Free chapter · Read without an account

BABI NA GOMA SHA HUDU (14): CIGABAN HIKAYAR DAN DAKO DA MATAN BAGADAZA: LABARIN KALANDAR NA FARKO

by Shuraihu Usman · DARE DUBU DA DAYA 1001 Mujalladi na Daya 1

====================================================================

DARE DUBU DA DAYA (ALF LAILA WA LAILA)

BABI NA GOMA SHA HUDU (14): CIGABAN HIKAYAR DAN DAKO DA MATAN BAGADAZA: LABARIN KALANDAR NA FARKO

[DARE NA GOMA SHA BIYU]

Fassarar: Shuraihu Usman

====================================================================

A babi na goma sha uku idan mai karatu bai manta ba, mun tsaya a inda Zubaida ta yi wa karnuka baqaqe biyu dukan bulala tana kuka, sannan Amina ta rera qasidun kuka ta yaye tufafinta aka ga tabon dukan kisa a jikinta har ta suma, Dan Dako ya tambaye su asirin abin da ya sa Zubaida ta sa qatta-qattan bayi suka daure dukkan bakin da igiyoyi aka zare takuba domin sare kawunansu, amma bayan Dan Dako ya rera baitocinsa ya fadi gaskiyar labarinsa aka kwance shi, sai Kalandar na farko ya matso gaba domin bayyana labarinsa a karshen DARE NA GOMA SHA UKU. To yanzu bari mu ji labarin wannan Kalandar na farko mai cike da al'ajabi da ban tsoro a cikin wannan DARE NA GOMA SHA BIYU.

--- DARE NA GOMA SHA BIYU ---

Gari ya waye, Sarki Shahriyar ya fita fada ya gudanar da al'amuran mulki ba tare da ya ambaci batun kisan Shahrazad ba. Babban Waziri ya koma gida yana godiya ga Allah da ya ga 'yarsa tana ci gaba da rayuwa cikin aminci.

Da dare ya tsala a cikin wannan DARE NA GOMA SHA BIYU, Sarki Shahriyar ya shigo daki ya kwanta da Shahrazad. Bayan ya gama biyan bukatarsa, sai qanwarta Dunyazad ta tashi daga qasan shimfida ta ce:

"Ya yayata, idan baki fara barci ba, don girman Allah ki ba mu wannan labari mai dadi na Kalandar na farko domin mu ji dalilin da ya sa aka aske gashinsa da yadda idonsa ya tsiyaye a cikin wannan dare!"

Shahrazad ta duba wajen Sarki Shahriyar cikin ladabi ta ce: "Zan ba da labarin idan har wannan babban Sarki mai daraja ya ba ni izini!" Sarki ya ce: "Fadi ina saurarenki!"

Nan take Shahrazad ta fara ba da wannan kyakkyawan labari a cikin wannan DARE NA GOMA SHA BIYU kamar haka:

"Kalandar na farko ya matso gaban Zubaida da 'yan'uwanta, ya sunkuyar da kansa cikin natsuwa ya fara ba da labarinsa kamar haka:

'Ki sani ya ke wannan shugabata mai girma, cewa ni asali na ba Kalandar ko mabaraci ba ne! Ni dan wani babban Sarki ne mai mulkin wata katafariyar daula. Mahaifina yana da wani kani wanda shi ma babban Sarki ne mai mulkin wani babban birni na daban.

An haife ni ni da dan baffana a rana guda cif! Saboda haka muka tashi a matsayin amintattun abokai tun muna qanana. Da na girma sai na riqa kai masa ziyara a fadar mahaifinsa, ina kwashe watanni a tare da shi cikin nishadi da soyayya. Ya kasance yana karrama ni matuqa: yana yanka mani mafiya kiba daga cikin dabbobinsa, yana shayar da ni mafiya dadi daga ruwan inabinsa, ba ma rabuwa dare da rana!

Wata rana, bayan mun sha ruwan inabi mun bugu sosai, sai dan baffana ya kalle ni cike da damuwa ya ce:

'Ya dan baffana, akwai wata babbar bukata ta sirri da nake so ka taimaka mani da ita, kuma ina so ka rantse da babban rantsuwa cewa ba za ka taba bijire mani ba, kuma ba za ka tambaye ni dalili ba!'

Na dube shi da dukkan yarda na ce: 'Na amince! Na rantse da Allah zan cika maka dukkan abin da kake bukata!'

Bayan ya karbi rantsuwata, sai ya fita daga dakin. Jim kadan sai ga shi ya dawo yana jagorantar wata kyakkyawar budurwa wadda aka lullube ta da mayafi mai kauri, tana sanye da tufafin zinare da lu'u-lu'u masu matuqar tsada!

Dan baffana ya dube ni ya ce: 'Dauki wannan budurwa ka yi gaba da ita zuwa makabartar birni, ka shigar da ita cikin wani babban kabarin gado da aka gina da duwatsu (ya kwatanta mani wajen sarai), ka zauna tare da ita a can har sai na zo!'

Saboda rantsuwar da na yi masa, sai na kasa yin tambaya. Na tafi da budurwar a cikin duhun dare har zuwa wannan makabarta, muka shiga cikin wannan katafaren kabari muka zauna.

Ba a dade ba sai ga dan baffana ya shigo! Yana dauke da kwanon ruwa, da buhun farar qasar siminti, da kuma wata fartanya mai kaifi. Ya tsaya a tsakiyar kabarin, ya fara fasa simintin qasan kabarin da fartanya yana kwashe duwatsun gefe guda.

Bayan ya tona qasa sosai, sai ga wani katon marfin qarfe mai siffar kofa ya bayyana!

Ya daga marfin qafen, sai ga wani matakala mai karkata mai dauke da takalman bene guda hamsin (50) yana sauka zuwa can kasan qasa!

Dan baffana ya kalli wannan budurwa ya ce da ita: 'Yanzu ki zabi abin da kike so a rayuwarki!' Budurwar ba ta yi wata-wata ba, ta fara sauka ta kan matakalar benen har ta bace a kasan qasa!

Daga nan sai dan baffana ya juyo wajena ya ce: 'Ya dan baffana, domin cika alherinka a gare ni: da zarar na sauka cikin wannan rami, to ka mayar da wannan marfin qarfe ka rufe kofar, ka mayar da qasa ka binne shi, sannan ka kwaba wannan farar qasar siminti da ruwan kwanon nan ka shafa a saman duwatsun ta yadda babu wanda zai san an taba bude wannan wuri! Shekara guda cif na kwashe ina gina wannan daki a qarqashin qasa babu wanda ya sani sai Allah! Allah Ya saka maka da alheri, kuma kada Ya raba mu da kai!'

Rufe bakinsa ke da wuya, sai ya sauka ta kan matakalar ya bace a qasan qasa!

Ni kuwa saboda mayen ruwan inabi da ke kaina, sai na mayar da marfin qarfen na rufe, na cika qasa, na kwaba farar qasar siminti na gyara wurin sumul kamar yadda ya umurce ni, sannan na koma fadar mahaifinsa na kwanta barci.

Washegari da safe na tashi, sai mayen ruwan inabi ya sake ni, hankalina ya dawo jikina!

Nan take na tuna dukkan abin da ya faru a daren jiya, sai matsananciyar nadama da fargaba suka kama zuciyata! Na ce a raina: 'Kashina ya bushe! Wane irin danyen aiki ne na aikata? Shin mafarki nake yi ko kuwa a zahiri ne?'

Na fita ina tambayar mutane ko sun ga dan baffana, amma kowa ya ce bai gan shi ba! Mahaifinsa kuma Sarki ya fita farauta a daji.

Na nufi makabartar a guje domin na bude kofar na fito da shi, amma abin mamaki: saboda yawan dubban kaburbura da ke wurin, sai na rasa gane ainihin kabarin da na rufe shi a ciki! Na yi ta zagaye ina kuka ina dube-dube har dare ya yi, amma ban gano wurin ba!

Na kwashe kwanaki bakwai (7) a cikin makabartar ina neman wannan kabari, amma na gaza samun sa. Hankalina ya gama tashi, na shiga cikin wata matsananciyar damuwa da hauka! Ganin babu mafita, sai na tattara kayana na kama hanyar komawa birnin mahaifina.

Amma yayin da nake shiga qofar birnin mahaifina, sai wasu rundunar mayaka suka auka mani, suka damqe ni suka daure hannayena a bayana tamkar wani barawo!

Na cika da matuqar mamaki domin ni dan Sarki ne, kuma a cikin wadanda suka daure ni har da wasu bayina na kaina! Na tambaye su: 'Me ya faru? Ina mahaifina yake?'

Daya daga cikinsu ya amsa mani da cewa: 'Mahaifinka ya riga ya mutu! Sojojinsa sun ci amanarsa, babban Wazirinsa ya kashe shi ya karbe mulkin masarautar! Kuma shi Wazirin ya bamu umarnin mu kama ka mu kawo ka gabansa!'

Duniya ta yi mani duhu! Suka tafi da ni kai tsaye zuwa fadar mahaifina, inda na tarar da wannan mugun Waziri zaune a kan karagar mulkin mahaifina yana takama!

Ki sani ya ke wannan shugabata, a tsakanina da wannan Waziri akwai wani tsohon qiyayya da gaba tun ina yaro:

Wata rana ina tsaye a kan rufin fada ina harbin tsuntsaye da wata 'yar baka mai harba duwatsun laka, sai na saki wani dutse domin na harbi wani tsuntsu da ya sauka a kan gidan Waziri. Amma kuskure ya sa dutsen ya kauce ya fada daidai a kan idon daman wannan Waziri ya tsiyaye shi sarai ya makance!

A wancan lokaci bai iya cewa komai ba saboda tsoron mahaifina, amma ya boye qiyayyata a qirjinsa yana jiran ranar daukar fansa! Kamar yadda mawaqi ya rera a kan qaddara yana cewa:

Muna taku a kan hanyar da qaddara ta tsara mana,

Hanyar da alqalamin qaddara ya rubuta dole ne mu bi ta!

Duk mutumin da aka rubuta zai mutu a wata qasa,

To babu wani wuri da mutuwa zata riske shi face a can!

Kuma wani mawaqin ya sake cewa:

Ka bar zamani ya yi duk abin da yake so,

Ka kwantar da zuciyarka ka yi biyayya ga hukuncin qaddara!

Kada ka cika farin ciki ko baqin ciki a kan komai,

Domin dukkan al'amuran duniya masu wucewa ne ba masu tabbata ba!

Ko da aka kai ni gaban wannan mugun Waziri a daure, sai ya dube ni da dariyar mugunta ya ce: 'Maza ku sare kansa!'

Na ce da shi: 'Wane laifi na yi da zaka kashe ni?'

Waziri ya nuna gurbin idonsa da ya makance da yatsansa ya ce: 'Wane babban laifi ne ya fi wannan? Ka cire mani idona kana yaro!'

Na ce: 'Kuskure ne na yi ba da gangan ba!'

Waziri ya ce: 'Idan kai ka yi da kuskure, to ni kuma zan cire naka da gangan!'

Nan take ya bayar da umarni aka matso da ni kusa da shi. Ya sanya dogon yatsansa mai kaifi ya danna a cikin idona na dama, ya kakkabe shi ya tsiyaye shi sarai a gabana!

Na saki wata qaqqarfar qara saboda tsananin azaba, jini ya wanke fuskata, na zama mai ido daya kamar yadda kuke gani a yanzu!

Bayan haka, sai Waziri ya sa aka daure ni a cikin wani akwatin katako, ya damqa ni ga Hauni mai fille kai ya ce: 'Kwashe shi ka kai shi can tsakiyar jeji, ka zaro takobinka ka sare kansa ka bar naman jikinsa dabbobin daji su cinye!'

Hauni ya dauke ni ya tafi da ni can tsakiyar hamada. Da ya fito da ni daga akwati ya daga takobinsa domin ya sare kaina, sai na fashe da kuka mara iyaka!

Na dube shi da idona guda daya, na rera wasu baitoci na waqa masu ban tausayi ina cewa:

Na dauke ku tamkar sulke na qarfe da zai kare ni daga kibiyoyin maƙiya,

Sai ga shi kun zama takobin maƙiyi da ke saran jikina!

Ina fatan samun taimakonku a dukkan tsananin rayuwata,

Ko da hannuna na hagu ya gaza taimakon hannuna na dama!

Kuna tsaye a nesa kuna jin zagin masu zagi da tozarci,

Yayin da kibiyoyinsu ke zuba a kaina tamkar ruwan sama!

Idan har ba za ku kare ni daga sharrin maƙiyana ba,

To ku tsaya a gefe, kada ku taimake ni kuma kada ku cutar da ni!

Sannan na sake karanta masa wani baiti ina cewa:

Na dauki 'yan'uwana tamkar sulke na qarfen qarafa mafi qarfi,

Kuma haka suka kasance—amma wajen tare kibiyoyina kada su sami maƙiya!

Na dauka kibiyoyinsu su ne mafiya daidaita a wurin harbi,

Kuma haka suka kasance—a daidai lokacin da suka saiti zuciyata suka harba!

Ko da Hauni ya ji wadannan baitoci nawa (shi bawan mahaifina ne kuma yana da bashin alherin mahaifina a kansa), sai tausayi ya kama shi ya fashe da kuka mai tsanani tare da ni!

Hauni ya jefar da takobinsa a qasa ya rera mani wasu baitoci na nasiha yana cewa:

Ka ceci ranka ka gudu a lokacin da masifa ta taso maka,

Ka bar kufan gida ya bayyana makomar ma'abocinsa!

Zaka nemi wata sabuwar qasa ka same ta a madadin wadda ka bari,

Amma ba za ka taba samun sabuwar rayuwa a madadin ranka ba!

Abin mamaki ne mutum ya zauna a wurin qasqanci da tozarci,

Alhali duniyar Allah tana da fadin gaske da daukaka!

Kada ka dogara da wani a cikin manyan al'amuran rayuwa,

Domin rai dole ne ya tsaya ya ceci kansa a lokacin qunci!

Zaki ba ya taba yawo yana karkada wutsiyarsa a cikin daji,

Idan har yana fatan samun taimako ko jinqai daga wani!

Hauni ya kwance ni ya ce: 'Ya dana dan Sarki! Ka gudu yanzu-yanzu kuma kada ka sake dawowa wannan qasa har abada, domin idan suka gano ka zasu kashe ka kuma su kashe ni tare da kai!'

Na sumbaci hannunsa cike da godiya, na ruga a guje cikin duhun dare ina gudu har sai da na tsallaka kan iyakar qasar na koma birnin baffana!

Da shigata fadar baffana, na fada gabansa ina kuka, na sanar da shi kisan da aka yi wa mahaifina da kuma yadda Waziri ya cire mani ido na dama.

Baffana ya fashe da kuka mai tsanani ya rungume ni ya ce: 'Ya dana, ka qara mani wani sabon baqin ciki a kan wanda nake ciki! Domin tun tafiyarka dana guda daya tilo ya bace a cikin gari babu wanda ya san inda yake har yau!'

Ganin yadda baffana ke kuka, sai na kasa jurewa, na yanke shawarar fada masa gaskiyar abin da ya faru tsakanina da dansa a makabarta!

Ko da baffana ya ji labarin ramin qarqashin qasa, sai ya yi tsalle ya ce: 'Maza zo ka nuna mani wurin mu fito da shi!'

Muka tafi makabarta tare da baffana. A wannan karon da taimakon Allah sai na hango kabarin kai tsaye!

Muka tona qasar da sauri, muka bude marfin qarfen, muka ga wannan bene mai matakalu hamsin. Muka shiga sauka a hankali har muka isa qasa.

Amma da isarmu kasan benen, sai wani mummunan hayaki mai kauri da zafin gaske ya tare mu!

Muka kutsa cikin hayakin har muka shiga cikin wani katafaren daki da aka shirya da kayan abinci, da shimfidu, da fitilu. A tsakiyar dakin akwai wani katafaren gado na alfarma mai labule.

Baffana ya nufi gadon ya yaye labulen domin ya ga dansa, amma sai ya yi arba da wani abin firgici wanda ba a taba gani ba a duniya!

Ya ga dansa da wannan kyakkyawar budurwa a rungume da juna a kan shimfida, amma dukkan jikinsu ya qone qurmus ya zama baqin gawayi tamkar an jefa su a cikin wutar jahannama! Fatar jikinsu da namansu duk sun kone baki wulik babu abin da ya rage sai toka da gawayi!

Ko da baffana ya ga wannan abin tsoro, sai ya tofa yawu a fuskar gawar dansa da ke kone, ya cire takalminsa ya riqa dukan fuskar gawar yana cewa:

'Wannan shi ne sakamakonka ya kai wannan lalatacce! Wannan shi ne hukuncin da Allah Ya yi maka a duniya, kuma hukuncin lahira ya fi wannan zafi da dorewa!'

Na cika da mamaki na ce: 'Haba baffana! Me ya sa kake dukan gawar danka bayan ga shi ya riga ya zama toka a gabanka?'

Baffana ya fashe da kuka ya ce: 'Ya dana, ashe baka san abin da ke tsakaninsu ba? Wannan yarinya da kake gani 'YAR'UWARSA CE TA JINI, 'yata ce ta cikina! Tun suna qanana ya kamu da son 'yar'uwarsa, na yi ta tsawata masa na hana shi na raba dakunansu amma shaidan ya rudi zukatansu suka kulla wannan aiki na alfasha! Lokacin da na matsa musu, sai ya zo nan ya gina wannan daki a boye domin su riqa aikata sabo a qarqashin qasa! To ga shi fushin Allah Ya sauka a kansu daga sama, wuta ta cinye su kurmus!'

Baffana ya rungume ni yana kuka, muka rufe qabarin muka fito.

Amma da isarmu fada, sai muka ji kade-kaden yaqi da bushe-bushen qaho! Ashe wannan mugun Waziri da ya kashe mahaifina ya tattaro rundunar mayaka dubu-da-dubbai ya kawo hari a kan birnin baffana domin ya qare daular gaba daya!

Baffana ya fita yaqi aka kashe shi a filin daga, birnin ya fada hannun maƙiya!

Ni kuwa ganin babu mafita kuma idan aka gane ni za a kashe ni, sai na aske gashin kaina sumul, na aske gemuna da girata gaba daya, na sanya tufafin Kalandarawa na fita a boye!

Na yi ta yawo qasa-qasa har qaddara ta kawo ni wannan birni na Bagadaza a yau da yamma. Ina tsaye a kan hanya sai na hadu da wannan Kalandar na biyu, bayan kadan sai Kalandar na uku ya zo, muka hadu muka zama 'yan'uwa baki daya har qaddara ta kawo mu wannan fada!

To kin ji dalilin aske gashina da kuma tsiyayewar idona na dama ya ke wannan shugabata mai girma!'

Ko da Zubaida da kowa a falon suka ji wannan labari mai ban tsoro da tausayi, sai suka cika da mamaki!

Zubaida ta dube shi da tausayi ta ce: 'Lallai labarinka ya cika da ban al'ajabi! Shafa kanka ka tashi ka kama gabanka lafiya, mun yafe maka!'

Amma Kalandar na farko ya sunkuyar da kai ya ce: 'Na rantse da Allah ba zan taba barin wannan wuri ba har sai na ji labarin wadannan 'yan'uwana guda biyu!'..."

A daidai wannan gaba, sai hasken alfijir ya fara ketowa a sararin samaniya, Shahrazad ta ga safiya ta yi, sai ta dakata da zancenta mai dadin sauraro ta yi shiru!

"

(A nan muka kawo qarshen DARE NA GOMA SHA BIYU da kuma BABI NA GOMA SHA HUDU cif!)

====================================================================

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol