Free chapter 路 Read without an account

KOGON SIRRI

by Khadija Haruna 路 Masarauta


  
馃挄馃挄馃挄馃挄

bismillahir rahamanirrahim 




Daren ya yi tsit. A waje an yi shiru. An tafi da Zayd.

Amal na cikin kogo, tana rawar sanyi. Duk jikinta kasa ce. Kuka take yi amma ba ta da sauti.

Zayd. An tafi da Zayd.

Ta fito a hankali daga kogon. Babu kowa a dajin. Fitilu sun bace. An tafi.

Ta yi kokarin gudu, amma kafarta ta ci karo da wani abu. Abu ne mai tauri a kasa.

Ta sunkuya ta duba. Wani tsohon akwati ne, an rufe shi da yashi. Kogon nan ba sabon wuri bane. Kamar wani ya taba boye wani abu a nan.

Ta bude akwatun da hannu mai rawa.

A ciki, ba zinari bane. Ba kudi bane.

Takardu ne. Takardu da yawa, da wata tambari da ta sani sosai. Tambarin Sarautar Masarautar Dausayi. Tambarin mahaifinta Sarki.

Ta dauki takarda daya, ta karanta da hasken wata.

Idanunta suka bude da mamaki. Hannunta ya fara rawa.

Wannan... wannan wasikar Mahaifina ne?

A cikin takardar an rubuta:

_Ni Sarki Usman na Dausayi, na amince na sayar da kasar dajin Dausayi ga Larabawa masu hakar zinari, don a bani zinari guda dubu. Kuma na amince na ba su damar amfani da mutanen kauye a matsayin bayi._

Amal ta rufe bakinta.

Mahaifinta. Sarki adali da take alfahari da shi. Ya sayar da mutanenta. Ya sayar da Zayd. Ya sayar da kauyen Zayd baki daya don zinari.

Sai ta ga wata takarda ta biyu. Sunan da ke kanta ya sa jini ya daskare a jikinta.

_Wanda ya shaida wannan ciniki: Yarima Faisal Dan Sarki Ibrahim na Masarautar Makwabta._

Faisal. Ba dan uwanta bane. Ba yarima na Dausayi bane. Shi dan sarautar makwafta ne da aka turo shi don ya yi leken asiri. Kuma shi ne ya shirya siyar da mutanen Dausayi.

Kuma gobe da safe, Larabawan za su iso su kwashe mutane.

Zayd. Kauyen Zayd.

A waje, wata muryar ta ji.

Gimbiya? Muryar wata mata. Zulaiha.

Amal ta juyo. Zulaiha baiwar ta ce, tsaye da fitila a hannu, fuskarta cike da hawaye.

Gimbiya na neman ki tun dazu. Sun kama Zayd. Suna shirin yanke masa kai gobe da safe a kasuwa don kowa ya gani. Sun ce ya yi kokarin kashe ki.

A'a! Karya ne!

Amal ta mike, takardun a hannunta.

Zulaiha, Zayd bai yi laifi ba. Mahaifina ne mai laifi. Duba abin da na gani.

Zulaiha ta duba takardun. Ta firgita.

Wayyo Allah! Idan Sarki ya san kin ga wannan takardar, zai kashe ki ma!

Amal ta matse takardun a kirijinta.

Bari ya kashe ni. Amma ba zan bar su su kashe Zayd ba, su kuma sayar da mutanena ba.

Ta kalli Zulaiha.

Zulaiha, ina bukatar taimakonki. Yaushe za su kashe Zayd?

Gobe da safe. Karfe bakwai. A idanun kowa.

Amal ta kalli duhu. Gobe karfe bakwai. Saura sa'o'i shida kacal.

A cikin sa'o'i shida din nan, dole ta ceci Zayd, ta ceci kauyensa, ta kuma fallasa babban sirrin da zai ruguje Masarautar Dausayi baki daya.

Amma ta yaya yarinya daya, a tsakiyar daji, da takardu biyu kacal, za ta iya dakatar da rundunar Larabawa da Yarima Faisal mai makirci?

Dare ya yi nisa. Kuma dawakan Larabawa sun fara shigowa Dausayi...

by Cutie 

---


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol