Free chapter 路 Read without an account
Chapter 11
馃挮BA TSANA BACE 馃挮
...........011
*WASHE GARI*
Ganin har wajen 11 ummee bataga Aboon ba sai ta aeka awateef Dan Gano mata shi....Amma sai tace Mata Baya dakin,ta kirashi wayar Bata shiga ba, suna a' haka Abba yafito da Shirin fita...ummee yanaga kunyi carko carko "Abba Aboon neh ya fita kuma na kira wayarsa Bata shiga gashi Yau weekend balantana nace makaranta yaje....Keh ma dai ummee Dan bakiga Aboon ba har Wani abun damuwa neh sai kace Wani yaro karamin yamun text da safen Nan wai anyi Masa Kiran gaggawa" shiru ummee Tayi snn tace shine baiyi mn sallama ba? Kinga nidai na fita toh abba adawo lfy"Allah yasa yafada tare da ficewa.daukar wayarta ummee Tayi tashiga Kiran Musawweer da layin sa na Qatar sai da ya kusa tsinkewa snn da dauka da sallama kasa kasa "Ummee Ina wuni ummee? Lfy lau Yanaji muryarka haka? Ummm lfy ummee y gdn "lfy lau shine ka tafi Babu ko sallama"ummee Kiran gaggawa neh akamun Daga sallar asubahy nawuce" toh Allah ya Bada sa'a yanxu Yaushe zaka dawo" ummee sai na cika 4 months sai nadawo Gaba daya "kana nufin baxa kazo bikin yaran nan ba kenan? Shiru yayi tacigaba"wato Dan Kai kaki aure suma suyi ta xama kenan? Toh ka tabbatar kazo auren Nan" toh insha Allahu ummee Daga haka sukayi sallama
*BAYAN WATA DAYA*
Rayuwa tacigaba da tafiya cikin iKon Allah Yau da Dadi gobe akasin haka, kwanan bayin Allah nata karewa.
Seconds na juyawa minutes yayinda minutes Ke juyawa hours, hours na juyawa sati,sati Kuma na juyawa watanni watanni na juyawa sheraku.
Musawweer nacan Qatar Yana aeki Yana Kuma fama da matsanan cin damuwa,yayi rama, yayi Baki sosai Kullum hankalinsa a tashe yake Yana irga kwanakin auren baby gabaki Daya ya kasa dangana da lamarin.Gashi Kuma bashi da abokin tattauna matsalar tasa gwara gwara ma yanadanyi da Chatgpt AI ne Amma Mai fahimta,Yana bashi shawarwari Amma Dai yakasa mantawa da ita ganin haka sai ya mika lamarinsa ga Allah ya dugufah da addu'ah
Itama a bangaren su baby su nanan cikin kwanciyar hankali
soyayyarh ta da Hafeez sai Masha Allah a yanxu an gama komai na auren su domin har lefe an kawo.
Hafeez ma ya kammala gdn sa Dake Abuja anan zasu xauna tunda Nan yake aeki.
Tunda akasaka bikin ummee ta dauko Mai gyaran jiki Yar Maiduguri take xuwa har gd tana musu gyaran jiki,tuni suka canza sukayi kyau fatarsu ta Kara fari da taushi
********. *******. *******. ******
Tsaye suke bakin main parlour da alama rakosa Tayi "Amarya ta kamar Karna barki nakeji wlh" sunkuyar da Kai Tayi tana mamakin yandan Hafeez ya koma mara kunya tunda bikin Nan ya matso"baby what are you thinking? Take taji wata muguwar faduwar Gaba Hasubunallahu wa nie'mal wakeel" tafada Da da'n karfin "lfy baby? Yaya kwana biyun Nan sai Nayi tajin tsinkewar Gaba nasara dalili' ta karshe tana hawaye a hankali yace" kiyi ta addu'ah kinji auren kenan baby Amma karki damu da Hakan" toh Yaya" yww baby Allah ya Miki Albarka Ameen "Yww ngd sosai xan wuce "sai Yaushe kenan? Ya Daga hannunsa alamun lissafi "Yau Monday koh Tuesday Wednesday Thursday neh Ranar waleema xanxo insha Allah toh shikenan
toh shiga gd
toh Yaya baka fada ba"ya maido da hankalinsa gareta menene? Tayi murmushi tare da rufe fuskarta da gefen hijab dinta"yasosa Kai Yana murmushi baby inasanki sosai Allah ya mallakamun Keh" Yaya da gaske kana sona? Baki yadda ba baby? Na yadda mn kawai dai sai nakeji kamar akwai Wani Abu daxai faru! Kamar meh kenan? Nima fah bansani ba Yaya Amma inajin tsoro" nace Miki kada wnn ya dameki koh? Kiyi ta mn addu'ah kinji" toh Yaya Daga haka ta shige shikuma ya wuce.....
Koda ta dawo daki ta Samu awateef makale da waya tana waya da naseer ganin kamar Bata ma San da ita ba ta fisge wayar ta manna a kunne "mlm naseeru ya isheka haka Ina da mgn da ita"Daga bangarensa yayi dariya Yana cewa gwana kafin ayi mgn da matata ae sai an Nemo ixina nah koh?iKon Allah kabari idan an kaita gdn naka sai akafamun wannan dokar...toh gwana kwana nawaneh ya rage? Kwana 5 biyar neh da yaddar Allah? Tabashi amsa tare da Kashe wayar tazauna, awateef ta kalleta kefa baxai yiwu ba Dan saheebinki ya tafi ki Hanani Jin muryar nawa masoyin" Haba ta rike tana cewa kiyi hkr Indai naseer neh sai kin gaji dashi "Allah ya kiyaye ni ae banxan taba gajiya dashi ba wlh" Kinga khaleed ya karbo mana dinki tashi ki Gani okay tace tare tashiga dubawa....
**********. **********. ********
Karfe 11 na dare Aboon ya sauka kasa Nigeria direct gdnsu ya wuce lokacin har an rufe gdn sai da yakira Ameer yazo ya Bude Masa dakyar yake Daga kafafunsa, Ameer ya kallesa cikin tashin hankali ganin yadda ya rame yayi Baki yakamasa ganin Yana layi Yana cewa"subnallahi Aboon baka da lfy ne? Bai iya ya basa amsaba sai yakamasa ya wuce dashi dakinsa direct lokacin numfashinsa sama sama yake part din Abba ya nufa yayi knocking kofar cikin sa'a kuwa Abba ya Bude kofar ganin Ameer yasa yace lfy"Nan yafada Masa yanayin da Aboon ya dawo yashiga ya tado ummee suka nufo dakin....lokacin Aboon nata kokari da numfashinsa" Kuka Ummee tafashe dashi ganin yadda Yakoma Abba neh yace su kamashi sukayi asibiti dashi.... Emergency direct aka nufa dashi likitoci suka rufu akansa sai wajen 12 suka Samu komai ya daidaita likitan ya fito Yana sharte gumi ganin Abba yafadada fa'ra'arsa Yana cewa "sheikh muje office sai na muku bayani" dukkansu suka shiga office sai da yayi Dan rubuce-rubucensa snn ya dago ya kallesu"umm sheikh Jikinsa da sauki Alhamdulillah mun Kuma Samu numfashinsa ya daidaita" toh yanxu doctor Mai yake damunsa?"Abba ya tambaya "Hakikah dai yanxu bisa binci kenmu mungano Jininsa ya hau sosai,Kuma Yana fama da damuwa Mai yawa wacce a yanxu xuciyarsa Ke bugawa da karfin Wanda hakanne yayi sanadiyar daukewar numfashinsa" likitan yanxu ya farfado" hajiya zai farfado sai xuwa safe insha Allah sauran bayanin zanyi muku idan ya farfado Kuna iya ganinsa yanxu"
Dakin suka nufa Yana kwance flat kamar gawa,hannunsa daure da ruwa,fuskarsa Tayi muguwar rama sai saje da gashi Daya taru a fuskar,farar jallabiya ce jikinsa Mai dogon hannu ummee sai da Tayi hawaye shima Abba dakewa kawai yake innalillahi wa innailaihi rajiunnn kawai Ameer da Abba Ke maimaitawa ummee ta xauna gefensa tana cewa"musawweer Mai yake damunka? wacce damuwa ce wannan haka kakeh fama da ita wacce kakasa sanar mana mu iyayenka" Abba yashiga bata hakuri kiyi hkr ummee insha Allah zaisamu lfy
Nan asibitin suka Kwana sai bayan sallar asubahy Ameer ya nufi gdn Dan sanar dasu halin da ake ciki
*********. *******. ******** . ******
Koda su baby sukayi sallar asubahy sai suka koma bacci,sai wajen 9 snn suka tashi sai da Tayi wanka snn tafito lokacin awateef na kitchen me ake Dafa mn neh? Ta tambaya chips neh...okay bari naje mu gaisa da ummee "ummee batanan"Ina taje da safen Nan? Wlh ban saniba" Amma Dai Bata nan haka dai suka karya cikin zullumin Ina ummee tashige takuma bar wayarta a daki suna cikin haka Ameer ya shigo yafadamusu abun dayake faruwa kukah Awateef tasaka itakam baby taji Babu sosae Nan dai suka hada break suka nufi asibitin harda khaleed suka rufe gdn
Sun girgixa kwarai da Yanayin dasuka gansa lokacin Yana xaune Amma binsu kawai yake da idanu Dan Koda suka gaidashi Bai amsa ba Yana dai kallonsu awateef sai Kuka take sai da Abba yace Tayi shiru kosu koma gd.
Abba neh da Ummee zaune office din doctor ya kallesu tare da Cewa"hajiya ga Saka makon test din damuka Mishi? Kamar yadda na fada muku Jininsa ya hau sosai,Yana Kuma fama da ciwon damuwa, snn Kuma xuciyarsa na bugawa da karfi sosai Kuma a halin yanxu jini ya fara taruwa a xuciyarsa Wanda Hakan zai iya sawa ya kamu da censern xuciya Hakan Kuma zai haifar da babbar matsala Wanda bama fata....yanxu dai Jininsa ya daidaita snn mun bashi maganin bacci Wanda zai Dunga Sha Yana samun bacci ishesshe" toh yanxu likitan xa'a sallah me saneh? "eh toh xamu iya sallamarsa tunda bashi da Wani ciwon na fili zadai mu Baku magani da allurorinsa snn Kuma xamu Baku shawarwari.... toh likitan Muna sauraronka cewar Abba"sheikh yazama dole ku samo Masa maganin damuwarsa snn kuzamana Kuna kwantar Masa da hankali yakuma Dunga samun ishesshe bacci da motsa jiki tare da amfani da maganguna damuka Baku" toh insha Allahu likita....
Bayan likita yasake duba Aboon sosai ya Basu sallama.
suka dauki hanyar gd har yanxu jikinsa Babu karfi ummee da Abba kawai yayiwa mgn tunda ya Kalli baby yaga yadda ta Kara kyau da fari yakuma tuna Yau aurenta saura kwana 4 yasake shiga tashin hankali Yana Kuma Allah wadarai da nauyin Baki irin nasa yayi nadama mara adadi...tabashi da Ameer yayi yadawo dashi hayyacinsa zai kamashi ya zame ya fara tafiya a hankali ya shiga ciki. toilet ya fada yayi wanka domin Jin jikinsa ya Masa Wani mugun nauyi Yana shiryawa Ummee da Abba suka shigo sukayi Masa ya jiki Abba ya kallesa musawweer xauna inason Muyi mgn ya zauna cikin ladabi babu wasa akan fuskarsa yakira sunan sa"Abdul musawweer" bazai iya tuna sanda Abba yakira full name dinsa ba,yasan ba karamar mgn bace"na'am Abba"ya amsa cikin sanyin murya meyake damunka musawweer" yayi shiru Ina Maka mgn Nan ma shiru Gani ran Abba ya fara Baci yasa ya fara bashi hkr"Abba kayi hkr Dan Allah" musawweer baza ka iya fada mana damuwarka ba kenan? Nafa Dade da fuskantar kana cikin damuwa ya kwantar da murya babana kafadamun kaji" a hankali yace Abba kayi hkr" mikewa Abba yayi ya fice Yana cewa ka tabbatar ka fadawa Ummeenku idan ba hakaba xanyi Maka abun da baka tunanin" tabbas lokaci yayi daxai bayyana abun da Keh ransa Amma yasan lokaci ya kure Masa ummee ta katse sa da cewa"Aboon menene yake damunka dahar kakamu da hawan jini? Yayi shiru kansa a kasa "inason na tambaye ka Wani Abu Kuma kada kamun karya"musawweer kanason baby neh?" A razane ya dago ya kalleta amsa xaka bani Kuma kada kamun karya"Take yaji xuciyarsa ta karye sai kawai ya fara Jan xuciya Yana hawaye"Haba Aboon nice fah na haifeka na raineka kana tunanin zaka boyemun damuwarka na Dade da Gane kanason baby Amma Ganin baka fadamun ba sai na nuna bansani ba, Kasani fah ni mahaifiyarka ce Bai kamata ka boyemun damuwarka ba musawweer? Ya Kara karfin kukansa "ummee wlh Ina tsananin Santa na Kuma Yi duk Mai yiyuwa Dan ganin na cireta Daga Raina Amma na kasa, Ummee idan ban sameta ba zan iya mutuwa wlh" rufe Masa Baki Tayi tana cewa "kayi wasa da damarka musawweer idan da Kaso, baby zata soka fiye da ko wanne Namiji"Kaine kayi ta nuna mata kiyyayya da tsana sai yanxu da aurenta ya rage kwana 4 xaka ce haka? Kayi hkr ka dangana Allah ya baka wacce tafita Amma baby matar Hafeez ceh insha Allahu"cikin kukah yace"BA TSANA BACE Ummee wlh Ina Santa so Mai tsanani, Ummee BA TSANA BACE RIKICEWAR XUCIYA CEH Dan Allah ki taimakamun wlh idan ban auri Baby ba zan iya rasa Raina ummee" ni Babu abun da zan iya Maka musawweer kasan ba'za afasa aurenta da Hafeez ayi da kaiba koh,?ka Kuma San Baby Bata sanka baxa Kuma mu tilasta taba"zaiyi mgn ta katsesa 'musawweer kabar maganan Nan kayi hkr Kaci Gaba da addu'ah kamar yadda na fada Maka tashi ka tafi masallaci...mikewa yayi ya shiga toilet ya dauro Alwaka jiki ba kwari ya nufi masallacin... sosai ummee ta tausaya masa Amma danshi baxa ta tauye baby ba yayi hkr dai kamar yadda ta fada Masa....
Duk yadda Taso kar ta fadawa Abba kasawa Tayi sai da ta fadamasa cikin fada yace"ban San musawweer bashi da hankali ba sai yanxu,Mai yaceson Mai damu kananan mutane ko? Xancen banxa kenan? Dama shine abun dayake damunsa har na tashi hankalina toh sai dai ya mutu aure Babu fashi insha Allah? Haka abba yayi ta fada da kyar ummee ta bashi hkr......
Hernarn Muhammad鉁嶏笍鉁嶏笍鉁嶏笍