Free chapter · Read without an account

19

by khadijah danasabe · FORBIDDEN LOVE

💫💫💫💫💫💫
         FORBIDDEN LOVE
                      💫💫💫💫💫💫


DijahAM(Oum Amani)


Assalamu alaikum🗣️🗣️

JAMA’A💃💃💃


Ina uwar gida, amarya, to duk ku matso muna d mgn, kufito kuyi booking set mai suna grooms set (5in1)natural remedies, with zero side effects acikin set dinan Muna da __

 1,DAHUWAR ZAKARA
2,ZUMA,
3,TSUMMI
4,SHA DA LIPTON   
5, TSUMMIN SANNYI

Hajiya inde kika siyawa oga wanan ko angon ki kuma yayi anfani dashi basu yimishi ba to kizo inbaki kudin ki hajjajju😉

A wanna set na maza 5in1

Akwai DAHUWAR ZAKARA😋
Zumar ingarman namiji😉
Akwai tsumin sanyi😗😋
Akwai Nasha d Lipton
Akwai tsumin  a fafata(yamayar dakai Dan 20yr )💃💃

Anfanin wanan set din suna d yawa

Yana wanke mara,yana mgnin sanyi,yana temakawa gurin dadewa ana gamsar d iyali, ga masu matsalar saurin kawowa,sanan yana mgnin kankancewar gaba,yana karamata girma dakuma karfi,sanan masu matsalar low spam count yana temakawa kawairai,Kai abubuwan d yawa bazasu gama faduwaba, sai Wanda ya gwadane zai gane me ake fadi🙌🏻🫶

Ina wadanda sukai planning sun Dena amma har ynxu ciki shiru, masu PCOS,infertility ko blocked tube. To don Allah kuzo muyi magana, Uwar Sudais na neman ku🫶💃💃💃

Kuyi maza don Allah🫰🏻 kun san dai a wanga harka baa sanya💃💃💃💃💃

Ga numbern mu nan da zaku same mu In sha Allah

***

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 



Page 19



 
     *RHYS*



Tafiyar 20mins ce ta kawo mu kofar gidan da David ya tabbatar mun cewa _Malyshka_ na ciki. Yadda bugun heart dina ya chanja kadai ya fahimtar ni cewa tabbas tana ciki.

Kallon sa Adam yayi ya ce “Anya this is a good idea kuwa Rhys?”

Hade rai nayi kawai na bude motar na fito, to zan tsaya ne yana tambaya ta abin da nake shirin yi is good or bad, one thing dana sani Malyshka tana ciki. 
  
   Knocking gate din nayi, ba’a dauki time ba gate man ya bude kofar. Kallon mu yake Kamar yadda muma muke kallon sa. A nasa bangaren kuwa mamaki yake mai ya kawo maza haka da asuba gidan su, kuma Baaba bai dade da wuce ba amma bai fada masa zasu yi baki ba.

Babbake kofar gate man din yayi ya ce “Mai gidan yasan da zuwan ku?”

Bude baki Rhys yayi zai magana sai kuma yaga bata lokaci ne kawai, dogon index finger din sa yasa yadan shafa girar sa. David daya dauki hint din abinda Ogan nasa yake nufi da sauri ya nufi Halilu mai gadi, pistol din sa kawai ya da masa a kai yana zare masa jajayen idon sa.

Tuni jikin Halilu ya hau rawa, cikin rawar baki ya ce “Bayin Allah don Allah kuyi hakuri, ni wallahi ba dan gidan bane aiki kawai nake musu”

Hankada sa cikin gidan David yayi still bai cire pistol din daga kan sa ba, tuni Halilu ya saki fitsari sbd tashin hankali.

Shiga gidan Rhys yayi yayin da Adam ya mara masa baya a ran sa yana adduar Allah yasa duk abinda zai biyo baya ya kasance mai sauki ba aminin nasa ya sake kwabe abubuwa ba.

A compound din gidan duk suka tsaya in da Rhys ya kalli Halilu da sai fitsari yake Kamar wanda ya kamu da ciwon yoyon fitsari.  Yamutsa fuska nayi ina dauke idona daga kan sa, murya ciki ciki na ce “kira mai gidan”

Halilu da bai gane mai Rhys din ke fada ba sbd yayi da turanci ne, kuma turanci ba irin wanda ya saba ji ba kawai sai ya fashe da kuka yana kallon Adam don yağan sa da jallabiya.

Adam ne ya fassara masa ai kuwa jiki na rawa ya shiga kiran Baaba, sai dai har wajen kira biyar Baaba bai dauka ba. Kara barke wa da kuka Halilu yayi jikin sa ban da rawa ba abinda yake, dabarar kiran Maama ce tazo masa ai kuwa yayi saurin dannan mata kira. Sai da ta kusa katse wa sannan ta daga, cikin kuka Halilu ya ce “Hajiya ki taso Alhaji don Allah, akwai matsala babba”

Maama jin Halilu na kuka yasa cikin faduwar gaba ta ce “me ya faru?”

Da karfi ya ce “don Allah ku sauko Hajiya kar şu kashe ni”

David bai basa damar karasa wa ba ya karbe wayar.

A cikin gida kuwa cikin tashin hankali Maama ta kalli Baaba wanda yake zaune a kan sofa din daki yana karanta Azkar, shima kallon ta yake yi don tun da ta fara wayar ya daga idon sa ya sauke a kan ta.

Fada masa duk abinda Halilu ya ce tayi sannan ta kara da cewa “duk abinda zai saka Halilu kuka haka babba ne Baa, cewa yayi fa zasu kashe shi”

Mike wa Baaba yai ya saka takalmin sa zai fita, da sauri Maama ta riko sa, cikin damuwa ta ce “ka bari a kira poliçe kar ka sauka don Allah”

Hannun sa ya zare daga cikin nata ya ce “no need, ina ga na san wanda yazo” daga haka ya fice zuciyar sa tamkar zata faso kirjin sa sbd bakin ciki.

Maama ma hijab ta şaka ta sauka da sauri, tana zuwa palon kasa taga har ya fita don haka ta mara masa baya, Adda ma da fitowar ta Kenan ganin yadda Maa ta fita da sauri yasa ita ma ta bi şu compound din.

Haala wacce ta fito daga daki don zuwa wajen Adda ta ara mata charger din ta ganin Adda din ta fita hadda gudu gudu yasa ita ma kawai ta fita.


  Har lokacin da şu Baaba suka fito David bai cire wa Halilu bindigar daga kan sa ba. Haka kuma duk irin kallo da Baaba yake wurga masa ko a jikin sa,don shima irin kallon yake wurga masa, don tabbas fa shi da ace yana da iko da kan sa ba abinda zai hana sa fasa brain din Baaba, ai shi tun da Baaba ya iya marin Ogan sa to a duniya ba shi da makiyi kamar sa, duk da kasancewar sa mahaifin Madam din sa yo Madam din sa mana tun da Babyn Boss ceh, hakan baxai sa ya daga wa Baaba kafa ba.

Baaba da bakın ciki ya sake mamaye wa bin su yake da kallo daya bayan daya yana jin zafin wannan raini da aka masa. Kamar shi ya kama d’iyar da rungume a jikin wani kato a jiya, yau kuma katon yazo gidan sa to uban me zai masa.

Adam ne yayi saurin matso wa ya durkusa kasa ya ce “Ina kwana Baaba”

Cikin bakin ciki Baaba ya kalli Adam kafin ya ce “a ta ina na zama Baaban naku, to ni ban haifi Christian ba kuma ban hada jini da su ba”

Shiru Adam yyi kafin ya dan saci kallon Rhys wanda idon sa yake kan Haala kamar bai ga fitowar ahalin gidan ba.

Ban damu dana kalli ko wanne daga cikin su ba, burina kawai na San ya Malyshka take. Don haka na nufi Haala wacce ke tsaye idon ta duk a kumbure da alama tayi kuka har ta gode wa Allah.

   Kai tsaye na ce “where’s Malyshka?”

Ai tuni hawayen da Haala ke ta kokarin rike wa suka sake zubo mata, don tasan zuwan sa gidan ma wani laifi ne mai zaman kan sa da Arwaa zata fuskanci hukuncin sa.

Sake maimaita mata tambayar da Rhys yayi ne yasa ta satar kallon Inda şu Baaba suke tsaye. Irin mugun kallon da suke mata ne yasa kawai ta durkushe a wajen tana sake fashe wa da kuka.

Da mamaki nake kallon ta gaba na yana wani irin bugawa…

Baaba da ta gama çıka cike da bacin rai ya ce “me kuka zo yi a gidana? Wallahi Allah ku fita tun kafin na kira muku police su fitar da ku. In ku baku da tarbiyya to ni gidana na tarbiyya ne, ko da yake ina Arne Ina tarbiyya dama”

Kallon sa nayi ina son sanin meye matsala ta da shi neh, tun jiya daga ya tashi magana sai ya ambaci religion dina kamar yana fadar abin kazanta. Though I’m not that religious amma baxan yadda ana wulakanta min addini ba.

“Morning Baaba” na fada ina zuba masa manyan idona cikin nasa, bude baki nayi zan fara nasa jawabi akan yadda yace bamu da tarbiyya, Adam yayi saurin katse ni ta hanyar cewa “don Allah Baaba kayi hakuri, zuwa muka yi don mu baka hakuri amma..”

Nima katse sa nayi da sauri, cikin deep voice dina na ce “ni na fada ma hakuri zan bayar Adam?” Na fada ina Kankance idona. 

Hangame baki Adam yayi zai magana amma maganar ta makale sbd tashin hankali, wai me yasa Rhys baya gane wa neh, an fada masa mutane irin şu Baaba ana musu haka. Duk da bai San Baaba amma daga fitowar sa da yanayin maganganun sa ya fahimci mutum ne shi mai tsananin tsauri da kuma kyamar wani religion din, Kamar yadda ya nuna. Ya tabbata in har basu kwantar da kai ba to kuwa tabbas baza ayi rabuwa mai dadi ba.

“Zuwa nayi naga lafiyar my little girl” na fada ina mayar da dubana kan Baaba, wanda lokacin da Rhys ya ambaci Arwaa da little girl din sa wallahi sai da numfashin sa ya dauke na seconds kafin ya fisgo sa a wahalce.

Tabbas da ace shi rago ne ba abinda zai sa hawaye zubo masa “tabbas tsakani na da kai Allah ya İsa, a irin tarbiyyar ka nasan dama dole zaka nemi lalata min tarbiyyar yarinya. A gabana kake kiran daughter ta da your little girl, wato kaga yarinya karama kana so ka mata wayo ka lalata min ita ko”

“What do you mean?” Na tambaye sa ina Juyowa gaba daya zuwa inda yake, ba dai mutumin nan tunani yake Ina da wani bad thought akan Malyshka bah.

Cikin zafin rai Baaba ya ce “eh abinda nake nufi kenan, irin ku dama mai kuka sani ban da lalata tarbiyyar yara ku…..”

Da sauri Maama ta riko hannun sa ta ce “Don Allah Baa kayi shiru, maganganun ka sun yi tsauri da yawa, ba wanda yasan gobe sai Allah kar ka fadi abinda zaka zo a gaba kana dana sani”

“A wani dalili zai yi danasani Bilkisu(sunan Maama) ai ba abinda zai sa yayi danasani kuma abinda ya fada ina gaskiya ce, ba su ne suke lalata tarbiyyar yara ba. In banda ma Allah ya takaita ai da tuni an wuce wajen Wallahi, don a yadda dai muka gan su jiya da ban dan mun isa da wuri ba da tuni ynxu haka sun fara plan din haduwa a wani waje” Aunty Hanifa ta fada zuciyar ta na wani irin suya. Kasa zama tayi a gudan ta kawai ta cewa Habeeb yazo ya kawo ta gidan Yayan nata. Shi kan sa Habeeb yayi mamaki yadda ta dage sai tazo da sassafe dinnan, amma sai ta ce masa wani abu ne yake faruwa tana so taji yadda aka kwana. A hanyar su ta zuwa ne take shaida wa Habeeb komai wanda yayi şhiru bai ce komai ba. Sai gashi kuma zuwa suwa suka tarar Halilu da bindiga a kan sa ga kuma mutan gidan sun yi cirko cirko anan ne suka tsinci maganganun da ake yi.

Habeeb kallon Rhys yake Kamar yadda shima yake kallon sa bayan yayi wa Aunty Hanifa kallo daya. Dole ya mata kallo daya ya dauke kai mana a matsayin sa na likiti a dai kallo dayan yaga kamar brain din ta bashi da lafiya. Sai kuma ya mayar da kallon sa ga saurayin da suke tare. 

     
     *ARWA’S POV*

“Ni ba yar iska ba ce” murya ta data shige ciki sosai ta fito da confidence din da ban yi tunanin ina da shi ba.

Tsit wajen yyi suka juyo gaba daya suna kallona. Bacci ne ya dauke ni bayan sallar asuba a kan dadduma sai dai dama baccin bana dadin rai bane. Hayaniyar da nake ji sama sama ce tasa ni mike wa n fito palo duk a tunani na a nan ake. Sai dai palon shiru ba kowa hakan ne yasa na bude window. Mutumin da na gani a compound din gudan mu nayi tunanin baxan sake ganin sa ba har abada, sai gashi a cikin gidan mu. Ina tsaye Ina sauraren yadda suke magana da Baaba ban yi kokarin fito wa ba sai da Aunty Hanifa tayi magana wacce har na manta ma da rigar jikina na fito waje.

Idona ne suka shige cikin nasa, take wasu hawaye masu mugun zafi suka zubo min. Kallon ta yake da manyan idon sa wadan da suka yi jajir.

Gaba dayan ta ta saura kamar ba ita ba, fuskar ta a kumbure haka ma idon sa, bin wuyan ta da hannayen ta yake d kallo don rigar jikin sa mai hannun vest ce kuma rubber, kan ta ko dan kwali babu gashin ta yana daure cikin wani messy bun. Hakan ne ya basa damar ganin yadda goshin ta yake a fashe ya kumbura.

Cikin fitar hayyaci ya nufo ta, duk da tazarar da ke tsakanin su taku biyar ne ya kawo sa gaban ta. Kara sake kallon jikin ta yake, gaba daya wuyan ta da hannun ta sun yi rudu rudu, jijiyoyin jikin sa sun fito sosai sbd bacin rai. Hannu biyu ya mika zai kamo ta sai da ya rage bai fi inci biyu ba hannun sa ya taba jikin ta sai kuma ya tsaya. Tuno wa yyi da maganar ya a lokacin da take shaida masa babu kyau a addinin da bayanin Adam, ga shi kuma yana tsoron kar ya taba ta yaji mata ciwo.

A hankali ya ce “Malyshka”

Ai kawai sai na fashe da kuka, irin kukan da ke nuni da zallar tashin hankalin da nake ciki.

Ya rikice ya rasa ya zai yi, shi ba abin ya rike ta ba tun da ba kyau kuma baya son kukan nata.

Juya wa yayi ya kalli Adam wanda ya ke kallon sa Idon sa ya tara hawaye. Cikin karyewar murya ya ce “if I touch her while wearing gloves shima ba kyau?”

Wani irin tausayin şu ne ya kama Adam, hawayen daya zubo masa ya share ya ce “ganin ta a haka ma is Haram tun da she’s exposed”

Juya mata baya yayi a take yana bata rai ya ce “ku juya kuma”

Ba musu Adam ya juya, David ma juya wa yayi bayan ya falla wa Halilu Mari don shima ya juya.

Kallon Habeeb Rhys yayi sannan ya kalli David, wanda kawai daga masa kai yayi ya nufi Habeeb, bai yi magana ba kawai ya buga masa kafa a gwiwar sa ba shiri ya zube kasa, David bai basa damar wani motsi ba ya juyar da fuskar Habeeb din don ta dinga kallon gate.

Shi dai Halilu yana samu David ya sake sa kawai ya kwanta flat a kasa yana rufe idanun da da hannu biyu biyu hadi da barke wa da wani Sabon kukan.





   Ni kai na sai da ma share hawaye🥹

My babies🥹😩

Kuyi hakuri kun ji but I want you to suffer😂🥹

MY GUY🥹




***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol