Free chapter · Read without an account

Page 1

by khadijah danasabe · FORBIDDEN LOVE

💫💫💫💫💫💫

          FORBIDDEN LOVE

                         💫💫💫💫💫💫



DijahAM(Oum Amani)



*Assalamu alaikum everyone!!

Ina mai farin ciki sosai na kasancewar mu a nan, mun sake haduwa a wani sabon adventure wanda nake fatan yafi na baya kayatar wa İn sha Allah.


In sha Allah baxan baku kunya bah bama da yadda kuka yi believing dina🌚

    Ina fatan zaku so book dinnan kuma zaku bani goyan baya kamar yadda kuka saba. Lots of love❤️



BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM



Page 1




ARWA'S POV



    Aiki a law firm da wahala ba kadan ba, kusan ko yaushe muna busy kasancewar a kwanakin nan muna da clients sosai, gashi Boss dina mugu ne zan ce masa ko kuma don yağa ban jima da fara aiki bane da su shiyasa yake loda min aiki? Anyways I'm exhausted . 


Lumshe idona na sake yi Ina rufe jikina da tattausan duvet din dake bada wani irin kamshi mai sake sani Jin bacci. Ringing din da waya ta take sake yi ne yasa ni jan tsakin, tabbas duk wanda ya katse min bacci nan da nake jin dadin sa da bukatar sa zai san bani da mutunci.

   

     "Haala Bashir Babangida" na fada da dan karfi a lokacin dana dauki wayar.


Dariya ta kyalkyale da ita cikin muryar data san zata sake kular da ni ta ce "Arwa Aminu Tafida ya aka yi neh?"


"Amma kin san baki da mutunci bah, weekend din ma don jaraba baza ki kyale ni na huta bah? Ina Mijin ki da kike damuna da sassafe?" Na karasa a kasalance idona yana sake rufe wa.


"Anya Tafida baki fara dan kora wa bah?" 


Banza na mata ban ce komai ba, don sai data yi magana ma na tuna ashe fa Mijin nata ya tafi Italy.


Numfashi Haala ta sauke ta ce "Ynxu dai mu hadu a spot din mu anjima, I'm bored"


Tura fuska ta nayi cikin pillow Ina Jin kamar na fasa ihu. "Ynxu sbd kawai you are bored sai ki tashe ni daga bacci, kin San yadda nake bukatar sa kuwa? Anya Haala kina da İmanı?"


"Haba my bf, kin san dai ba laifi na bane koh, babynki ke craving Cheesesteak din nan" Haala ta fada tana murmushi.


Baki na kawai na bude na kasa  magana, matar da a duniya ko ganin shi tayi take cewa zata yi amai ce ke craving. "Bana jin fita yau, kawai kiyi order mana"


"Ni a restaurant din nake son ci gaskia" ta fada da sauri and I can swear sai da tayi rolling eyes din ta.


Duvet din na yaye daga jikina ina mike wa daga kan king size bed dina, katon agogon dake kallon bed din na kalla, 12:40 ashe nayi baccin sosai ma, babban abinda ke saka ni kara kaunar weekend kenan sbd bacci. Murmushi nayi mai ciwo sbd tuna cewa sillar bacci ne ya fara hada ni da bugun zuciya ta.


Idona tuni ya soma ciko wa da kwalla wacce babu ranar da zata zo ta wuce bata re dana zubar da hawaye bah.


"Hey lover girl, this is not the right  time please, yau dai kiyi hakuri kiyi sparing dina yunwa nake ji" Haala ta fada da sauri, sbd a sanin da tayi wa aminiyar tata yncu zata iya zama tayi ta kuka har dare ba tare data damu bah.


Tuni hawayen sun fara sauka a idona, ba tare dana damu dana goge su bah na ceh "it's been 7 years since I last saw him Haala, everyday Ina tashi da hope din zan gan sa amma......" ban iya karasa wa ba don kukan da ya kwace min. Zama nayi a kam rug din daya mamaye dakin Ina sake kuka na. Kai kana saurara zaka san kuka ne wanda yake fito wa tun daga kasan zuciya ta.


"Kina ganin bai manta da ni bah" na fada cikin rawar murya.  "Ban gane bai manta da keh ba Arwa, wai kina tunanin Mr Rhys zai taba iya manta wa da keh neh, to ai iya watannin dana San Mr Rhys zan iya rantse wa duk halin da kike ciki shi ya fiki shiga ciki" Haala ta fada cike da tabbatar wa. Don fa ba wanda zai ce mata otherwise, duk wanda zai fada kuwa baza ma ta bata lokacin ta wajen musu da shi ba, tun da ita tayi rayuwa da su ta kuma ga yadda suka nuna wa juna tsantsar soyyaya duk da basu kai ga furta wa junan su bah.


Murmushi nayi na ce "nima wani lokacin ina tunanin haka, sai dai kawai tsoro nake ji. In aka zo ya manta da ni fa?"


"Kar ma ki fara wannan tunanin Tafida, kawai dai Ina ganin it's high time da zaki fuskanci rayuwa, na jima ina so na fada miki amma ban San yadda zaki dauki maganar bah" Haala ta fada da dükkan gaskiyar ta, don ita kam tana ganin shekara 7 sun İsa ai ga aminiyar tata, ya kama ta ace ynxu ta gama dakon soyayyar da ko fara wa baa yi bah.


"Ban gane ba" na fada Ina hade fuska ta. Yadda naji muryar Aminiyar tawa nasan baxan so abinda take so ta fahimtar da ni bah.


Ajiyar zuciya Haala ta sauke ta ceh "kawai ki taho mu hadu a spot din mu, maganar bata waya bace Tafida".


Ban kara ko seconds biyu ba na kashe wayar.  A gurguje nayi wanka na shirya cikin simple gown din atampa, ban daura dankwali ba sai veil dana yafa daga kai na kawai. I'm not a fan of dankwali ko kuma truth be told ban iya daura wa bane bah, shiyasa bana bawa kai na wahala kawai nake yafa veil dina.


Ban damu da duba Maama ba don nasan a time dinnan tana hospital. Mota ta na shige kawai na fice daga gidan a hankali, duk irin yadda ake cewa matasa suna tukin ganganci ban da ni, don sbd yadda nake driving a nutse mun sha fada da Haala da kuma Ya Abdul.


Cikin kankanin lokaci na isa restaurant din, Ina parking a parking lot na shiga ciki kai na tsaye. Sama sama muke gaisa wa da ma'aikatan cikin su, don sun gama gane mu neh ni da Haala. A shekara ta daya da dawowa daga Canada bana jin akwai satın da zai zo ya wuce ba tare da mun ci abinci a nan ba, ko da kuwa smoothie kawai zamu sha. 


A spot din da muka saba zama na hango Haala zaune, tana sanye da maroon boubou data haska chocolate skin din ta, cikin ta daya dan girma ya kara mata kyau na musamman.


Murmushi kawai nayi Ina zama a kujerar kamar wacce aka ma duka. Don kawai sai naji kuma kasala tana neman rufe ni.


Ba tare da Haala ta dago daga kan wayar ta ba ta ceh "2mins please, Ina tura wa Bae list din wannan kayan babies din dana nuna miki"


Ban ce komai na sai order din latte da nayi kawai, har aka kawo min Haala bata gama abinda take ba, nima kuma ban damu ba don hka kurin nake jin fargabar abinda zamu yi magana akai. 


   

    Numfashi Haala ta sauke tana ajiye wayar ta ta ceh "finally na gama, maza suna da damuwa Ina fada miki Tafida, kina gani fa na gama fada masa komai da nake bukata amma sai cewa yyi shi ya manta na masa sabon list kawai. Don dai Ina bukatar Kayan ne da share sa zan yi"


Tabe baki nayi ban ce komai ba Ina sipping ragowar latte dina daya rage a mug din.


Hirar mu muka fara kamar yadda muka saba, kasancewar mu aminai na sama da 20years bai hana wa kullum muka hadu da sabuwar hirar da zamu yi, duk kuwa da yadda a gida ma muna makale a waya.


Gyara zama Haala tayi yadda zata fi zama comfortable ta ceh "Tafida, magana ce zan fada miki ta gaskiya, kin San duk abinda kike so nima Ina taya ki kaunar sa bah? Amma kuma wasu abubuwan dole ne ni na ajiye son da nake musu don na fahimtar dake gaskiyar abinda zai amfane ki duniya da lahira....








Ya kuka ji sabon salon🌚 ya muku dadi? Ina fatan haka In sha Allah😍 


In kun ji dadin sa ku sambado mini kwaments🏌️‍♀️💃


Tooooo Jama'a🙃 Ga kuma Arwa an hadu da ita. Ya POV din nata ya muku dadi?😴


Waye kuma Rhys dinnan ne da ake masa wanga soyayya🏌️‍♀️


Next page ayi Rhys's POV ko kuwa a cigaba da ARWA'S POV🌚


Nifa already kamar na dangwala wa Rhys vote dina😎



Love you all guys🥰😍 soyayya cikin cokali🙄


Kar a manta da kwament🌸



Comments and share don Allah




***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol