Free chapter · Read without an account
BABI NA GOMA SHA TAKWAS (18): CIGABAN HIKAYAR DAN DAKO DA MATAN BAGADAZA: LABARIN KALANDAR NA UKU
by Shuraihu Usman · DARE DUBU DA DAYA 1001 Mujalladi na Daya 1
====================================================================
DARE DUBU DA DAYA (ALF LAILA WA LAILA)
BABI NA GOMA SHA TAKWAS (18): CIGABAN HIKAYAR DAN DAKO DA MATAN BAGADAZA: LABARIN KALANDAR NA UKU
[DARE NA GOMA SHA HUDU]
Fassarar: Shuraihu Usman
====================================================================
A babi na goma sha bakwai idan mai karatu bai manta ba, mun tsaya a inda Gimbiya Sitrul Husn ta fafata gagarumin yaqin wutar sihiri da Ifiritu Jurjanisu har ta qone shi ya zama toka, ta mayar da Kalandar na biyu mutum daga biri amma idonsa na dama ya salwanta a wutar tsafi, sannan ita ma ta cika a matsayin shahidiya, Sarki ya kori Yarima ya zama Kalandar har ya iso fadar Zubaida a karshen DARE NA GOMA SHA BAKWAI. To yanzu bari mu ji labarin Kalandar na uku wato Yarima Ajib dan Sarki Khasib wanda ya fi dukkan labaran baya cika da zallar al'ajabi da ban mamaki a cikin wannan DARE NA GOMA SHA HUDU.
--- DARE NA GOMA SHA HUDU ---
Gari ya waye, Sarki Shahriyar ya fita fada ya gudanar da al'amuran mulki ba tare da ya ambaci batun kisan Shahrazad ba. Babban Waziri ya koma gida yana godiya ga Allah da ya ga 'yarsa tana ci gaba da rayuwa cikin aminci.
Da dare ya tsala a cikin wannan DARE NA GOMA SHA HUDU, Sarki Shahriyar ya shigo daki ya kwanta da Shahrazad. Bayan ya gama biyan bukatarsa, sai qanwarta Dunyazad ta tashi daga qasan shimfida ta ce:
"Ya yayata, idan baki fara barci ba, don girman Allah ki ba mu wannan sabon labari mai dadi na Kalandar na uku wato Yarima Ajib domin mu ji yadda ya hadu da Dutsen Qarfe da kuma dalilin da ya sa ya rasa idonsa na dama a cikin wannan dare!"
Shahrazad ta duba wajen Sarki Shahriyar cikin ladabi ta ce: "Zan ba da labarin idan har wannan babban Sarki mai daraja ya ba ni izini!" Sarki ya ce: "Fadi ina saurarenki!"
Nan take Shahrazad ta gyara zama ta ci gaba da ba da wannan kyakkyawan labari a cikin wannan DARE NA GOMA SHA HUDU kamar haka:
"Kalandar na uku ya matso gaba, ya sunkuyar da kansa cikin natsuwa ya kalli budurwa Zubaida da bakin da ke falon ya ce:
'Ki sani ya ke wannan shugabata mai daraja, cewa labarina ya bambanta da na wadannan 'yan'uwana guda biyu! Domin su qaddara ce ta afka musu ba tare da sun sani ba, amma ni kuwa da kaina na janyo wa kaina dukkan bala'i da nadamar da nake ciki!
Ni babban Sarki ne kuma dan babban Sarki mai suna Sarki KHASIB. Bayan rasuwar mahaifina na gaji karagar mulkinsa, na gudanar da mulki cikin adalci da karamci. Birnin masarautata yana a bakin wata katuwar gabar teku ne, kuma ina matuqar son yawon shaqatawa a cikin teku!
Ina da rundunar jiragen ruwa guda dari biyu da hamsin (250): hamsin na fatauci, hamsin na jin dadi, dari da hamsin kuma na yaqi domin kare daula.
Wata rana sai sha'awar shaqatawa a kan tsibiran teku ta kama ni. Na shirya jiragen ruwa guda goma (10) shake da guzurin wata guda, na shiga teku tare da tawagata domin tafiyar kwanaki ashirin.
Amma a daren kwananmu na ashirin, kwatsam sai wata mummunar guguwa ta taso mana a tsakiyar teku! Ruwa ya fara toroko, taguwar teku tana dukan jiragenmu da qarfi, hadari mai duhu ya rufe sararin samaniya! Muka rasa hanyarmu, jiragenmu suka riqa yawo a kan ruwa ba tare da sanin inda muke nufa ba har tsawon kwanaki ashirin da biyu.
A rana ta ashirin da uku, sai Madugun jirginmu ya ce wa wani matuqi: 'Hau saman kogon igiyar jirgi ka leqa ko zaka hango wani tudu!'
Matuqin ya hau sama can koli ya duba, sai ya kwala kira da babbar murya ya ce: 'Ya shugabana! Ina hango wani abu mai baqi a hannun dama kamar wani katon kifi a kan ruwa, a hannun hagu kuma ina hango wani haske mai sheqi a tsakiyar ruwa yana haskawa yana disashewa!'
Ko da Madugu ya ji wannan batu, sai ya yaga rigarsa, ya buga rawanninsa a qasa, ya riqa dukan fuskarsa yana cewa: 'Kashinmu ya bushe! Dukkanmu mun zama gawarwaki! Babu wanda zai kubuta daga cikinmu a yau!'
Muka cika da tsananin firgici, na kalli Madugu na ce: 'Me ya faru ya kai Madugu? Me ya sa kake wannan kuka?'
Madugu ya fashe da kuka ya ce: 'Ya shugabana dan Sarki! Ka sani fa tun a daren da guguwa ta buge mu mun riga mun bata hanya, igiyar ruwa ta kwashe mu ta tunkaro da mu wani gagarumin dutse mai suna DUTSEN MAGANADISO MAI JANYO QARFE (Jabal al-Maghnatis)!
Wannan dutse an yi shi ne da wani irin baqin dutse mai matuqar qarfin janyo dukkan wani abu da aka yi da qarfe! Da zarar jirgin ruwa ya matso kusa da shi, to dukkan kusoshin qarfe, da sarqoqi, da qarafafen da ke jikin jirgin zasu fice daga jikin itace da kansu su ruga a guje su manne a jikin dutsen! Jirgin kuma zai tarwatse gida-gida a tsakiyar ruwa kowa ya nutse!
Kuma a qololuwar wannan dutse, akwai wata katafariyar qubba ta tagulla mai launin rawaya, a saman qubbar kuma akwai wani mutum mai hawa a kan wani DOKIN TAGULLA, yana riqe da mashi na qarfe a hannunsa, a qirjinsa kuma akwai wani farantin darma mai dauke da dalasuman sihiri! Kuma babu mai halaka mutane face wannan mahayin doki, kuma sirrin dutsen ba zai taba karyewa ba har sai an kifar da wannan mahayi daga kan dokinsa ya fada cikin teku!'
Ko da Madugu ya gama wannan bayani, sai kuka ya kaure a cikin dukkan jiragenmu! Kowa ya tabbatar da cewa ajalinsa ya zo, muka shiga yi wa juna bankwana muna roqon gafarar Allah.
Washegari da safe, sai muka tsinci kanmu a gindin wannan katon Dutsen Qarfe!
Kafin mu ankara, sai muka ji: 'Qwas! Qwas! Qwas!' Dukkan kusoshin qarfafen da ke daure jikin jiragenmu suka fice da kansu tamkar tsuntsaye, suka ruga a guje suka manne a jikin dutsen baqin qarfen!
Nan take dukkan jiragenmu guda goma suka kakkarye suka zama alluna a kan ruwa! Dukkan mutanena da mayakana suka nutse a kasan teku suna kuka suna neman taimako, amma babu mai iya ceton wani!
Amma da ikon Allah Madaukaki, sai na sami wani katon allon itaciya na manne a kai. Igiyar ruwa ta riqa tunkuda ni har sai da ta jefar da ni a gindin wannan Dutsen Qarfe!
Na fito a kan yashi a galabaice, na duba sai na ga wasu matakala da aka sassaka a jikin dutsen suna hawa zuwa qololuwar dutsen.
Na ambaci sunan Allah, na shiga hawa wannan matakala a hankali da kyar har sai da na isa qololuwar dutsen. Na shiga cikin wannan qubba ta tagulla, na ga babu kowa a ciki. Na yi alwala na yi salla raka'a biyu domin godiya ga Allah da Ya fitar da ni da rai, sannan barci ya kwashe ni a qarqashin qubbar.
Ina cikin barci, sai na ji wata murya mai ban mamaki a mafarkina tana cewa da ni:
'Ya Ajibu dan Khasibu! Idan ka tashi daga barci, ka tona qasa a daidai inda kafafunka suke: zaka sami wata baka ta tagulla da kibiyoyi guda uku na dalma masu dauke da sunayen sirri! Ka dauki bakar ka harbi wannan mahayin doki da ke saman qubba har sau uku! Idan ka harbe shi zai fado cikin teku ya nutse, shi kuma dokin tagullar zai fadi a gabanka: maza ka binne dokin a cikin ramin da ka tono bakar!
Da zarar ka binne shi, ruwan teku zai fara tafasa yana hawa sama har sai ya yi daidai da qololuwar wannan dutse! Sannan wani dan qaramin jirgi zai bayyana a kan ruwa, wanda wani mutum na tagulla ke tuqawa yana riqe da matuqan dalma! Zai zo bakin dutsen ya tsaya: ka shiga cikin jirgin ya tafi da kai, amma KA KIYAYE KANKA KADA KA KUSKURA KA AMBACI SUNAN ALLAH KO DA SAU DAYA NE A CIKIN JIRGIN! Zai tuqa ka na tsawon kwanaki goma har ya kaika Tsibirin Aminci (Jaza'ir al-Aman) inda zaka sami damar komawa gida lafiya!'
Na zabura daga barci cike da murna da nishadi!
Na tona qasa a inda kafafuna suke, sai ga wannan baka ta tagulla da kibiyoyi uku na dalma sun bayyana! Na dauki bakar na zuba kibiya ta farko, na harbi wannan mahayin tagulla da ke saman qubba! Kibiya ta same shi a qirji, ya yi girgiza ya fado daga kan dokinsa ya kife a cikin zurfin teku ya nutse!
Dokin tagullar kuma ya fado daidai a gabana! Na dauke shi na binne shi a cikin ramin da na tono bakar na rufe da qasa sumul.
Rufe qasar ke da wuya, sai teku ya fara tafasa yana kumbura yana hawa sama tamkar dutse! Ruwan ya riqa hawa har sai da ya cika fadin dutsen ya yi daidai da qololuwarsa!
Jim kadan sai ga wani dan qaramin jirgi ya taho yana yawo a kan ruwa. A cikinsa akwai wani mutum da aka kera shi gaba daya da tagulla, yana riqe da wasu manyan matuqai guda biyu na dalma a hannunsa!
Jirgin ya tsaya a gabana. Na shiga ciki ba tare da na ce komai ba, ban ko motsa bakina ba.
Wannan mutum na tagulla ya fara tuqa jirgin da dukkan sauri yana ratsa taguwar ruwa. Muka yi tafiya a rana ta farko, ta biyu, ta uku, har zuwa rana ta goma cif ina zaune sumul ban ambaci komai ba!
A rana ta goma da yamma, sai na hangi wasu kyawawan tsibirai masu duwatsu da bishiyoyi a gabana, wato Tsibirin Aminci!
Ko da na ga cewa na kusa isa gaci kuma na kubuta daga mutuwa, sai matsananciyar murna ta kusan kashe ni! A cikin tsananin zumudi da farin ciki, sai na mance da gargadin da aka yi mani a mafarki!
Na daga hannayena sama na yi kururuwa da qarfi na ce: 'ALLAHU AKBAR! BISMILLAHI WA LA ILAHA ILLALLAH!'
Rufe bakina ke da wuya, sai wannan jirgi na tagulla ya girgiza ya kife gaba daya! Ya jefa ni a cikin ruwan teku, shi kuma ya nutse zuwa kasan ruwa ya bace bat!
Na tsinci kaina a tsakiyar ruwa ina iyo da dukkan qarfina! Na yi ta iyo har dare ya yi, kafafuna da kafaduna suka gaji suka kafe, na tabbatar da cewa ajalina ya zo! Amma a daidai lokacin da zan nutse, sai wata katuwar taguwar ruwa ta zo ta dauke ni ta jefar da ni a kan wani busashen tudu!
Na fadi a kasa a sume har sai da safiya ta waye. Da rana ta fito na tashi na wanke tufafina na shanya a rana suka bushe, sannan na shiga dube-dube a kan tsibirin.
Na ga cewa wannan wuri wani dan qaramin tsibiri ne wanda ruwa ya kewaye shi ta ko'ina. Na ce a raina: 'Duk lokacin da na kubuta daga wani bala'i, sai na fada wani wanda ya fi shi muni!'
Ina cikin wannan baqin ciki da kuka, kwatsam sai na hango wani babban jirgin ruwa yana tunkaro tsibirin!
Saboda tsoro, sai na ruga a guje na hau kan wata katuwar bishiya na boye a cikin rassanta da ganyayyaki ina leqen abin da zai faru.
Jirgin ya tsaya a gabar tsibirin. Sai ga wasu manyan bayi bakake guda goma (10) suka sauko daga jirgin, kowannensu yana dauke da fartanya da kwando na qarfe.
Suka nufi tsakiyar tsibirin, suka shiga tona qasa da fartanya har sai da suka tono wani katon marfin qarfe mai siffar dutsen nika! Suka daga marfin qarfen, sai ga wani matakala na karkashin qasa ya bayyana!
Bayan haka, sai bayin nan suka riqa komawa jirgi suna kwashe kaya suna saukarwa a cikin wannan rami: suka kwashe kwanonin abinci, da buhunan gari, da zuma, da man shanu, da kofuna, da tufafin alfarma, da shimfidu na alharini, da madubai, da fitilu—wato dukkan kayan da ake bukata domin zama a katafaren gida!
Bayan sun gama kwashe kayan, sai suka sake komawa jirgin. A wannan karon sai suka fito tare da wani tsoho tukuf mai matuqar tsufa, wanda zamani ya kakkabe shi babu abin da ya rage na jikinsa face kashi da fata, tamkar yadda mawaqi ya kwatanta shi yana cewa:
Zamani ya sanya ni rawar jiki—kash yaya girman wannan cikas yake!
Yayin da shi kansa Zamani ke taku da cikakken qarfi da izza!
A can baya na kasance ina tafiya ba tare da na ji gajiyawa ba,
Amma a yau ina jin gajiyawa ko da ban taka ko taku daya ba!
Wannan tsoho yana riqe da hannun wani kyakkyawan saurayi matashi dan kimanin shekara goma sha biyar (15) a duniya!
Wannan saurayi ya kasance mai tsananin kyau da cikar zati wanda ba a taba ganin kamarsa ba: fuskarsa tana haske tamkar furen wardi, idanuwansa tamkar na barewa, takunsa cike da kasaita da kwarjini! Kamar yadda mawaqi ya rera a kansa yana cewa:
An kawo Kyau domin a gwada shi da siffarsa,
Amma sai Kyau ya sunkuyar da kansa cikin kunya da baqin ciki!
Suka ce: 'Ya kai Kyau, shin ka taba ganin kamarsa a duniya?'
Sai Kyau ya yi ihu ya ce: 'Kamarsa? A'a, babu kamarsa a ko'ina!'
Suka sauka cikin ramin tare da tsohon da bayin, suka kwashe kusan sa'a guda a ciki.
Bayan haka, sai tsohon da bayin suka fito su kadai ba tare da wannan kyakkyawan yaro ba!
Tsohon yana kuka da share hawaye, suka mayar da marfin qarfen suka rufe, suka mayar da qasa suka binne shi sumul kamar yadda yake a da, sannan suka koma cikin jirginsu suka tada shi suka kama hanya suka bace a cikin teku!
Ko da na ga jirginsu ya yi nisa, sai na sauko daga kan bishiya da sauri! Na nufi wurin da suka binne qasar, na shiga kakkabe qasar da hannuna da hakuri har sai da na gama kwashe ta tas!
Na daga marfin katakon, na ga wannan matakala na dutse. Na shiga sauka a hankali har na isa kasan benen.
Na tura qofa na shiga, sai na tsinci kaina a cikin wani katafaren daki na alfarma da aka qawata da shimfidun alharini da matashin kai masu qamshin fure!
A kan wata babbar kujera ta alfarma, sai na tarar da wannan kyakkyawan yaro zaune shi kadai, yana riqe da mafici a hannunsa, ga furanni masu qamshi a gabansa!
Ko da yaron ya hango ni na shigo, sai ya tsorata matuqa, fuskarsa ta zama fari fat, ya zaro wata 'yar wuka yana rawar dari!
Na matsa kusa da shi cikin nutsuwa na ce: 'Kada ka ji tsoro ya kai wannan kyakkyawan matashi! Ni ba aljani ba ne, ni mutum ne kuma dan Sarki tamkar kai! Qaddara ce ta kawo ni domin na taya ka zama na debe maka kewa a cikin wannan kebewa! Gaya mani wane ne kai kuma me ya sa kake zaune a qarqashin qasa haka?'
Ko da yaron ya tabbatar da cewa ni mutum ne ba aljani ba, sai hankalinsa ya kwanta, kyakkyawar fuskarsa ta dawo da fara'a!
Ya dube ni ya ce: 'Ya dan'uwana, labarina abin mamaki ne kwarai: Mahaifina wani babban attajiri ne mai sayar da lu'u-lu'u da duwatsu masu daraja, amma ya dade bai sami haihuwa ba har ya tsufa. Wata rana ya yi mafarki cewa zai sami da wanda ba zai yi tsawon rai ba. Bayan an haife ni, sai mahaifina ya tara dukkan manyan masana ilimin taurari da na lissafi da masu duba domin su duba makomata.
Masana taurarin suka duba suka ce masa: Wannan da naka zai rayu har zuwa shekara goma sha biyar (15) a duniya! Amma a cikin shekararsa ta goma sha biyar akwai wani babban hadarin mutuwa da ke jiransa: Ka sani a cikin Tekun Hadari akwai wani Dutsen Qarfe wanda a samansa akwai wani mahayi a kan Dokin Tagulla! Kwanaki hamsin (ko arba'in) bayan faduwar wannan mahayi daga kan dokinsa, to danka zai mutu! Kuma wanda zai kashe shi shi ne mutumin da ya harbi wannan mahayin tagulla ya kifar da shi, wato wani babban Yarima mai suna AJIBU DAN SARKI KHASIBU!'
Ko da na ji sunana da na mahaifina ya fito daga bakin wannan yaro, sai gabana ya yanke ya fadi! Jikina ya dauki rawa mara misali! Na ce a raina: 'Subhanallah! Ashe ni ne aka qaddara zan kashe wannan kyakkyawan yaro marar laifi?'
Amma na boye sirrina ban fada masa ko ni wanene ba!
Na rungume shi a qirjina ina kuka na ce da shi: 'Ya dan'uwana, ka kwantar da hankalinka! Na rantse da Allah ba zan taba barin wani abu ya cutar da kai ba! Zan zama mai tsaronka da hidimarka a cikin wannan daki har sai kwanakin nan sun cika ka fita lafiya ka koma wajen mahaifinka!'
Yaron ya yi murna qwarai, muka rungume juna muka fara zama tare cikin aminci da tsananin soyayya!..."
A daidai wannan gaba, sai hasken alfijir ya fara ketowa a sararin samaniya, Shahrazad ta ga safiya ta yi, sai ta dakata da zancenta mai dadin sauraro ta yi shiru!
Dunyazad ta dube ta da matuqar sha'awa da shauqi ta ce: "Kai ya yayata! Lallai wannan labari ya cika da zakin kunne, da dadi, da cikar nishadi da ban al'ajabi mara misali!"
Shahrazad ta yi murmushi ta dube ta ta ce: "Ai wannan ba komai ba ne idan aka kwatanta shi da labarin da zan fada muku a dare mai zuwa, idan har Allah Ya raya ni kuma wannan babban Sarki ya qyale ni?"
Ko da Sarki Shahriyar ya ji wannan batu, sai ya ce a ransa: "Wallahi ba zan kashe ta a yau ba, sai na ji sauran wannan kyakkyawan labari mai ban mamaki!"
Wayewar gari ke da wuya, Sarki ya fita fada ya gudanar da al'amuran mulki yana bayar da umarni da hani har dare ya sake rufowa, shi kuwa babban Waziri ya koma gida fuskarsa cike da farin ciki da godiyar Allah da ya ga 'yarsa tana ci gaba da rayuwa cikin aminci!
(A nan muka kawo qarshen BABI NA GOMA SHA TAKWAS cif!)
====================================================================