Free chapter · Read without an account
THE WARMTH OF YOU
ZAYD ARMAAN
CHAPTER 121
THE WARMTH OF YOU
JIDDAAH BARKUM
——-
Bayan sun gama gaisawa, Zayd ya miƙe. Ya juyo gare ta, sannan ya miƙa mata hannu. Raihana ta ɗora nata hannun a cikin nasa, ya taimaka mata ta miƙe tsaye.
Gaba ɗaya kunya ta mamaye ta. Wlh ba ta saba da wannan sabon yanayin nasa ba. Duk lokacin da yake ƙoƙarin kusantarta, sai ta ji kamar ba ita ba ce. Ta kasa ɗaga idanunta ta kalle shi, sai dai ta tsaya tana kallon ƙasa. Zayd ya ɗan kalleta na wasu seconds, kafin ya kai hannunsa kan gefen hijab ɗinta. A hankali ya fara cire mata shi, yana kallon fuskarta wadda ta ƙi ɗago kai ta kalle shi.
Zuciyar Raihana kuwa ta fara bugawa da sauri. Ta ji yadda yake cire hijab ɗin a hankali, har sai da ya gama ya ajiye shi a kan sofa. Bai ce komai ba. Ya sake matsowa kusa da ita, ya zura hannunsa ɗaya a kugunta ya janyo ta zuwa jikinsa, har jikinsu ya haɗu. Dayan hannunsa kuma ya kai shi bayan wuyanta, ƙarƙashin dogon gashinta da ya zubo a bayanta. Ya fara shafa wuyanta a hankali, yatsunsa suna motsi cikin natsuwa. Yana kallonta a kokarinsa na son su hada idanu Amma Raihana ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, tana jin wani irin yanayi da ba ta iya fassarawa. Numfashinta ya sauya, yayin da zuciyarta ke bugawa kamar za ta fito.
Zayd ya sunkuyo kaɗan, ya kawo bakinsa kusa da kunnenta. Muryarsa ta fito ƙasa-ƙasa, kamar rada. "Now, go and sleep, Habibti." Raihana ta ji wani abu ya ratsa jikinta saboda yadda ya furta kalmar. Ta buɗe idanunta a hankali, amma har yanzu ta kasa kallonsa. Zayd ya ɗan murmusa, ya sake shafa bayan wuyanta. "Uhmmm… ki kwanta ko?" Ta haɗiye yawu, ta kasa amsa masa da baki sabida uban kusancin su sai kawai tayi nodding a hankali.
Zayd bai sake ta ba. A maimakon haka, sai kawai ta ji ya ɗaga ta sama ba tare da ta ankara ba. Cikin firgici, Raihana ta nade hannayenta a wuyansa, ta kankame shi sosai saboda tsoro. Shi kuwa ko gezau bai yi ba, ya nufi gadon kai tsaye yana ɗauke da ita. A hankali ya kwantar da ita a kan gadon, amma bai miƙe ba. Ya tsaya a kanta, hannayensa biyu a tokare a gefen jikinta, yana kallonta.
Idanun Raihana a lumshe suke. Ganin yadda ya yi mata rumfa, bai kuma yi alamar tashi ba, sai gabanta ya fara faɗuwa. Zuciyarta ta ƙara bugawa da sauri, har ta ji kamar yana iya jin bugun nata. Zayd kuwa yana kallonta da waɗancan idanunsa masu zurfin kallo. Ya ɗan yi shiru, sannan a hankali ya miƙa hannu ya janyo duvet ɗin da ke ya saman kanta, ya ɗaga shi sama. Ya rufe ta da shi daga wuyanta har jikinta, kafin daga bisani ya ɗago daga rankwafawar da ya yi ya gyara bargon a kanta.
Da ta fahimci ba ya kan ta, kuma abin da ta ji kawai shi ne saukar bargon a jikinta, sai ta sauke numfashin da ta riƙe tun ɗazu. Ta sake lumshe idanunta, tana ƙoƙarin kwantar da hankalinta. Zayd ya sunkuyo a hankali, ya yi pecking goshinta sannan ya dawo da bakinsa ya yi daidai da kunnenta. Muryarsa ta sauka ƙasa-ƙasa, cikin wani irin rada mai taushi. "Close your eyes well and sleep, Habibti…" Ya ɗan dakata, sannan ya ƙara da wata murya can kasa wadda ita kadai zata ji ta. "Dream of us..."
Raihana ta ɗan motsa a ƙarƙashin bargon. Idanunta a rufe suke, amma ta haɗiye yawu, ta kasa cewa komai. Kalaman nasa sun isa su ƙara rikita mata tunani. Zayd ya ɗan tsaya yana kallonta na wasu seconds, sannan a hankali ya miƙe tsaye. Ya tsaya for some seconds yana kallonta, sai kuma ya juya ya fara tafiya zuwa ƙofa. Sai da ya fice daga ɗakin sannan Raihana ta buɗe idanunta a hankali. Ta bi hanyar da ya bi da kallo, kafin ta ɗora hannayenta biyu a kan kirjinta. Zuciyarta kuwa? Wani irin mahaukacin bugo kawai take yi. Ta lumshe idanunta ta sake buɗewa, kamar tana ƙoƙarin tabbatar wa kanta cewa abin da ya faru ɗin gaskiya ne. "Ya Allah…" Ta raɗa a hankali, tana ƙara jan bargon jikinta ta kankame.
Daga nan Zayd ya nufi ɓangaren Seeyama. Har zuwa lokacin da ya isa ɗakinta, ya same ta a zaune a kan sofa, ta jingina da bayanta, idanunta a lumshe kamar wadda ta daɗe tana jiran wani abu. Da ya shigo, sai ya ɗan tsaya a bakin ƙofar yana kallonta. Ganin yadda take zaune a wannan lokacin ya ɗan ba shi mamaki. This was very unusual of her, musamman bayan sallar Asuba. Yawanci idan ya shigo, yana samun ta har ta koma bacci.
Seeyama kuwa ta buɗe idanunta da jin motsinsa. Da ta ɗago ta gan shi, sai ta fara kallonsa from head to toe. Zuciyarta ta fara bugawa da sauri. Maybe he spent the night with her? Shin wannan ne dalilin da ya sa ya makara zuwa sallar Asuba? Ashe ya can yana lailayata Wannan tunanin ne ya fara cin kanta. Wani abu ya taso daga ƙasan zuciyarta ya tsaya a maƙogwaronta, har ta ji kamar yawun bakinta ba zai iya wucewa ba. Ta yi ƙoƙarin danne tunanin, but she couldn’t help it.
Zayd kuwa yana kallonta cikin natsuwa. "Ba ki koma bacci ba?" A hankali ta gyada masa kai. Ya ɗan kalleta, sannan ya ƙarasa ya zauna a gefen gadonta, yana fuskantar ta. "Lafiya?" Seeyama ta ji wani irin abu yana tokare mata maƙogwaro. Hawaye suka fara taruwa a idanunta, amma ta ƙi kallonsa. Ta juya fuskarta gefe, sannan ta amsa cikin rawar murya. "Bakomai…" Zayd ya yi shiru yana kallonta. He knew something was wrong, but he wasn’t going to force her to talk.
Bayan ɗan lokaci, sai ya miƙe ya ƙarasa inda take zaune. Ya tsaya a gabanta, sannan ya miƙa mata hannu. Seeyama ta zuba wa hannunsa ido kawai. A cikin ranta kuwa, abubuwa da dama ne ke gauraye. Kishin sa, soyayyar sa, tsoro da kuma wani irin zafin da ita kanta ba ta san sunansa ba. Tana son kasancewar sa a kusa da ita, amma a lokaci guda tunanin inda ya kwana yana cin zuciyarta. Ganin yadda ta ƙi ɗaga hannunta, kuma kamar ba ta cikin duniyar da yake, Zayd ya sake magana cikin sanyin muryarsa. "Come here." Ya ci gaba da miƙa mata hannunsa.
A hankali Seeyama ta ɗago, ta ɗora nata hannun a cikin nasa. Zayd ya kama hannunta ya mikar da ita a hankali ya janyo ta zuwa jikinsa, sannan ya rungumeta. Ya ɗora hannunsa a bayanta yana shafa mata a hankali. A wannan lokacin ne hawayen da take ƙoƙarin riƙewa suka fara zubowa. Ba ta san lokacin da ta fara kuka sosai ba. Ta ƙara matse jikinta a nasa, tana ƙoƙarin ɓoye fuskarta a ƙirjinsa. Zayd ya ɗan sauke numfashi, ya ci gaba da shafa bayanta a hankali. "What’s wrong…?" Amma maimakon ta amsa, sai kukan nata ya ƙara ƙarfi. Shi kuwa ya tsaya yana riƙe da ita, ya yi yana jin kukan nata.
Sai da kukan ya tsagaita sannan a hankali ya janye ta daga jikinsa, ya ɗan sunkuya yana kallon fuskarta. "What happened?" Seeyama ta share hawayenta da bayan hannunta, tana ƙoƙarin kakalo murmushi a fuskarta. A hankali ta ce, "Nothing… I just missed you." Zayd ya yi shiru yana kallonta. Fuskarsa ba ta nuna wani abu sosai ba, kamar ba zai ce komai ba. Sai dai bayan wasu seconds ya sake magana. "Is that the reason da kika zauna haka cikin damuwa?" Ta girgiza kai a hankali, sannan ta ɗan ɗago idanunta ta kalle shi. "Na saba da kai a cikin waɗannan kwanaki bakwai ɗin nan. Ko da ba za ka kula ni ba, at least ina jin motsinka. Amma yau… na tashi ban gan ka ba."
Zayd ya ɗan yi murmushi, irin nasa murmushin mai sauƙi. Ya ɗaga hannu ya shafa fuskarta a hankali. Bayan haka sai ya kama ta, ya kai ta har kan gadon, ya kwantar da ita sannan ya janyo duvet ya rufe ta. "Close your eyes and sleep." A hankali Seeyama ta gyada kai. "Good girl," ya faɗa yana kallonta. Ya miƙe tsaye, ya juya da niyyar fita. Amma kafin ya kai ƙofa sai ya ji muryarta. "Zan je wajen Mommy anjima." Zayd ya tsaya cak. Bayan ɗan lokaci sai ya juyo a hankali ya kalleta. "Me ake yi a can?" Seeyama ta kalle shi, tana tunanin abin da za ta faɗa. Ta ɗan yi shiru kafin ta ce, "Ba komai… akan Rabi ne." Zayd ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya gyada kai. "It’s fine. Allah ya kaimu." Ta jinjina masa kai, ba tare da ta ƙara cewa komai ba. Zayd ya juya ya fice daga ɗakin, sannan ya janyo ƙofar a hankali. Seeyama ta ci gaba da kallon ƙofar bayan ya fita, murmushin da ta yi masa tun farko ya ɓace daga fuskarta. Wasu sabbin hawayen suka maye gurbinsa.
Bintu ta ɗago kanta a hankali ta dubi Mama Sabuwa, fuskarta ɗauke da damuwa. Ta ɗan yi shiru kafin ta buɗe baki. "Mama…" "Na’am, Bintu?" "Ina so na je taron nan." Ta faɗa cikin damuwa, tana kallon Mama Sabuwa kamar tana neman mafita daga gare ta. "Kin ga dai abin da na samu a wancan zuwan. Kuma taron nan every three months ake yin sa. Gashi kuma yadda Baffa ya sa ido a kaina yanzu. Kina ganin zai bar ni na je ne?" Ta ɗan matsa kusa da ita, ta ci gaba da magana cikin sanyin murya. "Don Allah, Mama, ki haɗa min wani wayon da ba zai sa ya zargi komai ba. I need to attend this one, gaskiya ina son zuwa."
Mama Sabuwa ta kalleta, sai ta ɗan murmusa kamar wadda tuni ta fahimci damuwar da ke damun Bintu. "Ke dai ki kwantar da hankalinki. Kada ki damu da komai." Bintu ta ɗan zaro ido. "Amma Mama, Baffa fa…" Mama Sabuwa ta katse ta cikin natsuwa. "Na ce ki bar komai a hannuna. Mace ce ni fa, Bintu. Kin san irin waɗannan abubuwan ba sabon abu ba ne a wurina. Zan san abin da zan yi, kuma zan tsara yadda za ki samu damar zuwa ba tare da ya fara zargin wani abu ba." Bintu ta sauke ajiyar zuciya, duk da cewa har yanzu akwai ɗan fargaba a fuskarta. "Allah dai ya sa a dace, Mama." "Amin. Ke dai ki kwantar da hankalinki. Ki bar maganar a kaina." "Toh, yanzu ga shi ina so na je na karɓo dinkuna na. Na san dai zuwa yanzu Baffa ya yi nisa da unguwar nan yanzu. Mama, ko da zai dawo, ki ce masa kawai Anty Safiya ce ta kirani a waya, bata jin daɗi. Na je na kula da yaranta, na musu girki ma." Mama Sabuwa ta ɗan gyara zamanta, tana kallon Bintu. "Ba komai. Tashi ki shirya, ki yi tafiyarki. Idan za ki dawo, wannan furar mai kwakwa ki taho min da ita. Kwana biyu ban samu na sha ba." Bintu ta fashe da dariya tana miƙewa. "Mama, kin saba da daɗi kamar ba tsohuwa ba!" Mama Sabuwa ta ɗaga mata gira. "A gidan uban wa na tsufa? Nawa nake gaba ɗaya?" Bintu dai dariya kawai ta yi, ta juya ta shige ɗaki domin ta shirya.
Bayan ta shiga ɗaki ta shirya cikin sauri. Ta zaɓi wata atamfa mai kyau, ta yi ɗan gyaran fuska sannan ta ɗauki jakarta. Bayan ta gama, ta fito ta yi sallama da Mama Sabuwa, wadda ta sake tunatar da ita batun furar kwakwa kafin ta tafi. Bintu ta yi dariya, ta ce, "To Mama, zan taho miki da ita," sannan ta fice daga gidan. Ta nufi gidan Hajiya Hauwa kai tsaye.
Da isarta, ta yi sallama a ƙofar gidan. Ba a ɗauki lokaci ba aka buɗe mata, ta shiga tana murmushi. Hajiya Hauwa na zaune a babban falonta lokacin da ta ji sallamar Bintu. Da ta ɗago ta gan ta, nan take fuskarta ta washe da fara’a. "Babygirl…!" Ta miƙe tsaye tana faɗin, "Daughter! I miss you!" Bintu ta ƙarasa gare ta, Hajiya Hauwa ta buɗe hannayenta ta rungumeta sosai. "Kawai sai kika ɓace kamar ba kya duniya!" Bintu ta yi dariya tana ƙara rungume ta. "Mommyyy!" Ta ja maganar cikin shagwaɓa. "Kin san Baffa na yanzu idanunsa a kaina suke. Duk na takura, wallahi. Kamar ba ni da ’yancin yin komai."
Hajiya Hauwa ta ɗan ja ta baya tana kallon fuskarta, sannan ta shafa kumatunta. "Ah-ah, my baby. Har kin fara korafi kenan? Zo ki zauna." Ta riƙe hannun Bintu ta kai ta kan kujera, sannan ta zauna kusa da ita. "Look at you, you’ve been missed. Kin yi kyau sosai, sweetheart." Bintu ta yi murmushi, ta jingina da kafadar hajiya hauwa. "Mommy, ai kin san yadda nake cikin abubuwa. Kuma Baffa yanzu ya zama kamar security guard dina. Duk inda zan je sai ya san inda zan je da wanda zan gani." Hajiya Hauwa ta yi murmushi tana kallonta. "Don’t worry, my baby. Kina da ni fa. Yanzu ki gaya min, me ke damunki?" Bintu ta ɗan yi shiru, sannan ta fara magana cikin shagwaɓa. "Mommy, gaskiya na gaji. Kullum sai an sa ido a kaina. Even going out has become a problem." Hajiya Hauwa ta kama hannunta tana shafawa a hankali. "Poor baby. Kin sha zaman gida kenan. Ai da kin zo da wuri, da na rage miki wannan damuwar." Bintu ta yi dariya. "Mommy, kin saba da pampering dina ne." "Of course! Ai ke baby girl ɗina ce anything for you darling"
Hajiya Hauwa ta sake kallonta cikin murmushi, sannan ta tambaye ta me take so ta ci. Bintu ta ce ba ta ma tsaya cin komai ba saboda ta yi sauri ta fito, sai Hajiya Hauwa ta kira mai aikinta ta ce a kawo musu abin da Bintu take so. Bayan sun gama cin abinci, Hajiya Hauwa ta jingina da kujerarta tana kallon Bintu wadda ke goge bakinta da tissue. "Babygirl…" Bintu ta ɗago ta kalleta. "Yes, Mommy?" Hajiya Hauwa ta murmusa. "You need to take a shower. Ki ɗan huta, kin yi tafiya. Ko massage na yi miki? Yaushe rabonki da ki zo mu yi irin wannan?" Bintu ta yi dariya tana girgiza kai. "Mommy, you love me so bad. Ai ba sai kin wahalar da kanki ba." "Wace wahala kuma? Is that too much to ask? Ke dai ki tashi ki je ki freshen up. Zan sa a shirya miki wajen hutawa right away." Bintu ta shagwaɓe fuska tana kallonta. "Toh, amma fa ba zan daɗe ba. Sabida a yanda na samu na fito daga gıdan nan" Hajiya Hauwa ta ɗan yi murmushi. "Forget about everything for now. Just relax, my baby. You deserve to be pampered." Ta miƙe ta nufi toilet ta hada nata ruwan wanka…