Free chapter · Read without an account

18

by khadijah danasabe · FORBIDDEN LOVE

💫💫💫💫💫💫
         FORBIDDEN LOVE
                      💫💫💫💫💫💫


DijahAM(Oum Amani)


Assalamu alaikum🗣️🗣️

JAMA’A💃💃💃


Ina uwar gida, amarya, to duk ku matso muna d mgn, kufito kuyi booking set mai suna grooms set (5in1)natural remedies, with zero side effects acikin set dinan Muna da __

 1,DAHUWAR ZAKARA
2,ZUMA,
3,TSUMMI
4,SHA DA LIPTON   
5, TSUMMIN SANNYI

Hajiya inde kika siyawa oga wanan ko angon ki kuma yayi anfani dashi basu yimishi ba to kizo inbaki kudin ki hajjajju😉

A wanna set na maza 5in1

Akwai DAHUWAR ZAKARA😋
Zumar ingarman namiji😉
Akwai tsumin sanyi😗😋
Akwai Nasha d Lipton
Akwai tsumin  a fafata(yamayar dakai Dan 20yr )💃💃

Anfanin wanan set din suna d yawa

Yana wanke mara,yana mgnin sanyi,yana temakawa gurin dadewa ana gamsar d iyali, ga masu matsalar saurin kawowa,sanan yana mgnin kankancewar gaba,yana karamata girma dakuma karfi,sanan masu matsalar low spam count yana temakawa kawairai,Kai abubuwan d yawa bazasu gama faduwaba, sai Wanda ya gwadane zai gane me ake fadi🙌🏻🫶

Ina wadanda sukai planning sun Dena amma har ynxu ciki shiru, masu PCOS,infertility ko blocked tube. To don Allah kuzo muyi magana, Uwar Sudais na neman ku🫶💃💃💃

Kuyi maza don Allah🫰🏻 kun san dai a wanga harka baa sanya💃💃💃💃💃

Ga numbern mu nan da zaku same mu In sha Allah
***


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 



Page 18



*ARWA’S POV*


  
    Maama bata ko kalle ta ba ta wuce, direct stairs ta hau zuwa dakin ta, inda ta dauko sabon hand gloves ta fito, bata kalli Baaba ba don zuciyar ta wani irin baci take yi. Ita ma fa mahaifiyar Arwaa ce, duk irin yadda yake ji a zuciyar sa ta tabbata cewa tafi sa jin zafi, taya zai mata irin wannan dukan, shin ya manta cewa ita mace ce? Ba wai bata goyan bayan dukan bane amma yayi yawa.

Sai da ta kawo bakin kofar dakin sannan ba tare data jiyo ba ta ce “ka kira yar Uwar ka ta fice daga dakin, tun da ba ita ta haifar min yarinyar ba” daga haka taja bakin ta tayi shiru kuma bata shiga dakin ba.

Baaba bai wata magana ba ya mike zuwa dakin, daga tone din da tai magana yasan ran sa a mugun bace yake da dukan da ya ma Arwaa, shi kuwa ko kadan baya dana sani amma fa akan yar matar sa zai iya hakura da komai. Dakin y shiga ba’a shafe minti 2 ba sai gasu sun fito yana gaba tana bin sa a baya sai Harare Harare take.

Ita dai Maama ko bai ta kan ta batai ba ta shige dakin tare da rufe kofar da key, nufar gadon tayi ta tsaya tana kallon Arwaa wacce ita ma ta zuba mata kumburarrun idanun ta.

Cikin rawar murya na ce “Ma…aa…m…aa, k…e maaa bak….i ya…ddaaaa da n…i b…a?”

Dauke kan ta Maama tayi ganin haka ysa ni saurin rintse idona ina fashe wa da wani kuka. Wannan tun daga kasan zuciya ta yake fito wa. Cikin karyewar zuciya na ce “in baki yadda da ni ba waye zai yadda ni, Wallahi ba abinda ya taba shiga tsakanin mu, Taya ma zaki yi tunanin zan bawa wani namiji jikina Maamaa”. Kuka ne ya sake fin karfina ga wani mugun zazzabi daya rufe ni lokaci daya.

Maama bata sake bi ta kai na ba sai hand gloves din data sa ta shiga yin abinda ya kawo ta, ita ma tana bukatar duba war ko zata samu nutsuwa da kwanciyar hankali.

Sai da ta tabbatar ba abinda ya taba martabar yarinyar ta şu sannan ya sauke ajiyar zuciya, dagowa tayi ta kalli Arwaa wacce ta rintse Idon ta sai kuka take mara sauti.

Cikin wata iriyar murya Maama ta ce “mai ya kai ki rungume wani kato?, shin mai kika mayar da kan ki? Ina sanin ki na addinin ki? Kin bani kunya Arwaa? Kin bamu kunya” daga haka ta juya ta fice…

Kuka na nake sosai bayan fitar ta, shin ba wanda zai fahimce ni neh? Na amince nayi kuskure amma iyaye na mai yasa baza su bari na musu bayani ba..  wata zuciyar ce ta ce “kar kiga laifin su Arwaa, a jikin wani kato fa suka ganki a rungume, wani irin bakin ciki kike tunanin suke ciki….


A can palo kuwa Maama data fita kallo daya kawai tayi wa Baaba ya sauke ajiyar zuciya. Sun riga da sun san ma’anar ko wanne motsi na dan uwan şu shiyasa ya gane mai take nufi. Maama na kokarin hawa sama aka bude kofar palon aka shigo.

Haala ce sanye da kayan ta na graduation, bata cire komai ba sai rigar saman, kuma kallo daya zaka mata kasan tana cikin tashin hankali. Bin palon da kallo tayi daga yanayin mutanen palon tasan tabbas akwai matsala babba wani abu ya faru.

Cikin rawar jiki ta tsugunna a kan carpet din dake malale a palon, sai kuma ta kasa magana, sai satar kallon kofar dakin Arwaa take.

Kallon ta Baaba yayi yana jin wani bakin ciki na taso masa, shi yasan duk abinda Arwaa take to tabbas Haala na da masaniya amma bata taba ankarar da şu ba, yo taya dama zata ankarar da şu din bayan duk bakin şu daya, Tsaki yayi ya mike kawai ya fice daga palon. Ita na Maama sama ta hau yayin da Aunty Hanifa ta fice zuwa gidan ta da niyyar gobe da sassafe zata dawo. Adda ma tsohon dakin ta ta shige kawai aka bar Haala ita kadai, tana ganin duk sun watse ta mike a guje zuwa dakin Arwaa.

Yadda ta samu Arwaa din kawai sai ta rungume ta tana fashe wa da kuka, ta ma rasa ta yadda zata taimaka mata ga shi jikin ta yayi mugun zafi.

Toilet ta shiga ta kunna shower sai da ta dai dai ta ruwan sannan ta fito ta taimaka wa Arwaa cire kayan ta, towel ta daura mata tana kuka itama, hannun ta taja har toilet din ta tsaya. Hannayen Arwaa dake rawa ta sa a jikin bango sannan ta juya mata baya ta ce “ki daure Arwaa ki dan gasa jikin ki kin ji?”

Ban ce mata komai ba sai towel din dana cire na tsaya a kasan shower din, kuka kawai nake Kamar yadda ita ma take kukan. An rasa wanda zai rarrashi wani. Da kyar na samu dan kwarin gwiwar dauraye jikina don maganar ma sa soap bai taso ba tun da jikin nawa duk a fashe yake.

Alwala nayi bayan na gama na mai da towel din, Haala ce ta rike ni zuwa kan gado na, deodorant ta dauko da mai, shafa min tayi ta shiga shafa min man a jikina tana kuka ina yi. Ba wanda ya iya magana, pant kawai na sa sai doguwar riga mai hannun vest da hula. A zaune nayi sallar azahar da ban ba sai la’asar.

Ita kam Haala kitchen ta nufa ta hada min tea mai kauri, dawo wa tayi ta shiga lallashi na Akan na sha. Da kyar na sha na rabi sannan na jinginar da bayana ina sauke ajiyar zuciya. 

Fita Haala tayi waje ta fi minti 30 sannan ta dawo da wata leda ta pharmacy. Magungunan na shiga bani na sha, sannan ya shiga shafa mun ointment a duk inda taga yayi rudu rudu. 

A zaune nayi magriba da Isha’i ina idar wa Haala ta janyo ni ta cire min hijab sannan ta kwantar da ni akan gado, ina ta min adduar bacci ta shafa mun sannan ta kunna min karatun Quran, ina jin ta tana matsa min kafafuna a hankali ban San lokacin da bacci yayi awon gaba da ni ba.





             *RHYS*


Tunani na gaba daya yana kan Malyshka, ban san girman abinda mukai ba sai da Adam ya min bayani a addinin su it’s prohibited namiji that’s not your Mahram to touch you, na San wannan don ta taba fada min a time din dana so nayi holding hand nata. Amma yadda ya dinga min bayani dalla dalla yasa na gane kuskuren da mukai.

Tsoro na daya kar şu mata wani abu, don Adam ya ce ba karamin laifi bane kuma ba parents din da zasu ga haka su kasa daukar mataki.

Kallo waya ta na sake yi ina sauke ajiyar zuciya, har ynxu David bai kira ni ba tun dazu na ce ya nemo min Address din gidan şu Malyshka har ynxu. 

Adam da yake ta kallon aminin nasa shima ajiyar zuciyar ya sauke yace “calm down, In sha Allah komai zai zo da sauki”

Girgiza kai kawai nayi, Adam baxai gane ba na sani don haka no need ma na bata bakina wajen masa magana. In har suka taba min baby girl dina zan rufe ido na akan cewa sune iyayen ta na sa a kulle mun su kawai.

Hangame baki Adam yayi ya ce “ba dai wani abun kake tunanin zaka sa a ma parents nata ba koh?”

Kallon sa nayi da red eyes dina na ce “bara na ga lafiyan ta tukun, ko hair din ta suka taba sai na sa an kulle su”

Zaro ido Adam yayi yana bin sa da kallo, so yake yaga ko wasa yake masa amma kuma fuskar sa ba alamun wasa. Kusa da shi ya dawo ya zauna ya shiga fada masa şu da addinin su daban, kuma yiwa parents biyayya is a most, yana fada masa kadan daga cikin rights din parents akan yaran su. Ganin kamar ma ba gane wa yake ba yasa shi cewa “and ina tabbatar maka ko nails din iyayen ta ka sa aka taba ta bar ka kenan har abada”

Sai a lokacin na kalle sa da mamaki, duk abinda yake fada bama ina gane wa bane amma jin zata barni yasa ni dawowa cikin hankali na.

Gyada kai kawai Adam yke cikin tabbatar wa.

    A takaice dai ranar a zaune na kwana, time din da Adam ya nufi mosque ni kuma na shiga toilet, wanka nayi ina fito wa na shirya cikin Navy blue shirt da black jeans. Perfumes dina na fesa sosai sannan na saka Dior slippers na fito, na gaji da jiran David zan je school din ai nasa dole suna da address din.

Ina fito wa David na shigo da motar ciki, ban jira ya karaso ba na nufo sa da sauri, shima da saurin ta fito bai bani damar magana ba ya ce “har kofar gidan su na je Boss, ynxu ma sai da na tsaya naga fitowar father nata zuwa mosque da koma war sa to confirm sannan na dawo”. 

Bude back sit kawai nayi na ce “let’s go”

Adam da shigowar sa kenan da jallabiyar sa shima yai wuf ya shige motar..

David kam jiki na rawa ya tada motar sai gidan şu Arwaa…





  Sbd Allah Bakwa Kwaments, book din baya muku dadi neh?

Yan group din FORBIDDEN LOVE kuna bani kunya Allah😩 Taya za’a ce ku da kuke group din bakwa kwaments sai yan wasu group din. Sbd ku shiyasa ban cika typing kullum ba ko zan yi sai na ce no need basa kwaments😩

Gaskiya ku gyara☹️


Saura 2pages mu gama free pages 💃💃

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol