Free chapter · Read without an account
A SILENT RIVALRY
by Hau—waah · ZAYD ARMAAN
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER 137*
*THE SILENT RIVALRY*
*JIDDAAH BARKUM*
———-
Ummie ta ɗan kalli Suhaila, sannan ta ce, "Toh, ki tura mata mana. Me ya sa kike gaya min?" Suhaila ta yi ɗan murmushi, ta ɗauki wayarta tana kallon screen ɗin. "I don't know, Ummie. Abun ne… it sounds weird to me." Ummie ta ɗan ɗaga gira, amma ba ta ƙara tambayarta komai ba. Ta maida hankalinta kan talabijin, ta ci gaba da kallon shirin da ake yi a Sunna TV, ta bar Suhaila da tunaninta. Suhaila kuwa ta ci gaba da kallon wayar, tana tunanin yadda Seeyama ta kira ta da wannan tambayar. Daga karshe kawai tayi mata text message snn ta koma tayi kwanciyarta.
Bayan sallar Magariba ne Zayd ya dawo gida. Ya shigo cikin gidan a hankali, a bayyane yake cewa gajiya ta yi masa yawa. Tun da safe yake cikin haɗa-hadar business, meeting da wasu abubuwan da suka shafi tafiyarsu, har ya kai lokacin da jikinsa ya fara neman hutu. Kai tsaye part ɗin Raihana ya nufa. Da ya shiga parlour, sai ya tarar da ita zaune a kan kujera tana kallon wani cooking competition a talabijin. Ta mayar da hankali kan yadda masu gasar suke shirya abincinsu, sai ta ji motsin buɗe ƙofa. Ta waigo da sauri, sai ta hango Zayd a tsaye yana kallonta. Fuskarsa ta nuna irin gajiyar da yake ciki, har ma da yadda ya ɗan jingina da ƙofar. Raihana ta miƙe da sauri ta ƙarasa wajensa. Ta tsaya gabansa tana kallonsa cikin damuwa. "Lafiya?" ta tambaya, gabanta na faɗuwa. Zayd ya ɗan langwabe kansa, sannan ya furta cikin murya mai nuna gajiya, "Nagajiiii… and I missed my beautiful wife so much." Raihana ta sauke ajiyar zuciya. "Ai da na ga ka tsaya a haka, gabana ya faɗi. Na ɗauka wani abu ne." Zayd ya ɗan yi murmushi. "No, habibti. I'm just exhausted." Ta karbi jakar hannunsa snn ta kalleshi. "Now go and freshen up. Ka yi wanka, ka huta, sannan ka dawo ka ci abinci." Zayd ya girgiza kansa a hankali. "A'a, ni kaɗai zan je wai nufinki?" Raihana ta turo baki. "Ehh mana." Zayd ya ɗan ɗaga gira yana kallonta. "Come and help me, habibti. Kina ganin na gaji ko?" Raihana ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, sannan ta buɗe su tana kallonsa. "Are you a baby?" Zayd ya gyada kai ba tare da ko ɗan jinkiri ba. "Yes. Have you forgotten you breastfed me last night?" Da sauri Raihana ta juya masa baya, tana turo baki. Ya yi dariya a hankali, duk da gajiyar da ke tattare da shi. "What? Na dai tuna miki ne." Ta girgiza kai, tana ƙoƙarin ɓoye murmushin da ya so bayyana a fuskarta. Zayd ya matso kusa da ita, yana jingina kansa a hankali. "Please, habibti. Just help your tired husband a little." Ta make kafada alamun A'aa. Ya sake kallonta da idanunsa cike da roƙo. "Please, habibti." Raihana ba ta ce komai ba. Ta tsaya tana kallonsa na wasu seconds, kafin daga bisani ta sauke ajiyar zuciya. Zayd ya miƙa mata hannu, ta karɓa, suka nufi ɗakin tare. Da suka shiga, Raihana ta fara shirya masa kayan wanka. Ta haɗa ruwan ɗumi, ta tabbatar da komai yana nan, sannan ta ɗauko towel ta ajiye a gefe. Bayan ta gama, sai ta juya tana shirin fita daga bathroom ɗin domin ta ba shi wuri ya yi wanka. Amma kafin ta kai ƙofa, sai ga shi ya shigo. Raihana ta ja gefe tana kallonsa. "Toh, ga shi nan. A yi wanka lafiya." Zayd ya yi murmushi, sannan ya matso kusa da ita ya riƙo hannunta. A hankali ya ɗora hannunsa a kugunta, yana kallonta cikin shagwaɓa. "Ai ba ki gama ba." Raihana ta ɗan ɗaga gira. "Ban gama me ba kuma?" "Bath me, my Raii." Ta zaro ido tana kallonsa. "Wai ni ce zan maka wanka? How?" Zayd ya ɗan karkatar da kansa, yana nuna alamun gajiya. "Yes, you. Kina ganin mijinki ya dawo gida tired like this, har yanzu kina son ki bar shi ya yi komai da kansa?" Raihana ta girgiza kai, tana ƙoƙarin kada ta yi dariya. "You are something else wallahi." Ya ɗan matso kusa da ita. "Something else ɗin nan kuma mijinki ne." Ta turo baki. "Toh, amma fa ka san ni ba nurse ba ce." Zayd ya yi dariya a hankali. "I don't need a nurse. I need my wife." Raihana ta kalle shi na ɗan lokaci, sannan ta sauke ajiyar zuciya. "Kai dai ka iya amfani da gajiya wajen samun abin da kake so." "Because it works," ya amsa da sauri. Raihana ta sake kallonsa, ta kasa ɓoye murmushinta. "Okay, Mr. Shagwaɓa. Amma ka daina complaining." Zayd ya ɗaga hannuwansa kamar wanda ya miƙa wuya. "I promise." Raihana ta yi murmushi, sannan ta ce, "Oya, let's go." Zayd ya saki kugunta, yana tsammanin za ta tsaya ta taimaka masa. Amma kafin ya fahimci abin da take shirin yi, sai ta juya da sauri ta fice daga bathroom ɗin sannan ta rufo masa ƙofar daga waje. Zayd ya tsaya cak yana kallon ƙofar. Ya yi shiru na wasu seconds, sannan ya girgiza kai yana murmushi. "Habibtiii!" ya kira da ƙarfi kaɗan. "So this is what you mean by let's go?" Daga waje kuwa, Raihana ta fashe da dariya. "Yes! You can do it yourself, baby!" Zayd ya yi dariya yana girgiza kai. Raihana ta koma dining area ta shirya masa abinci. Ta tabbatar da komai ya yi kyau, ta sake gyara wajen, tana jiran fitowarsa. Bayan wasu mintuna, Zayd ya fito sanye da coffee-coloured jallabiya. Kamshi yake yi sosai, ya kuma gyara gashin kansa duk da ba mai yawa ba ne, da mayukan da yake amfani da su. Ya yi kyau sosai, looking effortlessly handsome. Wayarsa na hannunsa yayin da yake saukowa daga matakalar. Da ya iso ƙasan gidan, sai ya hango Raihana a dining area. Ya kalli yadda ta tsara masa abincin, murmushi ya bayyana a fuskarsa. Ya ƙarasa wajenta a hankali. Tana ganinsa sai ta fara ja masa kujera. "Toh, have a seat," ta faɗa cikin nutsuwa tana kallonsa. Zayd ya zauna, ita kuma ta matso da plate ɗin abincin da ta yi masa service, sannan ta ajiye masa glass cup ɗin fresh grape juice. Ya kalli abincin, sannan ya ɗago ya kalleta. Tana tsaye a gefensa, ta haɗe hannayenta a kirjinta. "Have you eaten?" ya tambaya. Ta gyada kai a hankali, alamun eh. Zayd ya jinjina kai, sannan ya ɗauki glass cup ɗin ya shanye juice ɗin gaba ɗaya. Daga nan sai ya miƙe. Raihana ta matso kusa da shi. "Ya ka tashi kuma?" Zayd bai amsa nan take ba. Ya ƙaraso gare ta, ya kama hannunta, yana kallonta. Sai kuma ya janyota a hankali ya haɗa ta da jikinsa. Hannunsa ɗaya ya sauka a kugunta, ita kuma ta ɗago idanunta ta kalleshi. Sun yi wasu seconds a haka, suna kallon juna cikin shiru. Daga bisani Raihana ta fara kau da idanunta, zuciyarta na bugawa a hankali. Zayd ya ɗago haɓarta da ɗayan hannunsa domin ta sake kallonsa. Ta ɗago idanunta a hankali, suka haɗu da nasa. "I'm full," ya faɗa cikin murmushi. Raihana ta tura baki, sannan ta kawar da kanta gefe. "Because you ate outside? I cooked for you, amma ka ci abinci a wajen aiki?" Zayd ya langwabe kansa kaɗan. "But I'm hungry, wife." Ta murguda baki. "Me ya sa ba ka aiko Sameer ya zo gida ya karɓa ba?" Zayd ya kai hannu ya kama kunnensa ɗaya, yana kallonta cikin neman afuwa. "I am very sorry, madam. Next time, kin ji?" Raihana ta ɗan jinjina kai, amma ba ta ce komai ba. Zayd ya sauke hannunsa, sannan ya ɗan gyara tsayuwarsa. "By the way, habibti, akwai wani abu da nake so in gaya miki." Ta ɗago ta kalleshi. "What is it?" "Zan koma part ɗin Seeyama yanzu. Na gama kwana biyuna a nan, saura nata." Raihana ta tsaya cak. A hankali ta kalleshi, kamar tana ƙoƙarin tabbatar da abin da ta ji. Gabanta ya fara faɗuwa, don ita shaffff, ta manta gaba ɗaya cewa akwai tsarin rabon kwanaki da suke bi. "Oh…" kawai ta iya furtawa. Zayd ya lura da sauyin fuskarta. Ya ɗan matse hannunta cikin nasa. "You know I have to, habibti. It's her turn." Raihana ta sauke idanunta ƙasa, ta jinjina kai a hankali. A zahiri ta fahimci hakan, amma zuciyarta ba ta so ta tuna cewa bayan kwana biyu tare da shi, dole ne ta sake barinsa ya koma wani ɓangaren gidan. Sai ta dago hannunta ta kama nasa dake kugunta ta janye a hankali, sannan ta ɗan matsa baya, ta yi wani ɗa step ta na ba shi sarari. Ta ɗan haɗiye yawu, sannan cikin nutsuwa ta ce, "You can go. Goodnight." Zayd ya tsaya yana kallonta. Bai yi tsammanin za ta amsa masa haka ba. Ya ɗan yi shiru, sannan ya matso kusa da ita a hankali. Da ya kai hannu zai riƙe nata, sai ta mayar da hannayenta bayanta. Ya kalleta na wasu seconds, sannan ya juya kansa gefe, yana tunanin abin da ya kamata ya ce. Bayan ɗan lokaci sai ya dawo da kallonsa kanta. "Are you angry?" ya tambaya cikin sanyin murya. Raihana ba ta amsa nan take ba. Ta kau da kanta gefe, tana ƙoƙarin nuna kamar babu abin da ya dame ta. Zayd kuwa ya ci gaba da kallonta, yana jiran amsarta. Sannan ta ce cikin nutsuwa, "Angry? No. Why would I be angry?" Zayd ya ɗan ɗaga gira. "Really?" Ta jinjina kai. "Yes. I understand. It's your turn to be with her. You can go." Zayd ya yi shiru yana kallonta. Ya san wannan calmness ɗin nata ba wai komai ba ne. Yadda ta ƙi kallonsa da yadda ta ɓoye hannayenta a bayanta sun riga sun ba shi amsar da yake nema. "Habibti..." "Hmm?" "Look at me." Ta juya masa fuska kaɗan, amma idanunta suna wani gefe. Zayd ya ɗan sauke ajiyar zuciya, sannan ya miƙa hannu ya kama nata. Ta yi ƙoƙarin janye hannun, amma ya riƙe shi a hankali. "Come on, My Raii. Don't do this." "I said I understand. You can go." Ta fada wata wutar kishi na cin zuciyarta. Zayd ya kalleta na wasu seconds, sannan ya girgiza kai. "I'm not leaving you like this." Ta yi masa shiru. "I'll stay until I make sure you've settled down and gone to bed. Come." Bai jira ta ba shi amsa ba. Ya fara tafiya a hankali yana riƙe da hannunta, ita kuma tana binsa ba tare da ta ce komai ba. Ya kai ta har bedroom ɗinsa, sannan ya saki hannunta ya nufi wardrobe. Ya buɗe ya ɗauko mata sleeping dress ɗinta, ya dawo inda take tsaye. "Here, habibti." Amma da ya yi ƙoƙarin taimaka mata ta saka, sai ta ƙwace kayan daga hannunsa. "Ni ba zan saka ba." Zayd ya ɗan langwabe kai. "But why?" Ta yi shiru, tana kallon kayan da ke hannunta. Zayd ya sake kallonta, yana jiran ta yi bayani. Sai dai kafin ta yi tunanin abin da za ta ce, sai bakinta ya furta, "Idan na saka, wa zai kalle ni ya yi min admiring tonight?" Zayd ya tsaya cak. Ya kalleta na wasu seconds, sannan a hankali murmushi ya fara bayyana a fuskarsa. "Ohhh…" Raihana ma sai a lokacin ta fahimci abin da ta faɗa. Ta yi saurin juya masa baya, tana jin kamar kawai kasa ta tsage ta shige. Zayd ya matso kaɗan. "So that's the problem?" "There's no problem." Ta amsa amma still taqi kallonsa. "Really? Because I just heard something very interesting." Ya yi dariya a hankali. "Habibti, you want me to admire you tonight?" Ba ta amsa ba. Maimakon haka sai ta juya da sauri ta nufi gado, ta shiga cikin duvet ta rufe har kanta. Zayd ya tsaya yana kallonta, murmushinsa ya ƙara faɗaɗa. "My Raiii?" Tayi masa banza. "My beautiful wife?" Ya zauna a gefen gadon, ya ɗan ja duvet ɗin a hankali. "At least let me see your face." Ta ƙara jan duvet ɗin ta rufe kanta sosai. Zayd ya girgiza kai yana murmushi. "Yaa Allah, …" Sai ya tsaya kawai yana kallon yadda ta lulluɓe kanta da duvet. Ya gyara mata gefen bargon a hankali, sannan ya yi mata addu'a. Bayan ya gama, sai ya ɗan sunkuya ya yi mata peck a goshinta. "Goodnight, baby. I love you." Raihana ba ta fito daga cikin duvet ɗin ba, kuma bata nuna ma taji abinda yakeyi ba. Zayd ya sake murmushi, sannan ya miƙe. Ya kashe fitilar ɗakin, ya bar ta cikin duhun da hasken bedside lamp kaɗai ya rage, kafin ya fice ya ja ƙofar a hankali. Seeyama ta dade tana jiran dawowar Zayd. Tun bayan kiran da ta yi wa Suhaila, ta tabbatar da cewa an gama gyara sashenta yadda ya kamata. Ita da Rabi sun share falon, sun gyara dining area, sannan suka shirya abincin da za ta tarbe shi da shi. Da misalin ƙarfe tara na dare, Seeyama tana zaune a falon cikin wata doguwar riga mai kyau, ta ɗaura dankwalin rigar a kanta. Duk da cewa tana ƙoƙarin wayarta ta dauke mata hankali daga jiran sa amma still, hankalinta yana kan agogo. Ta kalli Rabi da ke zaune a gefenta. "Rabi, kin tabbatar komai ya yi kyau?" Rabi ta ɗan yi murmushi. "Anty, kin tambaye ni wannan tambayar sau uku kenan. Komai ya yi kyau. Abincin ma yana nan a dining, in Shaa Allah komai zaiyi masa." Seeyama ta gyara zamanta. "I just want everything to be perfect. I don't want him to feel like I didn't prepare for his coming." "Ki kwantar da hankalinki komai yayi." Seeyama ta yi murmushi kaɗan. "Allah ya sa." A daidai lokacin ne suka ji motsin bude kofa. Seeyama ta ɗago kai da sauri, ta kalli ƙofar falon. Rabi ma ta lura da sauyin fuskarta. "Looks like he's here," Seeyama ta faɗa. Da sauri Rabi ta ruga ta gudu dakinta. Sai Seeyama ma ta miƙe tsaye, ta gyara rigarta sannan ta nufi ƙofar falon. Ba da daɗewa ba, aka buɗe ƙofar, Zayd ya shigo. Yana sanye da wata doguwar jallabiya, wayarsa a hannunsa, fuskarsa nan very calm and composed. Da ya ɗago kai ya gan ta tsaye a gabansa, sai ya ɗan tsaya. "Assalamu alaikum," ya faɗa cikin nutsuwa. "Wa alaikumus salam," Seeyama ta amsa, tana murmushi cikin ladabi. Zayd ya shigo sosai, ya saka wayarsa a aljihunsa. "You're still awake?" "Of course. I was waiting for you." Ya ɗan kalli falon, sannan ya dawo da kallonsa kanta. "You didn't have to wait up for me. You should have rested." Seeyama ta girgiza kai a hankali. "It's alright. I wanted to welcome you properly." Ya kalle ta na ɗan lokaci, sannan ya ce, "Thank you." Ta nuna masa hanyar zama. "Please, have a seat. You must be tired." Zayd ya zauna a kan kujera, ya jingina bayansa yana sauke numfashi. Seeyama ta zauna a kujerar da ke kusa da shi, tana ƙoƙarin kada ta nuna yawan farin cikin da take ji. "Would you like something to drink?" ta tambaya. "Water, please." Ta miƙe da kanta ta kawo masa ruwan. Bayan ya sha, sai ta tambaye shi ko yana jin yunwa. "I had something earlier, but I can eat a little." Fuskarta ta haska da murmushi. "I've prepared dinner for you." Zayd ya ɗago ya kalle ta. "You cooked?" Ta gyada kai. "Yes." Ya yi shiru na ɗan lokaci, kamar yana mamakin yadda ta yi ƙoƙarin shirya komai. Daga nan sai ya ce, "That's thoughtful of you. Thank you." "It's nothing. I just wanted you to feel welcome." Ta tashi ta nufi dining area, shi kuma ya bi ta a hankali. Da suka isa, ya ga an shirya teburin cikin tsari mai kyau. Ta ja masa kujera, ya zauna, ita kuma ta fara kawo masa abincin. Zayd ya kalli abincin, sannan ya kalleta. "Looks good." "Thank you." Ta zuba masa abin sha, sannan ta zauna a kujerar da ke gefensa. Kallonsa kawai take yana cin abincin a ranta tana girmama al'amarin ubangiji kan jarabawar da yayi mata akan soyayyar wnn bawan nasa. A wannan daren, Seeyama tana ƙoƙarin nuna masa cewa ta shirya masa wuri a rayuwarta, kuma tana son zaman aurensu ya kasance cikin kwanciyar hankali. Zayd kuwa yana lura da ƙoƙarinta, duk da cewa bai yi mata alkawarin komai fiye da abin da zai iya bayarwa ba. Bayan sun gama cin abinci, Seeyama ta tattara wasu plates din daga kan dining, sannan suka dawo falon tare da Zayd. Ita ta zauna a kan kujera one-seater yayin da Zayd ya zauna a kan three-seater. Zayd ya lura da littafin Fiqh da ke kan Centre table. Ya miƙa hannu ya ɗauke shi, yana buɗewa a hankali domin ya duba inda aka tsaya. Seeyama kuwa tana zaune cikin nutsuwa, hannayenta a haɗe a cinyarta. Bayan ya ɗan duba littafin, sai ya ɗago ya kalleta. "Come here." Ta ɗan yi shiru, ta kalle shi na wasu daƙiƙu kafin ta miƙe a hankali. Ta matsa zuwa inda yake, ta zauna a gefensa a kan kujerar da ya nuna mata. Zayd ya gyara zaman littafin a hannunsa, sannan ya kalle ta cikin nutsuwa. "Me da me kika koya a nan so far?" Seeyama ta gyara zamanta, ta ɗan yi tunani kafin ta fara amsawa. "Well, mun fara da abubuwan da suka shafi ibada da kuma tsarki. Mun yi bayani kan alwala, abubuwan da ke warware ta, da kuma yadda ake yin sallah yadda ya kamata. Rabi ta kuma fara koya min wasu daga cikin hukunce-hukuncen da suka shafi mace." Ta ɗan dakata, sannan ta ci gaba. "Har yanzu muna kan basics ne. I still have a lot to learn, but I'm trying to understand everything properly." Zayd ya kalleta yana sauraro, sannan ya ɗan gyada kai. "That's good. At least you're taking it seriously." Seeyama ta yi murmushi kaɗan. "I am. Kuma ina son in ci gaba da karatun. I don't want to rush it; I want to understand what I'm learning." Zayd ya sake kallon littafin, sannan ya ce cikin sanyin murya, "That's the right approach. Learning something is one thing, understanding it and practising it is another." Zayd ya ci gaba da yi mata bayani a kan Fiqh, yana nuna mata wuraren da take buƙatar ƙarin fahimta. Seeyama kuwa tana sauraronsa cikin nutsuwa, lokaci zuwa lokaci tana yi masa tambayoyi idan wani abu bai fito mata fili ba. Shi kuma yana amsa mata a hankali, wani lokacin har ya ba ta misalai domin ta fi ganewa. Sun shafe lokaci mai tsawo suna karatun tare, har agogo ya nuna ƙarfe 12:30 na dare. Seeyama ta fara hamma a hankali, tana ƙoƙarin danne gajiyar da ta fara bayyana a fuskarta. Ba karatun kaɗai ne ya gajiyar da ita ba. Tun da rana take kai-komo tana gyara gida, shirya abinci da kuma wasu ayyukan da ba ta saba yi da kanta ba. Jikinta gaba ɗaya yana mata ciwo, kuma tunda ta fara kokarin yin komai da kanta a gidaan ya zamana duk lokacin da ta zo kwanciya sai jikinta ya fada mata. Zayd ya lura da yadda take hamma. Ya rufe littafin, ya ajiye shi a kan stool din gefensa sannan ya kalleta da ɗan murmushi. "Are you sleepy?" Seeyama ta ɗan yi murmushi. "Yes." "Okay, mu je." Ya miƙe, ita ma ta tashi suka nufi bedroom ɗinsa tare. Da suka shiga ɗakin, Zayd ya lura da yadda komai yake cikin tsari. Kamshi mai daɗi ya cika ɗakin, kamar dai ba shine part din Seeyama na da ba. Zayd ya nufi gadonsa kai tsaye, ya zauna sannan ya kwanta a hankali. Seeyama kuwa ta tsaya a gefen gadon tana murɗe hannayenta cikin sanyin jiki. Ta kalleshi sannan ta tambaya cikin nutsuwa: "Babu wani abu da kake buƙata?" Zayd ya ɗan buɗe idanunsa, ya kalleta. Idanunsa sun ɗan lumshe saboda gajiya, amma har yanzu yana kallonta sarai. "Nothing. And thank you for everything. You really tried." Seeyama ta yi murmushi tana kallon ƙasa. "Toh… sai da safe." Seeyama ta juya da niyyar fita daga ɗakin. Amma kafin ta kai ƙofar, sai ya tashi zaune. "Seeyama." Ta tsaya, amma ba ta juyo ba. "Where are you going?" Seeyama ta lumshe idanunta na ɗan lokaci. Ta ji yadda hawaye ke son zubo mata, amma ta haɗiye su. Ta yi ƙoƙarin daidaita muryarta kafin ta amsa cikin sanyin murya mai ɗan rawa. "Zan je na kwanta ne…"