Free chapter 路 Read without an account

Page 7

by khadijah danasabe 路 FORBIDDEN LOVE

馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮
         FORBIDDEN LOVE
                      馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮


DijahAM(Oum Amani)




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 



Page 7



*RHYS*


   
    Baki bude Adam yake kallon Rhys bayan ya gama masa bayanin gobe zai tafi secondary school din yan mata ya dinga koyar wa. 陌n ban da ya san cewa Rhys ba mutum bane da zai zauna ya fadi karya ba, ba abinda zai sa ya yadda.

Numfashi ya sauke ya ce "ynxu da kake medicine me ya hada ka da teaching kuma?"

Daga kafada nayi duk da abin yana bata min rai amma ya zan yi, aikin Papa neh. Daga zuwa Nigeria kawai ya tura ni makarantar. A cewar sa da akwai criminals a wajajen location din school din, ya tura ni ne don na kula da yanayin motsin wajen. Abin da ya ce min kenan kawai na kula da motsin na dinga masa reporting, kaf Soldiers din Nigeria a tasa wa za'a bawa aikin nan sai ni. 

Maa da ta min magana ne yasa na yadda in da ba haka ba, sai dai a wayi gari a ga bana nan, na koma inda na fito.

Dariya Adam yayi yana kwanciya akan luxury sofa din da yake zaune ya ce "zan raka ka amma gaskiya, I want to see my best friend first day at work"



    The next day muka tafi Kano ni da Adam a one of the private Jet na Papa. Da muka 陌sa already ana jiran mu, don haka shiga mota kawai mukai muka tafi gidan na da ke Ahmadu Bello Way. Anan zan dinga zama weekends  sai weekdays kuma na dinga kwana a Teacher's quarters. 

Duk yadda Adam ya dinga naci akan mu tafi school din tun a yau ko kula sa ban yi ba. To me zai kai ni can ma bayan duk abinda zan bukata an jera min shi a can. 

    Tun 5am nayi wanka na shirya cikin navy blue jeans and black plain loose shirt. 

Karamar traveling bag na fito da ita kawai wacce ke dauke da duk wasu abubuwan da zan bukata sai wayoyina guda biyu. Kiran David nayi ya karba ya sa a motar da zan tafi da ita Black Model S Tesla. David zan iya cewa he's like my P.A. Yes P.A bayan ba aikin da nake yi for now. Aikin Papa ne since last year ya tura mun shi, bayan kuma soldiers din dayai assigning duk lokacin da na shigo Nigeria zasu dinga bina kusan ko ina. A cewar sa for my own safety, wanda ni ban ga amfanin sa ba tun da ba wanda na cuta ko na kashe.

Sai da na bari Adam ya tafi masallaci sallar Fajr ta sake da suke yi sannan nai maza na shige back seat, David kuma ya shiga driver seat yaja motar muka tafi.

Ina hauka ne zan bari Adam ya san inda zan dinga teaching. Ai in har ya sani almost everyday sai ya zo In bai dawo bama gaba daya ya tare da ni ba. 

1 hour drive ne ya kai mu makarantar. Muna zuwa office din principal na je mukai magana, ya fada min duk abinda ya kama ta na sani daya shafi school din sannan ya raka ni office dina.

Ba wani babba bane ba amma kuma ya min tun da ba zama nazo yi ba. 陌n nayi kokari na kai karshen term din.

    Zama nayi a kam sofa dake office din ina danna waya. Nayi going through classes din da zan dinga taking. Bana bukatar sanin wanne topic zan m眉艧眉 in har Maths ne u can call me a genius.

Ss3 Anayi taking an hour before break time. Daga su sai kuka Ss 2 B, shi sai last period don haka na mai da hankali na gurin karanta wani littafi daya shafi Medicine.


    Ban yi 4 hours ba da shigowa school din amma gaba daya na gaji, ni ban san wanne laifi nayi wa Papa ba yake son azabtar da ni, in ba wahala yake so ya bani ba taya zai turo ni kawai don nayi teaching sbd ayi tracing criminals.

Kayan bakin cikin bai gama kama ni ba sai da na shiga last class dina naga wata student tana kwance. Da farko ban mai da hankali akan ta ba, har nayi introducing kai na na fara koya m眉艧眉 abinda ya kawo ni, duk da bana son teaching ba hakan yana nufin zan yi wasa da duty na ba.

Ganin almost 30minutes da fara ma class din bayani amma student din still bata tashi ba ya sa ni nufar seat din ta.

"Hey" na fada cikin kame murya, amma bata ko motsa ba.

Sau uku ina magana amma bata motsa ba sai da wacce ke kusa da ita ta taba ta sannan ta tashi zaune tana hararar student din data taba ta.

Kallona tayi da wasu irin oily eyes da suka sa gabana ya buga da karfi. 

Kallon sa take ita ma cikin mamakin wane shi da zai zo ya tsaya mata akai. Duk da hazel eyes din sun masifar daukar hankalin ta hakan bai hana ta yatsina fuska ba.

"Who are you?" ta fada tana dage gira daya.

"Are you Mad?" Ya fada tana tsare ta da hazel eyes din sa masu sa mutum shiga taitayin sa. Lallai bata da hankali, 30mins ya dauka a class din su tana bacci sannan kuma ynxu ta masa wannan tambayar ta rainin hankali.

Ita kam kallon sa take kawai tana mamakin tsaurin idon wannan black Arab din dake tsaye a kan ta, shi yake cewa tana hauka. Mai ta masa don kawai ta tambayi ko waye shi...




NOT EDITED馃檶馃徎


Yau no kwaments daga gare ni馃槀

I'm lazyyyyyyy nasan daga yanayin typing dina you can guess




Ayi hakuri dai da yadda aka samu page din馃馃徎




Kwamentssss don Allah



***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol