Free chapter · Read without an account

BABI NA GOMA SHA DAYA (11): HIKAYAR DAN DAKO DA MATAN BAGADAZA

by Shuraihu Usman · DARE DUBU DA DAYA 1001 Mujalladi na Daya 1

====================================================================

DARE DUBU DA DAYA (ALF LAILA WA LAILA)

BABI NA GOMA SHA DAYA (11): HIKAYAR DAN DAKO DA MATAN BAGADAZA

[DARE NA GOMA]

Fassarar: Shuraihu Usman

====================================================================

A babi na goma idan mai karatu bai manta ba, mun tsaya a inda Sarki ya kashe baqin bawan matsafiya da takobi, ya karya sihirin birnin da mutanensa suka koma mutane daga kifi, sannan aka daura auren Sarki da Yarima Mahmud da 'ya'yan tsohon masunci a karshen DARE NA GOMA. To yanzu bari mu ji wani sabon labari mai cike da ban mamaki da zakin kunne da Shahrazad ta fara a cikin wannan DARE NA GOMA.

--- DARE NA GOMA ---

Gari ya waye, Sarki Shahriyar ya fita fada ya gudanar da al'amuran mulki ba tare da ya ambaci batun kisan Shahrazad ba. Babban Waziri ya koma gida yana godiya ga Allah da ya ga 'yarsa tana ci gaba da rayuwa cikin aminci.

Da dare ya tsala a cikin wannan DARE NA GOMA, Sarki Shahriyar ya shigo daki ya kwanta da Shahrazad. Bayan ya gama biyan bukatarsa, sai qanwarta Dunyazad ta tashi daga qasan shimfida ta ce:

"Ya yayata, idan baki fara barci ba, don girman Allah ki fara ba mu wannan sabon labari mai dadi na Dan Dako da 'Yan Matan Bagadaza domin mu debe kewa a cikin wannan dare!"

Shahrazad ta duba wajen Sarki Shahriyar cikin ladabi ta ce: "Zan baku labarin idan har wannan babban Sarki mai daraja ya ba ni izini!" Sarki ya ce: "Fadi ina saurarenki!"

Nan take Shahrazad ta fara ba da wannan kyakkyawan labari a cikin wannan DARE NA GOMA kamar haka:

"An ruwaito ya kai wannan babban Sarki mai daukaka, cewa a can zamanin dā, a cikin babban birnin Bagadaza na qasar Iraki, an taba yin wani saurayi dan dako. Wannan saurayi ya kasance gwauro wanda bai taba aure ba, yana da dabi'ar barkwanci da dadin baki da yawan fara'a.

Wata rana yana tsaye a cikin kasuwar birnin Bagadaza, ya jingina a jikin babban kwandonsa na dako yana jiran mai neman mai daukar masa kaya, sai ga wata mace mai daraja ta bayyana a gabansa!

Wannan mace tana sanye da mayafi na alharinin birnin Mosul da aka dinka da zaren zinare, takalmanta an qawata su da zaren zinare, gashin kanta a rabe yake da kitso guda biyu masu tsawo. Ko da ta juyo gefe guda ta yaye mayafin fuskarta kadan, sai ga idanuwanta guda biyu baqaqe masu dogayen gashin ido, masu cikar kwarjini da sanyin kallo!

Matar nan ta matso kusa da dan dako ta ce da shi da wata zazzakar murya mai dadin sauraro: 'Dauki kwandonka ka biyo ni a baya!'

Dan dako ya gigice saboda kyanta, ya kusan kasa gaskata abin da kunnuwansa suka ji! Ya sungumi kwandonsa a kansa da hanzari yana cewa a ransa: 'Na rantse da Allah yau rana ce mai matuqar albarka! Rana ce ta samun arziqi da nishadi!'

Suka kama tafiya har sai da ta tsaya a kofar shagon wani Kirista mai sayar da ruwan inabi. Ta qwanqwasa kofa, sai wani dattijo ya fito. Ta bashi dinare guda na zinare, shi kuma ya kawo mata wata gora cike da tataccen ruwan inabi mai qamshi mai kama da man zaitun saboda tsarkinsa. Ta ce wa dan dako: 'Dauki ka sa a kwando ka biyo ni!' Dan dako ya ce: 'Ran ki ya dade, wannan rana ce ta biyan bukatun bawan Allah!' Ya dauka ya bi ta.

Suka ci gaba da tafiya har ta tsaya a shagon mai sayar da 'ya'yan itatuwa. Ta sayi tuffan Sham masu kyan gaske, da safarjal na daular Usmaniyya, da khukhi na Omani, da khiyar na kasar Masar, da lemun zaki na Masar, da lemun Sultani da utruj; ga kuma furannin yasamin na Halab, da rassan as masu qamshi, da nilufar na Sham, da furen hinna da na babunaj, da shaqa'iqun nu'uman jajaye kankan, da furannin albanafsaj, da furen rumman, da nasrin, da kuma narjis masu ban qamshi, sannan ta sa su duka a kwandon ta ce: 'Dauka mu tafi!' Dan dako ya dauka ya bi ta.

Daga nan suka nufi shagon mahauci. Ta ce da shi: 'Yanka mani kafadar naman rago mai kiba fam goma!' Mahaucin ya yanka ta biya shi kudi, ya nade naman a cikin ganyen ayaba ta sa a kwandon ta ce: 'Dauka ya mai dako!' Ya dauka ya bi ta.

Suka nufi shagon mai sayar da busassun kayan marmari. Ta sayi busassun 'ya'yan itatuwa, da qwayoyin fustuk, da zabib na Tihama, da qwayoyin lauz wadanda aka bare bawonsu, da dabinon Madina, da dukkan abin da ake bukata na kayan marmari ta cika kwando ta ce: 'Dauka ka biyo ni!'

Dan dako ganin yadda kwando ke qara nauyi amma saboda kyanta sai ya ga kamar auduga yake dauke da ita, ya dube ta yana murmushi cikin barkwanci ya ce: 'Ya shugabata, da kin fada mani tun asali cewa dukkan wannan kaya zaki saya, da na taho da dabba ko jaki ko raqumi domin saukaka daukan kayan!'

Matar ta yi murmushi mai kayatarwa, ta dan buge qeyarsa a hankali ta ce: 'Mu je gaba kada ka cika surutu, domin da yardar Allah ladanka ba zai gaza ba!'

Daga nan suka nufi shagon mai sayar da kayan zaki da alawa. Ta sayi kowane irin fanke, da alawar zuma, da kayan zaki masu qamshin miski ta sanya a kwando.

A qarshe suka isa shagon mai magunguna da kayan qamshi. A nan ta sayi nau'o'in ruwan qamshi guda goma: ruwan wardi mai hade da miski, da ruwan furen lemu, da ruwan nilufar, da ruwan furen khilaf, da ruwan albanafsaj da sauran nau'o'i biyar; ta kuma sayi kankara biyu na sukari, da gorar yayyafa ruwan qamshi, da dunqulen luban zakar, da itacen al'ud, da ambari, da miski, tare da manyan kyandirori na kakin Iskandariyya. Sannan suka tsaya a shagon mai ganyaye da kayan abinci, ta sayi tsamin usfur da zaitun, tare da cuku mai kauri na Sham, ta zuba su duka a cikin kwando.

A wannan lokaci sai kwandon dan dako ya cika makil har ya fara zuba! Matar ta ce: 'Dauki kwandonka ka biyo ni!' Dan dako ya dauki kwandonsa ya bi ta a baya har suka isa wata katafariyar fada mai hawa-hawa, wadda take da manyan qyauraye guda biyu na katako mai qamshi na abnus da aka kawata da darma da jajayen zinare.

Matar nan ta tsaya a bakin kofar, ta karkata mayafin fuskarta gefe guda, ta qwanqwasa kofa a hankali da yatsunta, yayin da dan dako ke tsaye a bayanta ba ya tunanin komai a duniya face tsananin kyanta da kwarjininta!

Jim kadan sai kofar ta bude, qyaurorin biyu suka baje!

Dan dako ya zura idanunsa domin ya ga wanda ya bude kofar: sai ya yi arba da wata doguwar budurwa mai cikar zati, tsawonta ya kai qafa biyar cif! Wannan budurwa ta kasance abin koyi na kyan halitta, da haske, da daidaituwar siffa da cikar kwarjini mara misali!

Goshinta ya kasance fari fat tamkar furen gona mai tsarki; kumatunta jajaye rududdu tamkar furen shaqa'iqun nu'uman; idanuwanta tamkar na bauniyar daji ko barewa, tare da girar ido mai lankwasa tamkar jinjirin watan da ke kawo qarshen watan Sha'aban ya shigar da watan Ramadan!

Bakinta ya kasance siriri tamkar zoben Annabi Sulayman, lebanta jajir tamkar murjani, hakoranta kuma tamkar layin lu'u-lu'u da aka jera ko furen babunaj a kan sanyi!

Wuyanta yana tunawa mai kallonta da wuyan barewar daji; nonuwanta guda biyu tamkar 'ya'yan rumman guda biyu daidai da juna a tsaye cif; jikinta yana hawa yana sauka a qarqashin tufafinta tamkar ruwan alharini mai sheqi, cibiyarta kuwa zata iya daukar uqiyya guda ta man qamshi na luban jawi!

A taqaice dai ta kasance tamkar wadda mawaqi ya rera baitocinnan a kanta yana cewa:

Ka zuba idonka a kan wannan rana da wata na fada,

Ka shaida fuskarta mai kama da fure da haskenta mai qamshi!

Idanunka ba za su taba ganin baqin gashi mai duhu ba,

Wanda ke lullube da goshi mai tsananin haske da fari!

Jajayen kumatunta suna bayyana darajarta,

Ko da sunanta ya gaza fitowa a cikin baitocin yabonmu!

Yayin da take taku ina yin murmushi saboda fadin kugunta,

Ina kuma kuka saboda ganin siririyar qugunta da ke dauke da su!

Ko da dan dako ya kalli wannan budurwa da ta bude kofa, sai hankalinsa ya tashi, gabobinsa suka saki har kwandon kansa ya kusan fadowa a qasa! Ya ce a zuciyarsa: 'Ban taba ganin ranar da ta fi wannan albarka a dukkan rayuwata ba!'

Budurwa mai bude kofa ta dubi 'yar'uwarta mai sayayya, fuskarta dauke da murmushi mai sanyaya zuciya, ta ce: "Shigo daga ciki ya 'yar'uwata, ki hutar da wannan bawan Allah daga katuwar wahalar da ya sha da wannan kaya mai nauyi da ke kansa!"

Suka kutsa kai cikin fadar, dan dako na take musu baya yana kalle-kalle cike da mamaki da dimuwa, har suka isa wani katafaren falo na qasa mai fadin gaske! Falo ne da aka gina shi da gagarumar fasaha ta al'ajabi, aka qawata shi da zane-zane na kowane irin launi masu kayatar da idanuwa; ga manyan benaye, da kofofi na marmara masu sheqi, da labulaye na alharini masu laushi. A tsakiyar falon kuwa, wani katafaren tafki ne na marmara mai dauke da kwanon lu'u-lu'u wanda ke feshin ruwa sama yana kwarara tamkar lu'u-lu'u na azurfa, a kewayen tafkin kuma akwai wata babbar karagar alfarma da aka qawata da adon zinare da duwatsu masu daraja.

A kan wannan karaga kuwa, sai ga wata budurwa ta uku mai cikar zati da kwarjini! Wannan budurwa ta kasance mai tsananin kyau da hasken fuska wanda ke ba wa hasken wata kunya; idanuwanta tamkar sihiri ne na birnin Babila, gashin girarta a lankwashe yake tamkar baka, numfashinta yana fitar da qamshin ambari, lebanta kuma jajir tamkar murjani, dandanonsu kuma tamkar zuma! Idan ta yi murmushi, sai ka rantse layin lu'u-lu'u ne ke walkiya ko kuwa furen babunaj ne a kan kankara. Kamar yadda mawaqi ya rera a kanta yana mai cewa:

Murmushinta yana bayyana layuka biyu na lu'u-lu'u,

Tamkar furen babunaj ko tartsatsin kankara!

