Free chapter · Read without an account
THE SIN THAT LINGER
by Hau—waah · ZAYD ARMAAN
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER 142*
*THE SIN THAT LINGER*
*JIDDAAH BARKUM*
———-
Zayd ya fito daga falon Raihana, ya nufi part ɗin Seeyama. Yana tafiya yana duba wayarsa, bata falo sabida haka sai ya wuce direct zuwa bedroom dinta. Da ya isa ƙofar ɗakinta ya kwankwasa. Seeyama da ke zaune a gaban dressing mirror tana gyara hijab dinta ta ɗago kai. Da ta ji muryarsa yana cewa, “Can I come in?” sai ta amsa da sauri. “Yeah, come in.” Zayd ya tura ƙofar ya shigo. Kallonta ya yi daga sama har ƙasa, sanye take da wata doguwar riga mai kyau, ta ɗora hijab though ba wani babba bane but tayi kyau. Fuskarta har yanzu akwai dan kumburin kukan jiya dan gaskiya ba karamin kuka tayi bane. “You look beautiful,” ya faɗa yana murmushi. Seeyama ta ɗan yi murmushin yaqe dan Wlh a tsorace take tunda ya ce mata zasuje wani waje. “Thank you, babe.” Ta fada da sanyin murya. Ya ƙarasa inda take, ya tsaya a bayanta yana kallonta ta cikin mirror. “Are you ready?” “Yes. Just let me get my bag.” Ta miƙe, ta ɗauki handbag ɗinta daga kan gado, sannan ta ɗauki wayarta. Zayd ya karɓi handbag ɗin daga hannunta. “Let’s go.” Ta gyada kai, suka fito tare. Zayd ya rufe ƙofar ɗakin, suka nufi hanyar fita daga part ɗin. A hankali suka wuce babban falon, suka nufi parking lot.
A dai-dai lokacin Raihana tana tsaye a gefen window ɗin falonta, tana hanging curtains din. Ba wai tana leƙen su ba ne ko tana jiran fitowarsu ba. Kawai coincidence ne ya sa idanunta suka sauka a parking lot ɗin. Sai ta hango Zayd tare da Seeyama, yana rike da handbag dinta. Zayd ya fara isa motarsa, sannan ya zagaya zuwa passenger side. Ya buɗe wa Seeyama ƙofar gaba. “Come in,” ya faɗa yana nuna mata kujerar. Seeyama ta shiga cikin motar, ya ɗan sunkuya ya dora mata jakarta a laps dinta kafin ya rufe mata ƙofar. Daga nan ya zagaya zuwa driver seat ya shiga. Raihana kuwa tana tsaye a wurin, idanunta suna bin motsinsu ba tare da ta yi niyya ba. Ta ga yadda Zayd ya buɗe wa Seeyama ƙofa, yadda ya jira ta shiga sannan ya rufe mata. A wannan lokacin mai gadi ya fito da sauri ya buɗe musu babbar ƙofar gidan. Zayd ya kunna motar, ya yi reverse kaɗan sannan ya fitar da ita a hankali. Seeyama tana zaune a gefensa, tana magana da shi, shi kuma yana kallon hanya yana ba ta amsa. Motar ta wuce ta ƙofar gidan, mai gadin ya sake rufe gate ɗin. Raihana ta ci gaba da tsayawa a wurin na wasu daƙiƙu kafin ta sauke idanunta daga wajen. Ta juya ta koma cikin falon.
Motar Zayd ta ci gaba da tafiya a kan titi, Seeyama tana zaune a gefensa shiru-shiru. Tun lokacin da suka bar gidan take cikin wani yanayi na damuwa. Duk da ƙoƙarin da take yi na nuna komai lafiya, Zayd ya lura cewa hankalinta bai kwanta ba. Ya ɗan kalle ta daga gefen ido. “What’s wrong, Seema?” Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta amsa. “Babe, I’m scared.” “Scared of what?” Ta juya ta kalle shi. “I don’t know. What if things get worse? What if we meet someone and they tell us something frightening? What if…” “Hey, hey…” ya katse ta a hankali. “One step at a time, okay?” Ta yi shiru. Zayd ya ci gaba da magana cikin sanyin murya. “Kin san na gaya miki cewa za mu fuskanci wannan matsalar tare, ko? To, ki yarda da ni. Ba za mu je wajen wani da zai ƙara tsoratar da ke ba. Mutum ne mai ilimi, kuma ina da kyakkyawar alaƙa da shi tun kafin wannan matsalar ta faru.” “But babe…” “No buts.” Ya yi ɗan murmushi. “Ki kwantar da hankalinki. Ba za mu yi komai da ba ki yarda da shi ba. Duk abin da za a yi, za mu tattauna. I won’t let anyone intimidate you.” Seeyama ta sauke kanta, tana wasa da yatsun hannunta. “Are you sure he’ll help me?” “In shaa Allah. Shi ya sa ma na kira shi tun da wuri domin na sanar da shi halin da muke ciki. Ya san cewa za mu zo, kuma ya ce mu same shi a Gida ma.” “Okay,” ta amsa a hankali. Zayd ya miƙa hannunsa ya taɓa nata. “Look at me.” Ta ɗago ta kalle shi. “Everything will be fine, in shaa Allah. Ki yawaita istigfari, ki kuma tuna cewa Allah Mai rahama ne. Ba za mu yanke ƙauna daga rahamarSa ba.” Seeyama ta gyada kai. “Thank you, babe.” “Always.”
Bayan wasu mintuna, suka isa wani masallaci da ke cikin wani unguwa mai natsuwa. Masallacin yana da faffadan haraba, akwai wasu motoci a gefe, sannan ga wasu bishiyoyi da suka yi masa ƙawanya. Zayd ya rage gudu, ya shigo harabar, sannan ya yi parking a gaban wani gida da ke can ta baya da masallacin. Da ya kashe motar, sai ya ɗauki wayarsa. Seeyama ta kalle shi. “Is this where he lives?” “Yeah. Yana nan kusa da masallacin. Wani lokaci ma a cikin masjid din yake zama bayan ya gama karatu.” Zayd ya buɗe contact ɗin malamin, ya kira shi kai tsaye. A ka ɗaga wayar bayan ɗan ƙara. “Assalamu alaikum, Mallam.” “Wa alaikumus salam, Ahmad. Kun iso ne?” “Eh, mun iso yanzu. Muna a ƙofar gida.” “To, madalla. Ku shigo mana.” “Tohm in Shaa Allah.” Ya kashe wayar ya sa ta a aljihu, sannan ya juya ya kalli Seeyama. “Come on, we’re expected.” Seeyama, ta ɗauki handbag ɗinta, sannan ta kalle shi. “Babe, please don’t leave me alone.” Zayd ya ɗan yi murmushi. “I won’t. We’ll go in together.” Ya buɗe ƙofar motar, ya fito, sannan ya zagaya ya buɗe mata. Seeyama ta fito, suka tsaya a gefe ɗaya na motar kafin su nufi ƙofar gidan tare. A hankali Zayd ya yi sallama. Daga cikin gidan aka amsa musu, sannan suka buɗe ƙofar su ka shiga.
Bayan sun shiga gidan, sai wani matashi ya tarbe su da sallama, ya musu iso wani daki dake gefen gate din ya ce su zauna bari ya kira malam, zayd ya masa godiya suka zauna Seeyama kuma ta sunkuyar da kanta zuciyarta na bugawa. Ba a daɗe ba sai Malam ya fito daga wani ɗaki. Wani dattijo ne mai natsuwa, sanye yake da farar jallabiya, kansa da ɗan farin hula wacce ake cewa kwankwasa kaji hadisi. Da ya hango Zayd sai ya yi murmushi. “Ah, Ahmad! Lale, Marhabaaa.” Zayd ya miƙe tsaye da sauri ya gaishe shi. “Assalamu alaikum, Mallam.” “Wa alaikumus salam. Yaya hanya? Ya iyali?” “Alhamdulillah, lafiya lau. Allah ya saka da alheri.” Malam ya juya ga Seeyama. “Barka da zuwa, ƴar nan. Ya jiki?” “Lafiya lau, Mallam. Alhamdulillah.” “Madalla. Ka zauna mana.” Ya fada yana kallon zayd. Zayd ya zauna a kan kujerun da ke fuskantar inda malam ya zauna. Malam ya ɗan kalli fuskokinsu, musamman Seeyama wadda take zaune cikin dan nutsuwar da take kokarin nema, amma a fili yake akwai damuwa a tattare da ita. “Ahmad, ka ce min akwai wani abu da kake son mu tattauna..” Zayd ya gyara zamansa. “Na’am Mallam akwai wani abu ne da ya dame mu, shi ya sa na ga ya kamata mu zo mu same ka.” Malam ya gyada kai. “To, ina sauraronka.” Zayd ya ɗan kalli Seeyama kafin ya dawo da kallonsa ga Malam. “Mallam, gaskiya ba zan ɓoye maka komai ba. Abin da ya faru shi ne, zayd ya fada masa komai exactly yanda seeyama ta sanar da shi bai boye masa komai ba tunda mafita suka zo nema boye Abu ba zaiyi amfanin komai ba.
Malam ya yi shiru na wasu daƙiƙu bayan Zayd ya gama bayaninsa. Sai ya mayar da kallonsa kan Seeyama, ya kalleta daga sama har ƙasa, sannan ya gyara zamansa. “Seeyama, ko?” Ta ɗago kai a hankali. “Eh, Mallam.” Ya gyada kai. “To, Seeyama, ina so ki saurare ni da kyau. Abin da kika aikata ba ƙaramin kuskure ba ne. Na fahimci cewa kina son mijinki ya ƙara kula da ke, kina son ki samu soyayya da kulawar da kike ganin kina buƙata. Amma ƴar nan, shin saboda haka ne za ki manta da Allah?” Seeyama ta sunkuyar da kanta. “Ki sani, babu wani mutum da yake da ikon juya zuciyar wani yadda yake so. Soyayya da ƙauna daga Allah suke. Idan kina son wani abu, ki roƙi Allah. Ki yi addu'a, ki yi haƙuri. Ba za ki bi hanyar da za ta jefa ki cikin haɗari ga addininki ba.” Ya ɗan dakata, sannan ya ci gaba. “Abin da ya fi damuna shi ne yadda kika bari waɗannan mutane suka rinjayi tunaninki. Suka yi amfani da buƙatarki da raunin da kike ciki domin su shigar da ke cikin abin da ba ki fahimci girma da haɗarinsa ba. Ki gode wa Allah da Ya sa kika gane kuskuranki tun yanzu.” Seeyama ta ɗan goge idanuwanta. “Na yi nadama, Mallam.” “Madalla. Amma nadama ta gaskiya tana tare da barin kuskure. Kada ki sake komawa wajensu, kada ki sake neman irin wannan taimako, kuma ki yawaita neman gafarar Allah. Ki tuna cewa rahamar Allah tana da faɗi. Kada ki yanke ƙauna daga gare Shi.” “In shaa Allah, Mallam.” Malam ya gyada kai, sannan ya ce: “To, yanzu ki tashi. Ki shiga cikin gida. Ina son in yi magana da mijinki kaɗai.” Seeyama ta ɗago kai ta kalli Zayd. Zayd ya mata murmushi kaɗan. “Go inside. I'll join you shortly.” Ta gyada kai, ta miƙe ta dauki jakarta. Ta juya ta shiga cikin gidan, ta bar Zayd da Malam a falon.
Malam ya jira har ya tabbatar Seeyama ta shiga, sannan ya dawo da kallonsa kan Zayd. “To, Ahmad, yanzu mu tattauna abinda ya sa nace ta shiga ciki sabida bana son ta ji abinda zan fada hankalinta ya tashi.” Zayd ya jinjina Kai cikin gamsuwa. “Ahmad, gaskiya abin da ka kawo min yau ba ƙaramin abu ba ne. Amma ina so ka kwantar da hankalinka, ka saurare ni da kyau.” Zayd ya gyara zamansa. “Ina sauraronka, Mallam.” Malam ya ɗan sunkuyar da kansa kafin ya fara magana. “Bayan bayanin da ka yi min, akwai wasu abubuwa da na fahimta. Amma gaskiya, ina ganin akwai yiwuwar wannan matsalar ta wuce yadda kake tunani. Abin da ya sa nake son mu yi hankali da yadda za mu tunkare ta.” Zayd ya ɗan sauya Fuska alamun damuwa. “Me kake nufi, Mallam?” Malam ya kalle shi cikin natsuwa. “Gaskiya na ga aljanu a tare da ita. Kuma daga yadda abin yake, ba alama ce da ta nuna sun daɗe suna tare da ita ba. Sabon abu ne. Ina zargin wannan ne ma ya sa aka nemi budurcinta a lokacin da ta je neman aikin da zai sa ka ƙara sonta.” Zayd ya ɗan buɗe baki saboda mamaki. “Subhanallah!” Malam ya gyada kai. “Eh. Ina zargin wannan aljanin yana sonta ne, shi ya sa aka nemi wannan abu daga gare ta. Kuma daga abin da na fahimta, shi ne yake kawo mata wannan matsalar ta zubar jini duk lokacin da kake ƙoƙarin kusantarta.” Zayd ya yi shiru na wasu daƙiƙu. A fili yake maganar ta girgiza shi. “Mallam, kana nufin duk lokacin da na yi niyyar kusantar ta, shi ne zai haddasa hakan kuma yanzu kenan a jikinta yake?” “Wannan shi ne abin da nake zargi bisa bayanin da ka kawo min da kuma yanayinta da na fahimta a ganin farko da na yi mata. Amma kada mu yi saurin ɗaukar duk abin da ke faruwa a matsayin tabbataccen abu. Abin da nake so ka fahimta shi ne, matarka ta shiga wani abu mai rikitarwa saboda kuskuren da ta aikata. Bayan ta nemi taimako a wajen waɗanda ba su dace ba.” Zayd ya shafa fuskarsa da tafin hannunsa. “Innalillahi! Mallam, gaskiya ban san abin da zan ce ba. Ban taɓa tsammanin abin zai kai wannan matsayin ba. Ni dai abin da nake so shi ne ta samu lafiya.” Malam ya yi murmushi kaɗan, yana ƙoƙarin kwantar masa da hankali. “Ka kwantar da hankalinka. Ba abin tashin hankali ba ne. Kada ka bari tsoro ya rinjaye ka. Allah ne Mai iko a kan komai. Babu wani aljani da zai iya yin abin da Allah bai ƙaddara ba.” Zayd ya gyada kai, amma har yanzu akwai damuwa a fuskarsa. “Amma Mallam, ya za mu yi yanzu?” “Abu na farko, kada ta sake komawa wajen waɗancan mutanen. Abu na biyu, ta dage da addu'a, istigfari da karatun Al-Qur'ani. Za mu kuma yi mata ruqya ta hanyar da ta dace..” “In shaa Allah, Mallam.” Malam ya ɗan matsa gaba. “Kuma kai ma ka kasance kusa da ita. Kada ka tsoratar da ita da wannan maganar. Tana bukatar nutsuwa da goyon bayanka a yanzu. Ka taimaka mata ta dawo kan hanya madaidaiciya. Allah Mai gafara ne, kuma ƙofar tuba a buɗe take.” Zayd ya sauke ajiyar zuciya. “Allah ya saka da alheri, Mallam. Wallahi na gode. Gaskiya tun daren jiya ban samu nutsuwa ba.” Malam ya yi murmushi. “Allah Ya sauƙaƙa. Ka dogara ga Allah, Kada ka manta cewa Shi ne mafi ikon komai.” “Ameen, Mallam.” Malam ya ɗaga hannayensa suka yi addu'a tare. Zayd yana amsa Ameen a hankali, amma hankalinsa har yanzu yana kan Seeyama da irin halin da take ciki.
Malam ya ɗan yi shiru, sannan ya miƙe ya nufi wani ƙaramin ɗaki da ke gefen falon. Zayd ya bi shi da kallo har ya shige. Bayan wasu mintuna sai ya dawo riƙe da wani ƙaramin takarda da aka rubuta wasu ayoyin Al-Qur'ani da addu'o'i a jikinta sai wata jarka. Ya dawo ya zauna, sannan ya miƙawa Zayd jarkar da takaddar. “Ga wani rubutu na ruqya. Ina so ka kai mata, ta gwada amfani da shi na tsawon kwana biyu tukuna.” Zayd ya karɓa yana duban takardar. “Yaya za ta yi amfani da shi, Mallam?” Malam ya nuna masa yadda aka tsara amfani da shi. “Za ta karanta ayoyin da addu'o'in da ke cikin takaddar sannan ta yi addu'a ga Allah Ya ba ta lafiya. Za ta iya shan Wnn ruwan ayoyin Al’Qurani ne a ciki an tsara shine a yanayin ruqya, sannan ta shafa kaɗan a jikinta. Amma ina so ta yi komai da niyyar neman lafiya daga Allah, ba wai saboda ruwan ko wani abu ba. Allah ne Mai warkarwa.” Zayd ya gyada kai. “To, in shaa Allah. Zan sanar da ita.” Malam ya ƙara da cewa: “Ku gwada wannan tsarin na kwana biyu, sannan ku sanar da ni yadda take ji. Kada ku yi gaggawa wajen yanke hukunci wanann takardar kuma tayi kokari ta dinga karantawa ko da sau daya ne a rana.” Zayd ya sake kallon takardar, sannan ya saka ta cikin aljihun shaddarsa. “Allah ya saka da alheri, na gode sosai.” “Ameen. Allah Ya kiyaye ku, Ya ba ta lafiya, Ya kuma tabbatar da ku a kan gaskiya.” “Ameen.” Sukayi sallama da malam zayd ya dauko kudi ya ajiye masa malam yace ai saidai ya dauke kudinsa zayd ya dage akan sadaka ce ba wai biyansa Yayi ba da kyar dai malam ya gamsu daga karshe. Zayd ya miƙe tsaye, ya gaishe da Malam cikin girmamawa, sannan ya nufi hanyar fita malam kuma Yayi cikin gidan domin ya je yayi masa magana da Seeyama.
Motar Zayd ta fice daga harabar gidan Malam, ya shiga babban titi. Yana tuƙi cikin nutsuwa, amma hankalinsa yana can baya, yana ta nazarin duk abubuwan da suka tattauna da Malam. Ya yi shiru, hannunsa ɗaya a kan steering, ɗayan kuma yana shafa sajensa lokaci zuwa lokaci. Seeyama kuwa tana zaune a gefensa, tun bayan fitowarsu take kallonsa a hankali. Ta lura da yadda ya yi shiru, kamar yana da wani abu a zuciyarsa. Bayan wasu mintuna sai ta kira shi a hankali. “Babe…” Zayd ya ɗan ɗago kansa ya kalleta. “Yes..?” Ta ɗan yi shiru kafin ta tambaya. “What did he tell you when I left?” Zayd bai amsa nan take ba. Ya mayar da kallonsa kan hanya, yana ci gaba da tuƙi. Bayan ɗan lokaci sai ya sauke ajiyar zuciya. “Ya ba ki magani. Zaki dinga sha da kuma shafawa a jikinki.” Seeyama ta gyara zamanta. “Really?” “Yeah. Sannan akwai wasu addu’o’i da ya bayar ki dinga yi. Ya ce ki dage da karanta Al-Qur’ani, morning and evening adhkar.” Ta gyada kai. “Okay, babe.” Zayd ya ci gaba da magana. “Seeyama, akwai wasu abubuwa kuma da nake son ki gyara a rayuwarki. Ki rage yawan sauraron wakoki. Ki mayar da hankali kan karatun Al-Qur’ani maimakon ki riƙa kashe lokacinki da music.” Seeyama ta ɗan sunkuyar da kanta. “Sannan ki rage zama ba dankwali. Ki dinga saka shi yadda ya kamata. Wannan gashin da kike ƙarawa ma, ina so ki tsaida shi.” Ta juya ta kalle shi. “The hair too?” Zayd ya ɗan kalleta. “Yes. Ina so ki gyara wannan bangaren ma. Ba wai saboda wannan matsalar kaɗai ba, ina so ki kasance kina ƙoƙarin kusantar Allah a rayuwarki gaba ɗaya.” Ya ɗan dakata sannan ya ƙara da cewa: “And please, ki tsaida sallah akan lokaci. Kada ki riƙa jinkirta ta saboda wani abu. Idan lokacin sallah ya yi, ki yi ƙoƙarin gabatar da ita.” Seeyama ta yi shiru tana sauraron sa. Zayd ya ɗan rage gudun motar saboda wata mota da ta shigo gabansu. “I’m not saying you should change overnight, Seema. But I want you to take your deen seriously. Ki fara da waɗannan abubuwan a hankali, ki dage. Kuma kada ki ɗauki wannan a matsayin wani hukunci da nake yi miki. Ina son ki gyara kanki saboda Allah.” Seeyama ta ɗan gyada kai. “Okay, babe. I’ll try my best.” Zayd ya kalleta na ɗan lokaci. “Not just trying. I want you to be serious about it. Kuma idan akwai abin da ba ki fahimta ba, ki tambaya. We can learn together.” Ta yi ɗan murmushi. “Thank you for not giving up on me.” Zayd ya yi murmushi kaɗan. “I’m your husband, Seema. I want to see you become a better person. That’s all.” Ta juya ta kalli titi ta taga, tana nazarin maganganunsa a ranta. Bayan ɗan lokaci sai ta sake kallonsa. “Babe, did he say anything else about the problem?” Zayd ya girgiza kai. “Ya ce mu fara da wannan, sannan mu ga yadda abubuwa za su kasance.” Seeyama ta gyada kai. “Okay thank you so much Nagode and I love you so much.” Zayd ya miƙa hannunsa ya rike nata. “Everything will be fine, in shaa Allah.” Ta riƙe hannunsa na ɗan lokaci. “Ameen.”
Maimakon ya wuce da Seeyama gida kai tsaye, sai kawai ya juya motar zuwa hanyar gidan Ummie. Seeyama ta lura da sauyin hanyar, sai ta kalle shi. “Babe, where are we going?” “Gidan Ummie.” Ta gyada kai kawai, ba tare da ta ƙara tambaya ba. Bayan sun isa, Zayd ya faka motar a harabar gidan. Suka fito tare, ya kulle motar sannan suka nufi cikin gidan. A lokacin babu kowa a babban falon. Shiru ne kawai ya mamaye wurin, don haka Zayd ya jagoranci Seeyama zuwa sama, har zuwa bedroom ɗin Ummie. Suna shiga suka tarar da Ummie a tsaye a gaban wardrobe, tana jera wasu kaya da mai wanki ya kawo mata gasu nan a baje akan gado tana ninke su tana sanyawa a cikin drawer. Da ta ji motsin ƙofar, sai ta ɗago kai. “Ah, Habibie kune a tafe?” Zayd ya yi murmushi. Mune Ummie ya karasa Suka gaisa kaamr yanda Suka Saba. Seeyama ma ta matso kusa da ita cikin ladabi. “Assalamu alaikum, Ummie.” “Wa alaikumus salam, Seeyama. Ya kike?” “Alhamdulillah, Ummie. Ya aiki?” “Lafiya kalau, Alhamdulillah.” Bayan sun gaisa, Seeyama ta lura da yadda Ummie ta ajiye kayan akan gado Tana gyarawa Ba tare da Ummie ta nemi taimakonta ba, sai ta matso kusa da wardrobe ɗin. “Ummie, bari in taimaka miki.” Ummie ta ɗan tsaya tana kallonta. “A’a, Seeyama. Ba komai, na kusa gamawa.” “It’s okay, Ummie. Ki bar ni in ƙarasa.” Ta faɗa cikin murmushi, sannan ta miƙa hannu ta karɓi wasu daga cikin kayan da Ummie ke riƙe da su. Ta fara ware su a hankali, tana tambayar inda ya kamata ta ajiye kowanne. Ta ninke kayan da kyau, ta jera su cikin tsari. Sannan ta ɗauki waɗanda za a rataya, tana sanya su a cikin wardrobe ɗin ɗaya bayan ɗaya. Zayd kuwa yana tsaye a gefe yana kallonsu. Ya yi murmushi ganin yadda Seeyama ta karɓi aikin ba tare da wani ƙorafi ko nuna rashin jin daɗi ba.
Ummie ta dinga kallonta a gefe, mamaki yana bayyana a fuskarta. A da, Seeyama ba ta cika nuna irin wannan sakin fuskar ba idan tana tare da ita. Wani lokacin ma sai ta ji kamar tana yi mata magana ne saboda dole kawai, ba wai saboda tana jin daɗin kasancewarta ba. Amma yau ga ta nan, ta zo da kanta, ta karɓi aikin da take yi, tana taimaka mata cikin ladabi da natsuwa. Ummie ta kalli Zayd, sannan ta sake mayar da kallonta kan Seeyama. Me ya faru da wannan yarinyar ne? A ranta ta yi tunanin ko auren Zayd ne ya gyara halayenta. Ko kuma kasancewar yanzu ta fara fahimtar yadda ake mu’amala da manya ne ya sa ta sauya. Zayd ya yi murmushi daga inda yake tsaye. “Ummie, yau kin samu mataimakiya kenan.” Ummie ta yi dariya kaɗan. “Wallahi kuwa. Da ma ina neman wanda zai taimaka min kubura da suhaila sun tafi saloon tun safe haryanzu babu su babu alamun su.” Ya yi dariya, sannan ya ƙaraso ya zauna a gefe gado. Ummie ta kasa daina kallonta. Ta lura da yadda Seeyama ke aikin cikin nutsuwa kaamr dai wata daban aka canja ba wancan seeyamar ba. Bayan wasu mintuna, Ummie ta ce: “Seeyama, kin yi ƙoƙari. Ki bar sauran, idan sun dawo sai su ƙarasa.” Seeyama ta girgiza kai a hankali. “Bari in gama wannan ma, Ummie. Ai saura kaɗan.” Ummie tayi murmushi. “To ai shikenan. Allah Yayi albarka.” “Ameen.” Zayd yana kallonsu, sai ya ɗan sunkuyar da kansa yana murmushi. Bai ce komai ba, amma ya ji daɗin yadda seeyama ta nuna wa Ummie kulawa da girmamawa. Ummie ma kuwa, duk da mamakin da take yi, ta ji daɗin ganin wannan sabon yanayin na Seeyama. A ƙarshe Seeyama ta gama jera kayan, ta rufe wardrobe ɗin sannan ta juya ga Ummie. “Na gama, Ummie.” “Allah ya miki albarka..” “Ameen, Ummie.” Amma a ranta har yanzu tana mamakin wannan sauyin na seeyama.