Free chapter 路 Read without an account

Chapter 12

by Hernarn Novels鉁嶏笍鉁嶏笍鉁嶏笍 路 BA TSANA BACE

馃挮 BA TSANA BACE 馃挮





  ...........012






  Aboon Bai iya bacci ba ranar Yana ta tufka da warwara ya Kuma rasa yadda zai Yi..... Yanason baby so Mai tsananin gaske Kuma baya tunanin idan ya rasa ta xai rayu....Haka ya raba dare tunani Daga karshe ya dauro Alwala ya fara gabatar da sallah Yana kaiwa Ubangiji kukansa... Yakuma ji sauki abun dayake ji har yasamu karfin gwiwar tunkarar Abba da mgn.

   Suna fitowa Daga sallar asubahy yasami Abba kan suyi mgn.har cikin parlourn Abba suka shiga ya xauna kansa a kasa ganin wajen mintina 3 Bai ceh komai ba yasa Abba yin gyaran murya tare tacewa Ina sauraron ka Aboon"ya gyara zamansa"Abba kayi hkr da abun da xan fada nasan xai Bata Maka Rai.... Abba Allah ya jarabceni dason baby tun batasan kanta ba wlh Abba nariga Hafeez fara San baby...."Kai dakata Abba ya katsesa"musawweer Ina wasa dakai neh? Koh raini ya shiga tsakaninmu neh? Da sauri ya girgiza Kai A'a Abba"toh da kakeh cewa kariga hafeezu farasanta....meh ya Hana ka furta mata?a hankali yace"Abba wlh naso sanar mata,naso neh ta Kara Girma a lokacin ni Kuma na dawo Daga Sudan Amma lokacin Dana dawo sai naga sun shaku da Hafeez Nayi kokarin cireta a Raina, wlh Abba na kasa Dan Allah Abba ku tausayamun"shiru Abba yayi Yana kallonsa snn yace"a lokacin Mai yasa baka fadawa ummee ba ko ni sai yanxu"zai Yi mgn Abba ya tare shi"ka Bude kunnuwaka kajini da kyau Kuma ka haddace abun da zan fada Maka......Idan kaga baby Bata auri Hafeezu ba toh shine yace ya fasa domin Koda itace tace ta fasa baxan yadda ba Dan haka idan xaka dawo cikin hayyacinka kadawo idan Kuma baxa ka dawo ba wannan ya rage naka....Kuma wannan ya xama karo na karshe daza ka same ni da wannan mgnr kaji na fada Maka"sosai hankalinsa ya sake tashi yashiga baiwa Abba hkr Amma Bai saurare sa ba karshe ma cewa yayi ya tashi ya basa wuri haka ya fito giki a matukar sanyaye ya nufi part din ummee.

 Yau ta kama laraba bikin au baby saura kwanaki 3....sun tashi da wuri kasancewar yan'uwa sun fara xuwa dangin abbanta da sauran dangin ummee duk anxo
Ya'u xasuje wanki Kai snn ayi musu kitso gobe Kuma suyi Kunshin Baki da ja.
Yau suna da event "Mussaffah"
Gobe Kuma "waleema" giving daurin aure
Mussaffah iya sune neh Yan mata Dan haka tun wuri suka dawo Daga saloon din bayan an yar'yada masu kitso....abunka da Fulani gashinsu har gadon Baya gashi Baki Mai san'tsi da laushi
 
  Karfe 4 aka fara musaffar..... amare sunyi ado da abaya Bara Kal Mai ratsin gold sai Yar karamar Alkebba ta shifon shima Fari da stones gold Babu make up fuskar su Amma sunyi kyau matukar.....su Kuma kawaye suka Saka Black abaya ankayi decorating wajen da balloons white and black anci ansha ankuma Yi pics da video da karutun cikin kwanciyar hankali' musaffar izu 60 sukayi Dan haka sai bayan Isha'e suka kammala bayan sun Raba soveniers kala虏


   Musawweer Bai Samu sun tattauna da ummee ba sakamakon Baki datake fama dasu......yadai Yankee shawarar tattaunawa da Hafeez,har gidansu ya same shi sai dai Bai shiga ba a kofar gd suka tsaya bayan sun gaisa ya rasa ta Ina zai fara"Hafeez nazo neh wajen ka da wata mgn Mai muhimmanci,Amma bansan yadda xaka dauki abun ba Amma inaso Kasani banyi Dan naci mutunci ka ko xarafin ka ba,Kuma bawai Dan na Raina ka ba... Hafeez wanna babbar taimakoneh nazo neman wajen ka" Hafeez yayi shiru Yana sauraron sa har ya gama snn yace"Sheikh kafadi ko menene insha Allahu idan Bai fi karfin na ba xan Maka"tsayuwarsa ya gyara kafin ya shiga bawa Hafeez Labari tun Daga sanda ya fara son baby har yanxu da lokacin Daya dauka Yana fama da ciwon hawan jini da gwagwar mayar dasukayi da su Abba Bai boye Masa komai ba har yadda yake matsanancin kishinta da Kuma dalilin dayasa Bai bayyanamata soyayyarh sa ba"Hafeez yayi shiru Yana tunanin sunkusa mintina 10 ka'na Santa Hafeez Amma ka yadda Dani nafika Santa wlh idan ban sameta ba komai xai iya faruwa Kai likitaneh nasan kasan illar ta'ruwar jini a xuciya" sai da Yakuma daukar wasu mintina uku kafin yace"Aboon bantaba tunanin wannan ce mgnr daza kazo mun da ita ba Amma kayi hkr gsky Babu abun da xan iya....baxan iya barmaka baby ba inasanta har bansan adadiba hkr kawai xan iya baka Allah ya baka wacce tafita Yana gama fadin haka ya juya.... ihu neh kawai musawweer Bai sa ba Hafeez is his only hope" yanxu gashi shima Bai fahimce sa ba Da wannan tunanin ya shige motar ya dauki hanyar gd Bai Ankara ba yaji wata motar da bugi tasa take ta gangara......


  Abba Yana xaune a office yaji wayarsa na ringing ya dauka ganin Abba su Hafeez neh cikin firgici yace wane asibiti? Sai ya dauki car keys yafice hankali tashe har ward din yashiga ya Sami Abba su Hafeez tsaye Baki wata Kofa suka Yi musabaha abban su Hafeez yace"yayah Ina kokarin shigowa naga motar musawweer sai Kuma naga kafin na Ankara mun goge juna Kuma abun yaxo da tsautsayi motar tasa ta kifa da taikamon jama'a muka Daga motar Yana ma cikin hayyacinsa sai dai yazamu gaucewar gashi a hannu.....salati Abba yayi kafin yayi mgn likita da Aboon din sunfito' anyi dressing hannu nasa 'gaida Abba yayi suka wuce gd...Koda suka ida gd Bude motar yayi ya fita ya barsu cikin motan Abban su Hafeez ya Kalli Abba yace"meyake damun musawweer neh? Hmmm yaron Nan bashi da hankali Ashe 'Nan ya kwashe komai ya fada Masa...Abban su Hafeez yayi mamaki kwarai haka dai suka rabu Yana ta al'a jabi.......


   Ko da ya shiga dakinsa Wanda Ke cikin duhu a Koda yaushe" xama yayi bakin gado"yanxu kenan na rasa baby?Hafeez xata aura? Banajin xan iya cigaba da rayuwa matukar xata kasance gdn Wani nah"wata xuciyar tace Masa Mai xai Hana ta furta Mata soyayyarh ka kaifah Dan uwanta neh baxa ta kika ba"Daga kafadarsa dayaji anyi yasa ya dago Ummee ce"Aboon Mai kakeh tunani? Bai Bata amsa ba Yana dai kallon gefe"ta zauna bakin gadon itama a hankali ya koma ya xauna kan center rug din dakin"na fada Maka ka cire Da'muwar Nan a ranka koh? So kakeh ka Kashe kanka? Da har baka Kula da tuki.....Mai yake damunka Aboon kaifah ba karamin yaro bane"Ummee Kuyi hkr Amma nakasa controlling xuciyata neh inason baby sosai Dan Allah ummee kiyi mata mgn wlh nafi Hafeez santa"Aboon kenan nifa baxan daga wanna mgnr ba Kuma kaiba Banason kayi mata .....Bakai take Gani ba Hafeez neh....nafiso ka cigaba da xama matsayin Dan'uwan ta yanxu idan awateef ceh Wani yake kokarin Yiwa haka Kai a matsayin ka na wanta zakaso neh? Yayi shiru"nasan kana Son baby Amma ba rabonka bace kayi hkr Bai Kuma cewa komai ba.....tagama bashi Baki



   Suna xaune dukkan su a parlour Ummee da yan'uwa ana ta hirarraki wayar ummee ta fara ringing na dauka ganin Abba"Abba Ina wuni lfy baby Ina Ummee Tana part din Aboon bari na Kai mata" toh Maza Yi sauri'da sauri na na nufi wajen bayan na Kashe wayar Amma meh kafin na shiga naji Kalmar data daki xuciyata"Ummee Kuyi hkr amma nakasa controlling xuciyata neh Inason baby sosai kiyi mata mgn nafi Hafeez santa" Chak taji komai ya tsaya mata Daga Kuma wanna lokacin bata' kara fahimtar komai bah bata ma San ta'yaya' taxo daki ba sai Ganinta datayi a kan gado,tana ta kokarin tsaida numfashinta"Ni baby Aboon yake mgn akai ko wata babyn.....ni Aboon yake so wayar ummee Dake hannuta tacigaba da ringing,tana Gani har ta tsinke sai awateef ceh ta karba ta kaimata ta dawo ta taddani yadda nake"baby Mai yasa meki kike gumi haka? Ta Kalli kanta tana mamakin gumin data Keh duk da fanka da Ac Dake dakin....ta kama hannun awateef"Sister.....sai ta kasa mgn what happened sis? "Nan ta kwashe komai ta fada mata awateef Tayi shiru tana tunanin"sis nifa na sani dama da dadewa mun taba mgnr dashi dukda kamar wasa neh Amma ni nason Aboon na sanki sai dai Kuma kin Yi Masa nisa kefa matar Hafeez ceh"ta sauke ajiyar xuciya "awateef nasani Amma Ina tsoron su Abba su canxa mgn kinsan baxan ceh a'a bah...bana tunanin ummee xa suyi Hakan ki kwantar da hankalin ki"

********. ********. ********. *****

  Washe gari aka tashi Alhamis ranar Yana waleemarh.....gidan ya Kara cika kasancewar gobe daurin aure tun safe Hafeez ya kirata yace Yana so su hadu tace Masa yaxo gd yace A'a xai kirata ta fito tace toh idan suka cire Kunshin sai ta kirasa

  Karfe 10 ta sato jiki ta fito Dan tasan ko ta fadawa ummee baxa ta barta ba....can nesa da gdn yayi parking tun kafin ta karaso ya fito Yana sanye da jallabiya blue back Mai gajeren hannu da adon ruwan xaiba baxa ta iya fassarar yanayin fuskar saba Amma Bayi kaman yadda take ganinta Kullum ba idanuwansa ma kamar a kumbere"shiga mn baby tashiga batar da ta ce komai ba"sai da shukayi tafiya Mai nisa kafin ya Samu gefen kamar titi mara'r hayaniya yayi parking tare da juyowa ya kalleta"A Hankali tace Ina kwana Yaya"ya lumshe ido "lfy ykk" alhmdlh Yaya Mai yasamu fuskarta da idanunka sun kunbura"ya da'n sosa keya banyi bacci bane Daren Jiya"ta kallesa alamun saboda meh"Akwai abun da yake damunka nah neh baby......Dan Allah inason ki fahimce ni" tuni zuciyarta ta buga dama tun da ya kirata take a tsorace kawai dai ta dannene"ya katse mata tunani kinyi shiru"uhmmm Ina jinya Yaya kayi sauri kaga ummee Bata San na fito ba" ya ja numfashi"baby kinsan Ina sanki" Wlh ban taba son wata mace bayan Keh ba Kuma Keh ce nakeson aure.....Nayi fatan mu rayu karkashin inuwar aure....baby idan na roke ki wata alfarma zaki iya yimun ita ta dago tana kallonsa takasa mgn sai xuciyar ta Dake bugawa da sauri虏 "ya lumshe ido tare da budewa"Baby Keh yar'uwata ceh Kuma baxan Miki karya ba Kuma baxan cutar Dake ba "Yaya wai mene kakeh mun wadan Nan maganganun? Xan fada Miki yanxu Amma Dan Allah inaso ki fahimce lamarin Kuma ki kallesa ta kakyawar fuska"Musawweer Yana fama da hawan jini "hypertension" abun yayi worst har jini ya fara taru'war Masa a zuciya the condition is bad Baby....Yazo ya sameni da yafadamun komai wai Yana sanki da aure Kuma ya Dade Yana sanki....ban saurare Shiba Amma naje asibitin dayaje my friend was the doctor Daya dubasa baby inaso ki.....Inaso mu hakura da juna ki auri...ki auri...ki auri musawweer Yana sanki baby Kuma xai kula da Keh....... Hernarn Muhammad 鉁嶏笍鉁嶏笍鉁嶏笍

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol