Free chapter · Read without an account

A CHANGE OF HEART

by Hau—waah · ZAYD ARMAAN

ZAYD ARMAAN

CHAPTER 127

A CHANGE OF HEART

JIDDAAH BARKUM

——-

Raihana ta ƙara matse jikinta a nasa, ta cusa fuskarta a ƙirjinsa ta fara sakin kananan kuka sabida dumin ruwan dake ratsa jikinta kai tsaye Gashi bala'in jin kunyar ɗaga kai take ta kalleshi.. Zayd kuwa ya zauna a hankali a cikin bathtub ɗin, yana riƙe da ita sosai domin kada ta yi wani motsi da zai ƙara mata zafi. Ya sauke kansa kaɗan, ya sumbaci saman kanta. "See? You're safe, my love. Nothing to be shy about stop crying kinji?." Raihana ta ɗan ɗago kai, ta kalle shi da manyan idanunta, sannan ta sake sunkuyar da kanta. Zayd ya ƙara janye ta a jikinsa, ya daidaita zamansa a cikin ruwan wankan, yana tabbatar da cewa tana cikin kwanciyar hankali a hannunsa. Amma da ya lura da yadda take kuka a hankali, sai ya sunkuyar da kansa ya sumbaci goshinta. "Shhhh… my love. It's okay, Habibti. I'm here." Ya ɗora tafin hannunsa a bayanta, yana shafa ta a hankali, yayin da ɗayan hannunsa ke riƙe da ita sosai a ƙirjinsa. Raihana kuwa ta ƙara ƙanƙame shi, hawayenta na sauka a hankali, jikinta yana rawa saboda zafin da take ji. "I'm sorry, sweetheart. I know it hurts." Ya faɗa cikin murya mai taushi, yana sake sumbatar goshinta. "I wish I could take the pain away from you." Ta ƙara sakin wani kuka, amma ba ta ce komai ba. Sai dai ta ɓoye fuskarta a wuyansa, hannayenta har yanzu a maqale a bayan wuyansa. Zayd ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci, yana jin tausayinta. "Look at you, my little princess… you don't even have to say anything. I understand." Ya ɗan matsar da ita domin ta fi samun sauƙin zama, sannan ya ci gaba da shafa bayanta. "Just relax, baby. You don't have to pretend you're okay for me. If it hurts, let me know. I'll take care of you, I promise." Raihana ta yi shiru, sai hawayen da ke zuba a fuskarta. Zayd ya ɗan karkata kansa ya sumbaci gefen goshinta. "I'm not going anywhere, my Raii. Take all the time you need. There's no rush, okay? You're safe with me." Ya ci gaba da yi mata magana cikin sanyin murya, yana lallashinta kamar ya samu ƙaramar yarinya, har sai da ya lura kukan nata ya fara raguwa. Amma duk da haka bai sake ta ba. Ya ci gaba da riƙe ta a jikinsa, yana shafa bayanta a hankali, yana ba ta dukkan kulawar da take buƙata.

Bayan ya tabbatar da cewa ruwan ya bi jikinta sosai, ya lura da yadda take sauke ajiyar zuciya a hankali a ƙirjinsa. Kukan nata ma ya ragu, duk da cewa har yanzu tana manne da shi, fuskarta a ɓoye a wuyansa. Ya ɗan sunkuyar da kansa zuwa kunnenta, sannan ya furta cikin murya mai laushi, "It's time to bathe now, Habibti. Kin iya wankan tsarki ko?" Kamar an zuba mata ruwan sanyi, Raihana ta rufe idanunta da sauri, ta sake ɓoye fuskarta a ƙirjinsa. Kunyar da ta ji ta yi yawa har ta kasa ɗaga kai. A ranta kuwa tana jin kamar ƙasa ta tsage ta shige kawai ta huta. Zayd ya kasa hana Kansa murmushi. Ya fahimci dalilin da ya sa ta yi shiru, amma hakan bai hana shi ƙarasa maganarshi ba. "Uhm… Habibti, irin wankan da kike yi bayan kin gama menses ne kawai. Niyya ce za ki canja, kin gane?" Raihana ta ƙara ɓoye fuskarta, sannan ta furta cikin ƙaramar murya, "Ni ka daina…" Ta faɗa kamar za ta fashe da kuka. Zayd ya yi murmushi, ya sumbaci kanta. "Okay, okay. Na daina, princess. Don't cry." Ya ɗan yi shiru ganin taqi motsawa sai ya ƙara da cewa, "Bari na yi miki da kaina toh." "A'a! Ban sooo!" Ta katse shi da sauri, tana girgiza kanta a ƙirjinsa. Zayd ya ɗan yi dariyar jin daɗi, sannan ya ɗago kanta kaɗan daga ƙirjinsa domin ya ga fuskarta. Amma Raihana ta ƙi kallonsa, ta karkatar da kanta gefe, tana ƙoƙarin kauce wa idanunsa. Ya ci gaba da kallonta, murmushi dauke a fuskarsa. "Ba ki so na yi miki wankan?" Ta yi saurin girgiza kai, sannan ta ɗan ɗaga idanunta zuwa gare shi na daƙiƙa ɗaya kafin ta sake sunkuyar da su. "Ni ka fita kawai…" Zayd ya ɗan tsaya yana kallonta, murmushinsa na ƙara faɗaɗa. Ya sumbaci goshinta, sannan ya gyara mata gashin da ya manne a fuska. "Okay, princess. If that will make you happy, I'll give you your privacy." Ya ɗan matsa ya nuna mata cewa zai fita, amma kafin ya tashi sai ya sake kallonta. "Amma ki yi a hankali, okay? Kada ki yi gaggawa. Idan kina buƙatar wani abu, ki kira ni. I'll be right outside." Raihana ta yi masa alamar ta fahimta da ɗan motsa kai, har yanzu ba ta iya kallonsa sosai ba. Zayd ya yi murmushi, ya sumbaci goshinta a karo na ƙarshe. "That's my girl." Sannan ya dan janye ta a jikinsa da Sauri ta hade kirjinta a gwuiwarta ta rungume jikinta sai ya miƙe a hankali bayan ya ga yanda tayi murmushi ya sake bayyana a fuskarshi ko me take boyewa da bai gani ba? Ya ayyana a ranshi, sai kawai ya ɗauki towel ɗin da ya tanada ya ajiye mata a inda za ta iya kai wa, kafin ya juya ya nufi ƙofar bathroom ɗin. Da ya kai bakin ƙofa, sai ya waiwaya ya sake kallonta. "Take your time, Habibti." Sai ya fita, ya bar mata sararin da take buƙata.

Zayd yana zaune a ɗakin bayan ya fito daga bathroom ɗin, yana jiran Raihana ta fito. Ya ɗan jingina bayansa da kujerar, yana duba agogon dakin lokaci-lokaci. Amma ganin lokacin ya kusa ƙarfe biyu, sannan kuma har yanzu ba su yi sallar Azahar ba, sai ya miƙe tsaye. Ya san cewa Raihana tana buƙatar lokaci da kwanciyar hankali, don haka bai so ya sake takura mata ba. Ya yanke shawarar zuwa wani ɗakin da ke kusa, ya yi wanka, sannan ya gabatar da sallarsa. A ransa yana tunanin watakila kafin ya dawo, ita ma ta gama sallarta. Raihana ta lumshe idanunta tana sauke ajiyar zuciya a hankali, kafin ta sake buɗe su. Ta ɗan kalli ruwan wankan, sannan ta miƙa hannunta ta buɗe magudanar ruwan da take ciki. Bayan ruwan ya gama fita tas, sai ta sake tara wani ruwan mai tsafta har sai da ta tabbatar ya yi mata daidai. Daga nan ta fara wankan tsarki a hankali. Bayan ta gama, sai ta ɗauki alwala, tana yin komai cikin nutsuwa. Ta kama gefen bathtub ɗin, ta ɗan miƙe tsaye, idanunta a runtse. Ta ji wani irin sauƙi a jikinta, duk da cewa har yanzu tana jin ɗan raɗaɗin da ya rage mata. A hankali ta fito daga cikin bathtub ɗin, ta ɗauki towel ɗin da Zayd ya ajiye mata, ta naɗe jikinta da shi. Sai ta fara takawa zuwa ƙofar bathroom ɗin. Amma kafin ta fita, sai ta tsaya ta ɗan leƙa cikin ɗakin ta gefen ƙofar, tana duba ko yana ciki. Da ta tabbatar babu kowa, sai ta fito da sauri, ta nufi wardrobe. Ta buɗe ta, ta ɗauko wata riga mai faɗi ta saka, sannan ta zaɓi well ironed hijab dinta ta ɗaura. Bayan ta gama shiryawa, sai ta nufi wajen dadduma. A lokacin ƙarfe biyu da kwata na rana. Ta shimfiɗa daddumar, ta tsaya tana fuskantar alƙibla, sannan ta ɗaga hannayenta ta yi kabbarar fara sallar Azahar. Ta shiga cikin sallarta cikin nutsuwa, tana mai neman sauƙi da rahama daga Ubangijinta.

Bayan ya gama, sai ya fito daga ɗakin ya nufi ƙasa. Ba tare da wani shiri na musamman ba, sai ya tsinci kansa da shiga kitchen kai tsaye. A ciki ya tarar da Sadiya tana ƙoƙarin ɗora abincin rana. Fuskar nan ta sa haɗen ta take, Sadiya na ganin shi sai ta miƙe tsaye cikin girmamawa. "Good afternoon, sir." Zayd ya amsa gaisuwar a taƙaice, sannan ya wuce zuwa kitchen island inda ya hango tea flask a kai. Yana ƙoƙarin buɗe shi ne Sadiya ta yi saurin matsowa kusa. "Ko akwai wani abu da kake buƙata ne, sir?" Ta tambaya cikin ladabi, kanta a sunkuye. A hankali Zayd ya juyo ya kalleta daga sama har ƙasa, sannan ya ɗaga flask ɗin kaɗan. "Tea ne a cikin wannan?" "Eh, sir." Ta amsa da sauri. "Saboda na ga Anty ba ta fito ba har ƙarfe sha ɗaya, shi ya sa na dafa mata shayi. Na soya mata plantain da ƙwai ma. Yanzu kuma na fara girkin rana." Ta ƙarasa maganar tana ɗauko warmer ɗin da ta ajiye a gefe, ta buɗe shi ta nuna masa plantain ɗin da ƙwai da ta shirya. Zayd ya ɗan kalli yadda ta tsara komai, har da mug ɗin shayi da ta ajiye a gefe. A bayyane yake cewa ta yi ƙoƙari wajen kula da abincin. Bai ce komai ba. Sai ya buɗe fridge ya ɗauko bottled water, ya ajiye ta a kan tray ɗin. Sannan ya ɗauki flask ɗin shayin tare da tray ɗin a hankali. "Thank you," ya faɗa cikin sanyin muryarsa. Daga nan ya juya ya nufi ƙofar fita. Sadiya ta tsaya tana binsa da kallo, har ya fice daga kitchen ɗin. Ta ɗan sauke numfashi, sannan ta koma kan girkinta.

Raihana tana zaune a kan dadduma bayan ta idar da sallarta. Ta jingina bayanta da kujerar da ke bayanta, idanunta a lumshe, tana jin wani irin sauƙi a ranta. A hankali ta ji an buɗe ƙofar ɗakin, sannan ta ji motsin mutum yana shigowa. Ta gane shi tun kafin ya yi magana, amma duk da haka ta ƙi buɗe idanunta. Ta ci gaba da zama yadda take, kamar ba ta san da shigowarsa ba. Zayd kuwa yana kallonta tun daga ƙofar ɗakin. Ya lura da yadda ta lumshe idanunta, sannan ya yi ɗan murmushi. Ya ƙarasa inda take, ya ajiye tray da ke hannunsa a kan ƙaramin teburin gefen kujera, kafin ya zauna a gefenta. Ya ɗaga hannunsa ya shafa fuskarta a hankali. "Habibti…" Raihana ta ɗan motsa, amma ba ta buɗe idanunta ba. "Kin idar da sallarki?" Ta ɗaga kai kaɗan alamar eh. "Good." Ya faɗa cikin sanyin murya, yana shafa kumatunta da babban yatsansa. "Yanzu fa ya jikin na ki?" Ba ta amsa ba. Sai dai ta ɗan buɗe idanunta kaɗan, ta sake rufewa. Zayd ya ɗan karkata kansa yana kallonta. "Hmm? Har yanzu ba za ki yi magana da ni ba?" Ta yi ƙoƙarin kau da fuskarta daga hannunsa, amma ya bi ta a hankali, yana murmushi. "What's wrong, princess? Har yanzu kina jin kunya ne?" A wannan karon ta buɗe idanunta da sauri, ta kalle shi na ɗan lokaci, sannan ta sunkuyar da kanta. Zayd ya kasa daina murmushi. "Na gane." Ya fada yana mikewa zuwa sofa dake gefen raihana ya zauna sosai a kan kujerar, sannan ya miƙa hannunsa ya kama nata a hankali. Ya ɗan ja ta har ta miƙe tsaye a gabansa. Ba tare da ya ce komai ba, sai ya ɗaga hannunsa ya kama hijab ɗin da ke kanta, ya cire shi a hankali ya ajiye a gefen kujera. Ya ɗan tsaya yana kallonta. Rigar jikinta mai launin ja ta yi mata kyau sosai. Kanta babu dankwali, ga gashinta da ya ɗan jike ya manne a gefen wuyanta. Ƙananan gashin goshinta sun kwanta a hankali, suna ƙara fito da kyawun fuskarta. Amma yayin da idanunsa suka gangaro ƙasa, sai suka sauka kan ƙirjinta ganinta ba bra ya sa da sauri ya kawar da kallonsa, yana mai sauke numfashi a hankali. He had to remind himself to behave. Bai so ya ƙara mata kunyar da take ciki ba. A hankali ya janyo ta kusa da shi, sannan ya zaunar da ita a kan cinyarsa. Ya daidaita zamanta, yana tabbatar da cewa ba ta ji wani raɗaɗi ba. Daga nan ya miƙa hannunsa ya ɗauki tea flask din da ya kawo, ya zuba a cikin kofin da ke kan tiren. Bayan ya ajiye, sai ya ɗauki kofin ya ɗago shi zuwa bakinta. "My Raiii…" Raihana ta ɗan ɗago kanta kaɗan, amma idanunta suna ƙasa. "Open your mouth, ki ci wani abu. Ba ki yi breakfast ba." Ta ɗago masa idanunta, ta zuba masa su kawai, ba tare da ta ce komai ba. Shi ma kallonta kawai yake yi, idanunsa cike da ƙauna da wani irin shauƙi da ba ya iya ɓoyewa. A hankali ta furta, "Kai ma ba ka ci ba." Wani ɗan murmushi ya subuce masa. Ya sunkuyar da kansa kaɗan, sannan ya ce cikin ƙaramar murya, "Says who? Na yi breakfast mana… da abu mafi daɗi a duniya." Da ta fahimci inda maganarsa ta dosa, sai ta kawar da idanunta daga kansa da sauri, ta maida su gefe tana turo baki. Zayd ya saki wata ƙaramar dariya, ya ɗan matse ta a jikinsa. "Come on, sweetheart. Open your mouth. Don't tell me you're going to start being stubborn with me this early." Ya ɗaga kofin ya kai saitin bakinta. Raihana ta ɗan yi jinkiri, sannan a hankali ta buɗe bakinta ta karɓi ɗan shayin. Ta fara sha a hankali, yayin da Zayd ke riƙe da kofin, yana kallonta da murmushi. "Good girl," ya furta a hankali. "That's my baby." Raihana ta sunkuyar da kanta, ta ci gaba da shan shayin, tana ƙoƙarin kauce wa kallonsa. Shi kuwa ya ci gaba da riƙe ta a jikinsa, yana jin wani irin daɗi na musamman a zuciyarsa duk lokacin da ya kalli yadda take cikin kunya a gabansa. "Ina son kunyar kin nan" ya ƙara faɗa, yana kallonta cikin taushin murya. Ita kuwa sai ta ƙara sunkuyar da kanta, tana mai jin cewa wannan mutumin ba zai bar ta ta daina jin kunya ba ko kaɗan.

Seeyama ta ajiye Safina a gidanta. Bayan sun yi sallama, sai ta juya motarta ta nufi gida. A lokacin ƙarfe uku na rana. Da ta isa ƙofar gida, sai ta yi horn kai tsaye. Maigadin da ke zaune yana barci bai ji ba. Seeyama ta sake dannawa karo na biyu, amma har yanzu shiru. Sai da ta kusa karo na uku kafin maigadin ya farka a firgice, jikinsa yana rawa. Da ya leko ta karamar kofa ya ga motarta a ƙofar, sai ya qarasa Babban gate da gudu. Ya san halin Seeyama, kuma a ransa ya fara tunanin irin bala'in da zai biyo baya saboda jinkirin buɗe mata ƙofar. Da ya buɗe gate ɗin, sai ya fara magana cikin rawar murya. "Madam, dan darajar Allah ki yi haƙuri. Barci ne ya ɗauke ni, ban ji horn ɗin ba…" Amma kafin ya ƙarasa, Seeyama ta ɗaga masa hannu alamar ya yi shiru. Ba tare da ta ce komai ba, ta wuce da motarta kai tsaye zuwa filin ajiye motoci. Maigadin ya tsaya cak, baki a buɗe yana kallon ikon Allah. This is so unusual of her! Ya kasa fahimtar abin da ke faruwa. Seeyama ce kuwa? Ita ce wadda ko ƙaramin kuskure aka yi mata ba ta barin mutum ya huta? Ya girgiza kai a hankali, sannan ya rufe gate ɗin ya koma wajen zamansa. Idanunsa kuwa har yanzu suna kan motar Seeyama, wadda take tsaye a Parkin space amma har yanzu ba ta fito ba. Seeyama kuwa a hankali ta buɗe ƙofar motar, ta ɗauki jakarta, sannan ta fito. Ta ɗan tsaya tana kallon motar Zayd da ke ajiye a gefe, kafin ta kawar da idanunta ta nufi sashenta cikin nutsuwa. Kai tsaye ta nufi store din ta, inda ta sauki Rabi tun zuwanta. Rabi tana zaune a kan zanin da ta shimfiɗa, tana ƙoƙarin ware kitson kanta. Kwatsam sai ta ji motsin mutum a gabanta. Da ta ɗago kai, sai ta ga Seeyama tsaye a kanta. Da sauri ta zabura, ta janyo hijabinta tana ƙoƙarin rufe kanta. "Sannu da zuwa, Anty," ta faɗa cikin rawar murya. "Yauwa," Seeyama ta amsa a taƙaice. Ta ɗan zuba wa Rabi ido, sannan ta ce cikin muryarta mai sanyi, "Ki tattara kayanki. Daga yau za ki koma ɗakin da ke kusa da stairs. Shi ne ɗakinki daga yanzu." Rabi ta ɗago kai da sauri, tana kallon Seeyama cikin mamaki. "Anty…?" Amma Seeyama ba ta jira ta ƙarasa ba. Ta juya kawai ta fice daga ɗakin, kamar ba ta san da mamakin da ta bari a bayan ta ba. Rabi ta zauna cak, baki a buɗe tana kallon ƙofar da Seeyama ta fita. Me kuma ya faru? Ta kasa fahimtar komai. Wannan wane irin sauyi ne haka? Seeyama ta dawo gida, amma ba ta yi mata ihu ba, ba ta zage ta ba, har ma ta sauya mata ɗaki cikin nutsuwa. Rabi ta kalli kayanta da ke gabanta, sannan ta sake kallon ƙofar. Tabbas akwai wani abu da ke faruwa.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol