Free chapter · Read without an account
JAHILCI YAFI HAUKA
Page 5
Daadah tana fita ta nufi gidan babban wansu, kasancewar tun bayan rasuwar mahaifinsu shine abokin shawararta kuma su biyun kadai iyayensu suka haifa, a unguwar gidansa yake amma da yar tazara kadan, matansa biyu, Lami da Ladi haka haihuwarsa majority mata ne.
Daadah ta shiga da sallama, Lami tana girki yayin da Ladi ke wanke kayan yaranta, da murna suka tarbeta " Daadah kece a gidan namu, laale maraba da ke" da murmushi ta qaraso tana zama bakin tabarmar da Lami ta shimfida mata.
Bayan gaisuwa Daadah ke tambaya " Yaya bai dawo ba ko?".
" Ya dawo ya tafi dubiya gdan Malam Dauda , da yake kwana biyun nan jikin nashi yaqi dadi", cewar Lami dake qoqarin sauke tukunyar miyanta da alama ta kammala ne, kafin ta ida rufe baki sai ga sallamar maigidan, a tare suka amsa, ai kuwa yana yin arba da Daadh ya saki murmushi cike da murnar ganinta ya qaraso bakin tabarmar da take shima ya nemi gurin zama.
"Hajara kwana 2 kin daina leqowa, itama Rumaisa bata zuwa gun yan uwanta, fatan dai lafiya"?
"Yaya makaranta ke hanata fita, ni kuma ayyukan gida".
"Ai kuwa da gari ya waye ba zama, haka zakaga dare yayi, ba tare da an ankare ba" fadin Ladi dake qarasa shanyar kayanta.
Yaya Musa yayi qasa da murya yadda ba mai jiyoshi sai ita Daadar dake kusa gareshi yace " Hajara naga damuwa a tattare dake, fatan dai lafiya ko"?
Daadah ta sunkuyar da kanta tana qoqarin danne hawayen dake son kufce mata tace " Yaya wallahi na gaji da auren nan, ba don Rumaisa ba da na kashe aurn nan na koma qauye" wannan karon tana kasa riqe hawayenta.
"Subhnlh, Hajara da girmanki kike fadin haka? Abinda bakiyi ba a kuruciya sai yanzu kice kin gaji? Kin taba ganin inda aka gaji da bautar Allah da koyi da halin Ma'aiki ( S.A.W)? Ban sanki da wannan dabi'ar ba, nasan kina haquri kuma nasan duk abinda ke faruwa a gidan naku, amma ki qara haquri ina mai tabbatar miki da kece da riba insha Allah.
Yqnzu meke tafe dake?
Daadah ta goge hawayenta, sa'annan tace "Yaya zance ne kan kudin jarabawar yarinyar nan, tun jiya da nayi maganar yake ta sababi, Innah tana qara zugashi kan lamarin, a cewarta ba karatu take ba yawon ta zubar take zuwa".
Daadah ta qarasa fada wasu hawayen na qara kufce mata, da alama abin yana damun ranta fiye da kima.
"Subhnlh, tabbas hakan ba daidai bane, amma kiyi haquri Hajara, komai zai wuce kamar ba'ayi ba, tabbas kina cikin jarabawa, sai dai ba kanki aka fara haihuwar diya mata ba, Jahilci ne, bawa yayi adawa da wata rahama da Ubangiji yayi masa, yanzu nawa ne kudin makarantar"?
"Dubu talatin" Daadah ta bashi amsa tana qara share hawaye, sqi kuma taci gaba da fadin "Yaya a sayar min da wancan filin da na saya kwanaki, a biya mata, sauran canjin sai mu dan sayi wasu abubuwan mu ajiye gudun kada kudin su salwanta".
" Toh ba matsala Hajara, nima zan biya kudin na Ummusalma da Yahanasu, bani da kudi da na hadasu na biya".
Dadah tace " ba matsala Yaya, kayi yadda nace din kawai, ai kana qoqari da lamuranmu idan bamu gode ba, bazamu butulce maka ba, Allah dai ya jiqan iyayenmu da rahama.
" Amen" Yaya ya amsa, daga haka ya miqe ya nufi dakinsa yana kiran Lami, wanda suka shige dakunansu daga lokacin da Daadh suka fara magana, saboda fahimtar da sukayi cewa suna buqatar sirri.
A tare matan suka fito Lami ta nufi turakar mijin, yayin da Ladi ta zauna inda ya tashi kusa da Daadah, tana gabatar mata da abinci, ba tare da taci ba, ta miqe tana gyara mayafinta, tayi musu sallama tana barin gidan, cike da tunani da taraddadi, saboda dama tanadin aurar da Rumaisar take, sai kuma ga zancen karatu wanda har cikin ranta so take diyarta ta samu na rayuwa, saboda tana ganin illar JAHILCI wanda yafi HAUKA ciwo a gdansu.