Free chapter · Read without an account
A QUIET SURPRISE
ZAYD ARMAAN
CHAPTER 117
A QUIET SURPRISE
JIDDAAH BARKUM
————
The journey zuwa gidan Anty Mariya ya kasance cikin wani irin shiru, babu wanda ya ce komai, sai karatun Al-Qur’ani da ke tashi daga cikin motar a hankali yana cike gurbin shirun da ke tsakaninsu, Raihana na zaune a gefensa, idanunta suna kallon hanya ta window, lokaci-lokaci tana satar kallonsa kafin ta mayar da idanunta gefe, ba ta san inda suke zuwa ba, kuma duk da son da take yi na tambayarsa, sai ta kasa buɗe baki, shi kuwa Zayd, hankalinsa yana kan hanya, hannunsa ɗaya a kan steering wheel yayin da ɗayan yake sauƙe a gefensa, fuskarsa a yadda ta saba, babu wata alama da za ta nuna abin da ke ratsa zuciyarsa, a haka suka ci gaba da tafiya har suka isa gidan, ya rage gudun motar, sannan ya tsaya, ya kashe injin ɗin, ya juyo kaɗan ya kalli Raihana, “Ki shiga,” ya faɗa a taƙaice, “Zan je masallaci na yi Isha’i,” Raihana ta gyada kai a hankali, “To,” ta buɗe ƙofar motar, ta sauka tana gyara mayafinta, bayan ta rufe ƙofar, ta ɗan tsaya na ƴan daƙiƙu, kamar tana son ta ce wani abu, amma daga ƙarshe sai ta juya ta nufi cikin gidan, Zayd bai motsa ba har sai da ya tabbatar ta shiga gidan, sai ya buɗe nasa ƙofar, ya fito daga motar, ya rufe ta sannan ya nufi masallaci domin sallar Isha’i, gidan Anty Mariya ba shi da wani wahalar shiga, domin entrance ɗaya ne kawai, Raihana ta bi kai tsaye har bakin ƙofar falon, ta ɗaga hannunta ta yi knocking a hankali, ba a ɗauki lokaci mai tsawo ba, sai yar aikin Anty Mariya ta buɗe ƙofar, “Assalamu alaikum,” Raihana ta yi sallama a hankali tana shiga, “Wa alaikumus salam,” yarinyar ta amsa, ta shiga falon, amma ba ta ga kowa ba, abin da ya fara sauka a hancinta shi ne kamshin turaren wuta da ke tashi a falon, haɗe da ƙamshin girkin da ake yi a kitchen ɗin da ke cikin falon, yarinyar ta nuna mata wajen zama, “Ki zauna, bari na je na yi wa Anty magana,” Raihana ta jinjina kai, “To, shikenan,” ta nemi kujera ɗaya daga cikin kujerun falon ta zauna, ta ajiye jakarta a gefenta, idanunta suka fara zagaya falon a hankali, tana jiran dawowar yarinyar, ba ta daɗe da zama ba sai yarinyar ta dawo, “Zo mu je, na kai ki ciki,” Raihana ta ɗago kai ta kalle ta, “To,” ta amsa a hankali, ta ɗauki jakarta, ta miƙe tsaye, sannan ta bi bayan yarinyar har zuwa ɗakin Anty Mariya, Anty Mariya na kan prayer mat, ta idar da sallar Isha’i kenan, tana zaune tana lazimi, sai aka buɗe ƙofar ɗakinta a hankali, Raihana ta shigo kanta a ƙasa, hannunta riƙe da ƙaramar jakarta, Anty Mariya ta ɗago kai daga laziminta, idanunta suka sauka kan baƙuwar da ta shigo, sai ta ajiye casbahan da take riƙe da shi, ta miƙe daga kan prayer mat ɗin tana kallon Raihana da murmushi, “Ah-ah, ga amaryata!” Ta ƙarasa gare ta, ta buɗe hannayenta ta rungume ta cikin ƙauna, “Welcome, daughter,” ta faɗa tana murmushi, ta ɗan ja da baya domin ta kalli fuskarta, “Kin yi kyau, ma Shaa Allah,” Raihana ta sunkuyar da kanta cikin kunya, murmushi kaɗan ya bayyana a fuskarta, “Anty, ina wuni?” “Lafiya lau, my daughter, ya gida? Ya zama da zaman gidan?” Anty Mariya ta tambaya cikin kulawa, har yanzu murmushi bai bar fuskarta ba, “Alhamdulillah, lafiya,” Raihana ta amsa a hankali, Anty Mariya ta ƙara kallonta fuskarta da murmushi sosai, “Allah ya sa albarka, ya ba ku zaman lafiya,” Raihana ta danyi murmushi ta kasa cewa amin din, sai Anty Mariya ta tuna da wani abu, “Ina mijin naki?” Raihana ta ɗan ɗago kai, kafin ta sake sunkuyar da shi, “Ya tsaya a masallaci ne, zai yi sallar Isha’i,” “To, shikenan, Allah ya karɓa,” “Ameen,” kallo ɗayan da Raihana ta yi mata, sai ta fahimci cewa Anty Mariya tana da alaƙa ta kusa da Ummie, kamanninsu sun yi yawa, musamman yadda fuskarsu take da nutsuwa da kuma irin murmushin da ke bayyana a hankali, sai anty Mariya ya kamo ta ta zaunar da ita akan gadon ta ita kuma ta zauna a gefenta tana kallonta tana kallon kalar nutsuwar da take da shi Raihana ta ɗan yi shiru kafin ta ce, “Anty, zan yi sallah,” “Okay toh taso kiyi alwala!” Anty Mariya ta amsa da sauri, sai Raihana ta amsa inada alwala “Toh shikenan zo ki yi a nan,” ta nuna mata wajen da ta ta shi yanzu, sannan ta matsa gefe ta ba ta damar yin sallah, Raihana ta ajiye jakarta, sannan ta miƙe ta fara sallah, Anty Mariya ta tsaya tana kallonta na ɗan lokaci, kafin ta juya ta fita daga ɗakin a hankali, tana fita ta nufi kitchen domin ta kawo mata abinci, zuciyarta cike da farin ciki da ganin amaryar Zayd a gidanta, Raihana ta idar da sallarta lokacin da Anty Mariya ta shigo ɗakin, hannunta riƙe da tray ɗin da ya cika da kayan ciye-ciye iri-iri, ta ƙarasa ta ajiye tray ɗin a gabansu, sannan ta zauna a gefen Raihana tana murmushi, “Kinga mijin naki ma, ashe ya shigo yana falo, na dai ce ya jiramu, tunda ke nake son gani ba shi ba,” Raihana ta ɗan yi murmushi, amma ba ta ce komai ba, ta sunkuyar da kanta, tana wasa da gefen sallayar, Anty Mariya ta janyo tray ɗin kusa da ita, “Gashi nan, ki ci, I want you to finish everything here,” Raihana ta ɗago kai ta kalli tray ɗin, sannan ta sunkuyar da kanta tana murmushi, a zuciyarta kuwa, ta san Anty Mariya ta faɗa ne kawai, amma ta yaya za ta fara cin duk waɗannan kayan ciye-ciyen? Anty Mariya ta lura da yadda take kallon tray ɗin, sai ta girgiza kai a hankali tana murmushi, “Raihana, don’t tell me you’re already thinking of how to escape this food,” Raihana ta ɗago kai da sauri, ta yi ƙoƙarin ɓoye murmushinta, “A’a, Anty,” “Good, because I’m not taking no for an answer,” ta miƙa hannu ta ɗauki bottle water, ta buɗe ta zuba ruwa a glass cup, sannan ta miƙa wa Raihana, “Sha ruwa,” ta faɗa cikin murmushi, Raihana ta karɓa da hannayenta biyu, “Nagode,” ta sha kaɗan, sannan ta ajiye cup ɗin a gefe, cikinta a cunkushe yake kwanakin nan ba wani cin abinci take yi ba, kuma abin mamaki, yunwar ma ba wani jin ta take ba, tana dai cin abıncin ne dai a ba yanda ta iya, Anty Mariya ta kalleta da kyau, murmushin da ke fuskarta ya ɗan ragu yayin da ta lura da yadda Raihana take kallon gefe, ta ɗan yi shiru kafin ta gyara zamanta, sannan ta dubi Raihana cikin sanyin murya, “Raihana, ya kuke kuna zaune lafiya dai da mijinki da matarshi, ko?” Raihana ta ɗago kai ta kalleta, sannan ta gyada kai a hankali, “Lafiya lau, Anty,” Anty Mariya ta ɗan tsura mata ido, ba wai don tana son matsa mata ba, sai don ta fahimci ko akwai abin da yarinyar take ɓoyewa a zuciyarta, “Kin tabbata babu wata damuwa? You know, sometimes people say they’re fine when they’re actually going through a lot, kuma ni ba don na tsoma baki a cikin auranki na tambaye ki ba, ina son kawai in tabbatar kina lafiya,” Raihana ta sake jinjina kai, “Wallahi Anty, babu komai,” Anty Mariya ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta kama hannun Raihana, “To, Alhamdulillah, Allah ya sa haka ne, ya kuma tabbatar da zaman lafiya a tsakaninku,” “Ameen,” Raihana ta amsa a hankali, Anty Mariya ta shafa bayan hannunta, sannan ta fara magana cikin nutsuwa, “Kin san, my daughter, zama da kishiya yana buƙatar haƙuri, hikima da kuma zuciya mai faɗi, ba kullum za ku fahimci juna ba, kuma ba kullum abubuwa za su tafi yadda kike so ba, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne ki koyi yadda za ki zauna da ita ba tare da kin rasa kanki ba,” Raihana ta nutsu tana sauraron ta, “Ki yi ƙoƙarin zama da ita da zuciya ɗaya, ki girmama ta, ki guji shiga rigingimu marasa amfani, idan ta yi abin da bai yi miki daɗi ba, ki yi haƙuri ki yi tunani kafin ki mayar da martani, but remember, being patient doesn’t mean you should allow anyone to disrespect you, za ki iya zama mai haƙuri kuma har yanzu ki san darajarki,” Raihana ta sunkuyar da kanta, kalaman Anty Mariya suna shiga kunnenta a hankali, “Wani lokacin ma, abin da zai taimake ki shi ne ki san lokacin da ya dace ki yi magana da lokacin da ya fi kyau ki yi shiru, ba kowace magana ce sai kin mayar da amsa ba, kuma ba kowace matsala ce za ki warware ta a ranar da ta faru ba,” ta ɗan dakata, sannan ta ci gaba, “Sannan game da mijinki, ki tuna cewa aure yana buƙatar fahimtar juna, kada ki riƙa ɗaukar komai a zuciyarki har ya zama yana damunki a ɓoye, idan akwai abin da ya ɓata miki rai, idan lokacin ya dace, ki yi magana da shi cikin nutsuwa, ki ba shi damar ya fahimce ki, ke ma ki saurare shi, a marriage needs communication, not just silence,” Raihana ta ɗago idanunta kaɗan, tana sauraron ta cikin nutsuwa, “Ki kuma kula da kanki, ki ci abinci, ki huta, ki kula da lafiyarki, kada ki manta da kanki saboda ƙoƙarin faranta wa kowa rai, you matter too, Raihana,” kalaman na ƙarshe sun sa Raihana yin shiru na ɗan lokaci, ta ji kamar Anty Mariya ta lura da wani abu da ita kanta take ƙoƙarin ɓoyewa, Anty Mariya ta yi murmushi kaɗan, sannan kamar a bazata ta sauya zance, “Na ji Mommy ta kawo miki mai aiki, ko?” Raihana ta ɗago kai, “Eh, Anty,” “To, Alhamdulillah, hakan zai rage miki wahala, musamman idan kin fara zuwa makaranta, amma akwai abin da nake son ki sani,” ta matso kaɗan, muryarta ta sauka cikin hikima, “Ki yi mata mu’amala mai kyau, ki girmama ta, ki kuma ba ta haƙƙinta, but don’t hand over the control of your home to her, ki sani cewa mai aiki tana zuwa ne domin ta taimaka miki, ba domin ta zama mai yanke shawara a gidanki ba,” Raihana ta jinjina kai a hankali, “Ki koya mata aikin da kike so ta yi, ki bayyana mata dokokin gidanki tun da wuri, kada ki bar ta ta riƙa yanke shawara a madadinki ko ta san duk abin da ke faruwa a tsakaninki da mijinki, ba wai ina ce miki kada ki yarda da ita ba, no, you can trust someone and still have boundaries,” ta ɗan dakata tana kallon Raihana don ta tabbatar tana fahimtar abin da take nufi, “Kada ki bar ta da ragamar komai, ki riƙa sa ido a kan yadda take gudanar da aikinta, yadda take mu’amala da ku, da kuma yadda take kula da kayayyakin gidan, idan akwai abin da ba ki yarda da shi ba, ki gyara mata tun da wuri cikin mutunci,” sai ta ƙara da cewa, “Kuma wani abu mai muhimmanci, kada ki riƙa ba ta damar shiga tsakanin ki da kishiyarki ko mijinki, matsalolin gidanku ku ya kamata ku warware su, ba mai aiki ba, ki kiyaye sirrinki, my daughter,” Raihana ta gyada kai cikin nutsuwa, “To, Anty, na gode sosai,” Anty Mariya ta murmusa, ta taɓa kumatunta a hankali, “Ba komai, daughter, ina faɗa miki ne saboda ina son ki zauna lafiya, kin shiga sabon gida ne, kuma har yanzu kina koyon abubuwa da yawa, take your time, don’t rush yourself, kuma kada ki bari tsoron ɓata wa wani rai ya sa ki manta da abin da ya dace da ke,” ta sake kallon tray ɗin da ke gabansu, sannan ta ɗaga gira, “Amma duk wannan maganan da na yi miki, ban manta da abincin da ke gabanki ba fa,” Raihana ta kasa riƙe murmushinta, “Eh mana!” Anty Mariya ta faɗa tana dariya a hankali, “Ki fara cin abinci, sai mu ci gaba da sauran maganar, I need to make sure my daughter is taking care of herself,” Anty Mariya ta ci gaba da yi wa Raihana maganganu masu kama hankali, tana ba ta shawarwari kan yadda za ta kula da kanta da kuma yadda za ta tafiyar da aurenta cikin hikima, ba ta yi maganar cikin tsawa ko nuna kamar tana son ta tsorata ta ba, sai dai ta yi amfani da kalmomi masu laushi da za su sa Raihana ta yi tunani sosai, “Raihana, ki tuna da wannan abu ɗaya,” ta faɗa tana riƙe da hannunta, “Ba dole sai kin yi wa kowa komai yadda yake so ba kafin ki zama mace ta gari, ki yi abin da ya dace, ki kiyaye mutuncinki, sannan ki bar lokaci ya nuna wa mutane irin zuciyar da kike da ita,” ta ɗan dakata, sannan ta ƙara da cewa, “Kada ki yi gaggawar yanke hukunci a kan mijinki saboda wani abu da ya faru a yau, marriage is a journey, and sometimes you need patience to understand the person you’re sharing your life with, amma ke ma kina da zuciya, kina da feelings, kada ki riƙa binne su har su zama nauyi a gare ki,” Raihana ta sunkuyar da kanta, tana sauraron ta sosai, kalmomin Anty Mariya sun sa ta ji kamar tana magana ne da wadda ta fahimci abubuwan da take fuskanta, ko da kuwa ba ta faɗi komai ba, “Allah ya ba ki hikima, ya sa ki zama mace mai albarka a gidanki,” Anty Mariya ta ƙarasa da murmushi, “Ameen, Anty, Allah ya saka da alheri,” Raihana ta amsa cikin kunya, a daidai lokacin ne wayar Anty Mariya ta fara ringing, ta ɗauko wayar daga gefenta, tana ganin sunan wanda yake kiranta, sai ta girgiza kai tare da ɗan murmushi, ta ɗaga wayar zuwa kunnenta, “Hello?” Muryar Zayd ta fito daga ɗayan ɓangaren, Anty Mariya ta ɗan buɗe baki tana kallon Raihana, sannan ta mayar da hankalinta kan wayar, “Kar fa ka dameni! Idan ka gaji, ka tafi, sai ta kwana, kai, sai ka riƙa kirana kamar wanda bai san inda matarsa take ba, ya kake min kamar ba ka san inda na kai ta ba?” Raihana da ke zaune kusa da ita ta ji komai, ta sunkuyar da kanta sosai, tana ƙoƙarin ɓoye murmushin da ya fara bayyana a fuskarta, Zayd ya yi shiru na ɗan lokaci a ɗayan ɓangaren, kafin ya ce wani abu da Anty Mariya ta kasa bari ba tare da ta mayar masa da martani ba, “Eh mana! Ka bar ni in yi magana da ita mana, ko kai kadai ke son zama da ita ne?? Ni ma ina son zama da ita,” Raihana ta ƙara sunkuyar da kanta, yanzu kam kunya ta fara kamata sosai, to, shikenan, muna zuwa,” ta faɗa cikin wayar kafin ta katse kiran, ta ajiye wayar, ta juyo ta kalli Raihana, wadda har yanzu kanta yake a ƙasa, Anty Mariya ta yi dariya, “Come on, daughter, mu je, kin ji dai abubuwan da na faɗa miki ko?” Raihana ta ɗago kai ta jinjina shi, “Na ji, Anty, in Shaa Allah zan kula,” “Yawwa, ma Shaa Allah, Allah ya Baku hakurin zama da kuma yanzu ki samin number dinki idan kinje gıdan zan kiraki ” tohm raihana ta amsa snn ta karbi wayar anty Mariya ta saka mata numbers din Anty Mariya ta miƙe, ta ɗauko wata babbar leda da ta ajiye a gefe, sannan ta kama hannun Raihana, “Zo mu je,” Raihana ta ɗauki jakarta, ta miƙe suka nufi ƙofar ɗakin tare, Anty Mariya tana riƙe da ledar a ɗaya hannunta, ɗayan kuma rike d hannun Raihana, a hankali suka fito daga ɗakin, suka nufi falon, yana ganin sun sauko falon, Zayd ya miƙe tsaye yana saka wayarsa a aljihunsa, ya ɗago kai ya kalle su yayin da suke ƙarasa saukowa, Anty Mariya ta kalle shi da ɗan murmushi, “Waton sai azalzalamu kake yi da ga saukowarmu kenan, sai tafiya ba tare da bata lokaci ba?” Zayd ya ɗan yi dariya, har haƙoransa suka bayyana, Raihana da ke bayan Anty Mariya ta kalle shi ta gefen ido, ta ɗan tsaya a kallonsa na ƴan daƙiƙu, yaushe rabon da ta ga dariyarsa haka? Har ta manta irin wannan murmushin, “Anty, ai na faɗa miki za mu je wani waje ne, shi ya sa, kuma kin ga yanzu ƙarfe goma ta wuce,” ya amsa cikin sauƙin murya, Anty Mariya ta yi murmushi, “It’s fine, nagode da kuka zo,” ta juya ta rungume Raihana, “Take care of yourself, daughter, kin ji?” Raihana ta rungumeta ita ma, “Na gode, Anty,” Anty Mariya ta ɗan shafa bayanta kafin ta sake ta, sai ta juyo ta kalli Zayd, ta miƙa masa ledar da take riƙe da ita, “Gashi, kayanta ne, ka riƙe mata,” Zayd ya karɓa ba tare da wata magana ba, kafin ya mayar da idanunsa kan Anty Mariya, “Shikenan, Anty,” “Yawwa, kuma ka kula da ita, ka ji?” Zayd ya jinjina kai, Anty Mariya ta sake kallon Raihana da murmushi, sannan ta yi musu sallama, “Allah ya tsare hanya” “Ameen,” suka amsa kusan lokaci guda, Zayd ya juya zuwa ƙofar fita, Raihana kuma ta bi bayansa, tana sake waiwayen Anty Mariya itama anty Mariya tana tsaye tana mara waving har ta fice ta rufo kofar, bayan sun fito daga gidan Anty Mariya, Zayd ya buɗe wa Raihana ƙofar motar, ta shiga ta zauna, ya zagaya ya ajiye ledar hannunsa a back seat snn ya shiga driver’s seat, sannan ya kunna motar suka fice daga harabar gidan, har yanzu dai shiru ne a tsakaninsu, babu wanda ya yi magana, sai dai karatun Al-Qur’ani da ke tashi a hankali daga cikin motar, yana cika gurbin maganganun da babu su, Raihana ta gyara zamanta, ta jingina da kujerar motar, bayan ɗan lokaci, sai ta lumshe idanunta, tana jin nutsuwar karatun da ke tashi a hankali, Zayd kuwa yana tuƙi cikin nutsuwa, hankalinsa a kan hanya, bai ce komai ba, haka ita ma ba ta yi ƙoƙarin fara magana ba, bayan wasu mintuna, sai Raihana ta ji motar ta rage gudu, daga bisani ta tsaya cak, ta buɗe idanunta a hankali, tana kallon wajen da suka tsaya, sai kawai ta ga suna unguwarsu, can Malali, a gidan Baffanta, ta ɗan gyara zamanta, idanunta suka koma kan gidan, sannan ta juya ta kalli Zayd cikin mamaki, me ya kawo su nan? Ta sake kallon gidan, kamar tana son tabbatar da abin da idanunta suka gani, ba ta yi tsammanin za su zo nan ba sam, Zayd ya ɗan juya kansa ya kalleta, fuskarsa a yadda ta saba, cikin nutsuwa ya ce, “Ki shiga ku gaisa, ten minutes, ki fito,” Raihana ta juyo ta kalle shi, har yanzu mamaki bai bar fuskarta ba, ji take kaman ta rungumeshi ta ce masa tagode amma ta san bazata iya ba kafin ma tayi tunanin abin fada masa, ta riga ta buɗe murfin motar, da sauri ta sauka, ta gyara mayafinta ta rike gefe da gefensa, sannan ta nufi cikin gidan da dan gudu gudu, farin cikinta ya kasa ɓoyuwa, Zayd ya bi ta da kallo, har ta shige snn ya lumshe idanunshi ya jingina kansa da kujerar motar