Free chapter · Read without an account

6

by Halima Zakariyya Haruna · KAYAR RUWA

"Ƴaƴan da aka ba ki!"
Kalmar ta ƙarshe ta daki ƙirjina. Rumana da Atika, gaba ɗayansu ba su wuce shekaru takwas ba, yaran ba su kunya ga rashin ji, shi yasa jininsu ya zo ɗaya, ko iyayensu kuka su ke da halinsu, shi ne ni kuma yanzu zai ce zai ɗauko min su in riƙe a wannan yanayin da danginsa suka juya min baya?.

Salon wata rana su fusatani in sauke musu fushina in ƙara baƙin jini. Dama ya lafiyar kura bare an taɓota.
Na san dole akwai wata a ƙasa, sai dai ina roƙon Allah ya ɗora ni a kansu, ya kuma sauya duk wata baƙar manufa da aka ƙulla akan dawo da su gidana.

Murmushi na ƙaƙalo, don kar ma yace bana ƙaunar ƴaƴan uwansa, tunda ga shi nan har an fara tsegunta masa ina wulaƙanta su. Kuma saboda shima dama a yanzu ba ta ni yake ba, sai ya hau kan maganar ya zauna, halin da ya san ba nawa ba ne.
"Ai kuwa dai muna godiya matuƙa, Allah taya mu ruƙo, na ji daɗi sosai, ko ba komai ma rage kewa".

Na faɗa ina nuna jin daɗin da bai kai har zuci ba, domin cike na ke da fargabar rayuwarmu tare da yaran.
Bai ce da ni komai ba, na sauke ajiyar zuciya na fita daga ɗakin. Ɗakina na koma na canja kaya, dama a falo na bar jakata da wayata, kuma da zuwan nawa na tarar da kiran Ummani.

Sai na ji gabana ya faɗi ganin miscalls har guda biyar, take na fara tunanin anya lafiya, don bata taɓa min miscalls irin haka ba. Ummani duk inda ta kira waya sau biyu ba'a ɗaga ba haƙura take yi, sai tace bata san uzurin mutum ba, idan ya gani zai biyo baya.

Zama na yi kan kujera jiki na rawa na bi bayan kiran, sai dai ko da kiran ya tafi a lokacin kamfani ke shaida min bani da kati. 
Ƙaramin tsaki na yi na ƙorafi, tunawa fa ashe tun shekeranjiya muna waya da matar Yashaik katin ya ƙare.

Ina zaunen Hubbi ya fito.
Kallonsa da na yi ɓacin ran hana ni zuwa makarantar da ya yi ya ƙaru a raina. Na kawar kawai na kasa share shi, saboda ina so ya bani aron wayarsa. Cikin shakkar masa magana nace,"Hubbi don Allah aron wayarka in kira Ummani".

Yana zama kan kujera yace min,"Me ya sami taki?".

"Babu kati".

Zai miƙo min wayarsa sai kuma ya fasa yace,"Bari in saka miki katin, wanne layin?".

"Airtel".

Cikin wasu ƴan sakanni sai ga saƙon katin ɗari biyar ya shigo, na yi masa godiya sosai.
Na danna lambar Ummani na kira, sai dai haka ta gama ringinga har sau biyu ba'a ɗaga ba. 
Take gabana ya tsananta faɗuwa, ban san lokacin da nayi mazauni a gefen Hubbi ba, ina damƙar gefen rigarsa.

"Lafiya?".

A ruɗe kamar zanyi kuka nace masa,"Bata ɗaga wayar ba ne, kuma ka ga miscall ɗinta biyar na tarar".

Ganin yadda jikina ya ɗauki ɓari ya karɓi wayar daga hannuna, a ƙwayar idonsa na hangi guntun tausayina. Yana ƙoƙarin ƙara kiran, sai ga kiran Hindatu na shigowa. 
Ya ɗaga ya miƙo min, amma sai na kasa karɓa, don ban san me kunnuwana za su jiye min ba.

Shi ya amsa kiran, sai dai maimakon muryar Hindatu na ji muryar Ummani na cewa,"Sa'ida ina hanya ne shiyasa ban ɗaga ba, kuma na shigo gidan babu kati a wayar, shine na ari ta Hindatu".

Wata wawiyar ajiyar zuciya na sauke ina hamdala ga ubangiji. Shi kuma Hubbi su ka shiga gaisawa da ita.  
Abinda bai saba ba, sai na ga ya sake da ita, yana labarta mata rikicewar da na yi akan rashin ɗaga kiran nata.

Ina muryar Ummani dai na amsa shi cike da surukurtaka. Ya miƙo min wayar yana murmushin leɓe tare da tsokanata, wanda hakan ni kuma yasa raina sanyi, domin rabona da ganin annuri a fuskarsa har na manta, balle kuma murmushi irin haka, murmushin da ya bayyana min har yanzu akwai tsiron soyayyata a zuciyarsa.

Cikin wani irin jin daɗi mara misaltuwa mu ke waya da mahaifiyata. Kira kawai ta yi ta ji ya muke. Ashe ko da ta bar min miscalls da yawa, ba ita ta yi kiran ba, Yahanasu ta bawa.
Ita kuma dama bata iya kiran hankali ba, irin kiran da idan mutum ya zo ya tarar da miscalls ne dole sai gabansa ya faɗi, ya tsammaci faruwar wani mummunan abun, kusan kullum sai Abba ya yi mata faɗa akan hakan. 

Muna wayar da uwata sai na ji duk damuwata ta gushe, tana ta min hira mai daɗi, kamar ta san a cikin kaɗaici na ke.
Ni kuma ba ni da wani labari da zan bata wanda zai sanyata farin ciki. Can na ji muryarta ta fara sauyawa, wadda ke shaida min tana ƙoƙarin gano cewar ina cikin matsala ne.

Sai na yi saurin gusar da tunanin hakan a ranta, nima na bata labarin su Atika da aka bani, ina shaida mata cewar yau za a kawo su. Aikuwa farin ciki kamar ta yi me, ta ji min daɗi sosai, tana ta yi wa su Yaya godiya da sa albarka.

Tace na bawa Hubbi shima ta yi masa murna, na ba shi wayar suka ƙara gaisawa a karo na biyu, nan ta yi masa murna da addu'a, na ga jin daɗin hakan ɓaro ɓaro a fuskar da yanayinsa, sai zuba mata godiya yake yi kuwa.

Ya dawo min da wayar, ni kuma ta yi min nasiha sosai a game da ruƙon yaran.
Sai na ji ta koma cewa,"Sa'ida wannan kyauta ce daga Allah ya baki ta silar wasu, ki riƙe Ƴaƴan da aka baki da amana, kar ki cutar da su, yarda da amana kan cewar zaki kula da su, yasa har Iyayen yaran suka baku. Duk da cewar sun yi ne domin Ɗan uwansu, amma duk da haka, suna da yaƙinin Matarsa mutuniyar arziƙi ce, shi yasa su ka ba shi."

Nasihohinta su ka karayar min da zuciya sosai, tun ma in ji tana ambaton Ƴaƴanki. Wallah har muka gama wayar ban ji tana sagar min gwiwa da maganar da ake cewa, Ɗan Ruƙo na da wuyar sha'ani ba.
Kawai nuna min ma take yara nawa ne, ni na haifesu, wanda hakan yasa na dinga jin wani irin yanayi na tsarga min a dukka jikina, haka zuciyata ta dinga motsawa, ban san ma ta yadda zan kwatanta abin da na ke ji ba a tare da ni.

Hawaye na ji na sakko min, nasiharta ta ƙarshe abin da tace min shi ne.

"Ki so su tamkar ke kika yi naƙudarsu, kar ki cutar da su, kar ki dinƙa musu kallon ba ke kika haife su ba. Ki yi haƙuri da duk halinsu, don ko Ɗan da ka haifa sai ka yi haƙuri da shi, Allah ya tayaki ruƙo ya albarkaci zuri'a, idan kina da rabo kema Allah ya kawo lokacin muna raye".

Da haka muka yi sallama da ita, kuka sosai na saki, sama sama Hubbi ke lallashina, da ike ya ji duk wayar tamu.
Haka na miƙe ina jina wani iri, na shiga aikin tarbar Ƴaƴana, har na hau sama zan fara gyara musu ɗakinsu, sai kuma na ga dai gwara in fara ɗora abincin, don ban san ko gayya za su yo ba. Saboda haka na sakko na shiga kitchen ɗin ƙasa.

Ba ni na gama girki ba sai azahar, a hakan ma fa wai na ɗora da wuri. To da yake dashishi ne yafi dambu wahala shiyasa na jima. 
Ina kitchen ɗin ne na ke jiyo kamar tashin hayaniya daga falo, na wanke hannuna na fita cikin sauri.

Na tarar da su Anty Aisha tsaye a parlo. Da fara'ata na ke gaisheta, ta amsa min babu yabo babu fallasa. 
Na buɗewa su Rumana hannu ina murmushi, jin daɗi shimfiɗe a fuskata. Jikina su ka shige ina rungume su tsam. Ba tare da sani ba na ji saukar hawaye a kumatuna, na janye su a jikina muna gaisawa da su, yaran suma sai murna su ke yi, dama in dai yara ne a Familyn Mai Kalwa suna son zuwan gidan Baba Ƙarami.

Anty Aisha tace,"Ce na ke gidan ma ba kowa, da mu ke ta sallama ba'a amsa ba, wannan ai sai a shigo ayi sata ba ki san anyi ba".

Shirunta ya haɗe da sakkowar Yaya daga saman bene, tana watsan wani kallon banza tace,"Da kina ciki amma kina jin mutane kika kasa fitowa".

"Wallahi Yaya ban ji ba, da yake na kunna littafi a waya ne ina sauraro. Sannunku da zuwa".

"Yauwa". 
Ta amsa a daƙile kafin ta ƙara cewa,"Baban yaran nan yace ɗakinsu na sama, na hau da kayansu kuma na ga ba wani ɗaki gyararre".

To Allah masanin dalilin da yasa na ke jin mugun tsoro da shakkar mutanen nan.
Cikin fargaba nace,"Ehh ɗakin kusa da nawa ne na su, aikin da na ke yi ne ma yasa ban samu na gyara musun ba. Da ya ke za'a kawo musu gado, to su ma masu kawowar shiru na ga basu zo ba".

Anty Aisha tace,"Gyara ya hau kanmu kenan, to bara mu je mu gyara musu...".

Na yi saurin tarar numfashinta da cewa,"Haba Anty Aisha ban isa ba, saboda su wallahi nace gwara in gama dafa abincin. Amma ai na gama, yanzu zan je in gyara musu".

Ta wuce ni tana faɗin,"A'a gwara dai ki yi abin da kika saba, ki dafa ki ci ki kwanta, ki kasayar. Ni ai ba zan iya tafiya in bar su haka ba, ban ga wurin da kwanansu ba, ba zan samu sukuni ba sam. Ba da sauƙi na yi naƙudar ba. A haka ma don dai Nazifi ne, ai wallahi da da Ƴata zan juya. Ka yi sadaukarwar abinda ka haifa sukuntum guda, kuma tun ba a je ko ina ba, an nuna maka kulawa zata yi wuya."

Ta numfasa kamar ba zata ƙara faɗin komai ba. Sai kuma tace,"Ko da ya ke sanin ciwon Ɗa sai wanda ya haifa. Yaya ni na yi nan".

Zuciyata ta matse sosai da zafi, na mayar da ruwan hawayen da ya cika idona, ban iya cewa komai ba. Yaya ta bi bayanta su ka haye saman su ka bar ni tsaye da yaran. 
Na maida kallona ga yaran da ke a gabana, na dafa kafaɗunsu ina ƙaƙalo murmushi nace,"Ƴan albarka in zuba mu ku abinci?".

Atika ce tace,"Matar Baba Ƙarami me kika dafa?".

Na kama kumatunta ina cewa,"Abu mai daɗi, har sai kunnenki ya yi rawa".

Su ka ɗanyi dariya, Rumana na cewa,"Ferfesun ka ji?".

Kai na gyaɗa mata, nace,"Ehh har da shi, sai kuma dashishi".

Rumana na tsalle tace,"Irin wanda Ummaa ke yi?".

Na ɗaga mata kai tabbacin haka. Duk ɗin su suka kama murna, ina riƙe da hannayensu muka wuce kitchen. A tray na zuba musu na sanyo musu ferfesun naman kazar a bowl, su ka taya ni ɗauko wasu muka fito, nan kan carpet na ajiye musu, su ka zauna su ka fara ci, ni kuma na juya kitchen ɗin don zubowa su Yaya na su.

Kiran Hubbi ya shigo wayata, na ɗaga ya ke shaida min ga masu furnitures ɗin nan sun zo. 
Abin da na ke na bari, na fita na hau saman na shaidawa su Yaya. Sai sannan na ke ƙara ganin ashe ma ba su kaɗai ba ne, har da na su baƙin wanda su ka zo da su su yi musu gyaran.

Cikin su biyun dai babu wadda ta tanka min, bayan waɗancan da su ka gaishe ni.
Na juyo na sakko ina faɗawa mai gadi yay wa ma'aikatan iso. Ai dai na fita haƙƙinsu tun da na sanar musu za'a shigo.

Ina ɗakin Hubbi na jiyo muryar Yaya na kwakwazon faɗa,"Mene haka na ke ganinku zaune a ƙasa kamar wasu almajirai."

Ta yi shiru. Sannan ta ci gaba. "Don me Nazifin ya siyo wancan dining ɗin ya ajiye, ko dama na kwalliya ne? Kai ku tashi ku koma can ku ci abinciku, kar a ƙara baku abinci ace ku zauna kan kafet ku ci. Ba baƙi ba ne ku, nan gidanku ne gidan Babanku, ku yi yanda ranku ke so, yanda ku ka ga dama, kar ku ji shakkar yin komai, duk abin da ku ke so ku yi magana da Babanku, idan Antyn ta yi muku wani mugun abun ku dinga faɗa masa kun ji ko".

Anty Aisha ta ɗora da faɗin,"Umm ni dai Yaya ban da kin ce, da wallahi yaran nan ba zasu zauna ba. Ji fa don Allah yanda aka barsu su kaɗai a falo kamar wasu marayu, wallahi ko baƙo aka yi sai ya ce ƴaƴan ruƙo ne bana gida ba, don an banbamta ƙiri ƙiri. To ni dai har ga Allah ina ganin wani canji da ban gamsu da shi ba, zan zo in ɗauke yarinyata, ba zan cutar da kaina ba akan yiwa ƙanina kara".

Da babbar murya Yaya ta ƙwala min kira, kamar wadda aka hankaɗo daga ɗakin, sai ga ni na fito jiki sai ɓari ya ke yi.
Inda zaku ga yadda na ke ɓarin jiki na tsoron mutanen nan, sai kun zage ni ciki da bai.

Na dabarbarce ina ce mata,"Yaya kun sauko, ga abincin...".

"Ke dilla can dakata banza mara mutunci, ba yunwatattu ba ne mu, da fari ma in tambaye ki, nan gidan waye?".

Kaina a ƙasa murya na sarƙewa nace,"Gidan aurena".

Ta yi wani makirin murmushi da sake cewa,"To gyara zancenki mara kunya fitsararriya. Ko yanzu ba sai anjima ba, kina iya barin gidan nan ki tafi a fanko, dan haka nan gidan Nazifi ne, Nazifi kuma ƙanina ne, ba ƴan uba mu ka haɗa ba, uwa ɗaya uba ɗaya tafi gaban wasa, duk abinda yake mallakina, yana da iko da shi, kamar yadda duk mallakinsa ina da iko da shi. Soyayyar da mu ke yi masa da tausayinsa, yasa mu ka ɗauki Ƴaƴanmu mu ka ba shi halak malak."

Ta nuna inda Yaran ke zaune, sannan ta ɗora da cewa.
"Wannan yaran da kike gani ba bare ba ne yanzu, ba ki da ikon kallonsu ki ce nan ba gidan ubansu ba ne, balle ki yi musu iyaka da shi. Yanzu Nazifi ne uwarsu ubansu, ko a yau Nazifi ya faɗi ya mutu sun zama magadansa. Kin ga kuwa sun fi ƙarfin ki wulaƙanta su."

Ta watsa min wata harara, wadda ke nuna tsantsar tsanata a tare da ita. 
Da yatsanta manuniya take nuna ni, tace.
"Sa'ida ba marayu ba ne Yaran nan, ba Ƴaƴan kishiya ba ne, ba kuma Ƴaƴan tsintuwa ba ne, ba alfarma aka nema aka ba da su ba. Ko da kika ganki matar gida, ba wai ke aka bawa su ba, mai gidan aka bawa, don haka ki tsaya iyaka matsayinki".

To me zan ce? Banda baki wallahi. Kuma kun san mara baki cutarsa ake yi. 
Sannan da ace an min rainon raina na gaba da ni, da tabbas zan buɗe baki na yi fitsara daidai gwargwadon ikona. To itama rashin kunyar ban iyata ba.
Faɗa kuwa dama ba na wa ba ne, yanzu ina buɗe baki da zummar in rama kuka ne zai fito.
Saboda haka da na lura take-takensu na ayi tashin hankali ne, sai na ja baki ban ce musu kanzil ba. 

Don haƙurin ma idan na bayar zai iya zama wata rigimar, ƙarshe ma ƙanin na su ya dawo, su haɗa masa ƙarya da gaskiya su ce na zage su.
Shima nan zai juye min nasa rashin mutuncin.

Idona ya sauka akan Yaran, suna tashi daga inda su ke zaune ɗin, suka bi bayan budurwar da Yaya tasa ta kwashe abincin nasu ta kai musu kan dining. Can su ka ci gaba da cin abincinsu. Su kuma suka koma sama don ƙarasa gyara ɗakin yaran.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol