Free chapter · Read without an account

Page 9

by khadijah danasabe · FORBIDDEN LOVE

💫💫💫💫💫💫
         FORBIDDEN LOVE
                      💫💫💫💫💫💫


DijahAM(Oum Amani)



Assalamu alaikum🗣️🗣️

JAMA'A💃💃💃


Ina uwar gida, amarya, to duk ku matso muna d mgn, kufito kuyi booking set mai suna grooms set (5in1)natural remedies, with zero side effects acikin set dinan Muna da __

 1,DAHUWAR ZAKARA
2,ZUMA,
3,TSUMMI
4,SHA DA LIPTON   
5, TSUMMIN SANNYI

Hajiya inde kika siyawa oga wanan ko angon ki kuma yayi anfani dashi basu yimishi ba to kizo inbaki kudin ki hajjajju😉

A wanna set na maza 5in1

Akwai DAHUWAR ZAKARA😋
Zumar ingarman namiji😉
Akwai tsumin sanyi😗😋
Akwai Nasha d Lipton
Akwai tsumin  a fafata(yamayar dakai Dan 20yr )💃💃

Anfanin wanan set din suna d yawa

Yana wanke mara,yana mgnin sanyi,yana temakawa gurin dadewa ana gamsar d iyali, ga masu matsalar saurin kawowa,sanan yana mgnin kankancewar gaba,yana karamata girma dakuma karfi,sanan masu matsalar low spam count yana temakawa kawairai,Kai abubuwan d yawa bazasu gama faduwaba, sai Wanda ya gwadane zai gane me ake fadi🙌🏻🫶

Ina wadanda sukai planning sun Dena amma har ynxu ciki shiru, masu PCOS,infertility ko blocked tube. To don Allah kuzo muyi magana, Uwar Sudais na neman ku🫶💃💃💃

Kuyi maza don Allah🫰🏻 kun san dai a wanga harka baa sanya💃💃💃💃💃



BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 



Page 9



*ARWA'S POV*



A kwana biyun nan duk sai da na tattara bayani akan Mr Rhys kamar yadda naji sunan sa. Sai dai abin bakin cikin bayanan ba wasu masu amfani bane. Kawai dai sunan sa na sani sai kuma kasancewar sa ba musulmi ba, sai ko abın babban bakin cikin shine daga zuwan sa 3days ago har mata da ywa sun fara crushing, ba teachers ba kuma ba students ba.

A students din ma hadda Jidda ita nata yafi na kowa fito wa fili. Ai sai naji na kara tsanar Rhys dinnan, meye abin so Allah na tuba kawai don sun gan sa kamar bakin balarabe shine abin yake burge su. Ita fa Jidda sbd hauka har hostel din mu ta shigo tana fadin yadda ta fara jawo hankalin sa har sunan ta sai da ya kira. Dük da yadda ni da Jidda muka tsani juna sai da ta bani tausayi, ita kuwa ta rasa wa zata so sai Christian an fadi banza.

Tsanar sa a kullum kara hauhawa take a zuciya ta, ko da yaushe na tuno da abinda ya min ji nake kamar zuciya ta zata fashe. Haala tun tana min magana akan wannan tsanar da nake wa Rhys har ta kyale ni, to waye zai ce min na daina tsanar sa kuma naji, ai babu.

    Yau Monday tun da na tashi da safe nake cikin bacin rai sbd muna da further Maths first period, gaba daya rai na a bace yake amma haka bai sa naki kimtsa jikina ba, I want to prove him wrong da ya ce i stink don haka na bi jikina da duk turarukan da nake da su. Sai da naji kamshin yana hawa min kai sannan na ajiye na saba jakata na fito.

Already Haala tana dinning nima can na wuce, a dogon table din da ake zaune na hango Jidda da tawagar ta sai kuma Haala ita ma tana cin Noodles din ta hankali kwance. Ni na san Haala baza ta taba zama a table din ba bayan ta ga su Jidda, sai dai Jidda ce ta zo ta zauna. Ban sake kallon inda su Jidda ke zaune ba sai empty sıt din kusa da Haala na zauna tun da nasan ni ta ajiye wa.

Haala da tunda Arwaa ta shigo hall din ta saki baki da hanci tana kallon ta sbd mamakin yadda taga yau Arwaa din ta chanja, sai da ta zauna kusa da ita sannan taji azababben kamshin da ke tashi daga jikin aminiyar tata. Duk da fuskar nan ba powder amma sai sheki take yi gashi ta saka kwalli abinda ba ko yaushe take sawa ba, sai ya kara wa fararen idon ta wani irin kyau da kwarijini, lips dinnan sun sha lip gloss sai daukar ido suke. Ita wallahi sai abın ma yaso bata dariya, ta san halin aminiyar tata, wannan gayun dük sbd new teacher din su ya ce mata tana wari ne. Kasa kasa ta ce "wai baki hakura ba dama"

Ba tare dana kalle ta ba ina sipping hot tea dina a hankali na ce "Haala kenan, mutumin nan ya min abinda ba'a taba min ba, matukar ban rama wulakancin daya min ba Wallahi baxan taba samun nutsuwa ba.

Girgiza Kai kawai Haala tayi cikin kula wa ta ce "ki dai kula, kin ga he's your teacher"

Tabe baki na nayi ba tare da na sake cewa komai ba sai tea din da nake sha kawai, ni dama ba wai mayyar abinci bace, in aka ce maka tea da kuma Kayan zaki, anan nafi kauri sai kuwa nama ooooo ina kaunar sa, har na fara craving din sa can't wait lokacin lunch yayi....

   
     Jidda kuwa kallon inda Arwaa take zaune tayi ta dauke kai zuciyar ta tana tafasa, ita bata san mai yasa a komai Arwaa ta fita ba, duk abinda take so sai y kasance Arwaa ce ta ke da shi ba ita ba.
New Teacher din su tun shigowar sa zuciyar ta tayi wani irin bugawa da a take ta san iş love at first sight, tayi tunanin musulmi ne sai dai yana bude baki cikin thick British accent din sa ya kira kan sa da *RHYS EMMANUAL JIMOH* wanda take tsammanin kaf dangin su ba musulmi. Duk da haka son da take masa bai ragu ba sai ma karuwa da yake the more tana kallon sa. Ta basa attention din ta gaba daya don tana so ta gane abinda yake koya müşü, tayi alkawari wannan karan dai sai ta doke Arwaa daga first position din data rike tun Jss 1.
    Ba irin yadda bata karatu amma ana bada result sai kaga ita ce dai a second din, abın haushin kuma tafi Arwaa mai da hankali tayi karatu, tun da ko lokacin exam ne tana sa friends din ta suna spying akan Arwaa sai ace mata English novel ma take karanta wa. Ko kuma tana bacci, gashi in suna exam hall ana raba paper take kwanciya tayi ta baccin ta sai an yi ringing first bell dake indicating saura 50mins take tashi ta fara rubutu amma still ita ke daukar first. Ta rasa yadda zata yi shiyasa wannan term din tun da aka fara classes take karatun exam, ko wanne text ko assignment ko class work kokari take taga ta cinye duka, ita Arwaa dama sbd bakin hali bata nuna wa kowa Text din ta bayan anyi marking, ta rasa ya zata yi da yarinyar. Karin abin haushin bai kare ba sai da ya kasance Mr Rhys a Maimakon ya fara gane ta yayi magana da ita sai ya kasance Arwaa ce ya fara wa magana kaf class din ma. Amma dai bata wani damu sosai ba ganin yadda maganar ta su ta kare dük da kishi da take yi.

Sanin cewa a ynxu ba wanda Arwaa din ta tsana irin MR Rhys yasa Jidda kallon friends din ta tana murmushi ta ce "can't wait to see Mr Rhys today wallahi, kun san yadda na kagu na sake ganin beautiful face din sa dinnan" ta fada yadda ta san har Arwaa sai ta ji, sai dai bakin hali irin na Arwaa din nuna wa tayi kamar bata şan ma akwai wasu a table din ba.

Lubna aminiyar Jidda ce ta ce "wai da gaske dama kike Jidda"

Cikin nuna rashin fahimta ta ce "akan me?"

"Akan kaunar Mr Rhys mana" Lubna ta fada tana kashe mata ido daya.

Dariy suka sa dükkan su da sauran friends din su. Yayin da wata ta ce "magana ta domin Allah fa ya hadu, ni Kai na farkon shigowar sa na dauka black Arab ne, ku kunga kyau kuwa Maa sha Allah ga kuma class, sannan daga gani akwai masu gidan rana"

"Ke ban ganeba fah, kar ku dinga checking out my new boo fah" Jidda ta fada cike da shakiyanci...

Arwaa da duk abinda suke cewa tana sauraron su ji take kamar ta je tai ta gwara kawunan su sbd bakin ciki, wanne irin lalace wa ne wannan ko dai su basu da hankali ne. Ajiyar zuciya ta sauke tuna wa da tayi cewa ai dama su Jidda ba wai lafiyar brain isashshiya ce da su bah.



     Yau ba'a dade an assembly ba suka dawo class. A front sıt muke ni da Haala, bana kaunar zama a gaba yau amma bazan iya tashi ba in har yağa na tashi kenan ma na damu da abinda yai min.

Book din da zan yi amfani da shi na ajiye akan table tare da pen, Haala ke min magana tana so tayi waya da Bashir zan rakata gurin wata metron da muke karbar wayar ta in muna so muyi waya gida. A cewar Haala tayi missing Bashir.

Bashir cousin din ta ne wanda yake son ta tun tana shekara goma, sai da muka shiga Jss 3 sannan ta fara basa fuska suna magana kadan kadan wanda shima a lokacin ne dama ya fito ya fada mata baki da baki cewa yana son ta. Familyn su ba wanda be son Bashir Haala yake so ba, nima ina son ta da Bashir sosai don ya san mutuncin mutane kuma ni already ma na basa vote dina. Wannan year din ya gama university duk da dai ba maganar aure ynxu sai Haala ta gama school shima kuma ya fara aiki.

Ban san cewa Mr Rhys ya shigo ba sai kamshin sa naji kawai ya çıka min hanci. Wani irin faduwar gaba na yayi da sauri na dago Kai na idona cikin hazel eyes din sa.

Yana tsaye cikin designer shirt and jeans hannun sa daya cikin aljihun sa yayın da dayan yake rike da marker. Kallon ta yake yadda ta tsare sa da ido yana mamakin rashin kunyar ta. Abında ya mata last week bai zama ishara a gare ta ba kenan koh.

Ni kuwa cikin dakiya na dauke idona daga cikin nasa Ina kallon class din, sai a lokacin na lura kowa na tsaye ni ce kawai a zaune. Cikin basarwa na mike tsaye nima ina hade rai.........






Toooo Alhamdulillah🥰

Nadawoooooooo💃💃💃


Kunyi missing dina don ni kam nayi missing kwaments din my🤌🥹


Ga Arwaaaa ga Mr Rhysssss😘 mai zaku ce game da burin Arwaaa na rama abinda Rhys ya mata✌️


Ke kuwa Jidda ban san meye matsalar ki ba. Hassada ce ko kuwa rashin waye wa😏


Su masoya Haala da Bashir Allah ya sanya alkhairi Ameen mu sha biki💃💃💃💃




Ayi kwaments my People🏌️‍♀️🏌️‍♀️🏌️‍♀️


Comments and share please 🙏

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol