Free chapter · Read without an account
THE CONFESSION
ZAYD ARMAAN
CHAPTER 119
THE CONFESSION
JIDDAAH BARKUM
————
Ta faɗa a hankali, muryarta ta ɗan yi ƙasa da yadda ta saba magana. Ta ji kamar ta koma yarinya ƙarama sosai a gabansa, Zayd ya ɗan karkatar da kansa yana kallonta, sai kuma ya juyo gabadaya ya zuba mata idanunsa. Raihana ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, sannan ta buɗe su. Har yanzu tana tsaye a gabansa, hannayenta a haɗe, tana ƙoƙarin tara courage ɗin da zai sa ta faɗi abin da ke zuciyarta.
“Me ya sa za ka tafi ka kwana a wani wajen?”
Zayd ya yi shiru yana kallonta, sai kuma ya ɗan tako a hankali ya ƙaraso inda take. Suka yi daidai da juna, har yanzu yana riƙe da pillow da duvet ɗin. Ya sauke muryarsa, yana kallonta daga sama har ƙasa kafin ya tambaya, “If I sleep in this room, what do you stand to gain from it? Ko kuma ni, me zan ƙaru da shi?”
Raihana ta ɗan turo baki. Zuciyarta na bugawa da sauri, amma sai ta daure ta ce, “Amma a haka dai muke kwana tare ko? Kwanakin da ka yi ba ka nan, ai ba ka san yadda na yi su ba.”
Zayd ya kafe bakinta da kallo, yana sauraron kalaman da ke fitowa daga gare ta. Ya ɗan lumshe idanunsa kafin ya sake buɗe su. “Yanzun ma ki ci gaba da gwada kwanan ke kaɗai, tunda tun asali haka kike so.”
Ya juya zai fita. Da sauri Raihana ta ƙarasa bayansa. Kafin ta yi tunanin abin da za ta yi, sai kawai ta rungume shi ta baya, ta zagaye hannayenta a cikinsa. Zayd ya tsaya cak.
Raihana ta fara wasu irin ƙananan kuka, tana magana a hankali cikin kukan nata, “Ni dai wallahi na gaji da wannan abin… sai shareni kake yi. Kana gaba da ni, kuma ina ta ba ka haƙuri tun ranar amma ka ƙi kulani. Ni fa ban san haka abin zai kasance ba da ban yi abin da na yi ba. I regret it. Don Allah ka yi haƙuri, ka daina gaba da ni. Allah, ba zan sake ba…”
Ta ƙarasa maganar, sai kuma ta sake fashewa da kuka. Zayd kuwa, tun daga lokacin da ta rungume shi, ya lumshe idanunsa. Wani irin yanayi ne ya ratsa jikinsa, yanayin da ya kasa bayyana wa kansa. Bai san me ya sa ba, ko sunanta ya ji haka yake tsintar kansa a wannan yanayin, kuma yanzu ma yadda ta manne masa tana kuka, ya sa wani abu a cikin zuciyarsa ya motsa.
He stood still, unable to take another step.
Ya saba ganin Raihana cikin nutsuwarta, tana ƙoƙarin ɓoye duk wani abu da take ji a ranta. Amma yau, tana bayansa tana kuka saboda shi, tana roƙonsa ya daina fushi da ita. Ya ɗan sauke numfashi. Ba wai bai ji maganarta ba ne. Ya ji kowace kalma. Especially that “I regret it.”
A hankali ya sauke hannunsa da ke riƙe da pillow ɗin, ya riƙe su da hannu ɗaya amma bai juya ba tukuna. “Ki cikani…” ya faɗa cikin ƙaramar murya. Amma sai ta ƙara matse hannayenta a jikinsa, kamar tana tsoron zai sake tafiya idan ta sake shi.
“Please…” ta faɗa cikin kuka.
Zayd ya ɗan runtse idanunsa. A wannan karon, fushin da ya daɗe yana riƙewa bai zo masa da ƙarfi kamar da ba. Sai ya saki pillow da duvet ɗin da ke hannunsa, suka zube a ƙasa. A hankali ya kai hannayensa gare ta, ya kama hannayenta ya kwance su daga jikinsa, sannan ya janyo ta ta dawo gabansa. Amma da ta tsaya a gabansa, ta ɗago kai za ta kalle shi, sai ta kasa jure kallon idanunsa. Kafin ya ce wani abu, sai ta sake rungumeshi gammmmm, ta manna fuskarta a kirjinsa, hannayenta kuma suka zagaye bayansa.
Zayd ya ɗan tsaya cak yana kallon tsakiyar kanta. Ita kam ko motsi ba ta yi ba. Sai kawai ta ƙara matse shi, tana sauke numfashi cikin kuka. Ya sauke kansa kaɗan yana ƙoƙarin kallon fuskarta, sannan ya ɗaga hannunsa ɗaya ya ɗora a bayanta. Muryarsa ta fito a hankali, “Ke ce fa kika kore ni daga ɗakin nan da daddare. Na ɗauka ba kya son ganina a cikinsa a irin wannan lokacin.”
Sai ta fara girgiza kai a jikinsa. “Ni? A’a! Wallahi Allah ya gani, ba haka ba ne. Saboda na ga ba kwana na ba ne, shi ya sa na ƙi yarda. Ina tsoron zunubin da ni da kai za mu ɗauka a kanmu. Kuma ma, ba ka faɗa min dalilin da ya sa ka bar can ka zo nan ba. Sannan ko ni ce da kwana ka tafi can, ai ba zan ji daɗi ba…”
Ta kasa ƙarasa maganar, sai ta sake matse shi a jikinta. “Ka yi haƙuri.”
Zayd ya yi shiru. Kalmomin nata sun sauka a ransa kamar ruwan da ya wanke baƙin ran da yake yi da ita. Ya ɗan lumshe idanunsa, yana ƙoƙarin fahimtar abin da take nufi. A hankali ya sa hannunsa zai janyo ta kaɗan domin ya kalleta, amma sai ta ƙara manne masa kamar ba ta son ta sake shi. Ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya sunkuyar da kansa daidai kunnenta.
“Idan na kai mata kwananki za ki ji daɗi ba?”
Ya yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya ƙara da ƙaramar murya, “Me ya sa?”
Raihana ta ɗan motsa a jikinsa, sannan ta ce cikin muryar kuka, “Ai dai ba haka ake yi ba. Kowa ka mata iya kwanan ta…”
Ta yi shiru, tana sharan hawayenta da gefen rigarsa. Zayd bai ce komai ba. Yana sauraron ta ne kawai.
“Ita ai tana sona,” muryarsa ta fito a sanyaye. “Saboda haka ita ce za ta ji haushi idan na kawo miki kwananta. Ke kuwa, na tabbata za ki iya sadaukar mata da ni ma gaba ɗaya…”
Raihana ba ta san lokacin da ta fashe da kuka ba. Muryarta ta ƙara rawa yayin da take ƙoƙarin bayyana abin da ke ranta.
“Ni na ce bana sonka ne? Wallahi na fita sonka ma… ita dai ba ta jin kunyar kowa, ba ta da kunya, kuma ni…”
Sai ta yi shiru kwatsam. Kamar wacce ta tuna wani abu, sai ta yi saurin sakin Zayd ta juya masa baya, tana zare idanu.
Zayd ya ɗan ɗaga gira yana kallonta. A hankali gefen bakinsa ya ɗan motsa, wani ƙaramin murmushi ya bayyana a fuskarsa. Bai yi ƙoƙarin ɓoye shi ba, amma bai ce komai ba tukuna. Ya ɗan tako ya ƙaraso gare ta, sannan ya sa hannu a hankali ya janyo ta ta juyo gare shi. Amma Raihana ta ƙi ɗago kanta. Kunya take ji, har ta kasa kallon fuskarsa. Kamar ta yi kuka ma, haka take ji a ranta.
Shikenan! Yanzu fa ta nace ina sonsa. Wayyo Allah na!
Ta ji kamar ƙasa ta tsage ta shige. Da ace akwai inda za ta ɓuya a wannan lokacin, da tuni ta ɓuya. Zayd ya ɗan sunkuyar da kansa yana ƙoƙarin ganin fuskarta, amma sai ta ƙara sunkuyar da kanta.
“Look at me.”
Ta girgiza kai a hankali. Ya ɗan yi murmushi, sannan ya tambaye ta cikin sanyin muryarsa, “Kina sona kuma?”
Raihana ta ɗan motsa, amma ba ta amsa ba.
“Since when?”
Ta ji kamar tambayar ta ƙara mata nauyin kunya. Ta fara murɗa yatsunta, tana neman inda za ta sa fuskarta. Zayd ya ɗan karkatar da kansa.
“Ta yaya zan gane kina sona?”
Raihana ta ɗago idanunta na ɗan lokaci, ta kalle shi, sai kuma ta sake sauke su. “Ni… ni…”
Ta kasa haɗa magana. Ƙafafunta suka fara rawa a hankali, jikinta kuma ya yi wani irin motsi kamar ana zuba mata ruwan sanyi. Ta ji kamar kanta ma ya yi nauyi. Zayd ya lura da yanayinta, amma bai yi saurin ƙara mata tambayoyi ba.
“Hmm?”
Sai ta ɗan ja baya kaɗan, tana ƙoƙarin kwantar da hankalinta. “Ka daina tambayata mana…” ta faɗa da muryar shagwaɓa, tana ɗan buga ƙafarta.
“Me ya sa?” ya tambaya cikin sanyin murya.
Ta tsaya, ta sake haɗiye yawu. “Saboda kana sa ni jin kunya,” a ƙarshe ta amsa.
Zayd ya ɗan kalleta na wasu seconds, sannan ya kau da kansa kaɗan. Ɗan murmushin da ke fuskarsa ya ƙara bayyana. “Alright,” ya faɗa a taƙaice, kafin ya durƙusa ya ɗauki pillow ɗin da duvet ɗin da suka zube a ƙasa.
Ya bi ta gefenta zai fita, amma sai ta ƙi yarda. Da sauri ta miƙa hannu ta karɓi pillow da duvet ɗin daga hannunsa. Cikin wani irin shagwaɓa ta ce, “Allah, ba inda za ka je! A nan za ka kwana. Ni dai…”
Ta kasa ƙarasa maganar, sai ta sa hannunta ta riƙe nasa ta fara jan shi zuwa wajen gadon. Zayd kuwa kawai kallonta yake yi, yana bin ta kamar raƙumin da aka sa wa akala. Bai yi musu ba, bai kuma tambayi inda za ta kai shi ba, har suka ƙarasa wajen bed ɗinsa. Ta ja shi ta zaunar da shi, yana ta kallonta amma ita ta ƙi kallonsa.
“Ka kwana a kan gadonka, ai ɗakin ka ne.”
Ta ajiye duvet ɗin da pillow ɗin, sannan ta juya da niyyar ta tafi. Amma kafin ta yi nisa, Zayd ya miƙa hannu ya janyo ta. Nan take ta faɗo ta zauna a kan cinyarsa. Raihana ta zaro ido tana kallonsa. Ta buɗe baki kamar za ta yi magana, amma babu wata kalma da ta fito daga bakinta.
A hankali Zayd ya ɗora hannunsa a cikinta, sannan ya ɗaga ɗayan hannunsa ya cire hular da ke kanta, ya ajiye ta a gefe, ya janye bun ɗin da ta ɗaure gashinta, kitson ya bazu a bayanta. Ya ɗan karkatar da kansa ya matso da fuskarsa sosai kusa da wuyanta. Lips ɗinsa masu laushi suka fara shafan fatar wuyanta a hankali. Wani irin dumi da sanyi mai daɗi ya ratsa jikin Raihana lokacin da ta ji saukar ɗumin lips ɗinsa a wajen. Ta saki wani gajeren nishi da ba ta san yaushe ya yi escaping ba, ta lumshe idanunta, sai ya ɗora kansa a kan shoulder ɗinta.
Hannunsa na ci gaba da shafa cikinta a hankali, kamar ba wani babban abu ne yake faruwa ba, duk da yadda numfashinsu ya fara sauyawa. Cikin wata narkakkiyar murya ya fara magana a kunnenta, “And where did you think you were going after stopping me from leaving?”
Raihana ta ji kamar wani abu yana yawo a dukan jikinta bayan jin muryarsa a kunnenta da kuma yadda lips ɗinsa ke ta motsawa a wuyanta. Ta ɗan runtse idanunta sosai, sannan a hankali ta ɗora hannunta a kan nasa da ke cikinta. Muryarta ta fito a hankali, kusan cikin raɗa, “Mu kwanta… dare ya yi.”
Zayd bai cire hannunsa daga cikinta ba. Ya ci gaba da shafa cikinta a hankali, sannan ya sake sunkuyar da kansa kusa da kunnenta.
“Ni kuma fa ba na jin barci… ya za ki yi da ni?”
Ya faɗa cikin wata murya mai ɗan laushi, kamar yana son jin amsarta ne kawai. Raihana ta tsaya cak. Ta ji yadda kunnenta ya ɗauki maganarsa, sai ta ɗan motsa a kan cinyarsa, tana ƙoƙarin juya kunnenta daga wajen kunnensa.
“Ka… bari mana…” ta faɗa cikin shagwaɓa.
“Me zan bari?” ya amsa, yana lasar kunnenta da harshensa.
Ta kasa amsawa. Ta sake lumshe idanunta, jin wani azababben shock yana ratsa brain ɗinta. Sai kawai ta matse hannunsa da ke kan cikinta, tana son ya daina shafa ta. Jin abin da ta yi, sai Zayd ya zare hannunsa kamar zai janye shi daga jikinta. Amma ba ta ankara ba, sai ta ji ya ɗora hannayensa a kan ƙirjinta, ya fara shafawa a hankali.
Raihana ta yi shiru, jikinta ya ɗauki rawa. Zayd ya kalli hannayensa da ke kanta, sannan ya ɗago idanunsa zuwa fuskarta, ya ɗan ɗaga gira.
“What?”
Ta buɗe baki, amma ba ta samu abin cewa ba. Sai kawai ta lumshe idanunta, zuciyarta na bugawa. Ba ta son su yi faɗa da shi, tunda yanzu ta samu ya sauko. Sai ta fara tunanin yadda za ta kwace daga hannunsa yanzu.
Tana cikin tunanin abin da za ta kawo ta gudu, sai ta ji ya ƙara matsa ƙirjinta a hankali, idanunsa a kan fuskarta.
“Habibti…”
Ya kira ta a karon farko. Zuciyar Raihana ta buga da ƙarfi. Wani sanyi mai daɗi ya bi jikinta duka. Ta buɗe idanunta a hankali, amma ta kasa kallonsa sosai. Ya sauke muryarsa ƙasa sosai.
“Me ya sa kike wahalar da ni?”
Ta kasa magana. Kawai wani yanayi ne ya mamaye ta, ta ji kamar ba a duniyar take ba. Kamar ba wannan arrogant Zayd ɗin ne ke magana ba. Ta ji kamar tana cikin mafarkin da ta saba yi duk daren duniya idan ta kwanta.
Da ya ga ta ƙi amsawa, sai ya sake matsa ƙirjinta a hankali, idanunsa har yanzu a kan fuskarta.
“Ahhh…” ta saki wani ƙaramin sauti, ta rufe bakinta da hannunta.
“My Rai,” ya sake faɗa a hankali. “Tell me, me ya sa kike wahalar da ni, right from the day I first met you?”
Ta buɗe idanunta a hankali. Ba ta san lokacin da ta juyo ta kalleshi ba, sai kawai idanunta suka sauka a kan nasa. Yana kallonta kai tsaye. Babu wasa ko zolaya a cikin kallon nasa.
“I think the game should end here.”
Ya raɗa mata a hankali, sannan ya ɗan yi shiru kafin ya ci gaba.
“Kuma yanzu, I must confess…”
Ya ɗago hannayensa ya riƙe fuskarta a tafukansa, yana kallonta kai tsaye.
“I love you dearly, Rayhanaaa. Every beat of my heart beats for you…”
Idanun Raihana suka tsaya a kan nasa. Suka yi wa juna kallon wasu seconds, amma ita ta kasa cewa komai. Ta ji kamar maganar ta tsaya a kunnenta tana maimaituwa.
I love you dearly.
Da sauri ta ɓoye fuskarta a kafaɗarsa, kamar wacce ta tuna da wani abu.
“Wayyo Umma na…”