Free chapter · Read without an account

BABI NA TAKWAS (8): CIGABAN HIKAYAR SARKI YUNAN DA LIKITA DUBAN

by Shuraihu Usman · DARE DUBU DA DAYA 1001 Mujalladi na Daya 1

====================================================================

DARE DUBU DA DAYA (ALF LAILA WA LAILA)

BABI NA TAKWAS (8): CIGABAN HIKAYAR SARKI YUNAN DA LIKITA DUBAN

[YA KUNSHI: DARE NA SHIDA DA DARE NA BAKWAI]

Fassarar: Shuraihu Usman

====================================================================

A babi na bakwai idan mai karatu bai manta ba, mun tsaya a inda Sarki Yunan ya ba wa mugun Wazirinsa labarin Sarki Sindibad da shahonsa a karshen DARE NA BIYAR, domin ya nuna masa illar gaggawar kisa da kuma irin nadamar da ke bin mai zalunci. To yanzu bari mu ji yadda wannan mugun Waziri ya sake kulla wata sabuwar dabarar zuga Sarki a cikin wannan DARE NA SHIDA har sai da ya sa aka yanke hukuncin kisa a kan Likita Duban.

--- DARE NA SHIDA ---

Gari ya waye, Sarki Shahriyar ya fita fada ya gudanar da al'amuran mulki ba tare da ya ambaci batun kisan Shahrazad ba. Babban Waziri ya koma gida yana godiya ga Allah da ya ga 'yarsa tana ci gaba da rayuwa.

Da dare ya tsala a cikin wannan DARE NA SHIDA, Sarki Shahriyar ya shigo daki ya kwanta da Shahrazad. Bayan ya gama biyan bukatarsa, sai qanwarta Dunyazad ta tashi daga qasan shimfida ta ce:

"Ya yayata, idan baki fara barci ba, don girman Allah ki qarasa mana labarin Sarki Yunan da Likita Duban domin mu debe kewa a cikin wannan dare!"

Shahrazad ta duba wajen Sarki Shahriyar cikin ladabi ta ce: "Zan ci gaba idan har wannan babban Sarki mai daraja ya ba ni izini!" Sarki ya ce: "Fadi ina saurarenki!"

Nan take Shahrazad ta fara ba da wannan kyakkyawan labari a cikin wannan DARE NA SHIDA kamar haka:

"Ko da Sarki Yunan ya gama ba wa Wazirinsa labarin Sarki Sindibad da shahonsa, sai Wazirin ya rushe da kukan munafunci ya ce: 'Ya shugabana, na san ba ka son kanka da alheri ba! Wannan shaho da ka ba da labarinsa dabba ce marar hankali, amma shi wannan Likita Duban mutum ne mai basira da wayo!

Idan baka kashe shi ba to lallai shi zai kashe ka! Ka sani fa dogara da bako yana jefa mutum a halaka kamar yadda ya sami Yariman da ya bi shawaran Wazirinsa ya hadu da Mayyar daji wadda ta so ta cinye shi!'

Sarki Yunan ya dube shi ya ce: 'Mene ne labarin wannan Yarima da Mayya ya Waziri?'

Waziri ya ce: 'An ruwaito cewa wani babban Sarki yana da wani da Yarima wanda yake matuqar qauna. Wata rana wannan Yarima ya fita farauta a daji tare da Wazirin mahaifinsa. Suna cikin tafiya sai suka hango wata kyakkyawar dabba, sai Wazirin nan ya ce wa Yarima: Maza bi wannan dabba kai kadai ka kamo ta domin ka nuna jarumtakarka ga mahaifinka!

Yarima ya bi dabbar a guje har ya shiga zurfin wani daji mai duhu da hadari, dabbar ta bace masa, shi kuma ya rasa hanyar komawa gida.

Yana cikin kewayawa a cikin duhun daji yana neman taimako, sai ya hango wata kyakkyawar budurwa tana kuka a gefen hanya. Yarima ya matsa kusa da ita ya tambaye ta: Wacece ke kuma me ya kawo ki wannan daji?

Yarinyar ta ce cikin kuka: Ni 'yar wani babban Sarki ce daga qasashen Hindu, muna cikin tafiya a kan rakuma sai barci ya kwashe ni na fado daga kan dabba ban sani ba, ayarinmu kuma ya wuce ya bar ni a nan cikin tsoro!

Yarima ya tausaya mata qwarai, ya dauke ta ya dora a bayan dokinsa suka kama hanya. Suna cikin tafiya sai suka zo kusa da wani tsohon kango da kufai da aka dade da watsarwa.

Yarinyar nan ta ce da Yarima: Ya shugabana, don Allah ka tsaya a nan na shiga wannan kango na sauke kaina na dan huta kafin mu wuce!

Yarima ya tsaya a waje, ita kuma ta shiga cikin kangon. Amma da ta shiga, sai Yarima ya ji motsin wasu muryoyi a ciki, sai ya sauko daga kan doki ya leqa ta wata kofa ta sirri ba tare da ta ankara ba.

Ko da ya leqa, sai ya ga wani abu da ya firgita zuciyarsa: ya ga ashe wannan yarinya ba mutum bace, wata mummunar Mayya ce, mai cin naman 'yan adam, tana magana da 'ya'yanta qanana tana cewa: Ku yi murna 'ya'yana! A yau na kawo muku wani kyakkyawan saurayi matashi mai kiba da laushi, zaku ci naman mutum ku qoshi!

'Ya'yanta suka riqa tsalle da murna suna cewa: Maza kawo mana shi mu cinye shi!

Ko da Yarima ya ji wannan zance, sai jikinsa ya dauki rawa, ya tabbatar da cewa idan bai yi dabara ba to ajalinsa ya zo! Ya fito da sauri ya hau dokinsa, ya daga hannayensa biyu sama yana kuka yana roqon Allah da cewa:

Ya Wanda Yake amsa addu'ar wanda ya shiga tsananin qunci idan ya kira Shi! Ya Mai yaye dukkan damuwa Ka cece ni daga sharrin wannan mayya!

A daidai wannan lokaci sai Mayyar nan ta fito daga kangon tana washe hakora domin ta shake shi ta shigar da shi ciki. Amma ko da ta ji wannan addu'a da ya yi da dukkan zuciyarsa, sai tsoron Allah ya daki zuciyarta, gabobinta suka saki, ta kasa motsawa balle ta taba shi!

Yarima ya bugi dokinsa da kaimi ya ruga a guje har ya fita daga cikin dajin ya isa birninsu cikin koshin lafiya!

To kaji ya Sarki,' in ji Waziri, 'haka Likita Duban yake so ya yaudare ka ya halaka ka a boye!'

Ko da Sarki Yunan ya ji wannan labari, sai tsoro ya shiga zuciyarsa, shaidan ya qawata masa cewa lallai Likita Duban hadari ne a gare shi. Nan take Sarki ya sa aka kirawo Likita Duban zuwa fada.

Likita Duban ya shigo fada ba tare da ya san abin da ke faruwa ba, sai ya tarar da fada a cike da dakarun yaqi, ga hauni a tsaye kusa da Sarki da takobi zararra a hannunsa!

Sarki Yunan ya dube shi a fusace ya ce: 'Ka san dalilin da ya sa na kirawo ka a yau?'

Likita Duban ya ce: 'A'a ya shugabana, babu wanda ya san gaibi sai Allah!'

Sarki ya ce: 'Na kirawo ka ne domin na sare kanka da wannan takobi na raba ka da ranka!'

Likita Duban ya zaro idanuwa cike da firgici da mamaki ya ce: 'Subhanallah! Me ya sa zaka kashe ni ya Sarki? Wane laifi na aikata a gare ka bayan na warkar da kai daga wannan cuta?'

Sarki ya ce: 'Na sami labarin cewa kai dan leken asiri ne da aka aiko domin ka kashe ni! Kuma tunda ka iya warkar da ni ta hanyar sanda ba tare da magani ba, to zaka iya kashe ni da wani asirin da ban sani ba! Saboda haka ya zama dole na kashe ka yanzu-yanzu!'

Likita Duban ya fashe da kuka, ya durqusa a gaban Sarki yana roqo yana cewa: 'Ya Sarki, ka bar ni da rai domin Allah Ya bar ka da rai! Kada ka kashe ni don kada Allah Shi ma Ya kashe ka da mafi munin kisa!'

Amma Sarki Yunan ya rufe idanunsa, ya qi sauraren kowace magana.

Ganin cewa babu wata mafita, kuma Sarki ya nace lallai sai an kashe shi, sai Likita Duban ya ce: 'Ya Sarki, tunda ka kafe a kan kashe ni, to ina roqonka ka ba ni izini na je gidana na kwana daya kacal! Zan tafi na raba dukiyata ga iyalina, na biya basussukan da ke kaina, kuma akwai wani tsohon littafi mai ban al'ajabi da nake so na baka kyautarsa a matsayin gado!'

Sarki ya ce: 'Wane irin littafi ne wannan?'

Likita Duban ya ce: 'Littafi ne wanda ya kunshi asirai na musamman da ba a taba ganin irinsu ba a duniya! Daga cikin asiran da ke cikinsa akwai cewa: idan har ka sare kaina da takobi, ka sanya kaina da aka sare a cikin wani kwano da zan kawo maka wanda ke cike da wani garin magani, to kaina da aka sare zai fara magana da kai yana amsa dukkan tambayoyin da kake so game da dukiya da taskokin duniya da abubuwan da zasu auku a gaba!'

Ko da Sarki Yunan ya ji wannan magana, sai kwadayi da matsanancin mamaki suka rufe masa ido! Ya yi sha'awar ganin yadda kan da aka yanke zai riqa magana a gaban jama'a. Nan take ya amince ya ba shi damar zuwa gida har zuwa wayewar gari."

A daidai wannan lokaci, sai hasken alfijir ya fara ketowa a sararin samaniya, Shahrazad ta ga safiya ta yi, sai ta dakata da maganarta ta yi shiru!

Dunyazad ta dube ta ta ce: "Kai ya yayata! Lallai wannan labari ya cika da tsoro da matuqar shauqi!"

Shahrazad ta yi murmushi ta ce: "Ai wannan bai kai labarin da zan baku a dare mai zuwa ba, na yadda kan Likita Duban zai riqa magana a kan kwano da kuma yadda zai halaka Sarki Yunan ta cikin littafin guba!"

Sarki Shahriyar ya ce a ransa: "Wallahi ba zan kashe ta a yau ba, sai na ji yadda kan nan zai yi magana da yadda Sarki Yunan zai mutu!" Sarki ya fita fada ya gudanar da mulki, babban Waziri ya koma gida fuskarsa cike da farin ciki!

--- DARE NA BAKWAI ---

Da gari ya waye aka wuni ana harkokin mulki. Da dare ya tsala a cikin wannan DARE NA BAKWAI, Sarki Shahriyar ya shigo daki ya kwanta da Shahrazad. Bayan ya gama biyan bukatarsa, sai Dunyazad ta tashi daga qasan shimfida ta ce:

"Ya yayata, idan baki fara barci ba, don Allah ki qarasa mana wannan labari mai ban al'ajabi na kan Likita Duban da kuma Sarki Yunan!"

Shahrazad ta duba wajen Sarki Shahriyar cikin ladabi ta ce: "Zan qarasa labarin idan har wannan babban Sarki ya ba ni izini!" Sarki ya ce: "Fadi ina saurarenki!"

Nan take Shahrazad ta gyara zama ta ci gaba da labarinta kamar haka:

"Washegari da safe, Likita Duban ya zo fada dauke da wani tsohon littafi a hannunsa, da kuma wani dan qaramin kasko mai dauke da wani farin garin magani. Fada ta cika makil da manyan sarakuna, da fadawa, da dakarun yaqi domin kallon wannan al'amari.

Likita Duban ya matso gaban Sarki ya miqa masa littafin, sannan ya ajiye kwanon maganin a gabansa ya ce: 'Ya Sarki, idan aka sare kaina, to ka ajiye shi a cikin wannan kwano na magani domin jini ya tsaya, sannan ka bude wannan littafi shafi na shida ka karanta baitocin da ke ciki, za ka ji yadda kaina zai amsa maka!'

Sarki ya yi umarni ga Hauni. Hauni ya daga takobinsa mai kaifi, da sara guda daya ya sare kan Likita Duban!

Jini ya fantsama, kan ya fadi a kasa, sai Haunin ya dauki kan ya sanya shi a cikin wannan kwano na magani kamar yadda Duban ya fada.

Nan take wani abin al'ajabi ya faru: jinin ya tsaya cak, idanun kan suka bude suka kalli Sarki Yunan, bakin kan ya fara motsawa yana cewa da kakkausar murya: 'Ya Sarki, bude littafin da ke hannunka yanzu ka karanta!'

Duk jama'ar fada suka tsorata suka zaro idanuwa saboda ganin kan da aka yanke yana magana da kansa!

Sarki Yunan ya bude littafin cike da zumudi domin ya karanta shafi na shida, amma sai ya tarar shafukan littafin sun manne da juna sosai ba sa rabuwa cikin sauqi.

Sarki ya sanya yatsansa a bakinsa ya jika shi da miyau, ya buda shafi na farko, ya sake lasar yatsansa ya buda shafi na biyu, ya sake lasar yatsansa ya buda shafi na uku har zuwa shafi na shida!

Amma da ya duba shafi na shidan, sai ya ga shafin fari fat yake babu ko harafi guda daya a rubuce a kai!

Sarki ya kalli kan Likita Duban ya ce: 'Ya kai wannan kai, ai babu komai a rubuce a shafin nan!'

Kan ya motsa baki ya ce: 'Ci gaba da lasar yatsanka kana buda sauran shafukan gaba!'

Sarki ya sake lasar yatsansa yana buda sauran shafukan—ashe wata mummunar guba mai matuqar qarfi da zafi Likita Duban ya shafa a jikin dukkan shafukan littafin!

Cikin 'yan dakiku qanana, sai gubar nan ta fara aiki a jikin Sarki Yunan! Jikinsa ya fara karkarwa, idanuwansa suka kada suka yi jajir suka fito waje, harshensa ya kumbura ya cika bakinsa, jikinsa ya saki ya fadi daga kan karagar mulkinsa yana birgima a qasa yana nishi da radadi!

A daidai wannan lokaci, sai kan Likita Duban ya fashe da dariya a kan kwano, ya rera wasu baitoci na waqa yana cewa:

Sun yi mulki da qeta suka zalinci bayin Allah,

Yanzu ga shi qaddara ta maida musu da sakamakonsu!

Da kun yi adalci da kun zauna lafiya a kan mulkinku,

Amma kun zalunci marasa laifi shi ya sa kuka gamu da tozarci!

Duk wanda ya shuka sharri to zai girbi nadama,

Ga shi yanzu mutuwa ta riske ka a inda baka zata ba!

Rufe bakin kan Likita Duban ke da wuya, sai Sarki Yunan ya saki wata qaqqarfar qara ya mutu a nan take! Shi ma kan Likita Duban ya rufe idanunsa ya daina magana har abada!

To ka ji ya kai wannan Ifiritu,' in ji Masunci yana dukan battar tagulla da sanda, 'abin da ya sami Sarki Yunan ke nan saboda ya mayar da alherin da aka yi masa da sharri! Da ya bar Likita Duban da rai da Allah Shi ma Ya bar shi da rai, amma da ya kashe shi sai Allah Ya halaka shi! Haka kai ma kake so ka kashe ni bayan na fito da kai daga kasan teku! Saboda haka na rantse da Allah ba zan taba bude ka ba, zan jefa ka a cikin teku ka dawwama a can har abada!'

Ko da Ifiritun nan ya ji haka, sai ya shiga matsananciyar fargaba a cikin battar tagullar, ya fara kuka yana cewa: 'Ya masunci, na rantse da babban sunan Allah Madaukaki, da darajar hatimin Annabi Sulayman, idan har ka bude mani wannan batta na fito, to wallahi ba zan taba cutar da kai ba, kuma zan nuna maka wata hanya ta samun arziqi wadda zata mai da kai babban mai dukiya kai da zuriarka har abada!'

Masunci ya ji tausayinsa, ya karbi rantsuwarsa, ya dauki wuka ya cire darmar da ke bakin battar.

Hayakin nan ya sake turnuqe sararin samaniya, ya dunkule ya zama wannan gagarumin Ifiritu a gabansa!

Ifiritun ya daga kafarsa ya daki battar tagullar ya jefa shi can tsakiyar teku ya nutse. Sannan ya kalli masunci ya ce: 'Kada ka ji tsoro, alkawari na yi maka kuma zan cika! Taho tare da ni yanzu!'

Nan take Ifiritun ya wuce gaba, masunci yana biye da shi a baya. Suka ratsa duwatsu da dazuzzuka har sai da suka isa tsakiyar wasu manyan tsaunuka guda hudu. A tsakiyarsu kuwa sai suka tarar da wani katafaren tafki mai cike da kifi masu launuka hudu: Farare, Jajaye, Shudaye, da Masu launin Zinare!

Ifiritun ya ce da masunci: 'Jefa komarka ka kamo kifi hudu kacal—kowane launi guda daya—ka kai wa Sarkin birninku kyauta! Zai baka arzikin da baka taba tsammani ba! Amma kada ka kuskura ka jefa komarka a nan fiye da sau daya a rana!'

Daga nan sai Ifiritun ya daki qasa ya bace bat a kasan ruwa!..."

A daidai wannan gaba, sai hasken alfijir ya fara ketowa a sararin samaniya, Shahrazad ta ga safiya ta yi, sai ta dakata da maganarta ta yi shiru.

Dunyazad ta dube ta da matuqar mamaki ta ce: "Kai ya yayata! Lallai wannan labari ya cika da zallar ban al'ajabi da hikima!"

Shahrazad ta yi murmushi ta ce: "Ai wannan bai kai labarin da zan baku a dare mai zuwa ba, na yadda masuncin nan zai kai kifin nan fada a bashi dinare dari hudu, da kuma yadda za a dora kifin a kasko wata budurwa ta fito daga tsagewar bango tana magana da kifin a cikin tafasasshen mai!"

Sarki Shahriyar ya cika da shauqi, ya ce a ransa: "Wallahi ba zan kashe ta a yau ba, sai na ji labarin kifin nan masu magana da budurwar da ke fitowa daga bango!" Sarki ya fita fada ya gudanar da mulki, babban Waziri ya koma gida yana murna da godiyar Allah!

(A nan muka kawo qarshen DARE NA BAKWAI da Babi na Takwas. A babi na tara mai zuwa a cikin DARE NA TAKWAS DA DARE NA TARA, za mu ji yadda budurwa ta riqa fitowa daga bango tana kifar da kaskon kifi, da yadda Sarki ya fita daji shi kadai har ya isa fadar baqin dutse ya hadu da Yarima mai rabin jikin dutse!)

====================================================================

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol