Free chapter · Read without an account

RAYUWAR SUBAI'AH Part 1

by Fatima Dahiru Funtuwa Binta · RAYUWAR SUBAI'AH Part 1

*KATA'I*

             *Part   1*

*FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA*

DASHEN ALLAH WRITES ASSOCIATION 

   Zaune take tana ninke kayan makarantar ƙannan ta da suka taso yanzun bada jimawa ba.

      Subai'ah ce ta shigo đakin tare da fađin "Kinganni na shigo yanzun ko? Daga tasowa makaranta, nazo kiyimin turi, wane littafi- da wane littafi gareki? Allah dai yasa kinada masu zafi na soyayya."

     Asiya ta ce  "Ɗazun na samo wani littafi mai ban Al-ajabi, idan kina karanta shi saikin ƙosa kiji ci gaban shi."

     Subai'ah ta ce  "Ni duk ba wannan ba, a kwai zazzafar soyayya da rayuwar Aure a ciki? Kinsan nifa bana so ina karanta littafi inji salaf! Nafi so inji ana love ana romantic, inji rayuwar Aure faca-faca a ciki, haba! Ai shine labari."

     Asiya ta ce  "Allah ya shirye ki Subai'ah, ke ba matar Aure ba, amma ki zauna kina karanta labarin dazai tada maki hankali, kuma kina sane marubutan ma har kashedi sukeyi da kada ƴan mata su karanta masu littafi, amma ke baki jin magana, Allah ya shirye ki, su dai marubutan sun fita haƙƙin ki, tunda sunce kada ki karanta."

      "Attakbiiir!! Kin gama wa'azin, ai ni har so nake inga marubuciya tayi kashedin kada ƴan mata su karanta mata littafi, to ni irin shi nake nema, don inji uban me aka rubuta da ba'a so mu sani, in gorin Aure ne ai dai muma zamuyi ehee! Don haka gara in sani, kada inje ma mujina ina gidadanci💃. Don Allah Asiya turamin littafin sauri nake, ina so inje infara shirya kaya na gobe zamuje Abujaa."

  Tana maganar tana rawa da jikin ta.

     Asiya ta ce  "Wai tafiyar tazo kenan? "

      Subai'ah ta ce  "Can zamuyi futu, sati uku zamuyi, daga ni sai Sa'iha zamu, tura min novel ɗin in samu abokin fira a can."

🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷

         Alhaji Ahmad yana zaune ne a garin Abuja, da Matar shi H-Karima,  'ƴa'ƴan shi biyu,  NAZIR  da  TA'IBA,  Nazir saurayi ne kyakykyawa son ko wace mace, fari ne tas! Dashi, yanada tsawo dai-dai misali, ga faffađan ƙirji wanda sas-san-tsan baƙin gashi yake kwance liya-liya akan ƙirjin shi,  kamar yadda gashin kanshi ma ya kasance baƙiƙƙirin mai santsi da walƙiya, fuskar shi a cike take, ma'ana, shi mutum ne mai faɗin fuska, ga wani saje da yayi mai kwalliya a fuskar shi,  wanda jin daɗi da hutu suka ratsa ilahirin jikin shi, shi ɗin zai kai kimanin shekara Ashirin da bakwai. 

       Ta'iba kuwa zata kai shekara goma sha biyar. 

     Alhaji Ahmad su biyu ne iyayen su suka haifa daga shi sai Alhaji Aliyu. 

   Shi Alhaji Aliyu yana zaune ne a katsina, shima  'ya'ya biyu gare shi, SUBAI'AH da  SA'IHA.

    Ranar Juma'a su Subai'ah ka suka je Abuja, gidan Alhaji Ahmad  (yayan baban su kenan)

     An tarbe su cikin kulawa da jin daɗi sosai, domin kuwa nan ma gidan su ne.

    Suna zaune a falo su uku, Subai'ah, Sa'iha da Ta'iba, fira sukeyi sosai na 'yan uwantaka.

     Nazir ya shigo falon riƙe da makullin mota a hannun shi, da alama shigowarshi kenan gidan, cikin dariyar shi mai ƙarama fuskarshi tsananin kyawu, ya ce   "Baƙin sun iso kenan, sannun ku......

Fatima Dahiru Funtuwa Binta✍️

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol