Free chapter 路 Read without an account

Page 3

by khadijah danasabe 路 FORBIDDEN LOVE

馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮
         FORBIDDEN LOVE
                      馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮


DijahAM(Oum Amani)




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 



Page 3



*ARWA'S POV*


  Yau gaba daya a gajiye nake saboda tun da na 陌sa office ban zauna for good 30mins ba. Ni dai da badan nasan ba wanda na bata wa rai ba an office da sai na ceh Boss dina is torturing me Allah.

Kamar yau din d眉k wahalar dana sha an office bai 陌sa ba, Baaba sai da ya san yadda yayi yai forcing dina ganin Habeeb yau.

Ajiyar zuciya na sauke ina tuna kiran da Baaba ya min daren jiya a waya.  
           Ina kwance nayi shirin bacci around 10 kiran Baaba ya shigo waya ta, ban bata lokaci ba na dauka inda ya sanar da ni yana son gani na a palon sa.

Mike wa nayi ba tare dana daura mayafi akan pj's din jikina ba na nufi downstairs. Kofar palon sa na bude bakina dauke da sallama, wutar palon a kashe take sai hasken Tv kawai dake haska palon. Baaba na zaune akan kujera yay谋n da ya daura kafar Maama akan cinyar sa yana mata tausa, ita kuma tana basa Apple a baki suna magana fuskokin su dauke da murmushi.  Shin na manta na fada muku cewa iyaye na suna kaunar junan su sosai koh? Ni kam dai ban taba ganin inda ma'auratan da suka bawa shekaru 35 da aure baya ba kuma suke kaunar junan su kamar ranar da suka yi aure ba irin su Baaba, bama manya ba har young couples bana ganin suna wa juna irin wanga soyayya. Haka kurin sai su dauki leave a wajen aiki su tafi abroad huta wa, ko kuma da daddare su sha wanka su fita restaurant cin abinci. Sbd Allah Ina ganin irin wannan kaunar taya bazan yi nima fatan nayi irin ta da nawa masoyin ba.

    Ban wani damu da ganin su a haka ba tun daba sabon abu bane a waje na, guri na samu a kasa na zauna Ina mai gaida Baaba. 

A dake ya amsa min wanda bai dame ni bah sbd ynxu kam i'm no longer daddy's girl. Fuskar sa ba yabo ba fallasa ya ceh "gobe Habeeb zai zo?"

Is not a question is a statement, nasan ya san cewa ban sani ba ai tun da ba daukar wayar Habeeb din nake bah.

Numfashi na sauke ina murza goshina dake kwance da gashi na ceh "bai fada min bah"

"Taya dama zai fada miki bayan ba daukar wayar sa kike bah, ni fa ban ma san mai kika dauke mu ba mutanen banza ko kuma wadanda basu san inda ke musu ciwo bah. Shekarar ki nawa? Ina you are 25 amma har ynxu kin tsaya kina saka wa zuciyar ki wasikar jaki, ki sani in har k谋na haka ne sbd wannan arnen to wallahi ba a gida na bah" Baaba ya fada cikin fusata, don ab谋n kam yana neman yafi karfin sa da d眉kkan alama. Gwanda tun wuri ya taka wa abin birki.

Hawayen da ke neman zubo min na shanye, cikin dakiya na ceh "Ni bana s枚n Habeeb Baaba"

"To don ubanki Arwaa kar ki so sah, na ce miki kar ki so sa din kin ji" Baaba ya fada yana ji kamar ya mike ya wanka mata mari. Cikin takaici ya cigaba da cewa "ai ni tsakani na da wancan arnen sai dai Allah ya 陌sa, baki taba min musu ba sai a dalilin sa, taya ma zaki yi tunanin zan taba son sa bayan kasancewar sa Christian"

"Baaba ku taya ni da addu'a, sai kuga Allah ya shirye sa ya musulunta ku....." ban kai ga karasa wa ba sbd wani gigitaccen mari da Baaba ya dauke ni da shi.

Kukan da nake ta danne wa ne tun tuni ya kufce min, idona dake zubar da hawaye na dago na kalli Maama da ta mai da kallon ta Tv tana kallo kamar bata 艧an abinda ke faruwa bah.

Wani abu naji ya tsaya min a wuya wanda ya kasa wuce wa. Zan yi magana kenan Maama ta ceh "ke kuwa wani irin taurin kai ne haka da baza ki yi wa mahaifin ki biyayya bah Arwa, ko wanne d'a yana kokarin ganin ya faranta wa iyayen sa don neman albarka amma ke ayi ta fama da keh. Habeeb dinnan ba shi da m眉gun hali Arwa, cousin din ki ne wanda tun yana yaro a gaban mu ya tashi. Mu ba aure zamu miki na dole ba amma at least give him a chance kin ji"

Kuka na sake fashe musu da shi mai ciwo wai ko dan zasu tausaya min amma na makaro domin kuwa in har akan Wanda zuciya ta ta zaba matsayin shugaban ta neh su Maama basu goyan bayana ko kadan. Bama su kadai ba kaf duniya in ka cire Ya Abd眉l ba wanda yke bani hope tun da ita ma ynxu Haala ta koma team Habeeb da alama.

Baaba sai da ya kara min warning akan kin fita wajen Habeeb kafin ya sallame ni. 

A haka ne na samu kai na yau bayan na dawo daga office a zaune gaban mirror ina shafa lip balm bayan na gama shirya wa cikin wata navy blue A shape gown din shadda wacce aka wa aiki tun daga sama har kasa. Ba wani kwalliya nayi ba, kwalli kawai nasa sai lip balm wanda ya kara haska pink lips dina dake da dan fadi kadan.

Navy blue veil din dake kan gado na dauka na yafa daga kai na, sai da na tabbatar ya rufe mun gashi na sannan na zira black Gucci flat shoe na fita zuwa Palon baki.

Ina shirya wa daya daga cikin maids din gidan ta min knocking ta sanar da ni zuwan sa. Duk da yadda bana son sa amma baxan iya shanya sa ba. Son sa ne kawai bana yi, wulakanci ba abu bane da Maama ta koya mana.

Sai da nayi knocking kofar sau uku sannan na tura na shiga bakina dauke da sallama....





Ohkkkk!!! 

Ni dai ynxu ban san mai zan ceh bah馃槓 

Ke dai Arwaaa kamar son da kike wa wannan mutumin yayi yawa馃か ki dan bawa Habibu chance mana
馃え

Ke yadda ma Habeeb yake son ki in wasu neh ai da tuni an wuce wajen馃槒

Next page dai zamu ga Habeeb In sha Allah馃槈

Zamu ji in ya cancanci a basa chance ko kuwa a kyale sa馃槏



Comments and share please



***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol