Free chapter 路 Read without an account
Chapter 1
馃挮BA TSANA BACE 馃挮
001..........
BISMILLAHIR RAHMANIN RAHEEM DA SUNAN ALLAH MADAUKAKIN SARKI MAI KOWA MAI KOMAI SARKIN SARAKUNA CIKIN IKONSA DA ISARSA DA IZZARKA NA FARA RUBUTA WANNAN LITTAFIN.
INA ROKON ALLAH YA BANI IKON RUBUTA ALKHARI YAKAREMUN ALQALAMINA DAGA RUBUTA SHARRI
Hernan Muhammad鉁嶏笍鉁嶏笍鉁嶏笍
Durkushe take gabansa,xama irin ta masu Bada haddar Al-qurani Mai Girma,kanta sunkuye,jikinta na kerma,dukawar da tayi Bai bani damar ganin fuskarta ba, sai goshinta fari Kal Wanda yake kwance da kwantattun gashi Baki wuluk ,karatu take Amma muryarta Bata fita bakajin abunda take fada sobada rawa da muryarta keyi Gaba daya jikinta rawa yake sosae a matukar razane take
Xaune yake xama irin ta mutane masu wadatar nutsuwa,sanye yake cikin farar shadda half jampha wacce tayi matukar yimasa kyau Bakar hula da agogo yake sanye dasu.Ba fari ne canba Kuma baya sahun bakake, fuskarsa na dauke da dara-daran idanuwa Wanda suke dauke da xara-xaran eye lashes idanuwansa sudana kyau da kaifin mashi Yana da hanci Amma ba Mai tsayi canba, tare da small black lips, fuskarsa na dauke da saje ba Mai yawa canba,fuskarsa daure Babu alamun murmushi ko rahma ko annuri Wanda take kan screen din wayarsa
Jin ta kasa mgn ta tsaye da karutun sai in-ena take yasa ya dago ya Kai mintina 2 Yana kallonta kafin a hankali cikin Wani irin deep sharp voice yace tashi Daga gabana tunda bakisan yadda ake nutsuwa a karanta Al-qurani ba tanajin ya Fadi haka ta fashe da kukan da take da kokarin riqesa Maida kanshi yayi ga abunda yake cikin rawar murya da muryar kuka tafara mgn "Yarh sayyeedii Dan Allah kayi hkr wlh na nutsu xan nutsu, Bai dago ba, tamkar ma badashi take ba koko Baya wajen ganin haka ta mike tana Mai cigaba da kukanta tamkar wacce aka aikowa da saqon mutuwa sai yanxu na Samu damar kallon fuskarta,duk da kuka take sosae Hakan Bai hana fitowar baiwar kyau da Allah yayi mata ba tana da inadanuwa matsakaita masu kyau da dogon hanci Wanda ake cewa pointed nose ga karama pink lips dinta, tana da cikakkiyar gira da gashin idon zara-zara.Masha Allah tana da kyau first class domin Koda ita tayi kanta iya Hakan xata tsaya
Cikin sauri wata dalibar taxo ta soma karatu cike da nustuwa da tajweedi tagama wata tasake xuwa haka daliban nasa guda 9 sukayi ta xuwa suna karatu Banda ita cikon ta goman wacce take gefe tana faman ruskar kuka sai lkcn ya Kuma dagowa ya Kai kallonsa gareta suka hada idanu yakuwa dauke Kai Bata bukatar a fadamata taxo yake nufi Dan haka ta tashi ta nufo wajenshi ta xauna shikuwa ya dago tare da sake kallonta har yanxu hawaye take sosai har idanuwanta sunyi ja abunka da farar fata ko namiki a jiki ya fada a dakile lkcn har ya dauko wata dorina da sauri ta mika hannayenta duka biyu nanfa yashiga tsula mata bulalar tana kuka mara sautin sai da Yamata 20 duk da dukan Yana shigarta sosae Amma batako dauke hannuntaba sanin dokarsa sai da ya kammala snn ya aje itakuwa lckn hannunta har ya fara jini ta gyara xama ta fara karatun Alqurani Mai cike da tajweedi dukda tana kuka baiwar qira'ar Al-qurani da sauti da Allah Yamata sai da ya bayya sai da ta kammala batare da Yamata gyara ko 1 ba snn ta dago ta kalleshi Jin yayi shiru yasa tace nagama sai da ya dauki mintina 2 kafin yace ni xan Miki tilawar "kacefa sai ranar asabar" na canxa" yafada Yana kallonta karatun ta fara a ranta tana ayyana rashin Imani irin nashi da muguntar tsiya lkcn da ta gama har an kada kararrawa alamar an tashi ganin yayi shiru yasa tace nagama tare da mikewa ta koma mazauninta Inda sauran Yan ajin suke ta zauna Dan yadda takejin xuciyarta xataiya shaqeshi saboda tsana da kiyayya
****** ******
****** ****** ****
Sai da kowa na makarantar wnnda yake dalibi yafice har ma da wasu dg cikin Malaman,kafin ya musu adduar tashi wato khaffaratul juluss snn suka fice shikuwa sai da ya shafe sama da mintina 10 kafin ya Mike cikin takun nutsuwa da Kamala ya fice ya nufin Wani makeken office wnnda aka rubuta "Head office" da sallama yashiga Abba ya amsa Yana murmushi shigowa yayi cikin nustuwa yaduqa tare da cewa Abba Ina wuni Abba ya amsa tare da Kara fadada murmushinsa da lfy lau ya sayyeeedi anfito murmushin gefen Baki yayi Wanda yayi matukar yimasa kyau yace Abba kaima ya sayyeeedi zakace? eh mn xauna Abba ya fada xama yayi ba tare da yace komai ba yww musawweer kutafi da iya gd nixan wuce shago Bata da lfy kasata Tasha magani dole xakamata kaji koh? "eh Abba" ni fah Abba gsky bazani gd dashi ba gwara nahau Dan sahu wlh karasani xaiyi ae, tafada tana tura Baki Gaba, sai yanxu ya kula da ita Amma Hakan baisa ya Kalli Inda take ba mikewa yayi Tare da cewa Abba sai ka shigo a hankali ya kalleta suka hada idanu takuwa murguda Masa Baki duk Abba Yana kallo "Baby xan barki dashi fah bakijin mgnta ko bakiji xafin jikinki ba kuje kingi yarinta Yar Albarka ya Kalli musawweer yace kar kayimata komai Dan Allah kaga Bata da lfy a hankali yace to Abba tare da ficewa MOTA ya shiga ya xauna snn tashigo gidan Baya batare da ya kalleta ba yace waye drivern ki? kwanciya tayi tare dace nifa bani da lfy Baice komai ba ya ta-da motar ita kuwa baccin nema ya dauketa sunyi tafiya Mai Dan nisa kafin ya tsaya dai虏 Wani babban pharmacy yafita ya karbo drugs ya dawo ya nufin gidan mintina 15 ne suka daukesa ya iso gdn,gdn be babba irin tsarin ginin masu arxiki Yana da babbab gate wnnda gateman ya walgale masu ya shigo da mortar tare da parking dinta a parkingspace sai da ya dauki 2 minutes kafin ya Kashe motar, sai da ya tsaya na kusan mintina 5 kafin a hankali ya Bude murfin motar baya, ganinta yayi ta takure tana baccinta ta daura hannunta a fuska wnnda yayi ja sakamakon dukan da yayi mata daxu sai yaji Babu Dadi ganin Hakan har cikin xuciyarsa kallonta yayi na tsawon seconds 5 kafin ya aje ledar maganin ya nufi cikin gdn
Direct dakinsa ya Bude Wani sanyayyar khamshi ya daki Hancinsa ya lumshe ido tare da shiga da sallama dakin duhu wacce Hakan dabiarsace sam Banason yawan haske a hankali ya wuce ya xaune kan gado tare da rike kansa Yana tuna abubuwa da dama mikewa yayi Yana salati tare da cire kayan gikinsa ya wuce toilet Ya dauki sama da mintina 30 kafin ya fito a hankali cikin takun kasaita irin tasa kunna hasken dakin yayi Masha Allahu daki ne Mai kyau Kuma Babu tarkashe ko hayaniya a ciki, katon gado ne Fari sul a tsakiyar dakin sai wardrobe shima fari Daga gefe sai mirror da bedside Suma duka fari Daga can wajen windows akwai study table tare da shoerag Daga dayan gefen gaban gadon akwai kamarin center carpet shima fari Mai laushi da cottons Wanda suke farere Suma, haka yake Yana son fari sosoe a rayuwarsa Yana kaunar colour din sai Kuma ya kasance bashi da kaxanta Yana iya maintaining.Xama yayi gaban mirron tare da fara shafa Mai Vaseline yake amphani dashi ya shafa roll-on da body spray kafin ya Mike ya nufi wardrobe dinsa ya dauke jallabiya fara Kal tare da hula ta ustaxai ya Kuma feshe jikinsa da turaruka snna ya fito Daga dakin da niyyar xuwa masjeed sai da ya fito yaga motar a Bude snn ya tuna da ita da kamar baxai jeba sai ya daure ya karasa Haryanxu tananan yadda ya barta Dan kauda Kai yayi kafin yadan taba kafarta Dake cikin Bakar safa yaji da zafi rasa yadda xai Yi yayi sai ka koma cikin gdn Direct main parlour ya wuce ganin Babu kowa ya wuce dakin kannen nasa Awateef ce tsaye gikin wardrobe sallama yayi ta amsa tare da cewa Sannu dazuwa Aboon Ina wuni lfy ya amsa daita kafin yace Ina ummee tana kitchen ta bashi amsa Okay xo mn ya fada tare da fita itama da mara Masa Baya bakin motar ya tsaya tare da cewa tasheta ya wucewarsa Haka tashiga tashinta
A hankali tashiga Bude ido har ta budesu duka kan Awateef wata irin sarawa kanta yayi Awateef ta riketa tana fadin Baby lfy ko Baki da lfy nagi jikinki zafi rau hawaye ta fara tare da kokarin sakkowa kamata Awateef tayi suka shiga ciki ta kwanta a gado tare da cewa rufeni Dan Allah Sanyi nake ji rufeta tayi tana cewa subhanallahi baby Maiya sameki hk tare da ficewa ta nufin wajen ummee Nan ta fada mata halin da Baby Ke ciki cikin rudewa ummee tashigo dakin tare da cewa Baby tana Bude bargon da Awayeef ta rufa mata "Ummmeeeeeeeee" tafada tana kokarin miqewa xaune tana Kuma kuka Haryanxu "Baby snnnu tashi kiyi wanka sai kici abinci kisha magani ko? Mai yasameki? a hankali tashe aboon ne yamun duka a makarantar Hade Rai ummee tayi tare da cewa Yi hkr kinji kidena kuka Maza Awateef hada mata ruwan wanka nikuma bara na Hado mata abinci barni dashi kinji xanyi maganinshi tafada tana mikar da baby a hankali tashiga bathroom din tana cigaba da kukanta Bata jimaba ta fito ta shirya cikin riga mara nauyi ta tada sallah Awayeef tana ganinta Amma tasan daurewa kawai takeyi tana idarwa Ummee tashigo riqe da Babban tray zama ummee tayi tare da kamota baby xo kici abinci kisha magani kinji tashi tayi a hankali tace Ummee nakoshi banajin yunwa kallonta Ummee tayi cikin Jin tausayi da lallashi tace sorry baby Kisha ko tea dinne sai Kisha magani kinji karba tayi badon taso ba Dan batason musu da ummee tashiga sha ta hada da maganin Amma me kafin tayi Rabi ta Bude toilet tafara amayar da komai dataci sosoe Ummee ranta ya Baci Kuma ta tausayawa baby taimaka mata sukayi ta kwanta Nan da Nan baccin yayi Gaba daita baccin wahala
Sai bayan sallar isha'i yashigo gidan tare da Abba, Babu kowa a parlour dan haka ya wuce dakin ummee shikuwa Abba side Dinsa ya nufa, da sallama yashiga zaune yasameta bakin gado tana goge hawaye Da sauri ya karasa tare da cewa ummee.... Bata kallesaba saima goge hawaye fuskarta datayi Ummee waye ya rasu? yakuma tambaya Babu Wanda ya mutu sai dai ni Ina gab da mutuwa Kuma sanadin bakin cikinka Da sauri ya kalleta cikin murya kamar Wanda xai Yi kuka yace Ummee Dan Allah kiyafemun na tuba wlh
kullum haka kake cewa na fada Maka ka fita harkar yarinyar na Amma bakaji kullum sai ka taba marainiyar Allah gatacan xata mutu tabar Maka Duniyar kayi yadda kakeso musawweer nima Kuma binta xanyi ta karashe tana kuka sosoe hankali tashe cikin rarrauniyar murya yace ummee Dan Allah kiyafemun kidena xubar da hawayenki akaina fushin Ubangiji xai sauka akaina dan Allah kiyi hkr" wlh nafita harka'rta daga yanxu Dan Allah ki ya femun na tuba wlh Dan Allah ummee" ya karshe Yana hawaye tare da kama kafafunta A hankali tace tashi ka tafi durkushewa ya Kuma Yi tare da cewa Ummee Dan Allah wlh.. tashi kaje na nayafe Maka a hankali yace ngd ummee Dan Allah kiyi hkr a hankali tace Aboon ita kadai nake Gani matsayin dangina jinina naji sanyin Kai Kuma baka da aiki sai kuntata'mata yarinya marainiya ka takura mata bakaga yadda taxama ba Yau kadai Wani irin duka ka mata Kuma Mai taimaka shiru yayi kafin yace kiyi hkr ummee na tuba tambayar ka Nayi Nan yashiga labarta mata yadda sukayi takuwa jamasa warning sosoe sannan ya tashi ya fice........
Asalinsu
Alhaji Abdulrazaq Haifaffan garin Adamawa ne, ya kasance Mai tarin ilimin addini Dana xamani kasancewar su haifuwar birni Kuma tasowar birni Yayi karatu har matsayin masters yana aiki da Adama modibbo university Yola, Yana da rufin asiri koma ince arxiki mutum ne Mai son jama'a Kuma na jama'a, Yana da tausayi mutunci da Kamala ya iya xama da mutane Dan bashi da abokin fada Yana da matarsa daya Aminatu wacce itama tana da nata ilimin Dan haka suke xaune cikin fahimtar juna da kaunar juna matsalarsu Daya Rashin haihuwa Wanda sunyi tsawon wajen shekaru 10 Amma Allah Bai kawo ba Aminatu taso ya Kara aure Amma yaki yadda haka dai ta hakura suka cigaba da Addu'ah cikin iKon Allah kuwa tasamu ciki Wanda Bata luraba har sai da ya Kai wata 5 murna wajen Abdulrazaq ba'a mgn har Allah yasa ta haifo yarta mace Mai kama da mijinta wato baffa( Abdulrazaq) aka Saka mata suna Ummu-khursum(Ummee) suke cemata ambu batayi shekara ba takuma samun Wani cikin Nan ma cikin iKon Allah ta haifo yarta mace aka Saka mata ummu-salma wacce suke cewa Salamatu ambu da salamatu sun taso cikin soyayyarh da kaunar juna Aminatu(inna) tare da Abdulrazaq(baffa) sun basu yarbiyya tare da ilimin dai dai gwargwado Ambu da salamatu suna son juna sosoe komai tare sukeyinsa salamatu tana bawa ambu Girma sosoe dukda ba sosoe ta girmetaba.
Ambu ta kammala secondary tana da shekaru 17 Kuma lokacin ne ta Yi saukar Al-qurani ita Kuma Salamatu tana SS2 Kuma tare sukayi saukar Dake ambu nada manema sai suka fara fitowa neman auren ta Kuma Babu laifi suna da kyau na daukar hankali abunka da jikin Fulani. baffa yaso yaki Dan burinsa tayi karatu Mai tsayi Amma inna ta nuna Mishi tayi auren inyaso sai tacigaba da Karatun idan mijin yayadda haka kuwa aka Yi aka tsaida mgn aurenta dawani babban malamai maisuna sheikh Nuraddeen Mu'az Yana da ilimin addini sosoe Kuma shima asalinsa Dan Adamawa ne, Bada Bata lkc ba akayi auren su da Ambu salamatu tayi kuka sosoe ta Kuma xama shiru duk da dama Bata da yawan mgn
Bayan 19 months ambu ta haifo danta kakkyawa Mai kama da ubansa aka Saka Masa sunan baban Sheikh Abdulmusawweer suna cemasa Aboon, Aboon nada shekara 1 sheikh yasamu gurbin karatu a kasar saudiyya Nan suka koma dashi da ambu da aboon, salamatu tayi kuka sosae hakama ambu da inna
Haka rayuwa tacigaba da tafiya Inda salamatu ta kammala karatunta na secondary sannan ta shiga jami'ar haddar Al-qurani bangaren Ambu ma Hakan take yayinda sheikh Ke Kara karatu tare da koyarwa itama tashiga Jami'ar tana Haddar Al-qurani,bangaren aboon ma haka yatashi da Alqurani tun Yana Dan kankani
Bayan shekaru biyar salamatu ta kammala Hadda Al-qurani tare da manya littafai na addini
Lokacin kuwa ambu itama taxama malama sosoe ta Kuma yi kyau ga larabci Daya xauna bakinta sai ka dauka balarabiya ce ga aboon shima haka, hakama sheikh yaxama babban malami Wanda ake ji dashi sosoe a saudiyyan ma, lkcn Ambu ta haifi Yara 2 Namiji Daya mace Daya Ameer da Haleema lkcn Kuma aka Saka auren salamatu dawani lecturer Dake nan university a Yola Ahmad yanason salamatu sosoe Ambu taso taxo bikin Amma Allah baiyiba dan Har kuka tayi sosoe, haka akayi auren batanan
Sai da suka shekara goma snn suka dawo gd Nigeria lckn ambu yaranta 6 Abdulmusawweer,Ameer,Haleema, Ladeefah,awateef sai auta Khaleed murna wajen Su inna da baffa harma da Salamatu ba'a mgn kwana sukayi suna Hira da Salamatu wacce har yanxu Bata Samu haihuwa ba Nan ambu take fada musu ambaro Aboon da Ameer a Sudan suna karutu
Basu dadeba Sheikh ya Bude wata katuwar makarantar ta yan'mata da samari da Yara da matan aure na haddar Al-qurani Mai Girma tare da littafan addini cikin Dan Kankani lkc makrnt ta daukaka sosoe
Ashekarar Kuma Allah Yayiwa Baffa rasuwa mutuwar ta girgixa su sosoe Dake mutuwar Dare yayi da safe Inna ma tabisa fadin irin tashin hankali da Salamatu da Ambu suka tsinci kansu Bata lokacine har Hakan yayi sanadiyyar barin cikin salamatu Wanda batama San dashi ba haka aka hada inna da baffa aka kaisu makoncinsu
Cikin iKon Allah salamatu ta Kara samun cikin takuma Haifa Amma Babu rai sai ana ukun Sanna ta haifo yarta mace aka Saka sunan ambu Ummu-khursum suke cemata "baby khursum" harma sunan baby ya ringayi sunan baby khursum shikenan ake cemata "baby" batayi wata biyu ba Salamatu ta rasu rasuwar farat Daya tashin hankali wajen Ambu ba'a mgn har sai da sheikh Yamata rubutun dangana, takuwa karbi baby bisa waseyyar salamatu komai na baby ya dawo hannun sheikh da ummee lckn Kuma Su musawweer suka dawo Daga Sudan musawweer Yakama makarantar mahaifinsa sakamakon baiwar ilimi da Allah ya Mishi yaxama ya haddace Alqurani daduka riwayoyi 10 tare littafan addini Masu dama shima Ameer yayi haddar Amma Bai Kai Aboon ba
Aboon yayi musabaqa dadama Kuma yasamu nasarar xuwa na Daya har sau 3 ana Duniya ata kasa da kasa Kuma sau 2 Yana xama gwarzo Nan da Nan sunansa ya mamaye Duniya har yaso shafe sunan mahaifinsa da kankanin shekarunsa Dan lokacin Bai wuce 18 ba
Bayan shekara Daya mahaifin Baby wato Ahmad yarasu sakamakon hatsarin MOTA dayayi
Sai baby taxama marainiya Gaba da Baya Amma bana rashin Wani abun amfani ba sai dai na iyaye ummee da Abba suna matukar sonta sosoe Kuma ko Mai takeso shi suke mata
Ta taso da son karatu Kuma kullun tanafada tanason xama kamar Abba da Aboon Kuma tana da kwakwalwa sosoe tana shekaru 15 ta Haddace Alqurani lkcn tana ss1 Amma Kuma tana dakuwa wajen aboon Amma duk da haka Bata gajiya gobema xata koma Dan tanason karatun shikuwa sai yayi ta yimata Shan kanshi da Jan aji idan kuwa kanason ganin bacin ran ummee to ka taba Baby Bata ragawa kowa akanta
Baby tana gama secondary ta fara musabaqa a cikin states da local governments take Kuma tayi Suna Dan baiwar murya da sautin qira'a da Allah yayi mata dakuma kyawun fuska Nan take masoya suka fara mata tururuwa Amma Bata sauraron kowa,domin kuwa tana da kyau Mai daukar hankali tana Kuma cigaba da karatu na addini domin boko Daga secondary Bata cigaba ba so tayima a turata Sudan ko saudiyya Amma ummee taqi, kwata-kwata basa jituwa da musawweer ko kadan domin shi Yana da isa da son Mulki ita Kuma batason kowa yashiga harkar kowa Amma shi sam yafison Yayita jibgarta ita kuwa sai dai tayi kuka ko ta fadawa ummee da Abba Dan ko mgn bataiya mayar Masa Dan haka take Bata da hayaniya
Duk yaran gidan guda 7 suna da ilimi sosoe Haleema tayi aure tana xaune a Abuja Inda lateefah ma tayi aure tana xaune Nan Adamawa sai Ameer Awateef da khaleed da Baby da Aboon duk suna gdn
*Cigaban Labari*
Fita yayi a sanyaye ransa Babu dadi Yana Jin Wani irin bakin cikin har ya nufin hanyar dakinsa sai ya juyo yashiga na su baby tana kwance kan sallaya da hijab jikinta maroon colour alamar sallah ta idar idanuwanta rufe sai da ya karewa dakin kallo kamar dai yadda dakinsa yake sai dai su dakinsu pink and purple ne Kuma wardrobe biyu ne sai Carpet pink yatabe Baki,Jin khamsin turarensa ya tabbatar mata Yana dakin Amma Bata motsa ba Dan Bata taba Jin tsanarsa irin ta Yau ba
Awateef ce tafito Daga toilet ganinshi tsaye yasa tace Aboon ni kake nema lumshe idanuwa yayi tare da budewa snn yace tasha magani? eh ummee ta Bata Amma ta amayar okay jeki MOTA akwai wata Leda ki dakkomun da toh ta amsa tare da ficewa shi Kuma ya ida shigowa dakin keeee shine abunda yace ta Bude idanunta dasukayi mata nauyi batare da ta kallesa ba yacigaba da cewa Keh Baki da buri sai hada ni da mahaifana koh? Shiru tayi dama Kuma yasan ba mgn xatayi ba ya Mike tare da tabe Baki baxan Dena dukanki ba muddin baxa kiyi hankali ba ba snn Kuma ga magani Nan Kisha Dan wlh gobe idan bakixo hmmm yafada Yana kada Kai tare da ficewa kuka tafashe dashi marar sauri a ranta tana cewa menayi Masa haka ya tsaneni, ahaka Awateef ta shigo ta Bata maganin Tasha tayi Shirin bacci tayi addu'ah ta kwanta tare da kunna kira Al-qurani na suratul Baqara
Washe gari tun 5:30 ta farka tayi duk abubuwan datake Yi kasancewar taji sauki sai da Rana ta fito snn ta mike ta fara shiri Doguwar rigace nevy Blue sai hijab har kasa shima nevy blue din Babu komai a fuskarta Amma tayi matukar kyau daukar tote back dinta tayi shima nevy blue sai plat shoe Mai kyau shima nevy blue ta fito Daga dakin Abba na xaune main parlour Yana waya sai Aboon da Ameer Dake xaune gefen kafafunsa Sallama tayi da sanyayyiyar muryarta tare da xama Daidai Nan Abba ya gama wayar Abba Ina kwana ta fada cikin sanyin murya Lfy lau baby y jikin? Alhamdulillah Abba mkrnt xaki keda Baki Jin Dadi? Naji sauki Abba Alhamdulillah ki dai bari Yau ba juma'a ba badawuri xa'a tashiba kasancewar ranar juma'a karfe 12 ake tashin da toh ta amsa snn tace Yah Ameer Ina kwana Baby kin tashin lfy y jikin Alhamdulillah,Allah ya Kara sauki Ameen tace a hankali Tasaci kallonsa Wani wajen yake kallo a xahiri Amma a badini su yake kallo da kasan idanu "Ina kwana" ta fada a sanyaye sai..... Hernarn Muhammad鉁嶏笍鉁嶏笍鉁嶏笍