake yi ba, da na san cewa abin da na yi zai jawo maka irin wannan matsalar, wallahi da ban taɓa yi ba, ban san cewa abubuwa za su kai haka ba, babe, please, ka yi haƙuri,” ta share hawayenta da bayan hannunta, amma wasu suka sake zubowa, “Wallahi, ban so wani abu ya same ka ba, ni dai kawai ina son ka ne, ina son ka kusance ni, ka nuna min cewa kai ma kana sona, I just wanted to feel wanted by you,” Zayd ya ɗan sauke idanunsa kan laptop ɗinsa, sannan ya rufe shi a hankali ya ajiye shi gefe, ya gyara zamansa, ya ɗago kansa ya kalleta kai tsaye, “Seeyama…” Ya kira sunanta cikin sanyin murya, ta ɗago kanta da sauri, tana kallonsa cikin bege, kamar jiran kalamansa zai ba ta damar samun sassauci daga abin da ta aikata, ya nuna mata gefensa da hannunsa alamun ta zauna da sauri ta zauna tana share hawayenta Zayd ya ɗan yi shiru kafin ya ci gaba, “If you really need me, why won’t you just ask for it?” Seeyama ta tsaya tana kallonsa, hawaye na ci gaba da zuba daga idanunta, “Me ya sa za ki bi ta wata hanyar daban? Me ya sa za ki saka wani abu a cikin abin da zan sha ba tare da sanina ba?” Ya yi maganar cikin nutsuwa, babu ihu, babu ɗaga murya, amma yadda yake kallonta ya nuna cewa yana son ta fahimci abin da yake nufi, “Kin san cewa ban san abin da kika saka a cikin nonon ba, ban san irin maganin ba, ban san adadinsa ba, kuma ban san abin da zai iya yi wa jikina ba, kin taɓa tunanin abin da zai faru da ni idan abin ya yi min illa?” Seeyama ta girgiza kanta da sauri, “Babe, wallahi—” Ya ɗaga hannunsa kaɗan, ba don ya tsorata ta ba, sai don ya dakatar da ita a hankali, “Let me finish,” ta rufe bakinta, ta sunkuyar da kanta, hawaye na zuba a fuskarta, Zayd ya ci gaba da magana cikin sanyin muryarsa, “Idan kina son in kasance tare da ke, ki faɗa min, idan kina son mu yi magana, ki zo mu yi magana, idan kina jin cewa akwai abin da ya sabaa a tsakaninmu, ki gaya min, amma ba za ki tilasta min wani abu ta hanyar da ba ni da masaniya a kai ba, Seeyama,” ya ɗan tsaya, yana kallonta da idanunsa masu sanyi, “That’s not how you get someone to love you, and that’s not how you build trust,” Seeyama ta ɗaga kanta a hankali, tana kallonsa cikin wani irin nadama, “Ka yi haƙuri, please, na san na yi kuskure and I regret it…” Zayd ya sauke ajiyar zuciya a hankali, “Kin yi kuskure, Seeyama, kuma ba ƙaramin kuskure ba ne,” maganar ta sa ta sake fashewa da kuka, amma shi bai ɗaga murya ba, bai kuma yi wani yunƙurin ta’azantar da ita ba, ya tsaya ne kawai, yana kallonta cikin nutsuwa, “Ba wai don kin ce kina sona ba ne za ki iya yin duk abin da kika ga dama da lafiyata, my health is not something you can gamble with,” ta share hawayenta, tana ƙoƙarin yin magana duk da yadda muryarta ta raunana, “Wallahi, da na san abin da zai faru da kai, da ban yi ba…” Zayd ya kalleta na wasu daƙiƙu, “Abin da ya fi damuna shi ne, ba ki ba ni damar sanin abin da kike shirin yi ba, kin yanke shawara a madadina, game da jikina da lafiyata, kin fahimci yadda hakan yake?” Seeyama ta kasa ɗaga kanta, Zayd ya miƙe tsaye, ya ɗauki agogonsa da ke kan teburin ya saka a hannunsa, bayan ya daidaita hannun rigarsa, sai ya sake kallonta, “Ki daina tunanin cewa dole sai kin yi wani abu na daban kafin in saurare ki, if you have something to say to me, say it, idan kina son wani abu daga gare ni, ki faɗa, amma kar ki sake maimaita irin wannan abu,” “Ba zan sake ba, wallahi,” ta faɗa cikin kuka, “I promise you, babe,” Zayd bai yi saurin amsawa ba, ya tsaya yana kallonta, fuskarsa har yanzu a tsare, a ƙarshe, ya ɗauki laptop ɗinsa da takardunsa, yana shirin tafiya, ganin zai bar wajen, Seeyama tayi saurin tashi ta matso gabansa, “Babe, ka yafe min, don Allah,” ta faɗa cikin sanyin murya, hawayen da suka tsaya a idanunta suka sake zubowa, “Please, ka yafe min, I promise I won’t do it again,” Zayd ya tsaya yana kallonta, sannan ya ɗan gyara riƙon laptop ɗin da yake hannunsa, “Ki tabbatar ba za ki sake yin irin wannan kuskuren ba,” ya faɗa cikin nutsuwa, “I don’t want a repeat of this,” ta jinjina kanta da sauri, “Wallahi ba zan sake ba, babe, thank you, thank you so much,” kafin ya yi tsammanin abin da za ta yi, sai ta rungume shi da ƙarfi, ta matse jikinta a nasa kamar tana tsoron zai canja shawara ya ture ta, Zayd ya tsaya cak na ɗan lokaci, bai yi magana ba, “Thank you, babe, I love you so much,” ta faɗa tana murmushi cikin hawaye, “I’m at ease now, wallahi, yanzu na ji sauƙi a raina,” Zayd ya sauke ajiyar zuciya a hankali, sannan ya ɗaga hannunsa daya da ba komai ya shafa kanta a hankali, ba tare da ya ce komai ba, bayan wasu daƙiƙu, ya janye ta daga jikinsa, ya juya ya nufi hanyar fita, Seeyama ta tsaya tana kallonsa har ya fita daga falon, a hankali murmushi ya bayyana a fuskarta, ta share sauran hawayen da ke kan kumatunta, sannan ta ɗora hannunta a kan ƙirjinta, Ya Allah, me ya sa nake son shi haka? Ta tambayi kanta a zuciyarta, tana kallon hanyar da ya bi, even after everything, just one touch from him is enough to make me feel like nothing else matters, ta sauke ajiyar zuciya, tana jin wani irin farin ciki da ta daɗe ba ta ji ba, duk da cewa har yanzu akwai abubuwan da ba su daidaita a tsakaninsu ba, bayan ya fito daga masallacin Magrib, Zayd yana tsaye a ƙofar gida tare da Sameer, wanda ya zo domin su tattauna wasu abubuwa da suka shafi tafiyar da ta kama Zayd zuwa China, suna tsaye suna duba wasu bayanai ne a wayar Sameer, lokaci-lokaci Zayd yana yi masa ƙarin bayani game da shirye-shiryen tafiyar, a daidai lokacin ne wayar Zayd ta fara ringing, ya zaro wayar daga aljihunsa, ya duba screen ɗin kafin ya ɗaga, bayan sun gaisa na ɗan lokaci, sai Anty Mariya ta yi masa wata tambaya ba zato, “Yau a wajen wa kake, Zayd?” Zayd ya yi shiru na ɗan lokaci, bai gane ma’anar tambayar ba, a wajen wa nake? Kamar dai tambayar ba ta da wata ma’ana a gare shi, ya ɗan lumshe idanunsa, sannan ya amsa cikin sanyin muryarsa, “Ban gane ba, Anty,” Anty Mariya ta yi dariya daga can ɓangaren wayar, kafin ta sake magana, “Ina nufin, toh, ɗakin Raihana kake yau, ko na Seeyama?” Zayd ya ɗan dafe goshinsa da tafin hannunsa, ya sosa shi a hankali, sannan ya ɗan karkata kansa yana kallon Sameer ta gefen ido, Sameer kuwa ya ci gaba da duba wayarsa, bai nuna kamar yana sauraron tattaunawar ba, “Rayhaanaa,” Zayd ya amsa a taƙaice, “Yauwa!” Anty Mariya ta faɗa cikin jin daɗi, “Toh, ka ɗauko ta yanzu ku zo, ina son ganinku da kaina, da ni zan zo, amma wasu dalilai suka sa ban samu zuwa ba, don haka ka kawo min ita yanzu, before Isha, ina jiranku,” Zayd ya yi shiru na wasu daƙiƙu, yana nazarin abin da ta faɗa, ya san idan ya tambayi dalilin da ya sa take son ganin su, wataƙila ba zai samu amsar da yake nema ba, saboda haka kawai ya amsa cikin nutsuwa, “Okay,” “Allah ya kawo ku lafiya,” “Ameen,” bayan sun yi sallama, sai ya kashe wayar ya mayar da ita aljihunsa, ya tsaya na ɗan lokaci, idanunsa suna kallon wani wuri daban, me ya sa take son ganinsa da Raihana a wannan lokacin? Shin Raihana ce ta gaya wa Ummie wani abu, ita kuma ta kai wa Anty Mariya? Ko kuwa ta yi magana da Suhaila ne, ita kuma Suhaila ta je ta ba ta labarin? Ko akwai wani abu daban da yake faruwa wanda bai sani ba? Zayd ya ɗan matse laɓɓansa, gaskiya bai da amsar komai, ya ɗago kansa ya kalli Sameer, wanda yake jiran su ci gaba da tattaunawar da suka fara, “Sameer, za mu ci gaba da wannan gobe, ka tura min sauran details ɗin ta email,” “Okay, sir,” Zayd ya jinjina kansa a hankali, ya yi masa sallama sannan ya juya ya shiga cikin gidan, kai tsaye ya nufi ɓangaren Raihana, falon ba kowa ya lura da yadda komai yake cikin tsari, babu wani abu da ya warwatse, komai yana nan a inda ya kamata ya kasance, har ma da yanayin falon, akwai wani irin nutsuwa da yake tattare da shi, wani kamshi mai daɗi ya ratsa hancinsa, kamshin da yake da wani irin yanayi mai sanyaya zuciya a cikinsa, Zayd ya ɗan dakata, bai san dalilin da ya sa ya tsaya ba, amma idanunsa suka zagaya falon a hankali kafin ya mayar da su kan hanyar stairs, ya ci gaba da tafiyarsa, hannunsa ɗaya a cikin aljihun wandonsa, fuskarsa a tsare kamar yadda ta saba, sai dai a cikin zuciyarsa, tambayar Anty Mariya tana ci gaba da yawo, me take son ganinsu da shi da Raihana a kai? Zayd ya ƙarasa ƙofar ɗakin, ya tura ta a hankali sannan ya shiga, idanunsa suka sauka a kan Raihana wadda take zaune a kan sallayar da ta idar da Magrib a kai, Qur’ani a hannunta, tana karantawa cikin nutsuwa, idanunta suna bin ayoyin da take karantawa a hankali, jin an buɗe ƙofa ya sa gabanta faɗuwa, ta ɗago kanta da sauri, idanunta suka sauka a kansa, Zayd, ta riga ta san cewa shi ne, tun asuba, bayan ya yi mata knocking domin sallah, bai sake zuwa wajenta ba, yanzu kuma ga shi a gabanta, ta yi saurin mayar da idanunta kan Qur’anin da ke hannunta, zuciyarta tana bugawa a hankali, Zayd kuwa ya rufe ƙofar, ya ƙarasa cikin ɗakin ba tare da ya ce komai ba, ya nufi wajen mirror, ya ajiye wayarsa sannan ya cire agogon hannunsa, “Ina yini,” Raihana ta gaishe shi a hankali, muryarta ba ta wuce yadda za a ji ta ba, “Lafiya,” ya amsa sama-sama, har yanzu bai juyo ya kalleta sosai ba, ta yi shiru, tana jiran ko zai ƙara wani abu, amma sai ya juyo ya kalleta a taƙaice, “Ki shirya, za mu fita,” Raihana ta ɗago kanta, “Toh,” ta amsa a hankali, Zayd bai ƙara wani bayani ba, ya juya ya shiga toilet, ya bar ta zaune a kan sallayar tana kallon ƙofar da ya shiga, za mu fita? Where? Ta yi tambayar a zuciyarta, amma ba ta da wanda za ta tambaya, ya faɗa mata ne kawai ta shirya, kuma ta san idan ta fara yi masa tambayoyi da yawa, wataƙila amsarsa za ta kasance kamar yadda ta saba ji a waɗannan kwanakin, ba jimawa ya fito ya karasa wajen wardrobe dinsa ta shirya cikin haddadiyarrr shaddarsa brown da hula ya bulbulaaa turare ya fice ya bar mata kamshin saaa ta bi bayansa da kallo har ya fice ta ajiye Qur’anin a hankali, ta naɗe sallayar sannan ta tashi, da farko ta nufi toilet ɗin domin yin wanka da sabuwar alwala, sannan ta fito tana goge jikinta da tawul, ta dora hijab dinta snn ta wuce zuwa dakinta ta nufi wardrobe ɗinta, ta buɗe ƙofofin tana duban kayan da ke ciki, ta tsaya tana tunanin abin da za ta saka, ba ta san inda za su je ba, don haka ba ta san ko ya kamata ta saka abu mai sauƙi ko kuma ta ɗan yi kwalliya ba, ta ɗan ciro wata riga, ta sake mayar da ita, sannan ta koma kallon sauran kayan, a ƙarshe, idanunta suka tsaya kan wata atamfa mai launin dusty rose, mai kyau da tsari, wadda aka ɗinka mata cikin salo mai sauƙi amma na musamman, ta ciro ta, ta ajiye a kan gado sannan ta fara shiryawa, bayan ta gama saka kayan, ta tsaya tana kallon kanta a mirror, atamfar ta yi mata kyau sosai, ta fito da launin fatarta cikin yanayi mai daɗi, tayi daurin dankwali mai kyau, ta yi murmushi kaɗan tana kallon kanta, at least, I look good, sai kuma ta yi saurin haɗe fuska, kamar ta tuna wani abu, amma fa ban san inda za mu je ba, sai kuma tace bari ta saka sarka, sai ta zauna a gaban mirror ta fara zaɓar jewelry da za ta saka, ta zaɓi ƙananan ’yan kunne masu kyau, bracelet mai sauƙi da kuma zoben da ya dace da atamfar, ta saka su a hankali, tana ƙoƙarin kada ta yi abu da yawa, bayan ta gama, sai ta ɗauki babban mayafi mai launin cream, wanda ya dace da kayan, ta naɗe shi cikin tsari ta ɗauki ƙaramar jaka da takalminta masu launin nude, ta ɗan fesa turare kaɗan, sannan ta sake tsayawa a gaban mirror tana kallon kanta, ta gyara gefen mayafinta, ta ɗan karkatar da kanta gefe ɗaya, sannan ta sake kallon yadda kayan suka zauna a jikinta, gaskiya ta yi kyau, amma sai wata irin kunya ta ratsa ta, wallahi, kar dai ya ce na yi kwalliya ne saboda shi, ta turo baki kaɗan, tana kallon kanta cikin mirror, ai ba ta san inda za su je ba, ba ta san wanda za su gani ba, shi ne kawai ya ce ta shirya, kuma ta shirya ne saboda haka, bayan ta sake duba kanta a mirror a karo na ƙarshe, sai ta fito daga ɗakin, ta fara saukowa a hankali zuwa ƙasa, hannunta yana riƙe da gefen mayafinta, zuciyarta cike da tambayoyi, where are we going? Ta sake tambayar kanta, tana sauka daga mataki zuwa mataki, sai kuma tunaninta ya koma kan Zayd, ta sauke ajiyar zuciya, ta ɗan gyara mayafinta sannan ta ci gaba da saukowa, ba tare da sanin cewa duk waɗannan tambayoyin nata za su jira har sai sun isa inda za su je ba ta ganewa idanunta Raihana ta ƙarasa saukowa daga matakalar, tana riƙe da gefen mayafinta a hankali, da ta ɗago kanta, sai ta hangi Zayd zaune a kan kujera a falon, kafa daya kan daya wayarsa a kunnensa yana magana da wani a ɗaya ɓangaren, yana magana ne cikin nutsuwa, amma a daidai lokacin da Raihana ta sauko, idanunsa suka sauka a kanta, kuma suka tsaya, Zayd bai ɗauke idanunsa daga kanta ba, ko na second ɗaya, ya ci gaba da kallonta cikin nutsuwa, yana bin duk motsinta da idanunsa, fuskarsa har yanzu a tsare take, babu murmushi ko kaɗan, amma kallon da yake yi mata ya sa Raihana jin kamar an kama ta a wani irin yanayi da ba ta san yadda za ta fuskanta ba, ta ɗan dakata na daƙiƙa ɗaya, zuciyarta ta fara bugawa da sauri, ta yi saurin sauke idanunta, ta ci gaba da tafiya a hankali, tana ƙoƙarin yin kamar ba ta lura da yadda yake kallonta ba, amma gaskiya, ta lura, ta ji kallonsa a kanta har zuwa lokacin da ta ƙaraso ta tsaya a dan nesa da shi, Zayd kuwa bai ce komai ba, ya ci gaba da sauraron wanda yake magana da shi a waya, idanunsa suna bin Raihana kaamr zai cinyeta, “Alright, I’ll get back to you,” ya katse wayar, ya miƙe tsaye ya ɗauki makullin motarsa daga kan teburin, sannan ya nufi ƙofar fita, Raihana ta bi shi a baya ba tare da ta ce komai ba, a Dayan bangaren kuwa, Seeyama tana tsaye a gaban window ta dage curtains din tana kallon compound, wayarta a manne a kunnenta tana magana da Safina, ta katse maganar da take yi lokacin da idanunta suka hango Zayd yana fitowa daga cikin gidan, sai ta lura da Raihana da ke binsa a baya, ta ɗan lumshe idanunta, tana kallonsu, ina kuma za su je? Ta ci gaba da kallonsu yayin da Zayd ya nufi motarsa, bai tsaya ya yi magana da raihana ba, bai kuma waiwaya ya kalleta ba, kai tsaye ya buɗe ƙofar front seat, Raihana ta ɗan tsaya na ɗan lokaci, kamar ba ta yi tsammanin zai buɗe mata ƙofar ba, sai ta shiga a hankali, ta zauna ta gyara mayafinta, Zayd ya rufe ƙofar a hankali, sannan ya zagaya motar zuwa ɓangaren driver seat, Seeyama kuwa tana tsaye tana kallon abin da ke faruwa, har ta manta da cewa wayarta tana kunnenta, “Seeyama? Kina jina ne?” muryar Safina ta fito daga wayar, amma Seeyama ba ta amsa ba, idanunta suna kan Zayd ne, wanda ya shiga motar ya zauna, ya ɗaura seat belt ɗinsa sannan ya kunna injin motar, ta ga yadda ya ɗan juya kansa ya kalli Raihana, ya faɗa mata wani abu da ba ta ji ba, Raihana kuwa ta jinjina kanta a hankali, snn ta janyo seat belt ta daura, wait… he opened the door for her? Seeyama ta ɗan buɗe bakinta, tana kallon motar kamar ba ta yarda da abin da idanunta suke gani ba, “Hello? Seeyama!” Safina ta sake kira daga wayar, a daidai lokacin, motar Zayd ta fara motsawa, gateman ya yi saurin buɗe musu ƙofar compound, Zayd ya fitar da motar cikin nutsuwarsa, Seeyama ta tsaya cak, wayarta a hannunta, tana kallon motar har ta fita “Wannan kuma ina za su je?”