Gashin kanta zube yake tamkar daren da aka saukar,

Haskenta kuwa yana kunyata hasken safiya!

Budurwa ta uku ta miqe tsaye daga kan karagar, tana taku cike da isa da kasaita har ta isa tsakiyar falon, ta kalli 'yan'uwanta ta ce: "Me ya sa kuke tsaye a nan? Ku yi maza ku sauke wannan nauyi daga kan wannan bawan Allah!"

Nan take kuwa, budurwa mai sayayya ta tsaya a gabansa, mai kofa kuma ta tsaya a bayansa, ita kuwa budurwa ta uku ta taya su da hannuwanta, suka sauke wannan kwando daga kan dan dako suka ajiye a qasa. Suka shiga zazzage kayan da ke ciki suna ajiye kowane abu a muhallinsa. Bayan sun kammala, sai budurwa mai sayayya ta ciro dinare biyu na zinare da 'yan kudaden tagulla ta miqa wa dan dako, tana mai cewa: "Karbi ladanka ya kai wannan mai dako, ka kama gabanka lafiya!"

To amma ina! Dan dako ya gaza motsa qafafunsa daga inda yake! Ya tsaya cak yana kallon wadannan kyawawan 'yan mata guda uku, yana mamakin irin wannan tsananin kyau da cikar halitta da fara'a da ba a taba ganin irinsu ba a doron duniya. Ya zuba ido yana kallon tarin kayan marmari, da ruwan inabi da furanni masu qamshi, ga kuma gidan shiru babu kowa a ciki face shi kadai a tsakanin wadannan mata. Sai ya raya a ransa yana cewa: "La'ilaha illallahu! Idan har na juya na fita daga wannan fada na bar wannan aljanna ta duniya, wallahi na tafka babban rashi a rayuwata!"

Budurwa babba ta lura da yadda ya kafe qafafunsa ya qi tafiya, sai ta dube shi cikin mamaki ta ce: "Me ya same ba ka tafi ba ya mai dako? Ko kudin ladanka ne suka yi kadan?" Sai ta juya ga 'yar'uwarta mai sayayya ta ce: "Qara masa wani dinaren na zinare!"

Amma dan dako ya girgiza kansa cikin ladabi ya ce: "Na rantse da Allah ya shugabata, ba batun lada ba ne! Ni a al'adata ko dirhami biyu ne ladana a kowane dako! Sai dai wallahi zuciyata da dukkan hankalina sun kamu da son zama a tare da ku! Ina matuqar mamakin yadda kuka kasance ku kadai a cikin wannan katafariyar fada ba tare da wani namiji da zai debe muku kewa ba! Kuma ai kowa ya sani cewa hasumiya ba ta taba tsayuwa sai da ginshiqai hudu, ku kuma mata ne guda uku, kuna bukatar mutum na hudu domin jin dadinku ya cika! Domin kamar yadda mawaqi ya fada a cikin baitocinsa:

Ba ka gani ba, jin dadi ba ya cika face da abubuwa hudu:

Kuge da molo, sarewa da algaita!

Tare da qamshin furanni guda hudu:

Furen wardi, da as mai qamshi, da shaqa'iqun nu'uman, da banafsaj!

Kuma dukkan wadannan takwas ba su da wani dadi idan aka hana hudu:

Tataccen ruwan inabi, da kuruciya, da dukiya, da kyakkyawar masoyiya!

Ku mata ne guda uku, kuna bukatar mutum na hudu wanda ya kasance namiji mai hankali, mai cikar basira da kaifin tunani, wanda kuma zai iya kiyaye sirrinku ba tare da ya fallasa ba!"

Ko da wadannan 'yan mata suka ji kalaman dan dako da irin barkwancinsa, sai suka kwashe da dariya har kumatunsu suka kada suka yi jajir! Budurwa mai kofa ta dube shi tana murmushi ta ce: "Wane ne zai ba mu tabbacin cewa zaka iya riqe sirri? Mu 'yan mata ne kuma muna tsoron damqa sirrinmu a wurin da ba za a kiyaye shi ba! Domin mun karanta a cikin littattafan hikima inda Ibnus Sumam yake cewa:

Ka riqe sirrinka kada ka fadi wa kowa,

Domin sirri ya baci da zarar an fade shi!

Idan qirjinka ya gaza boye sirrinka,

Ta yaya kake tsammanin qirjin wani zai iya riqe shi?

Kuma mawaqi Abu Nuwas ya fada a kan wannan inda yake cewa:

Duk wanda ya damqa sirrinsa a hannun wani,

To ya cancanci a buga masa tambarin tozarci a goshinsa!"

Ko da dan dako ya ji kalaman wadannan 'yan mata, sai ya ce: "Na rantse da rayukanku ya shugabannina! Ku sani fa ni mutum ne mai natsuwa da cikar hankali, wanda ya karanta littattafan hikima da tarihin magabata! Ina bayyana alheri, ina binne dukkan wani aibi a qarqashin qasa! Kuma ina aiki da abin da mawaqi ya fada a baitocinsa inda yake cewa:

Babu mai riqe sirri face mutumin kirki,

Kuma mutanen kirki suna boye sirri a zuciyarsu!

A wurina sirri tamkar wani daki ne da aka kulle,

Wanda ba shi da makulli kuma aka buga hatimi a kofarsa!"

Ko da 'yan matan suka ji wadannan zafafan baitoci nasa da yadda ya mayar musu da amsa cikin fasaha da zance mai azanci, sai suka dube shi suka ce: "Ka sani fa mun kashe dukkan dukiyarmu wajen sayen wadannan kayan alatu da kake gani! To kai kuma wane abu zaka bamu a matsayin taka gudunmawa domin ka zama abokin shaye-shayenmu da nishadinmu? Domin kuwa ba za mu taba barin ka ka zauna a tare da mu, kana kallon kyan fuskokinmu ba tare da ka biya wani abu ba! Domin kuwa kamar yadda magabata suka ce:

Idan babu kwadayin riba,

To soyayya ba ta da ko qwayar zarra ta kima!

Kuma idan ka zo da wani abu to kai wani ne, amma idan ba ka zo da komai ba, to maza ka bace mana da gani domin kai ba kowa ba ne!"

Sai dai kafin dan dako ya yi magana, sai budurwa mai sayayya ta tsoma baki ta ce: "A'a ya 'yan'uwana! Ku bar yi masa tsokana haka mana! Na rantse da Allah a yau wannan bawan Allah ya nuna mani halin kirki da karamci mara misali, da wani ne daban ba zai taba jure kwasar wannan kaya mai mugun nauyi yana bina lungu da saqo a cikin birni ba! Saboda haka duk abin da za a nema daga gare shi, to na dauke shi a kaina!"

Ko da jin wannan batu, sai dan dako ya cika da matsanancin farin ciki! Ya durqusa har qasa ya sumbaci qasa a gabanta yana mata godiya mara iyaka. Sannan ba tare da wata-wata ba, ya zura hannunsa a cikin aljihu ya kwaso dukkan kudaden dinaren da suka ba shi ya ajiye a gabansu, ya ce: "Wallahi wadannan kudade su ne amfanin farko da na samu a yau, ga su duka na mayar muku kyauta a matsayin tukuicin zama a wannan fada!"

Ganin irin wannan karamci nasa, sai dukkan 'yan matan suka fashe da dariya mai kayatarwa. Budurwa babba ta ce: "Zauna maraba da kai! Na rantse da Allah ba za mu hana ka zama a tare da mu ba bayan ka nuna wannan karamci da cikar hali!"

To amma sai ta daure fuskarta kadan, idanuwanta suka yi kwarjini ta ce: "Sai dai akwai babban sharadi guda daya kacal da za mu gindaya maka: KADA KA KUSKURA KA YI TAMBAYA A KAN ABIN DA BAI SHAFE KA BA! Domin an rubuta a kan kofar wannan fada tamu da zallan ruwan zinare cewa: DUK WANDA YA YI MAGANA A KAN ABIN DA BAI SHAFE SHI BA, TO KUWA ZAI JI ABIN DA BA ZAI YI MASA DADI BA!"

Dan dako ya sunkuyar da kansa cikin ladabi da biyayya ya ce: "Na amince da wannan sharadi ya shugabata! A kan kaina da idanuwana! Ku dauke ni kamar kurma kuma bebe wanda ba shi da harshen magana a kan duk abin da bai shafeshi ba!"

Nan take kuwa, budurwa mai sayayya ta daure kugunta da kyalle, ta shirya teburin abinci a gefen tafkin marmara, ta zuba furanni a cikin kwanoni masu qamshi, ta tace ruwan inabi a cikin tasoshin kanti, ta jera kwalabe a kan teburi. Suka zauna ita da 'yan'uwanta mata, suka zaunar da dan dako a tsakiyarsu, shi kuwa dan dako yana jin kansa kamar a mafarki yake ba a farke ba!

Budurwa mai sayayya ta dauki gorar ruwan inabi ta tsiyaya a kofi na farko ta shanye tas domin nuna cewa ba shi da wata illa ko dafi a ciki, ta sake tsiyaya kofi na biyu ta shanye, ta sake tsiyaya na uku ta shanye! Sannan ta tsiyayi kofi na hudu ta miqa wa babbar yayarta, sannan ta cika wani kofi na alfarma ta miqa wa dan dako tana mai cewa cikin baitoci:

Sha wannan abin sha mai daraja, ka sha cikin nishadi da walwala,

Wanda ke warkar da kowace irin damuwa da radadin zuciya!

Dan dako ya karbi kofi yana mai rusunawa cikin tsananin ladabi da godiya, sai ya rera baitoci yana cewa:

Wannan ruwan inabi ya mayar da ni tamkar Sarki a kan karagarsa,

Yana gusar da duk wani tsoro da zullumi daga zuciyata!

Yau na tsinci kaina a cikin gidan alfarmar da babu kamarta,

A tsakiyar kyawawan matan da suka fi taurarin sama haske!

Dan dako ya kafa kofi a bakinsa ya shanye wannan ruwan inabi tas! Nan take wani irin shauqi da nishadi suka fara ratsa dukkan jijiyoyin jikinsa, kansa ya fara sarawa da maye mai dadi! Ya miqe yana rawa yana kada kai, yana zolayar 'yan matan nan da barkwanci, su kuma suna kwashewa da dariya. Suka ci gaba da shaye-shaye, da raye-raye, da ciye-ciyen nama da kayan zaki, da hirarrakin annashuwa a tsakaninsu har sai da dare ya tsala sosai..."

A daidai wannan gaba, sai hasken alfijir ya fara ketowa a sararin samaniya, Shahrazad ta ga safiya ta yi, sai ta dakata da zancenta mai dadin sauraro ta yi shiru!

Dunyazad ta dube ta da matuqar sha'awa da shauqi ta ce: "Kai ya yayata! Lallai wannan labari ya cika da zakin kunne, da dadi, da cikar nishadi da ban al'ajabi mara misali!"

Shahrazad ta yi murmushi ta dube ta ta ce: "Ai wannan ba komai ba ne idan aka kwatanta shi da labarin da zan fada muku a dare mai zuwa, idan har Allah Ya raya ni kuma wannan babban Sarki ya qyale ni?"

Ko da Sarki Shahriyar ya ji wannan batu, sai ya ce a ransa: "Wallahi ba zan kashe ta a yau ba, sai na ji sauran wannan kyakkyawan labari mai ban mamaki!"

Wayewar gari ke da wuya, Sarki ya fita fada ya gudanar da al'amuran mulki yana bayar da umarni da hani har dare ya sake rufowa, shi kuwa babban Waziri ya koma gida fuskarsa cike da farin ciki da godiyar Allah da ya ga 'yarsa tana ci gaba da rayuwa cikin aminci!

(A nan muka kawo qarshen BABI NA GOMA SHA DAYA cif!)

====================================================================

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol