Free chapter · Read without an account

Page 1-2

by Fatima Abdulhadi Garba · BAN AIKATA BA

*🔥💦 BAN AIKATA BA 🔥💦*





Story & Written By





Fatima Abdulhadi

Fateyzahraah





Destiny

Betray

Love





ALHAMDULILLAHI



Ya Allah kabani ikon faɗin abinda zai amfani al'ummarka ka tsare alƙalamina daga faďar abinda zai cutar da al'ummarka Ameen.

ina farincikin sake haďuwa daku a sabon littafina, mai suna BAN AIKATA BA.



Duk wanda ya canja mini wani abu a ciki ban yafe masa ba.





Ina mi'ko ďunbin godiya da gaisuwa tareda fatan alkairi ga dukkan masoyana, ina godiya da ɗunbin gaisuwarku gareni, ALLAH yasa mudace, muje zuwa LABARI😁👌🏻.



This Book is Dedicated to Na'ima Sulaiman Sarauta (Nimcy Luv) Allah ya ƙara girma da ɗaukaka❤️🥰 My Mentor🤍🌹





𝔖𝔥𝔦𝔪𝔣𝔦ɗ𝔞





Ƙaddara wannan kalmar na nufin faruwan wani abu wanda tuntuni Allah yayi hakan zai faru. A turance ana ana kiran shi da Destiny. Ita kaddara ba Wanda ya isa ya kauce mata kuma ba wanda yasan rananta sai lokacin da Allah yayi zai fara ba wanda ya san randa zata ƙare sai Allah.



__________________________________________





Mikiya Writers Ass...


YOTA/020




Page......1⃣__2⃣





Abuja



7:00AM





Manyan Mansions ne tun daga farkon unguwar har cikin Unguwar tsitt unguwar sai haushin karnuka ne kaɗai ke tashi.

 ~ABOUL MOEZ RATIB STREET ~ aka rubuta a jikin sign board din layin.Tsarin gidajen cikin layin yafi na unguwar ma kyau.

Wani mansion ne wanda yafi kowanne kyau da haɗuwa a buɗe ƙofar gate ɗin take bodyguard's ne a waje birjik suna hira, sanye suke da kayan sojoji wasu kuma na ƴan sanda. Daga compound ɗin gidan ma yafi waje kyau nesa ba kusa ba motoci ne kala-kala gurin guda goma a parking lot part biyu ne a ciki da babba da bene hawa uku a kai sai ƙarami, babban part ɗin da alamu shine na masu gidan. 

Tun daga tsarin ƙofar part ɗin mudubi ne a jikin bango, sai shoe rack da wata irin ƙofa mai ɗaukar hankali. Ƙaton palour ne kujeru set biyar ne a ciki, daga can gefe dinning area ne mutane huɗu ne zaune a gurin, Ƙarar chokula ne kaɗai ke tashi a dinning area, Kyakkyawan matashi ne mai kimanin shekara talatin zuwa da biyar, ya ajiye chokalin hannun shi ya ce "Alhamdulillah" sannan ya ɗauki tissue yana goge bakin shi. Babbar Mace mai kimanin shekaru hamsin da ɗoriya ta ɗago tana kallon shi tana haɗe rai "Har kayi me?, baka ci komai ba fa" Mamma ta faɗa tana kallon shi tare da ajiye spoon ɗin hannun ta, shagaɓe fuska yayi yana cewa "I'm full" dariya matashiyar budurwar dake facing ɗin Mamma ta saki sai kuma ta rufe baki da sauri tana muzurai lokaci guda ya haɗe fuska yana cewa "am i your mate?" "MAHBOOB ka fita a ido na, tohmm" tace tan miƙe wa ta bar gurin dinning ta koma palour, kyakkyawar mace ce wadda tunda suka zauna bata ɗago ba balle tayi magana ta miƙe da nufin barin gurin da sauri Mahboob ya ruƙo hannunta yana sakar mata wani killer smile Yana cewa "wifey ina zaki?"

A hankali da zazzakar muryarta kamar busar sarewa tace "Ɗaki" kamar bata so faɗa ba ɗan zaro ido yayi yana cewa "Bacin kin san yanzu zan fita zaki tafi ɗaki?, Ki bari muyi sallama sai ki je kiyi ta zaman ki"

Wani ɗan murmushi ta saki kana ta dawo ta zauna a kujerar tana cewa "Na zaci sai anjima zaku tafi duka duka fa 7:30 AM" tace tana kallon agogon dake maƙale a gurin sai kuma ta cigaba da cewa "tunda na ga Baby bata gama ba" "Baby yanzu zaku tafi?" Ta faɗa tana waiwayo wa ta kalli budurwar ɗazu jinjina mata kai tayi tana kurɓar tea ɗin hannunta shima juyowa yayi yana cewa "let's go Baby" yace yana tashi, itama miƙe wa tayi suka fice daga dinning area hannun su sarke da juna tsayawa suka yi a gurin Mamma suna ce mata zasu tafi addu'a tayi musu sai kuma ta kalli Fateymah Nu'aymah wadda har lokacin kanta na a kasa ta ce mata "Ke ma bin su zaki yi?" da sauri ta ƙara yin ƙasa da ƙwayar idanunta tana girgiza mata kai "Ni nace ta raka mu" cewar Mahboob, tsaki taja tana cewa "Allah ya kiyaye hanya" Baby ce tayi hugging din ta tana cewa "sai mun dawo" ɗaga mata kai kawai tayi tana maida hankalinta ga kallon da take yi...





Waje suka fito gaba ɗaya guards ɗin suka mike suna gaishe shi tare da sara masa a bakin mota suka tsaya Baby kuma ta shige "Nu'aymah!" Ya faɗa yana kallonta a hankali ta ɗago idanunta tun lokacin da Mamma tayi mata magana tayi ƙasa da su kwalla ce cike a cikin su, nan da nan ya ruɗe yana janyo ta jikin shi tare da cewa "Kuka kuma? Saboda me?, Haba wife?" hannu tasa ta share kwallar tana yin murmushi ta ce

"It has passed Habibie, Allah ya tsare min kai ya dawo da kai lafiya"

Shima murmushin ya sakar mata yana cewa "Shikenan, Ameen my sweety, ki koma ciki"

Riƙe mai kunne tayi tana cewa "Ka kula min da kanka, banda kallon mata" Baby dake mota ce ta fito tana cewa "Iyayen Love, please bro kazo mu tafi" hararar ta yayi da wasa bai ce mata komai ba ya juyo yana cewa matar sa

"Ina da ke me zan kalla a gurin wasu?, Ke ta daban ce"

Murmushi tayi tana yin ƙasa da kanta "Ka kula dai" tare da sakin sa ta juya zata tafi ringing wayar Mahboob ta fara hannu yasa a aljihu yana ciro ta yana ɗaga wa tare da cewa "Ina hanya Suhailat" tare da kashe wa

Nan da nan da haɗe rai jin da mace yayi waya da sauri ta juyo zata koma ciki yayi hanzarin riƙe hannunta yana cewa "Haba Fateymah Ina zaki kuma?" Yace da sauri

Juyowa tayi tana haɗe rai tare da harɗe hannunta a ƙirji tana cewa "Who is she Mahboob?"

"Just my secretary" ya bata amsa

Ɓata rai tayi tana cewa "Shine ta kira ka yanzu?, Amma kasan ba na so koh?"

"Ina da visitors a Office ne"

Kwalla ce ta taru a idon ta da ƙyar ta buɗe baki tana cije lips ɗinta tare da yarfar da hannunta ta hau cewa "Bana so tana kiran mijina, dan ina kishin shi bana son kowa ya raɓe shi Zan iya kashe ta in kashe ka sannan in kashe kaina" ta faɗa hawaye na zuba daga idanunta, shiru yayi mata yana riƙe da hannunta ya rasa abinda zai faɗa mata baya son ɓacin ranta ko kaɗan a hankali ta buɗe baki tana cigaba da cewa

"Kasan irin kishin ka da nake yi kuwa?" Ta faɗa tana dafe kanta tana cigaba da cewa "Oh My God, Wallahi Mahboob bana son ganin wata ta raɓe ka Indai mace ce bayan Mamma da Baby"

"I Already known that, ki sa a ranki ni naki ne ke kaɗai banda wata, ki koma ciki" girgiza masa kai ta hau yi kalamai masu sanyaya zuciya yayi ta yi mata da alƙawarin ba zai kula kowa ba har ya dawo, da ƙyar ya samu ya shawo kanta ta haƙura ta koma ciki, Baby dake gefe taja tsaki yafi cikin charbi dan ta tsani abinda matar ɗan uwan ta take yi In Allah ya ƙaddara sai ya ƙaro aure ai dole yayi ko ta na so ko Baga so shiga cikin motar suka yi suna ficewa daga gidan..

Sun ɗan yi nisa shiru kowa da abinda yake damunsa a zuciya Baby ce tayi ƙarfin halin kallon shi ta fara ce masa

"Yanzu haka zamu zauna da ita tana bamu kunya a cikin jama'a?" Kallonta yayi irin i don't understand tsaki taja tana cewa

"Wallahi Bro ya kamata ka ja mata kunne ta daina maka irin haka ai sai tasa a raina ka cikin guards tazo sai wani kuka take saboda mace ta kira ka?, Wannan shirme ne har wani cewa take zata yi kisa i think bata san *FURUCI* ba, a gaban mutane...." Ɗaga mata hannu yayi yana cewa "It's enough Baby"

Sakin baki tayi tana kallon shi a zafafe tace "It's not Bro, wannan ba kishi bane hauka matarka take yi, Ce mata aka yi Kishi hauka ne?, da zata ringa irin haka?" "Keep quiet, Baby I said is enough" ya faɗa da ƙarfi

"Bro I can't keep quiet, dole in faɗi abinda yake raina ya dade yana ci min zuciya abinda take yi"

"Stop the car" ya faɗa yana daka wa driver tsawa, da sauri driver ya taka burki kaɗan ya rage suyi accident, da hanzari ragowar motocin da suke tafiya ma duk suka tsaya, nuna wa Baby ƙofa yayi yana cewa "Get Out" shiru tayi bata ce komai ba, a harzuƙe ya sake cewa "i Said Out" Rai-rai tayi da ido da ƙyar ta furta "sorry bro" baice mata komai ba ya ɗauke kansa daga kallonta driver ya ja suka cigaba da tafiya, tun daga lokacin bata sake cewa komai ba ta ja bakin ta tayi shiru har suka je makaranta aka sauke ta tsayawa tayi ta fara cewa "in na fadi wata magana akan matar ka wadda baka ji daɗi ba kayi haƙuri, i don't mean to hurt you, gaskiya ce ba zan fasa faɗa ba" tana kaiwa karshe bata jira amsa sa ba tayi saurin rufe ƙofar tana yin gaba.....





Ban iya dogon page ba🥺 kuyi haƙuri da yanda labarin zai zo muku, da yawan pages ɗin.


# 2024

Arewa Books: fatimaintisar1

Wattpad: fatimaintisar1

***

***


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol