Free chapter · Read without an account

A LITTLE MORE OF LOVE

by Hau—waah · ZAYD ARMAAN

ZAYD ARMAAN

CHAPTER 129

A LITTLE MORE OF LOVE.

JIDDAAH BARKUM

———


Da suka shiga cikin ɗakin, Bintu ta ɗan tsaya tana kallon yadda aka tsara wajen. Babban ɗaki ne mai faɗi, an kawata shi da kayan alatu masu tsada. Akwai wani katon gado a gefe, wata sofa mai laushi a tsakiyar ɗakin, sai kuma wani babban wardrobe da ke manne da bangon ɗaya. Alhaji Sabo ya shiga gaba, yana cire hular da ke kansa. Bintu kuwa ta tsaya a gefe, handbag ɗinta a hannunta, tana bin duk motsinsa da idanuwanta. Ya fara cire babbar rigar shaddarsa, sannan ya juya gare ta, fuskarsa ɗauke da murmushi. “Baby, zauna mana. Why are you standing like that? Kamar zan yanka ki.” Bintu ta ɗan yi murmushin yaƙe, sannan ta sauke idanunta. “Nothing, Alhaji.” “Then come and sit down. Make yourself comfortable.” Ta matsa a hankali ta zauna a kan sofa, tana kallon wani gefen ɗakin. Alhaji Sabo ya yi murmushi, ya juya zuwa wajen wani ƙaramin box da ke kan wani tebur. Ya ɗauko shi, sannan ya dawo ya ajiye a kan stool ɗin da ke kusa da Bintu. “Now, look at this.” Ya buɗe box ɗin. Bintu ta ɗan buɗe baki. Cikin box ɗin akwai dalolin Amurka a jere, sababbi, an tsara su cikin tsari mai kyau. Idanunta suka tsaya a kansu, kamar ta manta da komai na ɗan lokaci. “Waw… crisp dollars!” Alhaji Sabo ya fashe da dariya bayan ya ji yadda ta furta kalmar a hankali ya zauna a gefenta. “Yes, baby. Duk naki ne.” Da sauri Bintu ta ɗago kanta daga kallon kuɗin, ta kalle shi. “Seriously?” “Of course, dear.” Ya zauna a kusa da ita, sannan ya ɗan matsa box ɗin zuwa gabanta. “Ki ɗauke shi a matsayin kyauta daga gare ni.” Bintu ta sake kallon kuɗin, tana ƙoƙarin ɓoye farin cikin da ya bayyana a fuskarta. Alhaji Sabo ya lura da yadda take kallon kuɗin, sai ya ɗan yi murmushi. “Na ga dai sun burge ki.” Ta yi ƙaramar dariya. “Who wouldn’t?” “Toh, akwai ma fiye da waɗannan.” Ya ɗan dakata, sannan ya kalli fuskarta. “Amma kafin ki karɓi waɗannan kuɗin, akwai wata magana da nake so mu fahimta.” Bintu ta ɗan gyara zamanta. “Okay, Alhaji.” Ya jingina bayansa da sofa, yana kallonta da nutsuwar mutumin da ya saba yin irin wannan maganar. “Ki saurare ni, baby. Ba na son ki fahimci abin da ya kawo ki nan ba daidai ba. Ba budurcinki nake nema ba, kuma gaskiya ba wannan ne abin da nake sha’awa ba.” Bintu ta ɗan lumshe idanunta, sannan ta sake buɗewa. “Toh, me kake so?” Alhaji Sabo ya yi murmushi. “Akwai wani abu daban da nake so.” Ya ɗan matsa kusa da ita, sannan ya faɗi abin da yake so a fili, ba tare da wani nau’in kunya ba. “I want us to have anal sex.” Bintu ta yi shiru. Kamar an zuba mata ruwan sanyi ne a jiki. Ta juya ta kalle shi, sannan ta sake kallon box ɗin kuɗin da ke gabanta. Alhaji Sabo bai nuna wata damuwa ba. A gare shi, magana ce kawai wacce ya saba yi. “Abin da nake nufi kenan, baby. Ina son mu yi jima’i ta baya. Ba ruwana da budurcinki, I am not after it.” Bintu ta kasa magana. Ya ɗan yi dariya, yana kallonta. “Me ya faru? Na gaya miki fa, ba budurcinki nake nema ba. Wannan kuma ba zai hana ki ajiye budurcinki ga wanda za ki aura a gaba ba.” Ta haɗiye yawu. “Alhaji…” “Na’am, my dear?” Ta yi shiru na ɗan lokaci, tana ƙoƙarin gano kalaman da za ta yi amfani da su. Shi kuwa ya ci gaba da magana cikin sanyin murya. “Ki duba, ba wai zan tilasta miki ba ne. Ina dai gaya miki abin da nake so ne, da kuma abin da zan ba ki a madadinsa. Sau ɗaya kawai, baby. Ki samu kuɗinki, ni ma in samu abin da nake so, kowa ya kama gabansa.” Bintu ta sake kallon kuɗin. A ranta, abubuwa da dama suka fara faɗa da juna. Tana son kuɗin. Ba ƙaramin kuɗi ba ne. Kuɗin da za su iya taimaka mata ta samu wasu abubuwan da ta daɗe tana mafarkin mallaka. Amma abin da mutumin yake nema ya sa zuciyarta ta yi nauyi. Ta tuna da yadda ta shigo ɗakin cikin murmushi, tana tunanin kawai za ta zauna ta yi hira da shi, wataƙila ya ba ta kyautar kuɗi kamar yadda Mommy ta faɗa. Amma yanzu… Ta sake kallon Alhaji Sabo. “Just once?” Ta tambaya a hankali. Alhaji ya yi murmushi, kamar ya fahimci inda hankalinta yake. “Eh, sau ɗaya kawai, baby. Na yi miki alƙawari.” Bintu ta sauke idanunta. A hankali ta fara ƙoƙarin shawo kan kanta. Aƙalla ba budurcinta yake nema ba. Idan har ta yi aure wata rana, mijinta ba zai san abin da ta yi a baya ba, ko? Kuma ba wai za ta zauna a nan har abada ba. Sau ɗaya kawai… ta samu kuɗinta, ta tafi. Amma duk da waɗannan tunanin, wani ɓangare na zuciyarta yana ƙin yarda. Ta ji Alhaji Sabo ya ɗan matsa kusa da ita. “So, baby… what do you say?” Bintu ta ɗago kanta a hankali. Idanunta suka haɗu da nasa, sannan ta sake kallon box ɗin dalolin. Ta ɗan cije leɓenta, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa. A ƙarshe, ta buɗe baki cikin sanyin murya. “Alhaji… idan na amince, you’ll give me the whole box?” Alhaji Sabo ya yi murmushi mai faɗi, sannan ya ɗan matsa kusa da ita. “Why not, my dear? Of course, za ki samu.” Ya ɗan nuna box ɗin da ke gabansu. “Kuma ba wannan kaɗai ba ne. Duk lokacin da kika buƙaci mu sake haɗuwa, ko kuma ni na sake buƙatar ganinki, za mu iya sake yin hakan. Zan sake ba ki wasu irin waɗannan kuɗin.” Ya ɗan dakata, yana kallonta don ya ga yadda maganarsa za ta sauka a ranta. “Infact, duk sau ɗaya da za mu yi, zan ba ki irin wannan amount ɗin. Wataƙila ma in ƙara miki fiye da haka. It all depends on you, baby.” Bintu ta zuba masa ido na ɗan lokaci. “Every time?” Ta tambaya a hankali. “Every time, my dear. Ba za ki yi nadamar haɗuwa da ni ba.” Ya sake kallon box ɗin kuɗin, sannan ya mayar da idanunsa kanta. “Think about it. Ba sai kin damu da komai ba. Duk abin da kike buƙata, za mu iya tattaunawa.” Bintu ta yi shiru. A wannan lokacin, kuɗin da ke gabanta sun fara zama kamar wata babbar dama a idanunta. Ba wai box ɗaya kawai ba ne zai shiga hannunta, akwai yiwuwar samun wasu da dama a nan gaba. Amma duk da haka, tsoron abin da yake nema bai bar ta gaba ɗaya ba. Alhaji Sabo bai sake magana ba. Kawai ya yi shiru yana kallonta, hannunsa ɗaya na kan cikinsa yana shafawa a hankali. Bintu kuwa ta ɗan sunkuyar da kanta, idanunta a kan box ɗin kuɗin da ke gabansu. Ta yi shiru na wasu daƙiƙu, kafin daga bisani ta ɗago kanta ta kalle shi a hankali. “Na amince.” Alhaji Sabo ya ɗan ɗaga gira, sannan murmushi ya bayyana a fuskarsa. “Are you sure, baby?” Bintu ta ɗan haɗiye yawu, ta gyada masa kai a hankali. “Eh.” Murmushin Alhaji Sabo ya ƙara faɗaɗa. Ya kalli box ɗin kuɗin, sannan ya mayar da idanunsa kanta. “Good girl. Kin ga? Ai yafi da muka fahimci juna tun farko.” Ya yi wata ƙaramar dariya, sannan ya matsa box ɗin kusa da ita. “Toh, waɗannan naki ne. Kuma ki sani, wannan ba shi ne na ƙarshe ba.” Bintu ta kalli kuɗin, murmushi kaɗan ya bayyana a fuskarta. Amma a ƙarƙashin murmushin, zuciyarta har yanzu ba ta samu cikakkiyar nutsuwa ba.
Bacci ne ya sake ɗaukar su, har zuwa wajen ƙarfe biyar na yamma. Raihana ce ta fara buɗe idanunta a hankali. A yanzu ita ce kwance flat a kan gadon, yayin da Zayd yake kwance da kansa a kan kirjinta, ya kankame ta sosai kamar wani zai iya zuwa ya ƙwace masa ita. Ta sauke idanunta a kan fuskarsa. Ta daɗe tana kallonsa na wasu mintuna, tana kallon yadda yake bacci cikin nutsuwa. Fuskarsa ta yi calm, babu irin wannan serious expression ɗin da ya saba kasancewa a tattare da ita. Ta yi murmushi kaɗan, sannan ta sake lumshe idanunta. A hankali ta fara motsi. Fitsari take ji sosai, kuma shi ne ma abin da ya tashe ta daga barcin. Jin tana motsi-motsi, Zayd ya buɗe idanunsa a hankali. Ya ɗago kansa daga kirjinta, sannan ya sauke idanunsa a kan fuskarta. “What did you want?” Ya tambaya cikin muryar bacci. Raihana ta ɗan turo baki, sannan ta amsa a hankali. “I want to pee.” Zayd ya ɗago hannunsa ya ɗora a saman marar ta, yana shafa wajen a hankali. Raihana ta runtse idanunta, wallahi ji tayi kamar ma fitsarin zai zubo mata. Zayd ya yi murmushi ganin yanayinta, sannan ya miƙe daga kan gadon. Ba tare da ya ce komai ba, ya sunkuyo ya ɗago ta sama cak a hannunsa. Bai tsaya ya zaunar da ita a wani wuri ba, sai da ya kai ta har ƙofar toilet ɗin. Ya sauke ta a hankali, sannan ya kalleta. “Ki yi, sannan ki sake wanka da alwala. We’ve already missed Asr prayer, kin ji?” Raihana ta gyada masa kai kawai. Zayd ya ɗan ja baya, amma idanunsa har yanzu suna kanta. “Take your time, okay?” Ta sake gyada kai, sannan ta murɗa handle ɗin ta shiga ciki. Shi kuma ya tsaya na ɗan lokaci yana kallon ƙofar, kafin daga bisani ya juya ya fice daga ɗakin. Raihana ta yi wanka da ruwan ɗumi, ta sake yin sitz bath kamar yadda tayi dazu. Ta zauna na ɗan lokaci tana ba jikinta damar samun sauƙi, sannan ta wanke jikinta sosai. Alhamdulillah, zuwa wannan lokacin ta ji sauƙi sosai. Kamar ma babu wani abu da ya faru. Jikinta ya sake warwarewa, ba ta kuma jin irin ciwon da ba. Gaskiya ba ta yi tsammanin za ta samu sauƙin haka cikin ɗan lokaci ba. Bayan ta gama, ta yi alwala, sannan ta fito daga toilet ɗin. Ba ta tsaya yin sallah a cikin ɗakin ba, ta wuce zuwa nata ɗakin. A can ta shimfiɗa darduma ta yi sallar La’asar, sannan ta zauna ta yi azkar ɗinta. Bayan ta gama, sai ta miƙe ta nufi gaban madubinta. Ta tsaya tana kallon kanta na ɗan lokaci, kafin ta ja kujerar madubin ta zauna. Ta ɗauki man shafawa ta fara shafawa a jikinta a hankali. Bayan ta gama, ta gyara fuskarta ba tare da ta yi kwalliya mai yawa ba. Amma duk da haka, fuskarta ta yi kyau sosai. Ta miƙe ta nufi wardrobe ɗinta, ta buɗe ta fara duba kayan da ke ciki. Ta ɗauko underwears ɗinta tare da wata doguwar rigar lace mai embroidery, light pink colour. Ta ajiye su a kan gadon, sannan ta juya kaɗan tana shirin komawa wajen madubi. A dai-dai lokacin ne Zayd ya shigo. Tun da ya koma ɗakinsa bai same ta ba, sai ya yanke shawarar zuwa nata ɗakin. A hankali ya turo ƙofar ya shigo. Yana sanye da wani yadi mai launin grey wanda ya yi masa kyau sosai, sai agogon hannunsa da ya ƙara masa armashi. Ganinsa ya sa Raihana ta juya da sauri. Saboda daga ita sai ƙaramin towel ɗin da ta ɗaura a jikinta, wando ko laps dinta bai rufe ba sosai nan take ta ɗago hannayenta tana riƙe shi da ƙarfi. Zayd ya tsaya yana kallonta na ɗan lokaci, sannan ya yi murmushi. A hankali ya tako zuwa gare ta, hannunsa ɗaya a aljihun wandonsa. Ya ƙarasa har bayanta, ya tsaya daf da ita. Sannan ya janye hannunsa daga aljihun, ya rungumota a jikinsa bayanta ya jingina da kirjinsa, ya ɗan sunkuyo kansa. Hannayensa suka sauka a kan ƙugunta, ya riƙe ta a hankali. “Dakin naki mai maciji kika shigo kika daɗe?” Ya raɗa mata a kunne. Raihana ta ja ajiyar zuciya, sannan ta ɗora hannunta a kan nasa. “Ai yanzu babu.” Ta fada cikin sanyin murya. Zayd ya ɗan ciji kunnenta a hankali, yana murmushi. “Dama can babu. So kike lokacin ki dawo ɗakina, shi ya sa kika ce akwai.” Da sauri Raihana ta juya ta fuskance shi. Kamar ta manta da maganar kunyar towel ɗin da take jikinta, ta ɗago fuska tana kallonsa. “Wallahi akwai! Na gan shi da idona. Me ya sa zan ce zan dawo ɗakinka a lokacin, bayan ko kallo ban ishe ka ba?” Ta faɗa cikin fushi irin na shagwaɓa, kamar za ta fashe da kuka. Zayd kuwa kallonta kawai yake yi, murmushi yana ƙara faɗaɗa a fuskarsa. “Ai so kike na fara kulaki lokacin shiyasa.” Sai raihana ta sake turo baki ta na bubbuga kafa Cikin shagwaba. “Ni wallahi sharri kayi min ba zan sake zuwa dakin ka ba kuma ma ko ranar ai kaine ka kaini da kanka ba nice na Kai na ba.” “Da gaske ba zaki sake zuwa dakina ba?” Ya tambaya haryanzu murmushin bai bar fuskarshi ba. Da Sauri ta amsa, “Ehh.” Ya gyada kai kamar ya amince da maganarta. “Okay. Then I’ll have to come and stay with you.” Raihana ta yi shiru. Zayd ya ɗan karkatar da kansa, yana kallonta da murmushi. “Ko wannan ma ba ki yarda ba?” Ta kasa amsawa, sai ta sauke idanunta. Zayd ya tsaya kawai yana kallonta. A wannan lokacin, ya ji wani irin abu a zuciyarsa da ba ya iya bayyana wa. Yadda take yin shagwaɓa, yadda take turo baki idan ya tsokane ta, yadda take ƙoƙarin kare kanta ko da kuwa ta san ba za ta iya yin nasara a kansa ba. He loved this girl desperately. Kamar soyayyarta tana sake ratsawa cikin jikinsa a duk lokacin da ya kalleta. Ba wai kawai yana son kasancewarta kusa da shi ba ne, yana son duk waɗannan ƙananan halayenta da take yi ba tare da ta sani ba. A hankali ya ɗago hannunsa ya gyara mata ɗan gashin da ya sulale a goshinta. “Come here, my love.” Ya faɗa cikin sanyin murya. Raihana ta ɗa make kafada taqi, sai ya dan janyo ta sai a sannan ta matso kusa da shi. Ya rungumota a hankali, ya manna leɓunansa a goshinta na ɗan lokaci. “Do you know something?” Ta ɗago idanunta ta kalle shi. “What?” Ya yi murmushi. “I could listen to you complain about that imaginary snake all day.” Raihana ta buɗe baki tana kallonta. “Imaginary kuma?” “Yes, sweetheart. Imaginary.” Ta sake turo baki, shi kuma ya fashe da dariya. “Okay, okay. I believe you.” Ya ɗaga hannayensa kaɗan kamar ya miƙa wuya, amma murmushin da ke fuskarsa ya nuna cewa har yanzu bai daina tsokanarta ba. Raihana ta yi ƙoƙarin kau da fuskarta, amma ya riƙe ta a hankali. “Hey, look at me.” Ta ɗago idanunta. “That’s my girl.” Ya sake yi mata kissing a goshinta, sannan ya kalli kayan da ta ajiye a kan gadon. “Are you getting dressed, sweetheart?” Raihana ta gyada masa kai a hankali, ba tare da ta ɗago idanunta ba. Zayd ya yi murmushi, sannan ya ƙarasa wajen kayan da ta ajiye a kan gadon. Ya ɗauko bra ɗin a hankali, ya tsaya yana kallonta na ɗan lokaci kafin ya ɗago idanunsa zuwa ga raihana. Raihana kuwa ta riga ta ɗauke kanta gefe, kamar ba ta ma san yana kallonta ba. Zayd ya yi murmushi. A hankali ya tako zuwa gare ta, ya tsaya a bayanta. Hannunsa ɗaya yana riƙe da bra ɗin, ɗayan kuma ya kai shi kan towel ɗin da ta ɗaura a jikinta. Ya ɗan kama gefensa yana shirin janyewa. Da sauri Raihana ta riƙe towel ɗin da hannayenta biyu. Zayd ya yi ƙaramar dariya, sannan ya sunkuyo kusa da kunnenta. “I want to help you prepare, sweetheart.” Raihana ta maƙe kafaɗunta. “Ni ba na so.” Zayd ya ɗan karkatar da kansa, yana kallon yadda take ƙoƙarin kau da shi. “Please, wife. I want to dress my baby myself.” Ta yi shiru, ta ƙi magana. Zayd ya ɗan matsa kusa da ita kirjinsa ya mannu da bayanta sosai sannan ya sunkoya da bakınsa dai dai kunnenta calmly yace, “Please…” Raihana ta runtse idanunta, tana jin kunyar ma kallonsa. Ta yi shiru na ɗan lokaci, kafin daga bisani a hankali ta sassauta hannayenta daga riƙe towel ɗin. Zayd ya tsaya yana kallonta na ɗan daƙiƙa, sannan ya janye towel ɗin a hankali ya fadi kasa. Ya ɗago bra ɗin, ya saka ma ta shi cikin nutsuwa. Raihana kuwa idanunta a rufe suke, zuciyarta na bugawa kamar za ta fito daga kirjinta. Da ya gama, sai ya gyara mata shi a hankali. “All done, sweetheart.” Ta buɗe idanunta kaɗan, amma har yanzu ba ta iya kallonsa. Zayd ya yi murmushi, ya sunkuyo ya yi mata kissing a kafaɗarta. Hannayensa suka dan sauka kan boobs din ya dan shafa lightly duk suka Sauke ajiyar zuciya kusan a tare. “See? Nothing to be nervous about.” Raihana ta ɗan turo baki. “Ni ka fita toh.” Ya yi dariya. “Naje ina? I was only helping my wife.” Ta girgiza kai, shi kuma ya ƙara murmushi. “Okay, okay. Na daina.” Amma daga yadda yake kallonta, Raihana ta san bai daina jin daɗin kunyar da take yi ba sam. Zayd ya dan juyo da ita ta dawo duna facing juna kamar irin zais barta ta karasa shirin yanzu, amma a zahiri yana son ya ƙara kallonta. Sai dai kafin ya samu damar yin hakan, Raihana ta yi saurin rungume shi, ta manne jikinta da nasa. Batason ya gan ta a haka, daga ita sai bra kawai. Zayd ya yi dariya, yana kallonta. “Toh, bamu gama shirin ba kenan? Kin riƙe ni kamar ba zaki sake ni ba.” Ta ɗa make kafaɗa, ta ƙara ɓoye fuskarta a ƙirjinsa. “Ka rufe idonka. Zan yi da kaina, please.” Ya sake yin dariya. “Me ya rage kuma? Pant ne fa zan sa miki sai……” “Ahhhhh!” Raihana ta yi ƙara da karfi, tana ƙoƙarin katse shi. Bata son ma ya ƙarasa faɗin abin da ya fara. Zayd ya fashe da dariya sosai, yana kallon yadda ta rikice. Amma ganin yadda ta fara shirin kuka ya sa ya dakatar da dariyar. “Okay, okay, sweetheart. Na ji.” Ya shafa bayanta a hankali, sannan ya cika mata alƙawarin da ta nema. Ya fara kokarin juya mata baya. “Just turn around!” Ta sake fada. Zayd ya yi dariya, sannan ya juya gaba ɗaya. “Here you go. Na juya. Ki ƙarasa shirin naki.” Raihana ta ɗan ɗaga kai ta tabbatar da cewa da gaske ya juya, sannan ya saki numfashi. Zayd kuwa yana tsaye a wurin, murmushi bai bar fuskarsa ba. “Amma fa, Habibti, kin san ni mijinki ne ko?” Ta yi shiru, ta ƙi magana yayin da take ɗaukar sauran kayan da za ta saka. “My Raiii?” “Me kuma?” Ya yi murmushi. “Nothing. Ina jiran matata ne kawai.” Raihana ta yi saurin ƙarasa saka sauran kayanta, tana gyara rigar lace ɗin da ta saka a jikinta. Ta kuma ɗauki dankwalin tana kokarin daurawa. Zayd kuwa yana tsaye har yanzu, yana jiran ta gama. “Okay, wife. Let me wait for you downstairs. Ki ƙarasa shirin ki. We’re having dinner outside, daga nan kuma za mu je wajen Ummie.” Raihana ta ɗaga kai ta kalle shi, sai ta amsa a hankali. “Toh…” Duk da ta yi ƙoƙarin ɓoye hakan, maganar zuwa gidan Ummie ta faranta mata rai. Zayd bai sake juyowa ba. Ya nufi ƙofar ɗakin, ya buɗe ta sannan ya fita, ya bar ta ta ƙarasa shirin cikin nutsuwa.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol