Free chapter · Read without an account

Page 4

by Khadija Haruna · Nurul kalb

💞💞💞💞

bismillahir rahamanirrahim 

wacece haleesa

Wasu soyayyar sukan fara ne cikin farin ciki, wasu kuma su fara ne a cikin yanayin da ba wanda zai taɓa zaton za su kai ga wani abu mai girma. Amma akwai wasu soyayyar da tun daga farkonsu ake rubuta musu ƙaddarar da ba za ta kasance mai sauƙi ba.

Irin wannan soyayyar ce ta haÉ—a Sarah Williams da wani matashi É—an asalin Dubai, wanda daga baya ya zama mahaifin Lieutenant Haleesa Rahman.

Sarah Williams kyakkyawar budurwa ce 'yar asalin Æ™asar Amurka.  inda ta taso Æ™arÆ™ashin kulawar iyayenta. Mahaifinta mutum ne mai tsauri, mai son a bi umarninsa ba tare da musu ba, 

Sarah ita ce babbar 'ya a gidan. Tana da Æ™anne biyu; Emily, wadda take Æ™anwarta mace, da kuma Daniel, Æ™aninta namiji. Dukansu suna Æ™aunar Sarah, musamman saboda yadda take kula da su. Tun suna Æ™anana take taimaka wa mahaifiyarta wajen kula da su, 

Sarah ta kasance mai fara'a, nutsuwa da kuma son rayuwa. Ba ta cika shiga rigima ba, kuma ba ta son abin da zai sa iyayenta su shiga damuwa. Amma duk da haka, akwai wani abu da ba ta taɓa tunanin zai faru da ita ba: soyayya da mutumin da iyayenta ba za su taɓa amincewa da shi ba.

Wata rana da yamma, Sarah ta fita domin shakatawa. Ta kasance tana son zuwa wani kyakkyawan wurin shakatawa da ke kusa da inda take zama. Wurin yana da bishiyoyi masu inuwa, furanni iri-iri, kujerun zama da kuma ƙaramin tafkin ruwa wanda ke ƙara wa wajen kyau.

A wannan ranar tana sanye da wata doguwar riga mai launin haske, gashinta kuwa ta bar shi a buÉ—e. Ta zauna a wata kujera, tana kallon mutane da suke wucewa da waÉ—anda suke zaune suna tattaunawa.

Bayan É—an lokaci, wani matashi ya shigo wurin.

Dogone, mai kamala, fuskarsa cike da nutsuwa. Yana sanye da kaya masu kyau, hannunsa riƙe da wayarsa. Ya duba wurin kamar yana neman inda zai zauna, daga bisani ya hango wata kujera kusa da Sarah.

Ya matso a hankali.

"Excuse me, is anyone sitting here?" ya tambaya cikin Turanci.

Sarah ta É—ago kai daga wayarta.

"No, it's free."

"Thank you."

Ya zauna, sannan ya ajiye wayarsa a gefe. Sarah ta koma kallon nata, shi kuma ya buɗe wata takarda da yake riƙe da ita.

Sun yi shiru na ɗan lokaci, har sai wani ɗan ƙaramin yaro da ke wasa kusa da su ya yi tuntuɓe. Sarah ta yi murmushi, tana kallonsa yayin da mahaifiyarsa ta taimaka masa ya tashi.

Matashin ma ya lura da hakan.

"Children are always full of energy," ya faÉ—a cikin murmushi.

Sarah ta juya ta kalle shi.

"Especially when they're happy."

Daga nan sai suka fara tattaunawa. Da farko zancen ya kasance na yau da kullum, amma daga baya suka fara tambayar juna inda suka fito da abin da ya kawo su wurin.

Sarah ta bayyana masa cewa ita Ba’amurkiya ce.

Shi kuma ya gaya mata cewa daga Dubai yake.

"Dubai?" Sarah ta maimaita, tana É—an buÉ—e ido.

"Yes."

"I've heard a lot about Dubai. It's a beautiful place."

Ya yi murmushi.

"It is. Have you ever been there?"

"No, not yet."

"Maybe one day you will."

Sarah ta yi murmushi, ba tare da ta san cewa wata rana za ta rayu a cikin wannan birni ba.

Tattaunawarsu ta yi daÉ—i. Sun yi magana har lokacin da rana ta fara faÉ—uwa. Kafin su rabu, suka yi musayar lambobin waya.

A wannan lokacin, babu ɗayansu da ya ɗauki haɗuwarsu a matsayin wani abu mai girma. Amma kamar yadda rayuwa take, wasu lokuta ƙaddara kan fara aiki ne ta hanyar haɗa mutane a wuraren da ba su taɓa tsammanin za su haɗu ba.

Bayan wannan rana, suka fara magana ta waya.

Da farko, saƙonni ne kawai. Daga baya suka koma kiran waya, har suka fara shirya yadda za su riƙa haɗuwa.

Matashin ya kasance mai kula da Sarah. Idan sun haɗu, yana ba ta cikakkiyar kulawa. Ba ya son ya yi mata alƙawarin da ba zai iya cikawa ba, kuma ba ya son ya ɓoye mata abubuwan da suka shafi rayuwarsa.

Sarah kuwa ta fara jin daÉ—in kasancewarsa.

Wani lokaci idan ta dawo daga aiki ko kuma daga fita, tana samun saƙonsa yana tambayar ko ta dawo lafiya. Idan ya kira ta, sai ta ji kamar duk gajiyar ranar ta ragu.

A hankali, ta fara fahimtar cewa ba wai kawai suna jin daÉ—in tattaunawa ba ne. Zuciyarta ta fara karkata gare shi.

Wata rana suna zaune a wani gidan cin abinci. Sarah tana ta ba shi labarin ƙannenta, tana dariya yayin da take magana kan yadda Daniel yake son takura mata.

Matashin yana sauraron ta, yana murmushi.

"You're very close to your family," ya faÉ—a.

"Of course. They're everything to me."

Ya gyara zamansa.

"That's good. Family is important."

Sarah ta kalle shi.

"What about yours?"

Ya yi shiru na É—an lokaci, sannan ya fara ba ta labarin danginsa da ke Dubai.

Ya gaya mata cewa yana da iyaye, da kuma irin yadda suka taso da shi. Ya kuma bayyana mata cewa iyalinsa suna da dukiya da kasuwanci a Dubai, duk da cewa shi ma yana da nasa harkokin.

Sarah ta saurare shi cikin sha'awa.

A hankali suka fara sanin juna sosai.

Lokacin da ya fahimci cewa Sarah ba Musulma ba ce, bai yi ƙoƙarin tilasta mata komai ba. Ya bayyana mata addininsa da yadda yake gudanar da rayuwarsa. Sarah ma ta yi masa tambayoyi, kuma yana amsa mata cikin natsuwa.

Duk da bambancin addini da al'ada, soyayyarsu ta ci gaba da ƙaruwa.

Wata rana, bayan sun yi doguwar tattaunawa, matashin ya kalli Sarah cikin nutsuwa.

"Sarah, I don't want this to be just a relationship without a future."

Sarah ta É—ago kai.

"What do you mean?"

"I mean I want something serious with you. I want us to build a life together."

Sarah ta yi shiru. Kalaman nasa sun taɓa wani wuri a zuciyarta.

"Are you sure about this?" ta tambaya a hankali.

"I wouldn't be saying it if I wasn't sure."

Sarah ta sunkuyar da kai tana murmushi.

A wannan ranar ne suka fara tattauna batun aure da gaske.

Sai dai akwai matsala guda É—aya da ba su iya kauce mata ba.

Iyayen Sarah.

Sarah ta daɗe tana ɓoye dangantakarta da matashin. Ta san irin tunanin mahaifinta, kuma ta san cewa idan ya gano tana soyayya da Musulmi, lamarin ba zai wuce cikin sauƙi ba.

Amma sirri ba ya zama sirri har abada.

Wata rana mahaifiyarta ta lura da yadda Sarah take yawan zama a gefe tana waya, sannan ta yi murmushi ita kaÉ—ai. Da farko ba ta damu ba, amma da abin ya ci gaba, sai ta fara zargin akwai wani mutum a rayuwar 'yarta.

A lokacin da ta samu damar kasancewa ita da Sarah su kaÉ—ai, ta tambaye ta.

"Sarah, sweetheart, is there someone in your life?"

Sarah ta É—an yi murmushi.

"Why are you asking, Mom?"

"Because I've noticed you've been smiling at your phone a lot lately."

Sarah ta yi shiru na É—an lokaci, daga bisani ta ce:

"Yes, Mom. There is someone."

Mahaifiyarta ta yi murmushi.

"Who is he?"

Sarah ta fara bayyana mata yadda suka haÉ—u. Ta ba ta labarin cewa shi É—an Dubai ne, Balarabe kuma Musulmi.

Murmushin da ke fuskar mahaifiyarta ya É—an dusashe.

"He's a Muslim?"

Sarah ta gyada kai.

"Yes, Mom."

Mahaifiyarta ta yi shiru. Ba ta yi wa Sarah fada ba, amma ta nuna mata cewa wannan magana tana da nauyi.

"Does your father know?"

Sarah ta girgiza kai.

"No."

Mahaifiyarta ta sauke numfashi.

"Sarah, you know how your father feels about these things."

"I know, Mom. But he's a good man."

Mahaifiyarta ba ta ƙara cewa komai ba.

Bayan wasu kwanaki, mahaifinta ya samu labarin cewa Sarah tana soyayya da wani Balarabe Musulmi.

Da aka tabbatar masa da hakan, sai ya fusata ƙwarai.

Ya kira Sarah zuwa falo.

"Sarah! Come here."

Ta fito daga É—akinta tana tunanin ko wani abu ne ya faru.

"Yes, Dad?"

Mahaifinta yana tsaye kusa da kujera, fuskarsa a murtuke.

"Is it true that you're seeing a Muslim man?"

Sarah ta tsaya cak.

Ta fahimci cewa sirrinta ya tonu.

"Yes, Dad."

"How could you do this?"

Sarah ta yi ƙoƙarin magana.

"Dad, please listen—"

"I don't want to hear anything! What were you thinking?"

Mahaifiyarta ta fito daga É—akin girki, ta tsaya tana kallonsu.

Sarah ta ji zuciyarta tana bugawa.

"He's a good person. I love him."

Mahaifinta ya kalleta kamar bai yarda da abin da ya ji ba.

"Love? You think love is enough to make this work?"

Sarah ta share hawayen da suka fara taruwa a idonta.

"I know he's different from us, but that doesn't make him a bad person."

Mahaifinta ya É—aga murya.

"I will never accept this relationship!"

A wannan lokacin Emily ta leÆ™o daga matattakalar bene, tana kallon abin da ke faruwa. Daniel ma ya fito daga É—akinsa, 

Sarah ta kalli mahaifinta, sannan ta kalli mahaifiyarta.

Ta yi ƙoƙarin bayyana masa yadda take ji, amma duk lokacin da ta fara magana, sai ya katse ta.

A ƙarshe ya umarce ta da ta daina hulɗa da mutumin.

Sarah ta koma É—akinta tana kuka.

Emily ta bi bayanta.

"Sarah?"

Sarah ta share hawayenta da sauri.

"I'm fine."

Emily ta zauna kusa da ita.

"You're not fine. I heard everything."

Sarah ta rungume ƙanwarta.

"I don't know what to do, Emily."

Emily ta riƙe hannunta.

"Maybe Dad will understand one day."

Sarah ta yi shiru.

Amma a cikin zuciyarta ta san cewa ba zai kasance da sauƙi ba.

A gefe guda kuma, mahaifin Sarah bai tsaya ga tsawata mata kawai ba. Ya fara neman cikakken bayani game da mutumin da take soyayya da shi.

Ya so ya san daga wane gida yake, wane ne iyayensa, da kuma irin matsayin da suke da shi.

Da ya samu wasu bayanai, sai ya gano cewa mutumin daga Dubai yake.

Wannan ya sa ya ƙara son sanin danginsa.

Ya fara ganin cewa dole ne ya tunkare su domin ya bayyana musu matsayinsa.

A zuciyarsa, yana ganin cewa idan ya je ya nuna musu cewa shi ma mutum ne mai kuÉ—i da matsayi, da kuma iko

Sai ya shirya tafiya.

A lokacin da ya isa Dubai, ya nemi adireshin gidan dangin matashin. Bayan ya samu bayanan da yake buƙata, sai ya nufi gidan.

Gidan ya kasance babba, mai ƙofofi masu kyau, babban fili da kyakkyawan lambu. Akwai motoci masu tsada a harabar gidan, kuma duk yanayin wurin yana nuna cewa masu gidan suna da babban matsayi.

Mahaifin Sarah ya kalli gidan daga cikin motarsa.

Ya yi mamaki kaÉ—an, amma bai bari hakan ya sauya tunaninsa ba.

Ya fito daga motar, ya gyara rigarsa sannan ya nufi ƙofar gidan.

Bayan an sanar da masu gidan zuwansa, aka buÉ—e masa gate.

Ya shiga cikin gidan.

A ciki kuwa, komai ya kasance cikin tsari. Kayan alatu, manyan fitilu, kujeru masu kyau da kuma ma'aikatan gidan da suke gudanar da aikinsu cikin nutsuwa.

Ya zauna a babban falo yana jiran masu gidan.

Bayan É—an lokaci, mahaifin matashin ya fito tare da matarsa.

Sun gaisa, amma daga yanayin fuskar baƙon, sun fahimci cewa ba wai ziyarar sada zumunci kawai ya kawo shi ba.

Mahaifin matashin ya zauna.

"Welcome. What brings you to our home?"

Mahaifin Sarah ya kalli shi.

"Your son is involved with my daughter."

Mahaifin matashin ya É—an É—aga gira.

"My son?"

"Yes. He's been seeing my daughter in America."

A lokacin mahaifiyar matashin ta kalli mijinta, sannan ta dawo da kallonta kan baƙon.

Mahaifin Sarah ya ci gaba da magana cikin wata irin murya mai nuna isa.

"She's my daughter, and I don't want her getting involved in a relationship that I don't approve of."

Mahaifin  Rahman ya saurare shi.

"May I ask why you disapprove?"

"Because she's not a Muslim. She's a Christian. I don't want this marriage."

Sai dai abin da ya fi tayar da hankalin iyayen Rahman  ba wai kawai kin amincewa da auren ba ne. Salon da mahaifin Sarah ya yi amfani da shi wajen magana da su ya nuna musu kamar ya zo ne domin wulaÆ™anta su da kuma nuna musu cewa ba su kai shi komai ba.

Ya ci gaba da magana cikin raini, yana nuna cewa shi ne zai yanke wa 'yarsa hukunci, 

Mahaifin Rahman ya yi shiru na É—an lokaci.

Mahaifiyarsa kuwa ta kasa ɓoye damuwarta.

Ba su saba a zo musu gida da irin wannan salon magana ba. Musamman ma daga mutumin da bai taɓa sanin su ba.

Mahaifin matashin ya gyara zamansa.

"Sir, we understand that you are concerned about your daughter. But you cannot come into our home and speak to us disrespectfully."

Mahaifin Sarah ya yi wani irin murmushi.

"I came here to make things clear."

"Then you can make your point without insulting anyone."

Ya ci gaba da bayyana cewa ba zai taɓa amincewa da auren ba, kuma yana son a kawo ƙarshen dangantakar nan.

Daga nan ya tashi.

"That's all I have to say."

Ya bar su a falon, ya nufi Æ™ofa ba tare da ya damu da yadda suka ji ba 

ran mahaifin Rahman yabaci sosai

Fuskarsa ta nuna irin ɓacin ran da ya shiga.

Mahaifiyar Rahman ta kalle shi.

"Did you hear the way that man spoke to us?"

Ya É—an gyada kai.

"I heard everything."

"How could he come into our home and treat us like that?"

Mahaifin Rahman ya sauke numfashi.

"He's a man who thinks his wealth gives him the right to disrespect others."

Mahaifiyarsa ta girgiza kai.

"His daughter may love our son, but that doesn't give him the right to humiliate this family."

Mahaifin Rahman yayi shiru na É—an lokaci, sannan ya ce:

"I will speak to my son. I need to understand why this matter has gone this far."

Ba su ji daÉ—in yadda mahaifin Sarah ya zo musu gida ya yi musu magana ba. Sun ji kamar an raina su a gidansu.

Amma duk da fushin da suka yi, abin da ya fi damunsu shi ne batun auren da aka zo da shi.

Sun san É—ansu Musulmi ne, kuma sun san cewa Sarah Kirista ce.

A ganinsu, wannan ba ƙaramin al'amari ba ne da za a ɗauka da wasa

Da yamma, iyayen Rahman suka kirashi zuwa babban falon gidan.

Mahaifinsa ya nuna masa kujera.

"Sit down. We need to talk."

Ya zauna.

Mahaifiyarsa tana gefe, fuskarta ba ta nuna farin ciki ba.

Mahaifinsa ya fara magana.

"Your girlfriend's father came here today."

Rahman ya É—ago kai da sauri.

"Sarah's father?"

"Yes. He came into this house and spoke to us in a very disrespectful manner."

Matashin ya yi shiru.

Mahaifiyarsa ta shiga magana.

"Is this how you want to bring someone into our family? Her father came here as if we were nobody."

Rahman ya sunkuyar da kai.

"I'm sorry, Mom. I didn't know he was going to come here."

Mahaifinsa ya kalle shi sosai.

"That's not the only problem. You want to marry a Christian woman?"Rahman  ya yi numfashi a hankali.

"Yes, Dad. I love her."

Mahaifinsa ya girgiza kai.

"Do you understand what you're saying?"

"Yes, Dad."

"Do you understand what this means for this family?"

Rah6 ya kalli mahaifinsa.

"Dad, Sarah is a good woman. She respects me, and I love her."

Mahaifinsa ya É—aga hannu yana katse shi.

"I don't want to hear about how good she is. This is about our religion, our family and our values."

Rahman ya yi ƙoƙarin bayyana ra'ayinsa.

"Please, Dad. At least give her a chance. You haven't even met her."

Mahaifinsa ya É—an karkata jikinsa gaba.

"Your mother's family and I raised you as a Muslim. We have taught you the values of this family. I will not bring humiliation upon this family by accepting a marriage to a Christian woman."

Kalaman sun sa Rahman shiru.

Ya kalli mahaifinsa, sannan ya kalli mahaifiyarsa.

"You're judging her without knowing her."

Mahaifiyarsa ta girgiza kai.

"We are not judging her as a person. But marriage is more than love. There are things you must consider."

Ya yi ƙoƙarin sake magana, amma mahaifinsa ya katse shi.

"I don't want you to rush into a decision that will affect your entire life. And after the way her father behaved today, I have even more reasons to be concerned."

Rahman ya yi shiru na É—an lokaci.

Sai ya ce cikin sanyin murya:

"Dad, I respect you. I respect this family. But please understand that Sarah means a lot to me."

Mahaifinsa bai amsa nan take ba.

Sai dai a ƙarshe ya ce:

"We have said what we need to say. Think carefully before you take another step."

Rahman ya miƙe a hankali

"Okay, Dad."

Ya tashi a nutse, sannan ya koma É—akinsa

Da ya shiga É—akinsa, sai ya zauna a gefen gadonsa.

Ya É—auki wayarsa, ya kalli hoton Sarah da ke cikinta.

Ya yi shiru na É—an lokaci.

A zuciyarsa akwai abubuwa da yawa da suke ta yawo.

A gefe guda akwai iyayensa, mutanen da suka haife shi suka raine shi, waÉ—anda yake girmamawa kuma ba ya son ya sa su cikin damuwa.

A ɗaya gefen kuma akwai Sarah, macen da ya ƙauna kuma yake son ya gina rayuwa tare da ita.

Ya san cewa mahaifinta ya yi musu rashin mutunci. Ya san cewa iyayensa sun ji zafi.

Amma shi kuma bai ga laifin Sarah a cikin abin da mahaifinta ya aikata ba.

Ya É—auki wayarsa ya kira ta.

Sarah tana ɗakinta lokacin da wayar ta fara ƙara. Da ta ga sunansa a fuskar wayar, sai ta ɗauka da sauri.

"Hello?"

"Sarah."

Ta fahimci daga muryarsa cewa akwai abin da ya faru.

"What's wrong?"

Ya yi shiru na É—an lokaci.

"Your father came to see my parents."

Sarah ta miƙe daga kan gadonta.

"What?"

"Yes. He came to Dubai."

Ta rufe ido.

"Oh my God..."

Ya ba ta labarin yadda ziyarar ta kasance, da yadda mahaifinta ya yi magana da iyayensa.

Sarah ta ji kunya da baƙin ciki.

"I'm so sorry. I didn't know he would do that."

"I know. But my parents are very upset."

Sarah ta fara hawaye.

"What did they say?"

Ya yi shiru.

"They don't want me to marry a Christian woman."

Sarah ta ji kamar an cire mata numfashi.

Ta zauna a hankali a gefen gado.

"So what happens to us now?"

Ya lumshe idanunsa.

"I don't know yet, Sarah. But I don't want to lose you."

Sarah ta fara kuka.

"I don't want to lose you either."

A É—aya gefen wayar, Rahman yayi shiru.

Dukansu suna son juna, amma yanzu soyayyarsu ta shiga wani sabon yanayi.

Ba wai kawai mahaifin Sarah ne ke adawa da su ba.

Iyayen Rahman ma sun fara nuna rashin amincewa.

Kuma abin da ya fi komai É—aukar hankali shi ne, kowanne daga cikin iyayen yana ganin cewa yana kare É—ansa ne.

Amma a tsakiyar wannan rikici, Sarah da Rahman ne suka fara É—aukar nauyin abin da ba su shirya fuskanta ba.

A wannan daren, Sarah ta yi kuka sosai.

Emily ta shigo ɗakinta, ta same ta zaune tana riƙe da wayarta.

"Sarah, what's wrong?"

Sarah ta kalli ƙanwarta, amma ta kasa magana.

Emily ta zauna kusa da ita.

"Is it about him?"

Sarah ta gyada kai.

"They're all against us, Emily."

Emily ta rungume ta.

"Maybe things will get better."

Sarah ta lumshe idanunta.

"Maybe..."

Amma a zuciyarta akwai tambaya guda É—aya da ba ta samu amsarta ba:

Shin soyayyar da ta fara a wani wurin shakatawa a America za ta iya tsallake duk waÉ—annan matsalolin?

Ko kuwa za ta zama farkon wani babban ciwo da ba za ta taɓa mantawa da shi ba?

Ba ta san amsar ba.

Abin da ta sani kawai shi ne, tana ƙaunar mutumin.

Kuma shi ma yana ƙaunarta.


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol