Free chapter · Read without an account
THREE TURNS OF FATE
ZAYD ARMAAN
CHAPTER 126
THREE TURNS OF FATE
JIDDAAH BARKUM
———
Seeyama ta tsaya cak, idanunta a kan fuskar bokan. Ta kasa ko motsawa, kamar kalamansa sun yi mata nauyi fiye da yadda take tsammani. Ta buɗe baki kamar za ta yi magana, amma babu wata kalma da ta iya furtawa. Bokan ya ɗan gyara zamansa, ya zuba mata ido na wasu seconds kafin ya sake magana. "Dama waɗanda suka faɗi sharadin aikin nan naki ba ni ba ne. Ni dai an kawo min ne kawai, aka sanar da ni abin da ake buƙata. Amma me kika ce a lokacin? Kin amince da kin tuna abinda kika fada?" Seeyama ta haɗiye yawu, ta ɗan kalli Safina, sannan ta mayar da idanunta kan bokan. Bai jira ta ba shi amsa ba. Ya ɗan yi murmushi, kafin ya ci gaba. "To, yanzu akwai abu guda da ya kamata ki sani. Daga cikin waɗanda suka saka hannunsu a cikin wannan al'amari, akwai wanda ba zai taɓa bari mijinki ya karɓi budurcinki ba. Ko da kuwa meye zai faru, ba zai bari hakan ta faru ba." Ya ɗan dakata, yana kallon yadda fuskar Seeyama ta fara sauyawa. "Amma abin da ya fi komai muni shi ne, wanda ya fara kyallawa tun farko, shi ne yake son ya karɓi wannan abu da kansa." Seeyama ta zaro ido kaɗan. "What?" ta furta a hankali. Bokan ya ɗaga kafaɗunsa, kamar shi kansa bai san yadda zai warware lamarin ba. "Ni ma gaskiya ban san yadda zan hana shi ba. Domin tun farko ba ni ne na bayar da wannan sharadin ba, kuma ba ni ne na zaɓi wanda zai karɓi abin ba. An riga an tsara komai tun kafin a kawo aikin nan gare ni." Safina ta kalli Seeyama, sannan ta mayar da kallonta kan bokan. "Wait… kana nufin akwai wani aljani da yake son ya kusanci Seeyama?" Bokan ya ɗan juya kansa ya kalle ta, kafin ya mayar da kallonsa kan Seeyama. "Ba wai yana so kawai ba ne. A ganinsa, wannan haƙƙinsa ne tun da ta Riga ta zo nan." Ya sake yin wata ƙaramar dariya, sannan ya jingina da bango. "Yanzu kin fara fahimtar abin da kika jawo wa kanki kuwa, Seeyama?" Seeyama ta girgiza kai da sauri, fuskar ta cika da alamun rashin yarda. "Amma ai ba wani abu na ce ba! Kawai na ce ba zan yarda kowa ya kusance ni ba sai mijina. To, meye laifina a maganata?" Bokan ya ɗago kansa ya zuba mata ido, kafin ya ce cikin sanyin murya, "Ba abinda ki ka faɗa ba ne laifinki, Seeyama. A yanda kika faɗa ne laifin."
Safina, wadda tun ɗazu take kallon su ba tare da ta ce komai ba, ta kasa daurewa. Ta matsa kaɗan gaba, tana kallon bokan cikin yanayin roƙo. "Dan Allah, me za mu yi yanzu? A taimaka mana, maigida. A basu haƙuri idan akwai wani abu da suke buƙata, ko kuma wani abu da ya kamata mu yi domin a warware wannan matsalar, muna shirye. Amma dan Allah, su yi haƙuri. Seeyama fa ba ta san abin da ta shiga ba Kenan." Bokan ya mayar da kallonsa kan Seeyama, ya ɗan zuba mata ido kafin ya ce, "Shi ya sa ake cewa ka iya bakinka. Ba kowa ba ne za ki riƙa yi wa magana yadda kika ga dama. Ba kowa ba ne za ki nuna wa gadara, ko ki yi wa girman kai saboda dukiya da ƙarfin ikon da kike da shi. Yanzu wannan alfaharin da kike yi, ina ya kai ki? Ina wannan dukiya da ƙarfin ikon da kike takama da su suka kai ki a yau?" Seeyama ta yi shiru, tana kallon ƙasa. Zuciyarta cike take da nadama da dana-sani, amma ba a kan maganar da ta yi wa bokan ba. Nadamar da take ji ta fi haka zurfi. Tana nadamar abin da ya sa tun asali ta zo neman taimako wajen wani mashurki, alhali tana da Allahn da za ta iya roƙa, kuma tabbas zai amsa addu'arta. Ta tuna cewa duk wanda ya bar Allah, Allah zai bar shi. Duk wanda ya kauce wa koyarwar Manzon Allah, zai yi dana-sani. A hankali ta ɗago kai, ta kalli bokan cikin sanyin murya. "Ka yi haƙuri da yadda na yi maka magana. Allah Ya ba ku haƙuri." Daga haka ta ɗauki jakarta kawai ta miƙe. Bokan da Safina suka bita da kallo. Sun ɗauka za ta ruɗe, ko ta shiga tashin hankali, ko ta fashe da kuka tana roƙonsa ya rufa mata asiri, har ta kai ga yarda ta sadaukar da budurcinta, amma abin da ya faru ya ba su mamaki matuƙa. Babu ko ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan da ta yi.
A hankali Safina ta juya ta kalli bokan, sannan… cikin damuwa ta ce, "To, yanzu meye abin yi? Dan Allah, ka ba su haƙuri." Bokan ya girgiza kai a hankali. "Babu wani abu da zan iya yi." Safina ta yi shiru, ta rasa abin da za ta ce. Daga nan ta miƙe tsaye, ta ɗan risina cikin girmamawa. "Mungode." Bayan haka ta juya da sauri, ta bi bayan Seeyama wadda ta riga ta fita. Seeyama da Safina suna cikin motar Seeyama, tun bayan da suka bar gidan bokan ba su sake cewa komai ba. Shiru ne ya mamaye motar, Seeyama na tuƙi cikin nutsuwa, idanunta a kan titi. Sai da suka ɗan yi nisa kafin Safina ta kasa daurewa. "Seeyama, meyesa kıka taso kıka fito bayan kınsan Cewa we didn’t get any solution." Seeyama ba ta amsa nan take ba. Ta ci gaba da kallon gabanta, kamar ba ta ji abin da Safina ta faɗa ba. Sai bayan wasu seconds ta buɗe baki cikin sanyin murya. "Zan nemi mafita ne a wajen Wanda Ya halicce ni, da aljanu gabadayansu." Ta faɗi hakan ba tare da sauya yanayin fuskarta ba. Daga haka ta yi shiru, ta ci gaba da tuƙinta. Fuskarta a matuƙar nutsuwa take, nutsuwa ta sosai wacce safina bata taba gani ba. Babu alamun firgici ko damuwa a tattare da ita. Safina kuwa ta yi shiru kawai, tana kallonta. Ba ta ƙara cewa komai ba, sai dai ta kasa cire idanunta daga kan Seeyama, tana mamakin irin nutsuwar da ta gani a fuskarta bayan duk abin da suka ji a gidan bokan.
Hajiya Hauwa ta tsaya a corridor na wasu seconds, tana kallon hanyar da Seeyama ta bi. Ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta juya ta koma cikin ɗakin Bintu. Da ta shiga, ta tarar da Bintu har yanzu tana kwance a kan gadon, wayarta a hannunta. Ta ƙarasa kusa da ita, ta ɗauki jarkar da ta kawo, ta ajiye ta a gefen gadon. A dai-dai lokacin ne wayarta ta fara ringing. Ta janyo ta, ganin sunan wanda yake kiranta ya sa ta ɗan yi murmushi. Ta ɗaga wayar, ta kai ta kunnen ta. "Hello, Alhaji! How are you doing?" Ta ɗan saurara, tana murmushi. "Alhamdulillah, Alhaji. Ai ba za a ce maka komai ba." Ta sake yin shiru tana sauraron mutumin da ke ɗaya ɓangaren wayar. "Okay, sir. Ai gata ma, muna tare." Ta kalli Bintu a hankali, sannan ta sake magana. "Awww okay. Ka shigo garin kenan? Ahh, bakomai, babu matsala. Za ta iya zuwa. Ba dai kana guest house ɗin ba?" Ta ɗan yi dariya. "Ba damuwa, Alhaji. Za ta zo, In Sha Allah. Yauwa, to sai an jima." Ta kashe wayar, ta ajiye ta a kan bedside table, sannan ta juya zuwa ga Bintu wadda ta ɗago kanta tana kallonta. Hajiya Hauwa ta matsa kusa da ita, ta zauna sosai, sannan ta shafa hannunta. "Get ready, my dear. Kudi sun zo!" Bintu ta buɗe idanunta sosai. "Really, Mommy?" "Of course, baby!" Hajiya Hauwa ta amsa cikin murmushi. "Alhajin nan fa mugun sonki yake. Kin san dai ni ma ina kishinki, but that won’t stop me from making sure kin samu abin duniya. Ki tashi yanzu ki shirya. Zai aiko driver ya ɗauke ki." Bintu ta ɗan hade rai snn cıkın shagwaɓa, ta juya ta kwanta da gefenta. "Mommyyy…" Hajiya Hauwa ta yi dariya. "Me kuma, babygirl?" "Dama ba don ki ganni ba kika ce na zo? Kenan ba ki yi kewata ba?" Hajiya Hauwa ta zaro ido kaɗan, sannan ta fashe da dariya. "Common, my dear! Says who?" Ta miƙa hannu ta rungume Bintu, tana shafa bayanta. "Who told you I don’t miss you? Ai kin san yadda nake sonki. Amma ke ma kin san cewa ba zan so ki zauna kina ɓata lokacinki a gida ba, alhali akwai abubuwan da za su taimaka miki." Bintu ta ɗan yi murmushi, amma sai ta sake tuna wani abu. "Mommy, amma fa na ce wa mama ba zan daɗe a nan ba. I promised her zan koma gida da wuri." Hajiya Hauwa ta ɗan sauya yanayin fuskarta, amma ba ta bari Bintu ta lura ba. "To, my dear, ai ba wani dadewa za ki yi ba. Sama-sama za ku gaisa, sai ki wuce gida. Ba wani abu ba ne. Besides, Alhaji ya bar abubuwan da yake yi a Dubai ya dawo garin nan saboda kawai yana son ya gan ki. Kin fahimta kuwa?" Bintu ta ɗan yi shiru, tana kallon Mommy. Hajiya Hauwa ta ci gaba da lallashinta. "Ki yi tunanin yadda ya yi tafiya mai nisa, ya dawo, kuma abu na farko da yake son yi shi ne ya gan ki. Don’t disappoint him, baby. Ki je ki gaisa da shi kawai, sannan driver ya dawo da ke gida." Bintu ta yi ajiyar zuciya. "Okay, Mommy." "That’s my girl!" Hajiya Hauwa ta miƙe, ta nufi wardrobe ɗin da ke ɗakin. Ta buɗe shi, ta fara duba kayan da ke ciki, har sai da ta ciro wata kyakkyawar luxury abaya mai tsada. Ta dawo da ita kusa da Bintu, ta ɗora mata a kan cinyarta. "Here, wear this one. Za ki yi kyau sosai da ita." Bintu ta ɗauki abayar, tana kallon ƙawarta. "Mommy, this is beautiful!" "I know, baby. Na zaɓa miki ita ne saboda na san za ta yi miki kyau." Ta taimaka mata ta tashi daga kan gadon, sannan ta fara shiryata cikin kulawa, tana gyara mata sauran kayan da za ta saka. "Now, let’s make you look beautiful. Alhaji yana jiranki fa." Bintu ta yi dariya cikin shagwaɓa. "Mommy, kin fi kowa son na yi kyau." Hajiya Hauwa ta yi murmushi, ta kalli fuskarta a cikin madubi. "Of course, my baby. You deserve the best." Bayan ta gama shirya Bintu, Hajiya Hauwa ta ɗauki jakar Bintu ta Mika mata sannan ta kamo hannunta suka fito daga ɗakin tare. A hankali suka sauko daga stairs ɗin, suna tafiya har zuwa ƙofar gidan. Motar da Alhaji ya aiko domin ɗaukar Bintu tana jiranta a waje, direban ma yana tsaye kusa da motar. Hajiya Hauwa ta buɗe ƙofar, ta raka Bintu har ta shiga motar. "Okay, my baby. Ki je lafiya. And don’t forget to call me when you get there." Bintu ta yi murmushi, ta rungume ta. "Okay, Mommy. Zan kira ki." Hajiya Hauwa ta shafa bayanta, sannan ta sake ta. Bintu ta zauna ta gyara abayar jikinta. Kafin motar ta fara tafiya, Hajiya Hauwa ta ɗaga hannu tana mata waving, murmushi dauke a fuskarta. Bintu ma ta ɗaga hannunta ta yi mata waving ta cikin gilashin motar. Da motar ta fara tafiya, Hajiya Hauwa ta ci gaba da kallonta har sai da ta ɓace daga ganinta. Daga nan ta sauke hannunta, ta juya ta koma cikin gidan.
Bacci suka yi sosai, Zayd yana kwance rungume da ita a jikinsa, hannunsa ɗaya a zagaye da ƙugunta, ɗayan kuma a saman duvet ɗin da ya rufe su. Ɗakin ya yi tsit, sai saukar numfashinsu kaɗai ake iya ji. Bayan wasu lokuta, Raihana ta fara motsi a hankali. Ta ɗan daɗe kafin ta buɗe idanunta, waɗanda suka ɗan kumbura saboda kukan da ta sha. A hankali ta lumshe su sau biyu, sannan ta buɗe su sosai. Abu na farko da idanunta suka sauka a kai shi ne fuskar Zayd. Yana kwance cikin nutsuwa sosai, yanda numfashinsa ke tashi da sauka a hankali ya nuna irin kwanciyar hankalin da ya shiga. Da alama ya yi bacci mai daɗi, babu wata alamar damuwa a fuskarsa. Raihana ta sauke idanunta a hankali a kan fuskarsa, sannan ta ɗan yi shiru. Sai kawai abubuwan da suka faru a daren suka dawo mata fresh a cikin kanta. Ta tuna kukan da ta yi, yadda ta riƙe shi tana roƙonsa ya tsaya, da yadda ta ji jikinta a lokacin. Nan take ta ɗan runtse idanunta, tana jin wani irin kunya ya mamaye ta. Ta haɗiye yawu, sannan ta sake buɗe idanunta. A wannan karon, kallonta ya tsaya sosai a kan fuskar Zayd. Lips ɗinsa sun yi wani mugun pink sai kyalli sukeyi, lebensa na ƙasa ya fi na sama kauri kaɗan. Dogayen eyelashes ɗinsa sun yi layi a saman ƙwayoyin idanunsa dake a rufe, suna ƙara fito da kyawun fuskarsa. Hancinsa madaidaiciya ne, ya zauna daidai a tsakiyar fuskarsa, yayin da manyan dark brows ɗinsa suka ƙara ba fuskarsa wani irin kamala. Sajensa da ya fito a gefen kumatunsa da ƙarƙashin haɓarsa ya ƙara fito da irin kwarjinin da yake da shi. Ko a cikin bacci, akwai wani irin nutsuwa da haɗin kai a fuskarsa, kamar yadda yake kasancewa a duk lokacin da yake cikin yanayinsa na Mr. Armaan. Raihana ta zuba masa ido, tana kallon kowane ɓangare na fuskarsa a hankali. Ta ɗan matsar da kanta kaɗan, tana ƙoƙarin ganin fuskarsa sosai ba tare da ta tashe shi ba. Zuciyarta ta fara bugawa a hankali, sai kuma bugun ya ƙaru ba tare da ta san dalili ba. Ta sake kallon lip dinsa ta tuni yanda ya dinga tsotsar each angle na jikinta tsigar jikinta ta wani mugun tashi da Sauri ta lumshe idanunta, sannan ta sake bude su ta koma kan idanunsa da ke a rufe. A hankali ta sauke ajiyar zuciya. Ta sake kallonsa. Hannunta da yake kwance a tsakanin su ta ɗan motsa shi, har yatsunta suka taɓa ƙirjinsa. Amma Zayd bai motsa ba. Ya ci gaba da baccinsa cikin nutsuwa, yana riƙe da ita a jikinsa kamar yadda ya yi tun kafin su yi barci. Raihana kuwa ta ci gaba da kallonsa, zuciyarta na bugawa a hankali, tana jin kamar ba ta son wannan lokacin ya ƙare.
Yana cikin wannan baccin ne a hankali ya fara motsa idanunsa, kafin daga bisani ya buɗe su. Tasss suka sauka çıkın ma Raihana kai tsaye. Raihana kuwa, cikin sauri ta runtse nata idanun, kamar wacce aka kama tana aikata wani laifi. Ta ɗan matse leɓenta, tana ƙoƙarin ɓoye kunyar da ta mamaye fuskarta. Zayd ya yi shiru na wasu seconds, yana kallonta. Sai kuma wani ɗan murmushi ya bayyana a gefen leɓensa. "My Raiii." Ya fada cikin husky voice dinshi da yanda muryarshi ta danyi karfi sabida bacci Bai samu amsa ba. Raihana ta ci gaba da runtse idanunta, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa. Zayd ya ɗan matsa fuskarsa kusa da tata. "Hmm… so, this is how you’ve been spending your time? Staring at me?" Raihana ta buɗe ido ɗaya a hankali, amma da ta ga yana kallonta, sai ta sake rufewa. Zayd ya ɗan yi dariya a hankali. "Really, wife? Yanzu har kallon mijinki ya zama abin kunya?" Ta ɗan motsa kanta, tana ƙoƙarin ɓoye fuskarta a kirjinsa. "Nothing…" ta amsa a hankali. "Nothing?" ya maimaita, yana ɗan ɗaga gira. "Then why did you close those pretty eyes the moment I opened mine?" Ta girgiza kai kaɗan, ba tare da ta ɗago ba. Zayd ya saukar mata da wani kiss a goshinta, sannan ya ɗan ja ta kusa da shi. "Habibti, you can look at me all you want. I won’t charge you for it." Raihana ta make kafada snn cıkın dakushashiyar muryarta tace "Uhmm …" ta fada a hankali. "Yes, my Raii?" Ta yi shiru, ta sake ɓoye fuskarta a kirjinsa. Shi kuwa ya yi murmushi, yana shafa bayanta a hankali. "Look at me, sweetheart. I want to see those beautiful eyes of yours." Zayd ya sake janta kusa da shi, yana son ya rungume ta sosai, amma kafin ya gama, Raihana ta saki wani irin ƙara, ta murɗe jikinta cikin azaba. "Ahhh! Wayyyo!" Nan take ya tsaya cak. Ya sauke idanunsa a kanta, sannan ya fahimci dalilin da ya sa ta yi ƙarar. Fuskarshi ta sauya nan take. "Oh, my poor baby…" Ya ɗan shafa kumatunta, yana kallon yadda ta fara ƙananan kuka, tana yarfa hannayenta saboda zafin da ya ratsa ta. "Habibti, I’m sorry. I didn’t mean to hurt you." Raihana ta runtse idanunta, hawayenta na taruwa a gefen ƙwayoyin idanunta. Zayd ya rikice sosai. Da sauri ya janye duvet ɗin, har ya manta da Cewa bakomai a jikinsa Ganin sa a haka ya sa Raihana ta sake fashewa da kuka, ta runtse idanunta sosai, tana juya fuskarta gefe cikin kunya. Ya ɗan tsaya, sannan ya fahimci dalilin boye Fuskarta bai damu da saka wani abu ya rufe kanshi ba ya karasa kusa da ita "Hey, hey… don’t hide from me, sweetheart. I’m sorry, okay?" Ta kasa amsawa, sai dai ta ci gaba da share hawayenta. A hankali ya saka hannayensa a ƙarƙashinta, ya ɗage ta sama cikin kulawa. Raihana ta sake yin ƙaramar ƙara, ta riƙe kafaɗarsa. "Ka ajiyeni… zan je da kaina. Wayyo…" Zayd ya ɗan matse leɓensa, yana kallonta cikin tausayi. "No, my love. You’re not walking anywhere like this. Just let me take care of you." Ya ɗan sumbaci goshinta. "Easy, princess. Hold on to me. I’ve got you." Raihana ta ɗan matsa fuskarta a wuyansa, tana jin kunyar kallonsa. Shi kuwa ya yi ɗan murmushi, ya ɗan sumbaci gefen goshinta. "Hmm… my shy wife. Even now, you’re still hiding that pretty face from me?" Ta ɗan girgiza kai, ba ta ce komai ba. "Okay, I won’t tease you. Not when you’re hurting." Ya gyara yadda yake riƙe da ita, sannan ya nufi bathroom ɗin a hankali, yana kula da duk wani motsinta. "Just tell me if anything hurts more, sweetheart. I don’t want you forcing yourself to do anything. Today, you’re my only responsibility." Raihana ta ɗan ɗago fuskarta daga wuyansa, ta kalle shi na ɗan lokaci. Shi ma ya sauke idanunsa a kanta, ya yi mata wani irin murmushi mai taushi. "My beautiful Raii…" Ya sake sumbatar goshinta, sannan ya shiga bathroom ɗin da ita.
Kai tsaye ya nufi babban bathtub ɗin da ke cikin bathroom ɗin. A hankali ya zo zai sauke ta a gefen wani kujerar da ke kusa, yana tabbatar da cewa tana zaune cikin kwanciyar hankali "Just a minute, sweetheart. Let me prepare something for you." Amma raihana taqi sakin sa ta sake kankame shi ganin Haka sai akwai ya Kara riketa a jikinsa Ya buɗe tap ɗin, ya fara haɗa ruwan ɗumi a cikin bathtub ɗin. Bayan ya tabbatar da zafin ruwan ya yi daidai, ya zuba ɗan gentle, fragrance-free bath soak da oatmeal bath additive, sannan ya dago ya dan kalleta Raihana tana nn shiru, kanta a ƙasa, tana share ƙananan hawayen da suka rage a fuskarta. Zayd ya matso kusa da bakınsa kusa da kunnenta. "Hey, my love. Kin danji sauki kadan ?" Ta ɗan gyada kai, ba tare da ta ɗago ba. Ya ɗan shafa gefen fuskarta. "Good girl. I’ve prepared warm water for you. It’ll help you relax a little." Daga nan ya karasa, ya ɗauko babban towel mai laushi ya ajiye a gefen bathtub ɗin. ya fara shirin taimaka mata ta sauko dağa jikinsa domin ta shiga ruwan. Amma da ta ga abinda zaiyi, sai ta miƙa hannayenta da sauri ta rungume shi gam. "Aa’aah …" Ya tsaya, ya kalleta. "What is it, baby?" Ba ta amsa ba. Maimakon haka, sai ta ƙara matse shi, ta zagaye wuyansa da hannayenta, ta cusa fuskarta a wuyansa tana sakin ƙananan kukan da ta kasa riƙewa. Zayd ya ɗan yi murmushi mai taushi, ya ɗaga hannayensa ya rungume ta. "Hey, hey… what’s wrong, my shy girl?" Ta girgiza kai a hankali, har yanzu fuskarta a ɓoye. "Ba zan iya ba…" "Can’t do what, sweetheart?" Ta ƙara cusa kanta a wuyansa. "Tsayawa Haka." Ta fada cikin wata shagwaba kamar yarinyar goye Zayd ya yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya fahimci abin da take nufi. Sai wani ɗan murmushi ya bayyana a fuskarsa. "Ohhh… is that what’s bothering my beautiful wife?" Raihana ta ƙara matse wuyansa, tana jin kunyar ko ɗaga kanta. Zayd ya shafa bayanta a hankali. "My Raii, look at me for a second." Ta girgiza kai. "Please, baby. I’m not going to rush you." Ya ɗan sumbaci gefen kanta. "Listen, sweetheart. You don’t have to feel embarrassed around me. But if you’re not comfortable, I’ll give you all the privacy you need. Just tell me what you want." Ta yi shiru, tana ci gaba da riƙe shi. Zayd ya yi ɗan murmushi, sannan ya raɗa mata a hankali. "Do you want me to turn around ?" Ta ɗan gyada kai a wuyansa. "Okay, my love. Anything that makes you comfortable." Ya ƙara rungume ta na ɗan lokaci, yana shafa bayanta a hankali. "Don’t cry, habibti. I’ve got you. We’re not in a hurry, okay?" A hankali ya ɗan ja ta daga jikinsa, ya share mata hawayen da yatsunsa. "Now, give me a little smile, even if it’s a tiny one." Raihana ta ɗan yi ƙoƙarin murmushi duk da kunyar da take ji. "That’s my girl," ya faɗa cikin murmushi, kafin ya juya kawai ya nufi cikin bathtub din da ita ya shiga a hankali snn da Sauri ya janyeta a jikinsa ya danna ta ciki…