Free chapter · Read without an account

02

by Ummiaisha · WUTAR CIKI...

2



***Fuskarshi a ɗaure babu walwala, no smile as usual yayi wanka ya fito daure da farin towel ya tsaya gaban mirror yana goge jikinsa yayin da sweetie kuma ke ta faman yan tsalle tsalle kan makeken gadon shi ƙirar ƙasar Italy, turarukan dake jere gaban mirror dinsa duk wanda hannunsa yakai kai shi yake dauka ya fesa until the scent was exactly how he wanted it, kaya marassa nauyi ya saka riga da wando ash color shafal shafal dasu ya dauki sweetie suka fita downstairs, kamar koda yaushe abincinsa gashi nan reras Salman ya ajiye masa amma kuma bai ga na sweetie ba shiyasa babu shiri yayi dialing number din Salman wanda ke can B/Q tare da abokan aikinsa suna hira kafin lokacin sallar magriba ya karasa,

"innalillahi wa inna ilaihir rajiun....." Salman ya fada lokacin da yaga wanda yake kiran sa,

"waye?" security man ya tambaye shi saboda ganin yanda ya rude lokaci guda,

"Tiger..." ya fada cikin dar dar wannan shine sunan da suke kiran sa dashi a bayan idonsa because of his terrible hot temper da kuma faɗa,

"wani laifin kayi?"

"bani da lokacin baku amsa bari naje na dawo tukunna...."

Cikin sauri Salman ya fito daga B/Q ya nufi cikin gidan inda yake zaune ya cika fam kamar koda yaushe a tunzure,

"Sir gani..."

He stared at Salman for some minutes with a tight face sannan cikin zafin izza yace,

"How long does it take you to answer your phone when someone calls you??"

"kayi hakuri ranka ya dade.... Lokacin da naga kiran ina cikin bathroom ne"

"ina abincin sweetheart?"

"kayi hakuri mantawa nayi ban fito dashi na zuba mata ba.... Yana kitchen"

He didn't say anything again ya fara bude abincin dake gabansa ya fara zubawa cikin flate, a hankali yake cin abincin kuma fitowar Salman ta sashi dakatawa yana kallonsa,

"This food is not what she eats at night..."

"ehh hakane ranka ya dade....matsalar da aka samu abincin nata ne ya kare.... Kuma....."

"shut up..... What kind of brain do you have? Sau nawa zan fada maka kafin abu ya kare ka sanar dani not when it has already finished..... Why don't you understand anything in your life.... A simple thing you cannot do, every time I have to repeat one thing"

Shi dai Salman sunkuyar da kai yayi yana fadin "sorry sir.... Insha Allah za a kiyaye next time... Hakan ba zata sake faruwa ba"

"get out..." ya fada ba tare da ya kalleshi ba, har ya kama hanyar fita yaji ya sake cewa,

"don't get out....." cak ya tsaya kafin ya juyo gabansa na faduwa saboda bai san wanne laifin kuma ya sake yiba,

"where is my coffee?" lumshe idanuwa Salman yayi kafin ya bude cikin ɗar ɗar yace,

"yana cikin kitchen sir...."

"I need it now..... Your brain never works, every time I tell you coffee, no flavor, no sugar, no milk, but you don't understand...... Useless people everywhere......."

Cikin sauri ya kawo masa coffee din ya ajiye sannan ya juya ya fita ya koma B/Q yana haki kamar wanda ya yi gudun tsere saboda tashin hankali,

"Ban taba ganin masifaffen mutum mai zafi marar hakuri mai izza irin wannan bawan Allahn ba..... Kullum baida aiki sai faɗa...." Salman ya fada bayan ya zauna kusa da security man,

"jin kansa yayi yawa shiyasa ko aboki bashi dashi bare budurwa ko mata..... Zafin kansa ya hana shi yayi aure, gashi nan baida kowa sai mage....."

"yanzun ma saboda ita ne kiran da yayi min, dan kawai na manta ban zuba mata abinci ba shine yake masifa kamar zai cinye ni nama ɗanye"

"nifa idan na samu wani aikin to zaku neme ni ku rasa dan na gama gajiya da wannan halin nashi na faɗa da zafin zuciya...." cleaner ya fada wanda tun bayan da suka fara maganar bai saka musu baki ba sai yanzu,

"ni dai babu inda zan iya zuwa saboda duk inda zanje na san babu mai iya biyana irin albashin da yake bani ko gwamnati na san albarka...". 

Yana gama cin abinci ya ɗauka sweetie zuwa cikin babban falonshi ya kunna musu tashar MBC action kasancewarshi ma'abocin son kallon action films,he was holding her on his lap, stroking her back suna kallon kamar wata bil'adama, ɗan nisawa yayi kadan ya ja wani dogon numfashi ya shafi bayanta yace,

"sweetie wannan rayuwar tana da wahala...... Kalli dai labarin nan da muke kallo kamar gaske.... Tofa irin abinda ke faruwa kenan yanzu a duniya....." shuru yayi sakamakon alarm dinshi na kan wayarshi da ya fara kadawa,

"sweetie lokacin baccinmu yayi.... Let's go and sleep" kashe kayan kallon yayi ya dauke ta zuwa cikin bedroom dinshi, akan couch ya ajiye ta shi kuma ya karasa gaban closet dinshi ya tsaya kayan jikinshi ya canja zuwa na bacci sannan ya wuce bakin gado sat down quietly thinking tunanin da ya dauke shi tsawon lokaci sannan a hankali ya zame ya kwanta bayan sweetie ta taho da gudu ta hau kan kafafunshi, duvet ya ja ya rufe jikinshi tare da Lumshe idanuwansa yana fatan Allah yasa gobe ya dace da samun abinda yake nema.

The next morning he didn't prepare early kasancewar sun jima suna yin bacci shida sweetie, lokacin da ya gama shiryawa ya sauko downstairs ko ina an share anyi mopping sannan ga breakfast dinshi nan Salman ya ajiye kan dining yayin da shi kuma ke cikin kitchen yana karasa yan aikace aikacensa,

Tsaki ya ja saboda bai ga ya ajiye masa coffee ba wanda kullum sai ya maimaita masa,

"Salman...." ya kirashi cikin zafin rai da kuma fushi, kira daya Salman din ya jiyo ya fito,

"wannan ƙwan da ka soya you put salt inside..... Bana cin kwai mai gishiri sanin kanka ne..... Albasa kadai sai pepper ko Maggi how long have i been telling you I don't want it inside..... Fix it, and check the time, I am late"

"I'm sorry sir" cikin sauri ya dauki flate din ƙwan ya juya ya nufi kitchen,

"Salman..... My coffee"

"wannan coffee na masifa..... Kai Allah ya sawwake ya Allah yasa kayi aure mu huta" Salman ya fada cikin ransa kuma cikin kankanin lokaci ya sake soya masa wani ƙwan ya hada da coffee din ya kai masa, cikin kasala da tunane tunane yake yin breakfast din har ya kammala ya tashi yana dauke da sweetie yana yi mata sallama, ajiye ta yayi ya fita yana rike da bag dinshi wacce yake zuwa office da ita, daya daga cikin motocin dake jere cikin parking space ya shiga yayi mata key ya nufi gate, ransa idan yayi dubu sai da yaji ya ɓaci saboda security man din baya kusa kuma ya rufe gate din nan ya soma yin horn kamar zai tashi garin Abuja gaba ɗaya, da wani irin mugun gudu security man din ya ƙaraso ya fara kiciniyar bude gate din,

"Idan na sake zuwa fita na tarar baka nan i will sack you ...... Sarrounded by fools" ya fada cikin dacin rai sannan a zuciye ya fice daga cikin gidan ya nufi office ya na jan tsaki. As always he was walking with a certain confident step into his office, sitting and watching everyone through the CCTV camera dake hasko masa tun daga harabar cikin company din, maganar PA tasa ya mayar da hankalinsa gaba ɗaya kansa,

"sir today's schedule.... You have legal meeting with Barrister Taj 10:00am, Board meeting 12:00pm......"

"cancel the board meeting and reschedule legal meeting to 11:00am"

"ok sir...." juyawa yayi ya fita kuma yana fita staff officer na shigowa, cikin girmamawa ta gaida shi duk da a haife ta girme masa,

"Ranka ya dade it is about the new staff to be employed, nayi musu test kuma mutum biyu sun samu nasara...... I will send them for you to interview them as you said"

"ok"

Juyawa tayi ta fita shi kuma ya bude system dinshi yana dubawa, wani shu'umin kamshi ne ya fara bugar hancin shi lokacin da wata budurwa ta shigo wacce ke sanye da wasu kaya na futsara riga da skirt na atamfa fitted wanda suka kamata sosai,

She was walking seductively, looking at his face which had carried her away since she laid her eyes on him, a hankali ta zauna bayan ta ajiye handbag dinta saman tebur dinsa tana tauna cingam ƙas ƙas,

"Barka da wannan lokaci ranka ya dade...."

Ɗauke hannunsa yayi daga kan laptop dinsa ya kalleta na wasu yan sakanni fuskarshi a ɗaure yace,

"Did you come to look for a job or to do prostitution?" a yanda yayi maganar babu alamar wasa ko kadan a tattare dashi dan fuskarshi da idanuwansa sun bayyana hakan,

"Ranka ya dade aiki na fito nema...."

"ba kiyi kama da wacce tazo neman aiki ba,you look more like someone who came to advertise herself or to find someone to sleep with her, my company is not a bar or a platform for immorality, company na ba bariki bane ko dandalin iskanci.... Dauke wannan handbag din naki daga kan tebur dina..." yana maganar yana buga yan yatsunshi guda biyu kan teburinshi, 

Cikin sauri da kuma rawar jiki ta dauke, " I'm sorry sir..... "

" Get out.... " ya fada cikin tsawa babu shiri jiki yana rawa ta dauki handbag dinta ta fita saboda irin kallon da yake yi mata kadai ya isa muzantata, tsaki ya ja bayan fitar ta yana masifa cikin zuciyarsa,

"people behave like goats..... Look at her, she is not even beautiful..... Walking naked like a goat..... Nonsense"  sallamar da yaji ta katse masa tunaninsa ya daga kai yana kallon wadda ke sallamar, wata matsakaiciyar mata ce nan ya nuna mata wurin zama ta zauna tana murmushi,

"Ranka ya dade ya aiki? Allah ya taimaka ya yi jagora ya bada sa'a, nidai a taimaka min a daukeni wannan aikin domin rayuwata tana cikin wani hali, ina cikin garari da tashin hankali, mijina ne ya gudu ya bar ni da yara takwas.... Rai takwas gashi babu wanda yake taimaka mana ko cikin dangin sa.... " dakatar da ita yayi ta hanyar daga mata hannu alamar ya isa because this story she started was giving him a headache, ya tsani surutu a rayuwarsa haka baya son mutum mai yawan magana shiyasa kawai yayi niyyar sallamarta,

" tashi kije.... "

"ranka ya dade kar kayi wannan kuskuren, ka daure ka bani aikin nan kaima Allah sai ya dubi bayan ka, ko dan wadannan yaran da nake riƙe dasu..... Ka tuna shifa ɗa na kowa ne sannan..."

"I said get out.... Don't make me call securities to throw you out..."

"amma ranka ya dade menene laifina, me nayi wanda bai kamata ba.... Ku dama masu kudi..."

Tsaki yayi kawai ya dauki kan wayar telephone dake ajiye kan tebur dinsa ya fara kiran securities ganin haka yasa ta mike amma duk da haka bakinta baiyi shuru ba,

"shikenan zan fita, wani hanin ga Allah ai baiwa ne.... Ta yuyu acan gaba in samu wani aikin wanda yafi wannan tsoka"

He was watching her through the glasses that surround his office as she left tana ta faman surutu ita kadai, kai da yawa na mutane fa yanzu basu da cikakkiyar lafiyar kwakwalwa ya fadi hakan cikin ransa kuma ya jima zaune bai iya tsinana aikin komai ba kawai ya tashi ya fita.

Zuciyarta babu dadi har ta ƙaraso cikin ma'aikatar wacce tun daga bakin gate wurin ya burgeta kuma ya bata sha'awa sosai, babban company ne na motoci hadaddu kuma tsararru, wurin ga kyau ga tsaro dan tun daga gate sai an bincikeka sosai kamar zaka je ganin shugaban ƙasa, zuciyarta a kuntace take saboda cin mutuncin da anty samiha tayi mata kafin ta fito akan kawai ta nemi ta bata aron naira dubu biyu dan tayi kudin abin hawa nanfa ta rufe ido ta wulakantata daidai gwargwado, kamar cikin mafarki taji tayi wani mugun karo da mutum wanda har sai da wayarshi ta fadi ƙasa, cikin kunci da damuwar da take ciki ta ɗago ta kalleshi, he was also looking at her with anger and intense fury,

"are you blind? Ke makauniyar Ina ce?"

"yi hakuri ban kula bane" ta fada kamar bata so dan harda kawar da kai gefe tayi,

"nan titin gidanku ne da zaki zo kina yiwa mutane tafiya a gadarance yanda kika gadama? Which gutter are you from?"

Cikin jin zafin maganarshi ta kalleshi idanuwanta cikin nashi ranta yana ɓaci ta hade rai kamar yadda yayi tace,

"ba titin gidanmu bane, kuma dama ban ce titin gidanmu bane, gware muka yi da juna ban san ma da wata halitta a gabana ba har sai da hakan ta faru kuma na baka hakuri akan wanne dalili zaka tsaya kana fada min magana har kana kirana da sokuwa? Companyn na gidanku ne? Sokaye dai.... "

" ke..... Ni kike fadawa haka? Do you know who i am? "

" waye kai? An rubuta a goshinka ne? Dalla malam matsa min in wuce.... " ta fada cikin bala'i ta gegaye shi ta gefen shi ta wuce ciki abinta tana sake bin kayataccen Companyn da kallo ko ina ka waiga motoci ne suna kyalli da daukar ido, shi dai yanda ta wuce shi ta barshi a tsaye anan ya daskare cike da ɓacin rai da kuma mamaki, wannan shine karo na farko da wata mace ta tsaya a gaban shi ta kalli cikin idonsa ta mayar masa da magana, ko maza yan uwansa yana yi musu kwarjini, komai girman mutum ko yawan shekarunsa yana shakkar mayar masa da martani amma yau wata wacce bai san ko wacece ba ta shigo har cikin companynsa ta zage shi, ji yayi ransa ya ɓaci zuciyarsa tana tafarfasa kamar ana rura wuta, wayarshi dake yashe a ƙasa ya ɗauka ya juya ya koma ciki ya fasa fitar da zai yi...........



Next chapter loading... ✍️✍️





*_Ummi Shatu_*👌🏻

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol