Free chapter · Read without an account

20

by khadijah danasabe · FORBIDDEN LOVE

💫💫💫💫💫💫
         FORBIDDEN LOVE
                      💫💫💫💫💫💫


DijahAM(Oum Amani)


Assalamu alaikum🗣️🗣️

JAMA’A💃💃💃


Ina uwar gida, amarya, to duk ku matso muna d mgn, kufito kuyi booking set mai suna grooms set (5in1)natural remedies, with zero side effects acikin set dinan Muna da __

 1,DAHUWAR ZAKARA
2,ZUMA,
3,TSUMMI
4,SHA DA LIPTON   
5, TSUMMIN SANNYI

Hajiya inde kika siyawa oga wanan ko angon ki kuma yayi anfani dashi basu yimishi ba to kizo inbaki kudin ki hajjajju😉

A wanna set na maza 5in1

Akwai DAHUWAR ZAKARA😋
Zumar ingarman namiji😉
Akwai tsumin sanyi😗😋
Akwai Nasha d Lipton
Akwai tsumin  a fafata(yamayar dakai Dan 20yr )💃💃

Anfanin wanan set din suna d yawa

Yana wanke mara,yana mgnin sanyi,yana temakawa gurin dadewa ana gamsar d iyali, ga masu matsalar saurin kawowa,sanan yana mgnin kankancewar gaba,yana karamata girma dakuma karfi,sanan masu matsalar low spam count yana temakawa kawairai,Kai abubuwan d yawa bazasu gama faduwaba, sai Wanda ya gwadane zai gane me ake fadi🙌🏻🫶

Ina wadanda sukai planning sun Dena amma har ynxu ciki shiru, masu PCOS,infertility ko blocked tube. To don Allah kuzo muyi magana, Uwar Sudais na neman ku🫶💃💃💃

Kuyi maza don Allah🫰🏻 kun san dai a wanga harka baa sanya💃💃💃💃💃
Ga numbern mu nan da zaku same mu In sha Allah
***


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 



Page 20



*ARWA’S POV*



Bai sake juyo wa ba cikin booming voice ya ce “Haala”

Yadda ya kira sunan ta yasa ta saurin mike wa jikin ta har rawa yake ta ce “Yes Sir”

“Help her to cover herself” ya fada kawai yana dunkule hannun sa a baya.

Da sauri Haala ta cire Hijab din jikin ta ta şaka wa Arwaa sannan ita ta ruga ciki da gudu don dauko wani Hijab din, yo hauka take zata tsaya har sai ta wani shiga ciki ya dauko wa Arwaa wani hijab din bayan ga nata, haka kurin ta ja wa kan ta.

Wannan abun da yayi ba karamin sake bakan ta ran Baaba yayi ba, don fa shi ko kadan hakan bai burge sa ba. Ita kam Maama hakan ya dan sanyaya zuciyar ta, har ta fara tunanin da alama yaron yasan mutuncin diyar ta ta.

Aunty Hanifa wacce ta saki baki da mamakin abinda David yayi wa tilon d’an ta tayi saurin karasa kusa da şu kamar zata kifa.

Cikin daga murya ta ce “don ubanka me yayi maka da zaka rike sa haka sai ka ce wanda aka kama ya danne yarinya”

Kara rike fuskar Habeeb yayi sosai sannan ya kalli Aunty Hanifa, sarai ya fahimci tana adawa da Boss din sa. Shi kuwa ai duk wanda baya son Boss din sa to shima ya tsane sa kenan har abada, bai bata amsa ba sai kallon Boss din sa da yayi, Gyada masa kai Rhys yayi hakan yasa shi sakin Habeeb yana dan bubbuga bayan sa ya ce “be a good boy okay”

Da mamaki Habeeb ke kallon sa don bai San mai yayi ba, ya dai fahimci sbd Arwaa da bata cikin shiga cikakkiya ne duk hakan yaja. Kenan da gaske ne abinda Maman sa ke fada cewa wani Arne ne yake son Arwaa din. Kallon Arwaa yayi wacce idon ta ke bayan mutumin tana kalla da wani irin yanayi, mugun kishin ta ne ya taso masa don Allah ya sani yana mata wata iriyar kaunar ta. Kaunar ce ma yasa da farko bai tunkari mahaifiyar sa ba sai da ya soma neman Arwaa da maganar, amma ta dinga zille wa, shi kuwa ganin baxai iya daure wa ba ne yasa shi fada wa mahaifiyar sa. Ya riga da ya san ma Arwaa ta sace In sha Allah, duk da irin kallon da suke jifar junan su da shi kadai ya isa ya bayyana kaunar şu hakan bai dame sa ba, ba yadda za’a yi Christian ya auri Arwaa don haram ne a addinin su, bayan haramcin hakan ma iya yadda Baaba yake jifan Rhys da kallo zaka san tsantsan kiyayyar da yake masa, sbd haka zai sake dage wa sosai wajen ganin ya samu soyayyar Arwaa. Kuma In sha Allah ita din tasa ce.

Horn aka yi a kofar gida hakan yasa Baaba da kan sa zuwa ya bude gate din. Motocin sojoji ne har uku suka shigo ciki kuma ko wacce cike da sojiji. Motocin na tsayuwa suka shiga dirowa ko wanne hannun su rike da bindiga kamar wadanda zasu je yaki.

Kallon su Baaba yayi yana murmushi sannan ya juyo ya kalli Inda Rhys yake, wanda shi hankalin sa ma gaba daya yana kan Arwaa ko juyo wa bai ba. 

Da mamaki Maama ke kallon Baaba wanda ya gyada mata kai kawai yana murmushi. Bayan shigowar Hanifa ne ya juya musu baya ya kira Aminin sa wanda yake General ne, a takaice ya fada masa abinda ke faruwa ya kuma roke sa ya turo masa wasu daga cikin yaran sa şu tafi da yan iskan, yadda yayi din ba wanda zai kawo waya yake.

Rhys Baaba ya nuna wa Captain din cikin su yana cewa “shi ne wancan, kar ku raga masa don Allah”

Cikin kulawa Captain Ahmad ya ce “In sha Allah Baaba, General ya mana bayanin komai” daga haka ya shiga nufo wa inda Rhys yake.

Kafin ya karasa David yai saurin shan gaban sa yana jifan sa da wani mugun kallo mai cike da gargadi.

Ganin haka yasa wasu manyan sojoji nufo wajen da sauri don rufe David da duka. ID carp din sa David ya zaro a aljihu ya nuna wa Captain Ahmad, Zaro ido yayi yana sake kallon ID card din sannan yai masa salute, ganin haka yasa sauran yaran gaba daya suma sukai saluting David. 

Hakan da Baaba ya gani yasa cikin bacin rai ya nufo Captain yana cewa “meye haka”

Captain Ahmad bai bawa Baaba amsa ba sai da ya kalli David cikin girmama wa ya ce “sorry Sir” sannan ya kalli Baaba ya ce “gaba yake da ni a wajen aiki”

Da mamaki Baaba ya kalli David sannan ya kalli Captain, “ban gane gaba yake da kai ba?”

“Eh Baaba, gaba yake da ni, ni Captain nake shi kuma Major neh” Captain Ahmad ya masa bayani.

Tsaki Baaba yayi “to in shi Major ne wancan din da nace ku kama ba sai ku kama sa ba tun da shi mai farin Kaya neh” ya karasa a kufule.

Kallon gargadi David ya masa “ina mai baka shawara ka dauki yaran ka ku tafi, don I swear ko dirt ne ya hau kan shoe din sa da niyyar gangancin ku I assure you his Papa will make sure dükkan ku an sallame ku bayan anyi punishing din ku, ka San ko ni kadai I can punish you bah, let alone his Papa, ko baka ga cewa ni yaron sa bane bah ehh” David ya karasa da daga murya.

Da mamaki Captain yake kallon bayan Rhys wanda ko juyo wa bai ba kuma ba shi da alamar yin hakan, so yke ya gan sa ko kuma ya San waye shi amma da alama baxai samu wannan damar ba. Don haka kawai ya bawa Baaba hakuri ya dauki yaransa suka tafi.

Sai bayan tafiyar şu sannan Adam y sauke ajiyar zuciya. Wajen Rhys yazo ya masa magana kasa kasa, sai da ya masa yadda zai gamsu sannan Rhys din ya daga masa kai.

Mai da duban da yayi kam Arwaa ya ce “Malyshka”

A hankali na dago ina kallon sa da idona wadanda har ynxu basu bar zubar hawaye ba.

“Promise me zaki daina kuka kin ji” ya fada cikin wata iriyar murya da ke sani jin kaunar sa na sake mamaye ni.

Gyada masa Kai nayi ina share hawaye na. Murmushi ya sakar min cikin bani kwarin gwiwa ya ce “*_wait for me Malyshka, wait for me_* Zan dawo anjima Ohkay” kara gyada masa kai nayi ina jin kokarin mayar da hawaye na. 
Ashe ban sani ba daga wannan maganar baxan sake jin maganar sa ba….

Ina kallon su har suka fice daga gidan, Marin da aka kifa min ne yasa ni zabura.

Aunty Hanifa ce tsaye sai huci take, cikin bacin rai ta ce “amma Arwaa kin cuce mu, ynxu sbd tsabar dükkan mu baki ganin mu da kima ace a gaban mu kike magana da katon arne, har yana cewa ki jira sa. To ki jira sa yazo ya miki uban me?”
 Sai kuma ta kalli Baaba ta ce “Wallahi yaya yama Raina mana hankali ne, don yafi karfin hukuma ai bai fi karfin ka ba tun da kai ne mahaifin Arwaa kuma kai ke da iko da ita. Ganin ta da yake haka ne ma yasa yake da sauran hope din karasa lalata ta.”

“Ni ba lalata nin da yake son yi, ni San sa baxai taba tunan….” Ban karasa ba sbd wani Marin da aka sake kifa min. Wannan Karan Baaba ne wanda yake tsaye yana huci.

“Ba laifin ki bane Arwaa” daga haka ya juya ya kalli Habeeb. “Habeeb, Hanifa ta fada min kana son ta, da gaske neh?”

Jiki na rawa Habeeb ya gyada kai. “Alhamdulillah” Baaba ya fada yana kallon Aunty Hanifa sai kuma ya cigaba da cewa “ki koma gida ki shaida wa Nura(mahaifin Habeeb) ba dai dan iskan yaron can ya ce zai dawo ba, to kuwa sai dai ya dawo yağan ta a matsayin matar aure” daga haka ya shige ciki.




 Sosai naso ya kasance daga wannan mun gama free pages amma Allah bai nufa ba☺️ da alama akwai pages 2 a gaba ko page daya kafin mu gama free.


Domin son yin payment zaku biya 500 ta wannan account din 
***
Khadijah Dan’asabe Adamu
OPay 

Sai ku turo shaidar biya ta wannan numbern 
***

Ngd sosai
Taku har kullum Uwar Amani da Azlan💃😂

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol