Free chapter 路 Read without an account
Chapter 13
馃挮BA TSANA BACE 馃挮
......013
Tunda ya fara mgn ta tura Mishi ido ko kiftawa batayi niqabin fuskar ta ta kunce tana hawaye"Wnn itace mgnr daza muyi? Pls Baby understand Wlh Ina sanki Amma mu hakura Banason Wani Abu ya shiga tsakaninmu da musawweer Banason ya Dunga kallona da abun Koda ya'ushe pls baby ki aure shi insha Allah Akwai Alkhari" dakata Hafeez wnn itace soyayyarh dakekeh yimun? Itaca ceh soyayyarh dakekeh cewa kana yimun?Ashe bani da muhimmanci agareka dahar xaka iya sadaukar Dani ga Wani cikin sauki haka Hafeez"ta fashe da kuka.....Kaifah kasan Aboon neh kawai a fuska" ni na zauna dashi muke kwana gd Daya muke tashi muke wuni a makaranta tare....kaf gdn Nan Babu Wanda baisan ya tsane niba Baya kaunar ganinah a cikin farin"Koda duka zaiyi..... nawa sai yafi na kowa shine kakeh cewa Yana sona da aure......Naji Hafeez idan har ka fasa aurena basai ka fitomun da wnn hanyar ba"idanuwansa sunyi j'a sosai "wlh baby ba haka beneh bawai Baki da muhimmanci baneh Kuma bawai bana sanki ba....na fahimci Musawweer sosai Yana sanki duk kishi neh yasa yake wadan Nan abubuwan koni farko Daya zomun ban saurare Shiba sai bayan mun rabu nake samun labarin cewa"yayi accident Allah ma ya kiyayeh Bai ji rauni sosai ba musawweer loves u baby"Hafeez ni kakeh kallon idanuwa nah kakeh fadamun na auri musawweer ana gobe daurin aurena da Kai innalillahi wa'inna ilaihi rajiunnnn"baby ki fahimce ni Dan Allah bakisan radadin Dana Keh jiba wlh ko bacci na kasa yadda naga dare haka naga Rana ta share hawayen ta "inaso ka amsa mun wanna tambayar Dan Allah Kuma ka fadamun gsky"toh insha Allah"da ace ka aure ni.... musawweer yaxo yafada Maka abunda ya fada Maka sai ka sakeni ya aura koh? Da mamaki yake kallonta yakasa mgn Tayi murmushi tana hawaye masu Dumi"Hafeez Ashe baka kallona matsayin matar ka nice nake hau'kata na Dade Ina Maka kallon miji Amma Kai ba haka baneh....zai Yi mgn ta Daga Masa hannu ya isa haka Naji duk abun da kafada Kuma na gode auren ka neh na fasa baxan yiba insha Allah tana fadin haka ta fashe da kukan tare da Bude motar ta fice ya fito cikin hanxari Yana mata mgn Amma Bata saurare saba ta Tari adaidaita tashige batare da ta fada Mishi Inda xa'a kaita ba Hafeez ya dafe kansa yana Jin Wani irin bakin cikin
Tunda ta shiga adaidaita take Kuka Mai ban tausayi sai da Mai napep din yayi da gaske snn ta fada Maka Inda xai kaita suna isowa kuwa ta sauka tare da basa duka kudin hannunta ta shige gdn da sauri batakoh kula mutane Dake Tayi mata mgn suna amarya amarya ba Tayi wucewar ta ciki tana xabga kukanta......
A Daidai wnn lokacin Kuma Abba,Abban su Hafeez da ummee nata fafatawa
Yaya kayi hkr ba wai xan ja da Umar'ninka baneh Amma Aboon shine Wanda yafi dacewa da auren ta....meh kakeh nufineh Al-qaseem? saboda Wani banzar kudinrinka mara dalili' xaka tauye yaro koh meh?Abba ya fada cikin Daga murya Yaya ka saurare ni" bayan mun rabu da Kai ranar laraba na koma gd da xancen a Raina Amma wlh ban fadawa kowa ba...bayan sallar Isha'e hafeezu ya sameni ya fadamun duk yadda sukayi da Musawweer harma yace yaje Asibiti yayi bincikeh ciwon musawweer din? Na nuna Masa bansan mgnr ba har sai da yagama yacemun shi yanxu baxai yanke hunkunci ba sai yadda nace.Na tambaye shi shin xai iya hakura da Ita Ummu-khursum dan'uwansa ya aura yaceh dama abun Dake ransa kenan Amma yafison yaji ta bakinah shawarar da muka yan'keh shi Kuma xai fahimtar da ita Ummu-khursum din Amma wlh Yaya ban tilas tasaba"Amma da ummee sukayi jimm can Abba yace"Naji duk abun da kace Amma ni Keh Gaba daku duka Dan haka aure Babu fashi" idan shi hafeezu zai iya hakura ita Kuma baby baxa ta iya xama da musawweer ba Kuma baxan mata doleh ba..... nasan ka sani Amma bari na sake tuna Maka"Baby amana ceh a hannuna xaluntarta babban laifi neh a wajen Allah Dan haka baxan mata doleh ba" zai Yi mgn ya katse sa qaseem kada ka Bata mun Rai"yayah kayi hakuri nikai na baxan so ayi mata doleh ba Amma xanso aji ta Bakin ta Dan shi hafeezu yace Koda Bata auri musawweer ba shima baxai aureta ba....sai dai dukkan su biyu su rasa.jin'jina Kai Abba yayi snn yace xakuwa su rasa duka su biyun
Duk wannan dam'baru'war da'ake Aboon da baby Basu da Labari baby na can tana kuka awateef Tayi tambayar Duniya Amma Bata Kula taba ganin haka yasa ta nufi wajen ummee Dan ta sanar mata Amma sai akaceh mata tana part din abba
Shikan shi Aboon ya can Yana kukan xuci baxai iya bayyana halin dayake ciki ba yadai San Yana gab da rasa ransa
Har wajen 3 Baby Bata sara'rawa kanta ba da Kuka awateef Tayi Tayi tatashi ayi musu make up Amma Bata Kula suba dama ba sallah take ba Dan haka tun da ta kwanta batako motsa ba....Ummee ce ta shigo mamaki neh ya kamata ganin halin da Baby take ciki batace komai ba ta kamata suka nufi part dinta ta SATA a daki Tayi luff jikin ummee tana kuka kasa虏 cikin tausayi ummee tashiga tambayar ta menene Nan ta kwashe komai ta fada mata ummee ta kalleta"kiyi hkr baby Babu Wanda xai aura Miki Wanda Baki so kinji tashi ki wanke fuskarki abban ku na kira cikin Sanyi jiki ta wanke fuskarta ummee ta Bata Wani hijab din ta Saka tacire nata Daya jiqe da hawaye suka nufi parlourn Abba"Aboon,, Abbansu Hafeez,, Hafeez sai Kuma mommyn su Hafeez din duk xaune suke a parlourn a hankali ta gaida su suka amsa suna kallonta kur Aboon Yamata da idanu ganin yadda fuskar ta yayi ja ga idanunta sun kunbura Baya bukatar a fada Masa kukah Tayi"Abba ya gyara murya snn yace mun Tara kuneh anan Dan mu warware mgn xan fara da Kai hafeezu Wani saqo ka Bada a kawo mun"yayi kasa da kansa"Abba kayi hkr Bawai na Raina ku baneh koh inaja da umarninku face nasowa dan'uwana abun Dana so wa kaina na hakura da auren baby Abba na barwa musawweer ita batare da wata manufa ba Kuma Babu Wanda ya tilastani..... Abba Koda musawweer Bai auri baby ba ni na hakura da auren ta har abada" tunda ya fara mgn musawweer ya kafesa da ido tabbas yayi mamaki ba Dan kadan ba Ashe Hafeez Yana da mutunci haka, tabbas ya cika dan'uwa na gari" ita kuwa baby hawaye take... Abba yayi shiru Yana nazari snn ya Maida kallonsa ga musawweer "Kai Kuma Mai xaka ceh"cikin sanyin murya yace Abba Kuyi hkr Dan Allah" yasan sarai tunda yace haka bazai Yi mgn ba "Ummu-khursum ya kira sunan ta ta amsa da na'am Abba cikin dashas'shiyar muryar ta"Ummu-khursum baxan Miki doleh ba kinji abun da hafeezu yace shin zaki'iya auren musawweer ko a'a"hawaye ne suka xubo mata Wanda kowa sai da ya gansu takuma Yin shiru Abba yace"baby baxan Miki tilas ba idan bakyaso....xamu cigaba da addu'ah Allah ya fito Miki da Wani kinji"a hankali tace "Abba duk yadda kukayi Daidai neh baxan bijire mukaba"nasani Amma inaso ki yadda kafin ayi komai Kinga shi hafeezu ya rantse bazai aure kiba Koda Baki auri musawweer ba"shine nakeson Ji Daga bakin ki kin yadda da auren musawweer ko sai A'a Allah ya kawo Wani ta goge hawayenta tare da Daga musu Kai Abba yace kin amince kenen baby Nan ma ta Daga Kai a hankali jikin kowa yayi Sanyi harshi kansa Aboon din yaji tausayinta matuka Bata sake fahimtar xantukan da Abban yake ba har taji ummee ta kama ta suka koma daki Kuka take sosai bayan ta kwanta akan gadon baxa ta iya kallon su Abba tace baxa ta auri dansu ba
Koda awateef ga shigo ta Shirya tsaf da shirinta na xuwa waleemarh Tayi kyau sosai ummee wai baby Bata da lfy neh "eh kuje ita baxa taba"baxa taba Kuma Ummee tana Amaryar tsawa ummee ta Daka mata tana cewa fice mun Daga daki haka ta fita tana mamakin abun Daya faru tasan akwai Wani Abun a kasa Amma ake boyemata ko awajen waleemar Bata saki jikin taba tana ta tunanin Mai yasami yar'uwa tata gashi mutane sai tambayar ta suke sai dai tace musu Bata da lfy.......
Kunsan magrib Tayi wanka da taimakon ummee ta Bata kaya cikin na bikin tasaka "baby kiyi hkr ki daina kukan nan haka"ta share hawaye tana Jin Wani irin tukikin bakin cikin"Baby bansan Wani hukuncin Abban ku xai yanke ba Amma na fada Mishi bana goyon bayan aura Miki musawweer saboda nafi kowa sanin halinsa" ita dai batayi mgn ba Kuma hawaye Basu Daina fita ba
Ummee ceh ta fita sai gata sun shigo da Nusy ta zauna bakin gado"Subnallahi Amarya me yake faruwa rungumeta Tayi tasake fashewa da Kuka" ganin ummee ta fice Daga dakin"shi zasu aura mun Nusaiba"shi'wa? Baby? Kuka take sosai da kyar Nusaiba ta lallashe ta tana cewa"munje wajen waleemarh nida noor bakuxo ba baby"na tambayi awateef tace naxo gd Baki da lfy baby meyake faruwa?"Ta ja numfashi"tafara bawa Nusaiba Labari tundaga farko har karshe ta daura da cewa"wlh Nusaiba bana Sansa ko kadan baxan iya xaman aure dashi ba ji nake kamar xan'mutu kirgina xafi yake mun Nusaiba wlh bana sonsa" kiyi hkr baby Amma nima tabbas na zargi ya sayyeeedi Yana sanki"xan Baki shawara kiyi addu'ah snn kiyi istikhara idan akwai Alkhari Allah ya tabbatar idan Babu Allah ya kawo wanin sa"tana Kuka tace "xuciyata xafi take mun Wani Abu ya tokaremun numfashi nah"kiyi hkr kiyi ta addu'ah kinji haka Nusaiba Tayi ta Bata hakuri da Bata Baki har magrib snn ta tafi da niyyar gobe xata dawo.....
Yadda baby Taga Rana haka taga dare sai da aka kira sallar asubahy tada'da tabbatar da ido biyu ta kwana Sai bayan Tayi sallar bacci ya Dan dauketa a zaune
Sai wajen 11 ta tashi Tayi wanka,da taimakon ummee suka Shirya cikin lace pink Mai ratsin fari da gold" suka Sanya farin mayafi"aka zuba musu make up Wanda ya Kara fito musu da kya'u da sukayi....ta tsaya da kukan Amma fuskar ta Babu wal'wala Hakan Kuma Bai Hana kya'u datayi bayyana ba...... Friends dinsu sai pics suke musu suma Wanda suka Sha gayu cikin angon lace fari da silver......bayan sallar juma'a aka daura auren"Awateef Nurad'deen muaz da angon ta Naseer Mubarak akan sadaki 500k,sai Ameer Nurad'deen Mua'z da Aisha Al-qaseem Mua'z akan sadaki 500k da Kuma Hafeez Al-qaseem Mua'z da amarya Ummu-khairee abubakar akan sadaki 500k sai Abdul-musawwer Nurad'deen Mua'z da Ummu-khursum Ahmad akan sadaki 1M auren neh Wanda ya Samu halartar manyan manyan mutane malamai dama ya'n siyasa ko wanne ango fuskarsa dauke da murmushi da fara'a Amma Banda Hafeez Wanda yak'e kawai yake Yi tun bayan xaman su da su Abba"Abban su yace dashi kar ya fasa gayyatar duk wadan'da ya gayyata da fari Kuma ya cigaba da shirye-shirye domin aure Babu fashi shidai hankalin sa Bai kwanta ba Amma yanxu yaji an daura aurensa da wacce Bai sani ba mutanen Dake tayasa murna bayama fahimtar abun da suke cewa Yana dai mika musu hannu yace Nagode Yana Nan tsaye Abba ya kirasa ya gaida Wani mutumi bayan sun gaisa yake fada Masa shine mahaifin matarsa snn ya ja sa gefe "Hafeez nasan Kai Mai biyayyah neh siyasa na aura Maka Ummu-khairee Yar amini nah ceh Kuje khaleed ya kaika gdn su kayi hkr kaji"Babu komai Abba na ngd "sosai Abba yaji Dadi yayi ta Saka masa albarka"khaleed ya rakasa gdn dashi da abokansa Babu laifi yarinyar nada kyau da kunya Bai ce mata komai ba sundai Yi pics Yakuma gaisa da iyayenta snn suka fito
Tana xaune ta xabaka uban tagumi labarin daurin auren ya isomata dama tana fama da bugun zuciya sai abun ya karu..... mutane sai murna da adduo'e suke musu wasu siraran hawaye ne suka xubo mata yanxu shikenan naxama matar Aboon shikenan ya rabani da Hafeez nusy ceh tashiga Bata Baki Amma hawayen yaki tsayawa....suna haka akaceh ga angwaye sun shigo Baby bari a gyara Miki fuskar sai muje koh"ni Babu Inda xanyi Nusaiba"cikin lallashi Nusaiba tace "kiyi hkr mn baby Bai kamata kowa ya fahimci bakyason auren ba idan kinsan Wani abun da zai fada Wani bakasan bakin saba kiyi hkr kinji" ganin su awateef da kawayen ta sunyi Gaba yasa itama ta fito kawai suka wuce
Yana zaune saman two seater ya cakare cikin farar shaddah malun'-malun' wacce akayiwa aikin hannu da farin zare kyawunta shine ya bayyana tsadarta komai Daya Sanya fari neh in banda Rolex wrist watch dinsa Daya kasance silver yayi kyau har ya gaji fuskarsa dauke da tattausar murmushi-gefensa aka jeta har tana gogansa sai da ayiki addu'ah da fatan Al-khari kafin angwaye suka tashi suka un-vailing Brides dinsu musawweer ya sakar mata murmushi Yana cewa"Alhamdulillah Ummu-khursum you're finally Mrs musawweer"ita dai kanta a kasa Kuma bataji ya burgeta ba ko kadan sai ma hawaye data hau'yi Nan aka hau pics da video kala kala duk Kuma yawanci fuskarta na kallon kasa shi Kuma Yana kallonta kafin suka fice...........
Hernarn Muhammad鉁嶏笍鉁嶏笍鉁嶏笍
(Mrs Sudais)
Finally Mrs Musawweer馃拑馃拑......Hafeez fans Kuyi hkr bamu barshi hakaba mun Sami Masa Ummu-khairee Amma Muna Baku hkr馃檹馃檹
Congratulations Musawweer fans finally baby matar musawweer ce Allah ya Basu xaman lfy馃敟馃挴