Free chapter 路 Read without an account
AMANI
馃挒馃挒馃挒馃挒馃挒
bismillahir rahamanirrahim
SAFIYAR WASHEGARI
Da misalin karfe bakwai na safe, Amani ta bude idanunta.
Ta mike zaune, ta dauki wayarta domin duba lokaci. Bayan ta gama duba wasu sakonni, ta sauka daga kan gadon ta nufi bandaki.
Bayan ta gama shiryawa, ta fito sanye da wata doguwar riga mai sauki.
Ta bude kofar dakinta ta nufi falon.
A can ta tarar da Mommy da Inna suna zaune suna hira.
"Assalamu alaikum."
"Wa alaikumus salam, Amani ta," Inna ta amsa cikin fara'a.
Amani ta karasa ta gaishe da ita, sannan ta zauna kusa da Mommy.
"Ina kwana, Mommy?"
"Lafiya lau. Kin tashi?"
"Eh. Amma har yanzu ina jin gajiyar tafiyar jiya."
Mommy ta yi murmushi
"Shi ya sa nake gaya miki ki dahalar da kanki da aiki. Ko a hutu ba kya iya hutawa."
Amani ta yi dariya.
"Mommy, ai ba ni da laifi."
Inna ta shiga maganar.
"Ke dai ki bar ta. Tun tana karama haka take. Idan ta sa wani abu a gaba, sai ta yi shi."
Amani ta yi murmushi.
"Inna, kin fara tona min asiri kenan?"
Dukkansu suka yi dariya.
Bayan sun dan yi hira, Amani ta tambayi Mommy.
"Yau ma akwai wani shiri ne?"
"Eh. Ana ci gaba da shirye-shiryen bikin. Daga baya za mu je mu ga Maryam."
"To, shikenan."
Ta dauki kofin shayi ta sha.
Amma a cikin zuciyarta, tunanin wani abu daban ya dan ratsa ta.
Ta tuna da mutumin da suka sake haduwa da shi jiya.
Tariq.
Ta girgiza kai kadan, ta mayar da hankalinta kan hirar da ake yi.
A bangaren Nanne kuwa, tun da safe aka fara shirye-shiryen ranar.
Tariq yana zaune a falon yana kallon wasu labarai a wayarsa.
Salma ta shigo cikin sauri.
"Captain!"
Ya daga kai.
"Me ya faru kuma?"
"Don Allah, ka taimaka min da wani abu."
Ya ajiye wayarsa.
"Me kike so?"
"Ina son ka kai ni wajen da ake gyaran gashi."
Tariq ya kalleta.
"Ni?"
"Eh mana."
"Salma, ni direbarki ne?"
Ta yi dariya.
"Don Allah. kaji yaya.
Asiya da Safiyya suka shigo a lokacin.
Asiya ta ji karshen maganar. yaya dan Allah kakaimu nima zanje .
Safiyya ta zauna tana dariya.
"Ni dai na san yau akwai wanda yake son ganin Doctor."
Tariq ya daga kai da sauri.
"Wace Doctor?"
Salma ta kalli Safiyya.
"Ke kuma me kika sani?"
Safiyya ta yi murmushi.
"Ba komai. Ina wasa ne."
Tariq ya girgiza kai.
Ya dauki wayarsa ya mike tsaye.
Amma a lokacin da ya juya, sai ya ji Salma tana rada wa Asiya:
"Kin ga yadda ya yi sauri ya tambaya?"
Dukkansu suka fashe da dariya.
Tariq ya juya ya kalle su.
"Na ji fa!"
Suka kara dariya.
ALHAJI AMEER
A cikin wani daki, Alhaji Ameer yana zaune tare da wasu mutane biyu.
Fuskarsa a murtuke take, yayin da yake sauraron bayanin daya daga cikinsu.
"Alhaji, kayan sun iso."
Alhaji Ameer ya daga kai.
"Komai?"
"Eh. Amma akwai wani abu."
"Me ne kuma?"
Mutumin ya yi shiru na dan lokaci.
"An samu tsaiko a kan hanyar da aka tsara. Wasu mutane sun fara yawan tambayoyi."
Alhaji Ameer ya zuba masa ido.
"Wa蓷anne mutane?"
"Ba mu da cikakken bayani tukuna."
Ya jingina da kujerarsa.
"Na gaya muku tun farko cewa bana son sakaci. Wannan harkar ba wasa ba ce."
Daya mutumin ya shiga magana.
"Alhaji, akwai wasu kayan maye da suka shigo tare da sauran kayan. Muna son sanin abin da ya kamata mu yi da su."
Alhaji Ameer ya yi shiru.
Ya dauki kofinsa ya sha ruwa kafin ya ajiye shi.
"Ku tabbatar komai ya kasance a karkashin kulawa. Ba na son wani abu ya fito fili."
Mutumin ya gyada kai.
"An fahimta."
Ameer ya kalli su duka.
"Kuma ku sani, duk wanda ya kasa rike bakinsa a wannan harkar, zai jawo mana matsala."
Babu wanda ya sake magana.
A wannan lokacin wayar daya daga cikinsu ta yi kara.
Ya duba sakon, sai fuskarsa ta canza.
"Alhaji..."
Ameer ya kalle shi.
"Me ya faru?"
"An ce akwai wani jami'i da yake yawan bibiyar wasu daga cikin mutanen da ke da alaka da wannan harkar."
Alhaji Ameer ya daure fuska.
"Wane jami'i?"
Mutumin ya sunkuyar da kai.
"Har yanzu ba mu tabbatar da sunansa ba."
Alhaji Ameer ya yi shiru.
Amma a cikin zuciyarsa, ya fara tunanin wani abu.
BIKIN MARYAM DA NABIL
Da rana ta yi, shagalin bikin ya kara armashi.
An yi wa wurin taro kwalliya ta musamman. Mata suna ta shiga da fita, ana gyaran gashi, ana saka kayan ado, yayin da wasu ke taimakawa wajen shirya abincin baki.
A bangaren Inna, Amani tana zaune tare da wasu 'yan uwanta.
Maryam ta shigo cikin fara'a.
"Amani!"
Amani ta mike tsaye.
"Maryam!"
Suka rungume juna.
"Yanzu kin zama amarya kenan?" Amani ta fada tana dariya.
Maryam ta rufe fuskarta da hannuwa.
"Ki daina mana!"
Amani ta kara dariya.
"Me ya sa? Ai gaskiya nake fada."
Maryam ta zauna kusa da ita.
"Wallahi har yanzu ban yarda cewa wannan ranar ta zo ba."
Amani ta kama hannunta.
"Allah ya sanya alheri. Allah ya sa aurenku ya zama mai albarka."
"Amin. Na gode sosai."
Suka ci gaba da hira.
Bayan dan lokaci, Amani ta tashi domin zuwa wani bangare na gidan.
Tana tafiya ne sai ta hangi wani mutum a can gaba.
Tariq ne.
Yana tsaye tare da wasu 'yan uwansa, suna tattaunawa.
Ta dan rage tafiyarta.
Shi ma a daidai wannan lokacin ya daga kai.
Idanuwansu suka hadu.
Tariq ya yi dan murmushi.
Amani ta mayar da martani da dan murmushi kadan, sannan ta ci gaba da tafiyarta.
Tariq ya bi ta da kallo na dan lokaci.
Daya daga cikin abokansa ya lura.
"Me kake kallo?"
Tariq ya dawo hayyacinsa.
"Babu komai."
"To, mu je. Ana jiranmu."
Ya gyada kai suka wuce.
Amani kuwa, tana komawa wajen da take zaune sai Maryam ta tambaye ta:
"Me ya sa kika tsaya?"
Amani ta zauna.
"Babu komai. Na ga wani ne kawai."
Maryam ta yi murmushi.
"Wani?"
Amani ta kalleta.
"Maryam, don Allah ki daina."
Maryam ta yi dariya.
"To, na ji."
Da yamma, Tariq yana zaune a wani bangare na gidan da ba hayaniya sosai.
Wayarsa ta yi kara.
Sadiq ne.
Ya daga wayar.
"Na ji ka."
"Captain, muna da wani sabon bayani."
Tariq ya gyara zamansa.
"Ka yi magana."
"Mun samu wasu bayanai da suka nuna cewa akwai wata harkar kayan maye da ake gudanarwa a boye. Kuma akwai wasu mutane masu matsayi da ake zargin suna da alaka da ita."
Tariq ya yi shiru.
"Kun tabbatar?"
"Har yanzu muna tattara hujjoji, amma akwai alamun da suka dace mu kula da su."
Tariq ya sauke numfashi.
"Ka saurara, Sadiq. Kada ku dauki mataki bisa zato. Ina son ku tabbatar da dukkan bayanan."
"Na fahimta."
"Ka kuma yi hankali. Idan har wannan abin yana da alaka da mutanen da muke zargi, akwai yiwuwar su ma suna bibiyar ku."
Sadiq ya amsa.
"Za mu kula."
Bayan sun katse wayar, Tariq ya zauna shiru.
Ya kalli sararin da ke gabansa.
A cikin zuciyarsa, ya fara hada wasu bayanai.
Barazanar da aka yi masa.
Wasu sunaye da ya dade yana bibiyarsu.
Yanzu kuma batun kayan maye.
Ya san cewa wannan binciken ya fi yadda ya zata girma.
Sai dai bai san cewa Alhaji Ameer yana da hannu a cikin wannan harkar ba.
AMANI
Da dare, Amani ta koma dakinta bayan ta shafe lokaci mai tsawo a cikin shagalin bikin.
Ta zauna a gefen gado tana cire 'yan kunnen da ta saka.
Ta dauki wayarta ta fara duba wasu sakonni.
Sai ta tuna da yadda ta sake ganin Tariq.
Ta dan yi murmushi.
"Mutumin nan dai..."
Ta tsaya.
Sai ta girgiza kai.
"Me ya dame ni ma?"
Ta ajiye wayar.
A wannan lokacin ne Mommy ta shigo.
"Amani, har yanzu ba ki kwanta ba?"
Amani ta kalleta.
"Zan kwanta yanzu, Mommy."
Mommy ta zauna a gefen gadon.
"Kin ji dadin bikin?"
"Eh, sosai. Maryam ta yi kyau."
Mommy ta yi murmushi.
"Alhamdulillah."
Ta kalli Amani.
"Amma ina son ki yi amfani da wannan lokacin wajen jin dadin kasancewa tare da 'yan uwanki. Kin san ba kasafai muke haduwa haka ba."
Amani ta gyada kai.
"In sha Allah, Mommy."
Mommy ta tashi.
"To, ki kwanta. Sai da safe."
"To, Mommy. Sai da safe."
Bayan Mommy ta fita, Amani ta kwanta.
Alhaji Ameer yana zaune shi kadai a cikin falonsa.
Wayarsa ta yi kara.
Ya daga.
"Hello."
"Alhaji, akwai matsala."
Ya mike zaune.
"Wace matsala?"
"Mun samu labarin cewa wani jami'in bincike yana kara kusantowa ga wasu bayanai game da harkar."
Alhaji Ameer ya yi shiru.
"Sun san wani abu?"
"Ba mu tabbatar ba."
Ya daure fuska.
"To, ku tabbatar kun san abin da ke faruwa. Bana son a yi min sakaci."
"An fahimta, Alhaji."
Ya katse wayar.
Ya kalli kofar falon na dan lokaci.
A karon farko cikin kwanaki da dama, ya fara jin cewa akwai wani abu da zai iya lalata shirinsa.
Ya dauki wayarsa ya kira wani mutum.
"Ka zo wajena gobe da safe. Akwai abin da za mu tattauna."
Ya katse wayar.
Ya jingina da kujerarsa.
"Ba zan bari komai ya lalace ba."
Amma abin da bai sani ba shi ne, Tariq ya riga ya fara bin sawun wannan harkar.
Kuma duk da cewa yana Kaduna domin bikin Maryam da Nabil, bincikensa bai tsaya ba.
by Cutie