Free chapter · Read without an account

JAHILCI YAFI HAUKA

by Zainab Bello · JAHILCI YAFI HAUKA

Page 3

************

Wani lafiyayyen katafaren company ne, wanda ko wucewa kazoyi kasan mamallakinsa yaci ya tada kai, especially idan ka shiga cikinsa, to kuwa da wuya idan baka rude ba duk wayewarka kuwa.

A hankali Khalid ya qarasa fitowa daga cikin dunkulalliyar motarsa, cikin takun qasaita yake jefa qafafunsa kmr baya son tafiyar har ya kaiga elevator, seven floor nan ne inda katafaren office dinsa yake, yana shiga yabi ko ina da kallo kmr mai qoqarin tantance wani abu, sai kuma yayi  qaramin tsaki gami da qarasawa kan kujerar da take girke cikin office din.
  
A hankli ya kifa kansa kan table din yana lumshe hazel eyes dinsa wadanda suke bayyana gajiya gami da kasala, a hnkli akayi Knocking kofar ba tare da ya dago ba, ya bayar da umarnin shigowa, secretary dinsa ce mai suna Jennie ta shigo, cikin shigar qananan kaya, tana ta faman karairaya, kan table din ta ajiye files din hannunta gami da qarasawa inda yake.

 "Good morning my love" ta fada tana qoqarin kai hannunta wanda yaji fixed nails saman kanshi.

A kasale ya dago gami da fadin "morning".
 
Jennie ganin bai disgata ba, ta qara gyara zaman boobs dinta wadanda suke leqowa ta saman yar bingilar rigar jikinta, wacce take tamkar idan anyi qwaqqwaran motsi zata yage, ta qara matsowa tana fadin " are you alright sir"?

Fincikota yayi sai gata kan cinyarsa, dare-dare, ba tare da bata lokaci ba ta lalubi soft lips dinsa ta fara bashi wani azababben romance. Khalid cikin fitar hayyaci ya hau biye mata, can dai kamar an doki kansa ya wani irin tureta sai gata a qasa.

"Get away and never come close to me, you are fired"!  ya fada cikin wani irin bacin rai mara misaltuwa.

A fujajan Jennie ta miqe tana fadin " so sorry sir, its just a mistake" ta fada hawaye na qoqarin gangarowa kan cheeks dinta.

" kije account section ayi settling dinki, you are fired bitch, and idan kin fita please don't forget to close the door" ya qarasa fada yana kwanciya kan rest chair dake office din.

Jennie jiki a sanyaye ta miqe tana sharar qwallah, ta fice daga office din zuciyarta cike da alwashi iri-iri.

Khalid kuwa barci ne mai nauyi yayi gaba dashi nan kan kujerar, bai farka ba sai 12 kamar ba wanda yazo aiki ba, kai tsaye ya fada rest room, yayi uzurinsa ya fito ya koma kan kujerarsa gami da janyo computer dinsa ya fara aiki, ba jimawa ya fara yamutsa fuska alamar akwai abinda yake damunsa, ba tare da bata lokaci ba daga landline din dake office din cikin husky voice dinsa ya furta " to my office".

Ba jimawa kuwa sai ga knocking, wannan karonma ba tare da ya motsa ba ya bayar da umarnin shigowa, Mus'ab wanda ke riqe da muqamin Director, matashi wanda a haife zasuyi age mates da Khalid din yana sanye cikin lafiyayyen suit ne ya shigo, " yau kuma kaga damar zuwa aiki knan momma's boy".

Khalid ya dan yamutsa kyakkyawar fuskarsa gami da dafe cikinsa, ba tare da ya kula maganarsa ta farko ba, yace " buddy am starving".

Baki ya saki yana kallonsa, ba don ya san waye Khalid ba, don kuwa cousins suke, da wallahi cewa zaiyi dan daudu ne, don kuwa komai a kasale a yangace yake yinsa, ga shegiyar shagwaba tamkar wani dan yaye,

Murmushi ya danyi gami da fadin " Oya eat me up, tunda a duniya bayan Maama babu wanda ka raina sai ni, tuzurun banza kayi aure ka tsaya rigima da wasa da hankalin yaran mutane".

Wannan karon shima Khalid murmushin yayi wanda ya bayyana dimple dinsa dake bangaren hagu, yace " next time babe dinka zanyi snatching idan ba ka daina mocking dina ba, and thank God naga tana da kayan alatu za'a huta da ita". 

"What"!!!  Mus'ab ya fada yana zaro ido cikin kaduwa da jin kalamansa, Allah na gani yana matuqar jin tsoron Khalid akan mata, don kuwa da wuya ya taya ba'a sallama masa ba.
 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol