Free chapter 路 Read without an account
RAUDAH
by Khadija Haruna 路 RAUDAH
馃挄馃挄馃挄馃挄馃挄
bismillahir rahamanirrahim
---
*BOOK 1: RAUDAH - 'YAR MARARABA*
Raudah bata taba mafarkin University ba.
'Yar Mararaba ce. Mararaba da Abuja kamar sama da kasa. Gidan su daki daya ne. Mama mai soya kosai a gefen titi, Baba mai tuka keke napep, kafarsa daya ba ta da karfi sosai.
Amma Allah ya bata kwakwalwa.
JAMB - 387. Ta daya a Abuja duka.
Royal Haven University - University mafi tsada a Nigeria, 8 Million a shekara - ta bata scholarship 100%. University da 'ya'yan Sarakuna, Ministoci, da Attajirai kadai suke karatu. A Asokoro, cikin Abuja.
Litinin na farko.
Raudah ta sanya atamfarta mai launi da hijabinta pink, jakar Ghana-must-go, takalmin roba mai rahusa. Ta hau bus din Mararaba zuwa Asokoro, hannunta na rawa.
Gate din Royal Haven University ya girgiza ta. Babban gate na zinare, tsaro da uniform. Motoci - G-Wagon, Benz, Range Rover. Dalibai da kaya masu tsada, wayoyi iPhone 15 Pro Max.
Ta shiga 100 Level Business Administration.
Aji ya yi kyau kamar otal. AC na kadawa.
A ciki akwai mutane biyu da kowa ya sani.
*SULTAN* - 21 years. Dan Alhaji Sadiq mai kamfanin mai. bashida mutumci izza da gadara da jinkai mai kudin da ba a iya lissafawa.
*AHMAD* - 22 years. Cousin din Sultan. Babansa Ministan Kudi, Kakansa Sarki. Dogon gaske, fari tas kamar Larabawa, fuska mai haske, gemu kadan, idanu manya masu sanyi. Ya sanya farin kaftan mai zane na zinare. Baya magana da yawa. Amma kowa ya san shi ne mafi kyau a University duka - ya fi Sultan kyau da hankali, da mutunci. Kyan da Allah ya halitta, ba na kudi ba.
Kofa ta bude.
Raudah ta shigo da kunya, jakar ta na hannu.
Aji ya yi shiru, sannan aka yi dariya.
"Wayyo Allah! 'Yar aikin gida ce ta bace? Wannan jakar Ghana-must-go fa a Royal Haven?"
Sultan ya yi dariya da karfi, ya jingina a kujera.
"Ke 'yar Mararaba, anan Royal Haven University ne ba kasuwar Mararaba ba. Kina da laptop? Ko da wayar ki mai maballi kika zo da ita?"
Aji ya fashe da dariya.
Raudah ta tsaya a bakin kofa, hawaye na taruwa a idanunta. Ta ji duniya na juyawa.
Ahmad ne kadai bai yi dariya ba.
Ya dago daga laptop dinsa na MacBook. Idanunsa masu sanyi suka hau kan Sultan, sannan suka sauka kan Raudah.
"Zauna," ya ce mata da murya mai sanyi da iko da ta cika aji.
Ya nuna kujerar da ke gabansa. Kujerar da babu wata yarinya da ta taba gigin zama agun saboda bayasqn surutu bame zama kusa dashi .
Raudah ta je ta zauna tana rawa, zuciyarta na bugawa kamar ganga.
Sultan ya fusata. Ya mike.
Ahmad, wannan 'yar talaka ce. Ka manta alkawarin mu? Ba ma fada akan mace. Kuma ita ba ajin mu bace."
Ahmad ya kalle shi
"Wannan yarinyar ta fi kowa a nan cancanta," ya ce, muryarsa na isar kowa. "Ta shigo da kwakwalwarta, ba da kudin baban ta ba. Kamar yadda wasu suka shigo da kudin baban su kawai."
Kalmar ta sami Sultan kamar mari. Duk aji ya yi shiru. Kowa ya san Sultan ya shigo da kudin baban sa ne, ba kwakwalwarsa ba.
Duk idanu sun koma kan Raudah da Ahmad.
Raudah ta juyo ta kalli Ahmad. A karo na farko, ta kalli fuskar da ta fi kowa kyau da ta taba gani a rayuwarta - kyan Yarima mai daraja da mutunci.
Ahmad ya kalle ta, ya gyada kai kadan, ya ce da sanyi:
"Welcome to Royal Haven University. Idan wani ya ci mutuncin ki, ki fada min. Kar ki ji tsoro. Kina tare da ni."
Sultan ya damke hannunsa, kishi da fushi sun cika kirjinsa. Ya kalli Raudah - 'yar talaka da atamfa da hijabi pink - amma wacce ta sa aka nuna a gaban kowa cewa Ahmad ya fi shi kyau, da daraja, da karfin zuciya.
Raudah ba ta san cewa ta shiga tsakiyar yakin sarauta ba. Yakin cousins biyu na Asokoro. Yakin da sanadinsa ita ce - 'yar Mararaba mai scholarship.
*KARSHEN BABI NA DAYA*
by Cutie