Free chapter 路 Read without an account

Page 2

by Khadija Haruna 路 Nurul kalb

馃挒馃挒馃挒馃挒馃挒


bismillahir rahamanirrahim 

茦arar agogon 茩ararrawa da ke gefen gadonta ce ta tashe Haleesa daga barcin da ta yi fama da shi. Ta bu蓷e idanunta a hankali, tana kallon agogon kafin ta mi茩a hannu ta kashe shi. Duk da cewa jikinta yana bu茩atar 茩arin hutu, ba ta da lokacin 蓳atawa. A yau ma aikinta yana jiranta.

Ta sauka daga kan gadon, ta nufi ban蓷aki. Bayan ta yi wanka, ta shirya cikin kayan aikin soja kamar yadda ta saba. Ta gyara uniform 蓷inta sosai, ta 蓷aure takalmanta, sannan ta tsaya a gaban madubi tana kallon kanta.

Kamar kullum, Haleesa ta yi kyau cikin uniform 蓷in. Ta 蓷auki turarenta mai tsada ta fesa ka蓷an a jikinta, sannan ta 蓷auki wayarta da sauran kayanta. Ta yi 茩o茩arin ha蓷a fuskarta da murmushi, amma tunanin Melissa ya sake fa蓷o mata a rai.

Ta girgiza kai a hankali kamar tana 茩o茩arin korar tunanin, sannan ta nufi 茩ofar fita.

Tun daga bakin 茩ofar 蓷akinta ta hango Mommy da 茩aninta Yusuf zaune a 蓷akin cin abinci suna karin kumallo. Yusuf kuwa yana sanye da uniform 蓷in makarantarsa, jakarsa na ajiye kusa da kujerarsa.

Haleesa ta fara saukowa daga matakalar bene a hankali. Da ta isa 茩asa, sai ta nufi wajen Mommy.

"Assalamu alaikum, Mommy. Ina kwana?"

"Wa alaikumus salam, Haleesa. Lafiya lau, kin tashi?"

"Lafiya lau, Mommy. Ya kika kwana?"

"Alhamdulillah. Amma ke fa? Na lura kamar ba ki samu isasshen barci ba."

Haleesa ta 蓷an yi murmushi. "Ina lafiya, Mommy. Kawai na 蓷an gaji ne."

Ta sunkuya ta sumbaci goshin Mommy cikin girmamawa, sannan ta ja kujera ta zauna.

Yusuf yana ta kallonta, sai ta lura da yadda ya yi shiru fiye da yadda ya saba.

"Yusuf, kai kuwa yau ka yi shiru. Ko dai ka dai naimun magana ne ?

Ya 蓷ago kansa yana murmushi. "Ai ke ce kika zo da fuskarki kamar kwamanda. Wa zai kuskura ya yi magana?"

Haleesa ta fashe da dariya.

"Da gaske ?

adinga dagewa a makaranta banda wasa 

"Na ji, Madam Lieutenant!"

Mommy ta girgiza kai tana murmushi 

Haleesa ta 蓷an ci abincinta tana sauraron hirar Mommy da Yusuf. Duk da cewa tana 茩o茩arin nuna walwala, akwai wani abu a cikin zuciyarta da ba zai bari ta manta da abin da ya faru da Melissa ba. Duk lokacin da ta tuna da ita, sai wani irin nauyi ya sauka a kirjinta.

Mommy ta lura da sauyin fuskarta.

"Haleesa, 'yata, ki kula da kanki. Na san aikinki yana da muhimmanci, amma kada ki manta cewa ke ma mutum ce. Kina bu茩atar hutu da kulawa."

Haleesa ta 蓷ago ta kalli mahaifiyarta.

"In sha Allah, Mommy. Zan kula da kaina."

Bayan ta gama karin kumallo, ta mi茩e tsaye ta 蓷auki kayanta.

"Zan tafi yanzu, Mommy."

"Allah ya kiyaye ki, 'yata. Allah ya tsare ki daga dukkan sharri."

"Amin. Na gode, Mommy."

Ta juya ga Yusuf.

"Ka kula da kanka, 茩aramin soja."

Yusuf ya yi mata sallama da hannunsa. "Sai kin dawo, Yaya!"

Haleesa ta yi murmushi kafin ta fice daga gidan.

Ba da da蓷ewa ba ta isa ofishin aikinta. Da shigarta, sai ta lura da yadda kowa ya yi shiru. Mutuwar Melissa ta bar wani gibi a cikin zukatan ma'aikatan da suka san ta. Wasu suna zaune a ofisoshinsu, wasu kuma suna tattauna abin da ya faru a jiya.

Haleesa ba ta tsaya yin doguwar hira da kowa ba. Ta nufi ofishinta kai tsaye, ta ajiye kayanta, sannan ta zauna a kujerarta.

Ta 蓷auki wayar ofishin ta kira 蓷aya daga cikin jami'an da ke 茩ar茩ashinta.

"Ku kawo min wa蓷ancan mutanen da muka kama a aikin jiya. Ina so a fito da su 蓷aya bayan 蓷aya domin in yi musu tambayoyi."

"Yes, ma'am."

Ta ajiye wayar, ta bu蓷e wasu takardu da ke gabanta. Bayan wasu mintuna, aka shigo da wa蓷anda aka kama.

Haleesa ta 蓷ago kai daga kan takardunta. fuskarta a hade . Ta kalli mutanen 蓷aya bayan 蓷aya, sannan ta yi magana cikin murya mai kauri.

"Ku zauna. Ina son ku fahimci cewa ba zan 蓳ata lokaci ba. Akwai tambayoyin da nake son ku amsa, kuma ina bu茩atar gaskiya daga gare ku."

Ta 蓷an dakata, tana kallon fuskokinsu.

"Abin da ya faru a dajin jiya ba 茩aramin abu ba ne. An rasa rayuka, kuma ina da dalilin da ya sa nake son sanin wanda ke bayan wannan harin. Don haka, ku fara magana. Wa ya aiko ku? Kuma mene ne ainihin manufarku?"

Mutanen suka yi shiru, babu wanda ya bu蓷e baki.

Haleesa ta jingina da kujerarta, idanunta a kansu.

"Na ga kamar kun manta cewa ba ni da lokacin wasa. Zan tambaye ku sau 蓷aya ne kawai. Ku ba ni bayanan da nake bu茩ata."

A wannan lokacin, Haleesa ba ta zama matar da ta yi kuka saboda rashin 茩awarta ba. Ta koma jami'ar soja mai tsauri, wadda ta san aikinta kuma ba ta yarda a raina mata hankali.

Amma a can cikin zuciyarta, har yanzu akwai sunan Melissa.


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol