Free chapter · Read without an account

BABI NA GOMA SHA BAKWAI (17): CIGABAN HIKAYAR DAN DAKO DA MATAN BAGADAZA: CIGABAN LABARIN KALANDAR NA BIYU

by Shuraihu Usman · DARE DUBU DA DAYA 1001 Mujalladi na Daya 1

====================================================================

DARE DUBU DA DAYA (ALF LAILA WA LAILA)

BABI NA GOMA SHA BAKWAI (17): CIGABAN HIKAYAR DAN DAKO DA MATAN BAGADAZA: CIGABAN LABARIN KALANDAR NA BIYU

[DARE NA GOMA SHA HUDU]

Fassarar: Shuraihu Usman

====================================================================

A babi na goma sha shida idan mai karatu bai manta ba, mun tsaya a inda Ifiritu Jurjanisu ya mayar da Yarima Kalandar na biyu siffar Biri, ya shiga jirgin ruwa har ya isa wani katafaren birni inda ya rubuta khattin larabci na alfarma iri bakwai a gaban Sarki, ya doke Sarki a wasan dara, Sarki ya yi murna ya sa aka kirawo 'yarsa budurwa mai suna Sitrul Husni domin ta ga wannan abin mamaki a karshen DARE NA GOMA SHA SHIDA. To yanzu bari mu ji irin gagarumin yaqin wutar sihiri da zai kaure tsakanin wannan budurwa da Ifiritu Jurjanisu a cikin wannan DARE NA GOMA SHA HUDU.

--- DARE NA GOMA SHA HUDU ---

Gari ya waye, Sarki Shahriyar ya fita fada ya gudanar da al'amuran mulki ba tare da ya ambaci batun kisan Shahrazad ba. Babban Waziri ya koma gida yana godiya ga Allah da ya ga 'yarsa tana ci gaba da rayuwa cikin aminci.

Da dare ya tsala a cikin wannan DARE NA GOMA SHA HUDU, Sarki Shahriyar ya shigo daki ya kwanta da Shahrazad. Bayan ya gama biyan bukatarsa, sai qanwarta Dunyazad ta tashi daga qasan shimfida ta ce:

"Ya yayata, idan baki fara barci ba, don girman Allah ki ba mu wannan labari mai cike da mamaki na Kalandar na biyu domin mu ji yaqin wutar sihirin da kuma yadda aka karya sihirin birin nan a cikin wannan dare!"

Shahrazad ta duba wajen Sarki Shahriyar cikin ladabi ta ce: "Zan ba da labarin idan har wannan babban Sarki mai daraja ya ba ni izini!" Sarki ya ce: "Fadi ina saurarenki!"

Nan take Shahrazad ta gyara zama ta ci gaba da ba da wannan kyakkyawan labari a cikin wannan DARE NA GOMA SHA HUDU kamar haka:

"Kalandar na biyu ya gyara zama ya ci gaba da ba wa Zubaida da bakin da ke falon labarinsa kamar haka:

'Bayan Sarki ya bayar da umarni, sai ga 'yarsa Gimbiya SITRUL HUSNI ta shigo cikin falon fadar. Wannan budurwa ta kasance mai matuqar kyau da haske tamkar farin wata, tana sanye da mayafi mai kauri na alharini.

Amma ko da ta shiga dakin ta hango ni a matsayin biri a kan kujerar alfarma, sai ta ja da baya da sauri, ta rufe fuskarta da mayafinta ta daka wa mahaifinta tsawa ta ce:

'Subhanallah! Ya mahaifina, wace iriyar tozarci ce wannan? Ta yaya zaka kira ni har cikin daki a gaban wani qaqqarfan namiji baligi ba tare da na rufe jikina ba?'

Sarki ya zazzare idanuwa da mamaki ya duba ko'ina a falon, ya ce: 'Ina namiji a nan ya ke 'yata face wannan birin da ke zaune a gefena wanda ya kware a rubutu da wasan dara?'

Gimbiya Sitrul Husn ta yi murmushi ta ce: 'Ya mahaifina, wannan ba biri ba ne da kake gani! Wannan babban Yarima ne dan Sarki, wanda tsinannen IFIRITU JURJANIS BIN RAJMUS ya mayar da shi siffar dabba bayan ya sare hannayen 'yar Sarkin Jaziratul Abnus!'

Ko da Sarki ya ji wannan batu daga bakin 'yarsa, sai ya zaro idanuwa cike da firgici da mamaki! Ya kalle ni a matsayin biri, ya ga yadda nake gyaɗa kaina ina nuna tabbatarwa ina zubar da hawaye!

Sarki ya rungumi 'yarsa ya ce: 'Ya 'yata, kin san cewa tun kina yarinya wata tsohuwa mai karamci ta koya miki dukkan sirrikan ilimin sihiri da na dalasumai na kofofi saba'in (70) na zamanin Annabi Sulayman! Shin za ki iya taimaka wa wannan bawan Allah ki karya masa wannan sihiri ya dawo mutum kamar yadda yake?'

Gimbiya ta yi ajiyar zuciya mai sanyi ta ce: 'Zan iya karya sihirin da izinin Allah Madaukaki, amma wannan aiki yana da matuqar hadarin gaske, domin akwai yiwuwar na rasa rayuwata a cikinsa! Amma zan daure domin Allah!'

Nan take Gimbiya Sitrul Husn ta ciro wata 'yar qaramar wuka mai dauke da rubutun khattin Ibraniyanci a jiki. Ta tsaya a tsakiyar falon marmara, ta zana wani babban da'ira a qasa, ta rubuta wasu dalasumai da sunaye masu tsarki da khattin Kufiyya a kewayen da'irar, sannan ta tsaya a tsakiya ta fara karanta wasu miyagun dalasumai tana tofa iska!

Rufe bakinta ke da wuya, sai rana ta dusashe a sararin samaniya, duniya ta yi duhu tamkar tsakiyar dare! Walkiya ta riqa fantsama, qasa tana rawa!

Katsam sai ga Ifiritu Jurjanis ya bayyana a tsakiyar falon a ainihin siffarsa ta tsoro: hannayensa tamkar manyan mahaka masu kaifi, kafafunsa tamkar rassan itatuwan dabino, idanuwansa tamkar manyan garwashin wuta suna zubar da tartsatsi!

Ifiritu ya daka wata gigitacciyar tsawa ya ce: 'Barka da zuwa ya ke wannan mayya! Me ya sa kika keta alqawarin da muka yi cewa kowa ya zauna a bangarensa?'

Gimbiya ta daka masa tsawa ta ce: 'Babu alqawari a tsakanina da kai ya kai wannan tsinannen kafiri!'

Nan take Ifiritu Jurjanis ya fara karkarwa, ya rikide ya koma wani qaton ZAKI mai matuqar muni da girma! Zakin ya bude bakinsa yana gurnani ya rugo da dukkan qarfinsa domin ya shake Gimbiya!

Amma Gimbiya Sitrul Husn ta yi wuf! Ta cire gashi guda daya daga kanta, ta tofa asiri a kai ta jefar a iska: nan take gashin ya rikide ya zama wata qatuwar TAKOBI mai kaifi tamkar walkiya! Da sara guda daya takobin ta datse zakin nan gida biyu daga tsakiya!

Amma abin mamaki: kan zakin da ya fadi sai ya rikide ya zama wata baqar kunama mai matuqar muni da dafin kisa!

Gimbiya ba ta tsaya ba, nan take ta rikide ta zama wani katon MACIJI mai kauri, ta shiga fada da wannan kunama! Suka yi ta kokuwa da juyawa a tsakar falon har tsawon sa'a guda.

Ko da kunamar ta ga zata mutu, sai ta fiffike fukafukai ta rikide ta zama wata babbar ungulu!

Nan take macijin ya rikide ya zama wata babbar mikiya, ya bishi a guje a sararin samaniya yana dukansa da fikafikai!

Ungulun ya gaza tsira, sai ya sauko qasa ya zama wata baqar kyanwa mai fitar da miyau tana kuka!

Mikiyar ta sauko ta rikide ta zama kerkeci, ya shiga kai wa kyanwar hari ta ko'ina!

Kyanwar ganin cewa ajalinta ya kusa, sai ta yi wuf ta rikide ta zama wata 'yar qaramar tsutsa, ta kutsa kai cikin wata katuwar 'ya'yan rumman da ke ajiye a gefen kogi a tsakiyar falon!

Rumman din nan ya kumbura a iska ya zama kamar kankana, sannan ya fadi a kan marmara ya fashe gida biyu! 'Ya'yan rumman din nan jajaye dubu-da-dubbai suka bazu a dukkan fadin falon!

Nan take kerkecin nan ya girgiza jikinsa, ya rikide ya zama wani farin zazaran zakara! Zakaran ya shiga tsintar wadannan 'ya'yan rumman yana hadiyewa da gaggawa da bakinsa domin kada ya bar ko qwaya daya wadda Ifiritun ke ciki!

Zakaran ya gama cin kusan dukkan 'ya'yan rumman din, sannan ya fara kakarwa da buga fikafikansa yana dube-dube a qasa!

Amma ashe da qaddarar Allah, akwai qwayar rumman guda daya tilo wadda ta gangara ta fada cikin ruwan tafkin marmara ta boye a qasan ruwa!

Zakaran ya hango ta, ya ruga da sauri domin ya tsince ta, amma kafin ya isa sai qwayar ta rikide ta zama wani KIFI mai sauri a kasan ruwa!

Zakaran bai bata lokaci ba, ya zabura ya kutsa cikin ruwan ya rikide ya zama wani babban KIFIN RUWA mai hauri, ya nutse kasan ruwan yana bin sa a guje!

Muka shiga jin wasu qaqqarfan kururuwa da kuka mai ban tsoro daga kasan ruwan har sai da falon ya fara girgiza!

Bayan dan wani lokaci, sai ga Ifiritu ya fito daga kasan ruwan a ainihin siffarsa, amma a wannan karon ya zama WUTAR DAJI mai cin kanta! Yana fesa harshen wuta da kauri daga bakinsa, da idanuwansa, da hancinsa!

Gimbiya Sitrul Husn ma ta fito daga ruwan a matsayin wani garwashin wuta mai tsananin haske da zafi!

Suka rungume juna a cikin wutar suna kokuwa! Hayaki mai kauri da zafin gaske ya rufe dukkan falon fadar, har numfashinmu ya fara daukewa saboda zafin iska!

Sarki ya dafe kansa yana kuka yana cewa: 'Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Kashina ya bushe! Da na san haka zata faru da ban sa 'yata a cikin wannan bala'i ba!'

Ifiritu ganin cewa wutar Gimbiya ta kusa cinye shi, sai ya daka wata mahaukaciyar tsawa a cikin wutar, ya juyo wajen da muke tsaye a kan dandamali, ya fesa mana wani gagarumin garwashin wuta a fuskokinmu!

Gimbiya ta rugo da sauri domin ta kare mu da wutarta, amma kafin ta gama tare wutar:

Sai wani tartsatsin wuta daga bakin Ifiritun ya fada daidai a kan IDONA NA DAMA! Wutar ta qone idona na dama qirrr ya zama toka a take!

Wani tartsatsin kuma ya fada a fuskar Sarki, ya qone gemunsa da fuskarsa ya kakkabe masa hakoransa na qasa!

Wani tartsatsin kuma ya fada a qirjin babban bawan Sarki, ya qone shi ya mutu a nan take!

Muka tabbatar da cewa ajalinmu ya zo!

Amma a daidai wannan lokaci, sai muka ji wata murya mai zaki da amo tana cewa: 'ALLAHU AKBAR! ALLAHU AKBAR! Taimako da nasara sun tabbata ga ma'abota gaskiya, tozarci da hallaka sun tabbata ga kafirai!'

Ashe Gimbiya ce ta kwararo wa Ifiritu Jurjanis wani farar wuta ta musamman, ta cinye shi qas! Ifiritu ya saki wata qara ya bace ya zama wani tulin toka a qasa!

Gimbiya ta fito tana haki tana cewa: 'Maza ku kawo mani kofin ruwa!'

Aka kawo mata ruwa a kofi. Ta tofa wasu kalmomi a ciki, sannan ta yayyafa mani ruwan tana cewa: 'Da darajar gaskiya da girman sunan Allah Madaukaki, ka fita daga siffar dabba ka koma mutum kamar yadda kake a asali!'

Rufe bakinta ke da wuya, sai na girgiza, gashin dabbanci ya zube tas, na miqe tsaye a matsayin mutum kamar yadda nake! Amma idona na dama ya riga ya bace ya zama gurbi babu komai a ciki!

A daidai wannan lokaci, sai Gimbiya ta fashe da kuka ta zube a qasa tana cewa:

'Wuta! Wuta! Ya mahaifina, wani kibiya na wutar tsinannen aljanin nan ya shiga har cikin hantata da zuciyata! Ban saba da yaqin aljanu ba, na kashe shi amma shi ma ya raunata ni da raunin mutuwa! Ku yi mani afuwa, domin tafiyata ta zo!'

Sarki ya rungume ta yana kuka yana ihu: 'Wayyo 'yata! Kada ki mutu ki bar ni!'

Amma a take sai wata baqar wuta ta fara tashi daga yatsun kafafunta tana hawa zuwa cinyoyinta, sannan ta haura zuwa qirjinta da fuskarta!

Gimbiya ta share hawayenta ta kalli sama ta ce: 'ASH-HADU ALLA ILAHA ILLALLAH, WA ASH-HADU ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH!'

Rufe bakinta ke da wuya, sai wutar ta shanye ta gaba daya, ta zama wani dan tulin farar toka a kusa da baqin tokar Ifiritu Jurjanisu!

Ko da Sarki ya ga mutuwar 'yarsa tilo, sai ya suma ya fadi a kasa! Dukkan fada ta cika da makoki da kukan kade-kade har tsawon kwanaki bakwai!

Aka gina wata katafariyar qubba mai haske a kan tokar wannan budurwa ta sadaukarwa, ita kuma tokar Ifiritu aka watsa ta a iska domin la'ana!

Bayan wata guda Sarki yana kwance yana jinya, sai ya sami sauqi. Ya kirawo ni ya dube ni da hawaye a idanunsa ya ce:

'Ya kai wannan saurayi, mun kasance cikin aminci da jin dadi kafin zuwanka! Amma zuwanka ya zama sanadin mutuwar 'yata wadda ta fi mani maza dari, na rasa hakorana, bawana ya mutu! Ban zarge ka ba domin qaddarar Allah ce ta riga fata, amma ba zan iya jure ganin fuskarka a wannan birni ba! Maza ka fita daga qasata lafiya, kuma kada ka sake dawowa har abada!'

Na fito daga fadar ina kuka, na je gidan wanka na aske kaina, da gemuna da girata sumul, na sanya tufafin Kalandarawa na kama hanya!

Yayin da nake tafiya a cikin daji ina kuka ina tunanin dukkan irin masifun da suka same ni, sai na rera wannan qasida ta haquri ina cewa:

Hankalina ya tashi, amma jinqan Ubangijina yana tare da ni,

Ko da rundunonin masifu sun kewaye ni daga inda ban sani ba!

Zan yi haquri har sai shi kansa Haquri ya gaji da haqurina,

Zan dawwama a kan haquri har sai Ubangiji Ya cika mani qaddarata!

Zan zauna a kan haquri ba tare da yin kuka ko korafi ba,

Tamkar mutumin da aka zalunce shi kuma aka karya masa gwiwa!

Zan yi haquri tamkar mai tsananin qishirwa a tsakiyar hamada,

Wanda ke tattaka zafafan yashin hamada ba tare da ruwa ba!

Zan yi haquri har sai itacen madaci (sabara) ya shaida cewa,

Ina haquri a kan abin da ya fi kowanne daci daci a duniya!

Babu abin da ya fi daci a wurin mutane face itacen madaci ko haquri,

Amma yaudarar zamani ta fi wadannan biyun zafi da daci a gare ni!

Idan da duwatsu zasu dauki irin nauyin baqin cikin da nake dauke da shi,

To da duwatsun sun rushe sun zama qura a qasa saboda nauyi!

Wannan nauyi zai iya saita iska mai guguwa kuma ya kashe harshen wuta,

Kuma duk wanda ya ce duniya tana da dadi, to zai ga wata rana mai cike da zallar daci!

Na yi ta yawo a duniya har na iso Bagadaza a yau da daddare, na hadu da wadannan 'yan'uwa nawa guda biyu muka zo wannan fada! Wannan shi ne dalilin aske gashina da kuma tsiyayewar idona na dama ya ke wannan shugabata mai girma!'

Ko da Zubaida da kowa a falon suka ji wannan kyakkyawan labari mai ban al'ajabi da ban tausayi, sai suka cika da mamaki mara misali!

Zubaida ta ce da shi: 'Lallai labarinka abin mamaki ne! Ka shafa kanka ka tafi lafiya!'

Amma Kalandar na biyu ya ce: 'Na rantse da Allah ba zan taba tafiya ba har sai na ji labarin wannan Kalandar na uku da kuma yadda zata kaya da mu baki daya!'..."

A daidai wannan gaba, sai hasken alfijir ya fara ketowa a sararin samaniya, Shahrazad ta ga safiya ta yi, sai ta dakata da zancenta mai dadin sauraro ta yi shiru!

Dunyazad ta dube ta da matuqar sha'awa da shauqi ta ce: "Kai ya yayata! Lallai wannan labari ya cika da zakin kunne, da dadi, da cikar nishadi da ban al'ajabi mara misali!"

Shahrazad ta yi murmushi ta dube ta ta ce: "Ai wannan ba komai ba ne idan aka kwatanta shi da labarin da zan fada muku a dare mai zuwa, idan har Allah Ya raya ni kuma wannan babban Sarki ya qyale ni?"

Ko da Sarki Shahriyar ya ji wannan batu, sai ya ce a ransa: "Wallahi ba zan kashe ta a yau ba, sai na ji sauran wannan kyakkyawan labari mai ban mamaki!"

Wayewar gari ke da wuya, Sarki ya fita fada ya gudanar da al'amuran mulki yana bayar da umarni da hani har dare ya sake rufowa, shi kuwa babban Waziri ya koma gida fuskarsa cike da farin ciki da godiyar Allah da ya ga 'yarsa tana ci gaba da rayuwa cikin aminci!

(A nan muka kawo qarshen DARE NA GOMA SHA HUDU da kuma BABI NA GOMA SHA BAKWAI cif!)

====================================================================

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol