Free chapter 路 Read without an account

Chapter 6

by Hernarn Novels鉁嶏笍鉁嶏笍鉁嶏笍 路 BA TSANA BACE

馃挮BA TSANA BACE 馃挮





     006.......... 









  Sai wajen 9 tafita, nusy amarya Tayi kyau cikin lace fari da stones Baki da golden, Tasha make up sai xuba khamshi take itama baby Tayi kyau cikin ankon su na manyan kawaye lece Golden da stones Baki batayi makeup ba Amma tasaka lip gloss da kwalli tayi kyau matuka....bayan daurin aure angwaye suka shigo akayi halal hug da pic Dake mijin nata Dan boka ne sosai.bayan magrib aka kaita gdn ta Hadde domin mijin nata nada halii ba laifi....
 
  Tafiya suke cikin bakin dajin Wanda bakajin Komai sai kukan wasu halittu bazaka tantance tsuntsaye neh ko Karnuka ba, Zunnirah jikinta rawa yake sosae yayinda Raudah hankali kwance take tafiya har suka karaso Wani bukka Babu ko sallama suka banka cikin bukkar Raudah ce ta fara mgn "Barka babban boka Mai aeki da manyan Aljanu munkawo kukan mu wajenka Kuma Muna fatan xaka share mn hawaye. Mutumin Dake xaune cikin wasu kaxaman suturu,suma ya mamaye dukkan jikinsa cikin wata murya Mai ban tsoro ya fara mgn" sannunku bil adama make tafe da ku? Bulu Bulu wannan kawatace Kuma takamu da son Wani neh Amma ta kasa samun soyayyarhrsa shine mukeso ka iya mn wata dariya ya sheke dashi tare da dakko Wani turare ya watsa take wata Bakar aljana mai ban tsoro ta bayyana "Duduwa inaso ki Sakawa Musawweer soyayyarhr Zunnirah yaji duk Duniya ita kadai yake so Nan take tace An gama Bulu Bulu ta bace bat" Zunnirah Dan kidima har fitsari tayi ba tare da tasani ba wata dariya boka Bulu Bulu ya sheke da ita snn ya dubesu yace aekin ku ya kammala cikin in'ena Raudah tace Mai Nene Xamu bayar Boka? Wata dariya ya sheke da ita snn yace bakune xaku bayar ba.....hhhhhhh.... Mune Samu karba da kanmu Kuma a lokacin da mukaso.....hhhhhhhhhhh ku tashi ku tafi.... toh boka mun gode suka fada tare da mikewa suka fita da mugun gudu,sunyi gudu yafi karfin na 30 minutes kafin suka fito bakin titi Inda sukayi parking motar su, ba karamin tafiya sukayi ba kafin suka iso cikin gari Raudah ceh Ke tukin da kanta domin har yanxu Zunnirah a kidime take.....

  Bayan sunyi wanka sun kimtsa Raudah ta Kalli Zunnirah tare da fashewa da dariya, duka Zunnirah takai Mata tana cewa " Keh fah Baki da dama bestie ni wlh na Maida har zawo Nayi ba fitsari kawai ba, kinsan yadda na tsorata kuwa? Ta karshe tana dariyar itama dariya Tayi tana cewa hmmm ae bestie lokacin Dana fara xuwa wlh sai danayi xaxxabi saboda kidima amma shi aikin sa tamkar kiftawar ido ne lokacin mahaifiyar habeeb data matsa sai mun rabu dashi can nayi maganinta dariya Zunnirah Tayi snn tace "ki ceh siyasa take biyayyah suka Tafah tare da fashewa dariya Keh dai bari wlh kamar ta goyani idan ta Ganni " yanxu 茩awata musawweer xai Soni "insha Allahu ae aikin Bulu Bulu Babu wasa ko kadan ki dai kwantar da hankalin ki kamar kin auri musawweer kin gama murmushi Tayi snn tace dakuwa naji Dadi bestie
******* ********. ********. *******. 
  
  Musawweer sun sauka kasar Qatar tun karfe 12 Dake tun karfe 8 suka tashi, a makarantar Daya Samu koyarwa suka bashi gd Mai daki Daya da parlour da kitchen 1 da toilet 2.
Tunda yatafi kullum sai sunyi waya da Ummee da Abba, Wani lokacin harma dasu Ameer da awateef, Amma basu taba mgn da baby ba,shima Bai taba Koda tambayar taba itama tana jinsa Wani lokacin Amma Bata taba Gigi gin karbar wayar ba.... karfe ukun dare ya tashiga a matukar firgice sakamakon Wani mummnan mafarki dayayi wasu mata biyu xaune wajen Wani bakin mutum suna cewa musawweer! Musawweer! sai wata Bakar aljana datake ta dariya addu'oe kala虏 ya fara snn ya wuce bandaki ya dauro alwala kamar dai yaga wulgawar Abu Amma sai yacigaba da Addu'ah, ta cikin madubi ya hango mace Doguwa wacce, Bai taba ganin halitta Mai tsayin taba, sanye da bakin kaya, ya fito Daga bandakin ya shimfida sallaya ya fara karanta suratul Baqara cikin muryarsa Mai Dadi. yayi nisa sosae yafara Jin kamar kukan mace kasa虏 Bai sauraraba ya cigaba, kukan ne ya cigaba da karuwa har ya xamana da karfin sosoe murya Mai cike da tsoratarwa 
haka musawweer ya cigaba da kartunsa Babu alamun tsoro a tare dashi tunda yafara har ya kammala suratul Baqara ihun Yana tashi Dan haka sai yajuya.....Bai sauraraba har sai da ya Dena Jin ihun snn ya hau gado ya kwanta bayan ya tofe dakin da Addu'ah Kuma ya bar kira'ar sheikh Sudais a wayarsa.






NIGERIA




 Baby kenan kin kusa Dena mun wnn Shan kamshin,da zarar an daura xan kawo karshe sa yakarasa mgn in a low voice Bata kulashi ba tana dai kallon gefe sai a hankali yace "baby....kina wahad Dani dayawa"sai tadan kallesa ni ceh neke wahallar dakai Yaya" ta fada tana nuna kanta Bata Rai yayi snn yace bafa nasan sunan Nan wlh murmushi Tayi Bata ce komai ba,ya koma ya jingina da kujerar tare da cewa " September su Aisha zasuyi Graduation inaso akasa bikin namu xuwa December koh? Ummm wnn mgnr ku ce ta manya ae" murmushi yayi snn yace" eh Amma nafiso kema ki Fadi opinion dinki koh amarya? hannu tasa ta rufe fuskarta tana dariya "baby" ya kira sunanta cikin wata murya Bata iya ta am'sa ba yacigaba" Baby INA SONKI INA SONKI SOSOE HAR BANSAN ADADIBA" Baby Idan har na sameki xan nuna Miki soyayyarh da kauna,xan kulada Keh fiye da yadda xan kula da kaina insha,Insha Allahu baby baxa kiyi Kuka a gdnaba xan Baki duk wata kulawar da kariya xan riritaki tamkar kwa'i idan har na xama mijinki baby baxa kiyi Kuka da ni ba Insha Allahu" murmushi Tayi har haqwaranta suka bayyana tana kallon gefe tace " Yaya kullun mgnrka fah kenan" hmmm baby bakisan yadda nakejin ki a Raina ba koh? Dakin sani dabaza ki Fadi hakaba? Ni kadai nasan irin sa'ar da Nayi na samun ki a matsayin matar aure ta tareshi da sauri " yaayah ae ba Kai kadai kayi sa'ar ba harda ni,nima Nayi sa'ar samunka Kuma Ina godewa Allah akan Hakan"Koda kinyi sa'a baby ni nafiki sa'a,kina da ilimi na tutiya gaki da hankali da tarbiyya snn kunya kinsan baby inason mace Mai kunya Kuma kina da ita, shiyasa nake sanki sosae Kuma fah kinada kyau kinsan haka koh baby? A'a nidai ban saniba dariya yayi snn yace "kina da kyau mn baby, number Daya ma' Kuma fah duk da wnn qualifies din naki kikace ni kikeso ni kika zaba matsayi miji nida bani da haddar ko izu 20...Kinga kuwa doleh nace Nayi sa'a "yaayah nifah bawai doleh sai mahaddaci xan aura ba,Kuma kasan Haka.Da kakeh cewa Kai ba mahaddaci bane ae ba jahili bane Kai koh? kana da iliminka Kuma nima Mai SSCE na Ha蓷a kaina da Mai 3 degree ne Kuma Doctor.. bafah Kai kadai kayi sa'ar ba......hakane baby Amma abun da zaki duba mahaddata nawa ne da masu kudi harma da masu Mulki kikaqi kika xabeni? Kai ma doctors nawa da nurses nawa ka tsallake ka zabo ni? Dariya yayi tare da cewa Babu adadi gsky....sai dai Basu cika qualities din dakikeh dasu ba babynah ya karshe mgnr Yana kallonta " nidai yaayah abar mgnr kawai toh an barta Yaa sayyada dariya sukayi su duka....

 


 ******** ********* ******** ******




Haka rayuwa ta cigaba da gudana,komai Yana tafiya Daidai cikin hukuncin Ubangiji musawweer nacan kasar Qatar Yana aekin sa cikin Nasara Yana Kuma samun Alkharai da dama,Yana da Wani fili Wanda ya mallaka tuntuni, ummee tasan dashi hakama Abba Dan haka ya turo kudi masu kauri aka fara Masa aekin gdn,Kuma cikin iKon Allah aekin ya fara tafiya Dake harda masallaci xa'ayi a jikin gdn.






 ******* *********. *********.   




  Tun lokacin dasuka je wajen boka bulu bulu take Tsanmanin kira Daga Musawweer Amma shiru,har sai ta gaxa tayiwa Raudah mgn Amma tace tadan Kara lokacin idan Bai nemetaba sai su koma wajen bokan' toh haka dai ta sake shafe sati 2 cikin jiran Tsanmanin Amma Babu Wani sauyi Dan Haka ta kirasa cikin rashin sa'a wayar Bata shiga ba tashiga damuwa sosai Dan har sai da ta kira Ladeefah Nan take shaida mata Baya kasar,taso Ladeefahn ta bata numbersa na Qatar din' Amma tace mata ya mata gargadi Mai kyau akan Hakan 
haka dai ta hakura Badan taso ba.
    
    Ta bangaren baby ma komai Yana tafiya dai虏 tana cikin farin ciki,ta kanje karantarwa makarantar lokaci xuwa lokaci ko idan Abubuwa sunsha kan Abba soyayyarhta da Hafeez kuwa Gaba Gaba takeyi, sosai suka sake shakuwa duk weekends sai yaxo kasancewar yanxu yasamu transfer an maidashi Abuja.tama Manta da Wani Aboon ko rayuwarsa,idan ma ba taji suna waya da su ummee ba, Bata tunawa dashi, Kuma har yanxu Bata taba cewa a Bata waya su gaisa ba, shima Kuma haka. Yanxu Bai wuce saura 3 Months su Aisha su kammala karatun suba Daga Kuma sun kammala za'a tsayar da ranar auren su.
 




*******. *********. *******. ******




     Cikin haka azumi ya karato akashiga shirye-shirye sosai,na zakkah da kayan azumi Dake duk shekara ana abincin axumi kwana 30 koh 29 ga mabuqata,an fara shirye-shiryen dawuri wnn karon kasancewar ummee xata tafi Ummra ita da baby duk da sai axumi ya raba zasu tafi Amma Dai tafiso komai ya shiga kan tsari.....gab da axumi Abba ya tafi nasa ummrar ya dawo. Haka aka fara axumi aeki ya Runcabe ta ko wane bangare Abba Yana tafsirin Ramadan a masallacin kofar gd, maxa bayan Sallar la'asar, mata Kuma bayan an idar da magrib kafin lokacin Sallar tarawee,Ameer ne Yake Jan Sallar tarawee.... sai gdn ya kasance kowa ya shiga busy sosae.



   Axumi sha Daya visern su ummee ya fito Sha 14 ga wata zasu tashi Dan haka shirye虏 ya Kara kankama.
  
 14 ga watan Ramadan Su baby suka sauka kasa Mai tsarki Ummrar suka fara Yi snn suka shiga madinah....itadai Taga Ummee Tana waya Amma Bata San dawaye Tayi wayar ba, kofar dakin Hotel din nasu taji ana knocking ta mike da nufin dubawa tunaninta koh matar Da dakinta Keh gikin nasu neh Dan tare suke xuwa masjid Sallar Isha'e da ummee.......Hernarn Muhammad鉁嶏笍鉁嶏笍鉁嶏笍

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol