Free chapter · Read without an account
9
Lokaci guda na fita a hayyacina, na ƙara yin wata muguwar rama, na yi duhu.
Auren gaba ɗaya ba ya min daɗi, domin na kai gejin da na ke jina kamar mara lafiya a ƙwaƙwalwa. Wani lokacin har firgita na ke yi. Banda burin da ya wuce dare ya yi, ɓarawon bacci ya ɗauke ni ko na samu salama.
Saboda tashin hankalina a cikin gidan nan shine ace gari ya waye. Da zarar safiya ta yi na shiga fargaba da taraddadi kenan, na abinda zai je ya dawo tsakanina da shi.
Uhmm So kenan, wallahi duk wannan tsananin da na ke ciki, ban ji ko kaɗan soyayyar mijina ta taɓu a zuciyata ba. Duk da cewa na ji auren ya ishe ni, amma ba na jin nadamar aurensa.
Son mijina na ke da dukkan raina, bana fushi da tarin wulaƙancin da yake min. Ina ganin kamar ba yin kansa ba ne.
Shiyasa kawai na ke masa uzuri da kuma addu'a. Addu'ar da tun aurena da shi ban canja akalar yinta ba. Kafin na yiwa kaina, shi na ke fara yiwa.
Ni fa na ma fi so ya zo yana min bambami akan ya share ni, ya zama kwata kwata ba ya magana, ina damuwa da rashin maganarsa gare ni.
Kuma kullu yaumin bana fasa zuwa neman yafiyarsa, da basa haƙuri a kowanne daren kafin kwanciyata. Zan ta haƙuri ba zan karaya ba, Allah na zan ta faɗawa ya daidaita tsakaninmu, ya kuma bani ikon cinye jarabawar.
Yau na tashi da matsanancin ciwon kai, hakan yasa na kasa fitowa gaba ɗaya, tun da na yi sallar asuba na duƙufa kan sallaya. Bacci ma na ke so na koma amma na kasa saboda gabana da ke ta faɗuwa, ga shi ina so na tashi in je in tada yara su yi shirin makaranta, sai dai ina tashi jiri sai ya mayar da ni.
Da ƙyar dai na lallaɓa na tashi a daddafe na fita, ɗakinsu na shiga. Kai tsaye banɗaki na shiga na tara musu ruwan wanka, sannan na fito na tashesh su yi wanka.
Suka tashi da ƙyar kowacce na faman ɓata rai, zama na yi ina lallashinsu da ba su haƙuri akan cewa wata rana sai labari, yanzu ne suke da dama da lokaci na yin karatu, idan ba su yi ba nan gaba za su ciji yatsa.
Haka dai na lallama su da ƙyar su ka sauko suka wuce banɗakin, na jaddada musu da su yi sallah in sun shirya.
Na koma ɗakina saboda sanyin zazzaɓi da ya rufe ni. Ina shiga na ƙudundune cikin bargo ina ta karkarwa, kaina jinsa na ke kamar zai faɗo, haka cikina ma wani bala'in ciwo ya ke min.
Ban ankara ba kawai na ji amai, duk ƙoƙarina na kar in yi akan gadon hakan sai da ya faskara, amai na yi sosai mai wahalarwar gaske.
Gaba ɗaya jikina sai ya saki, da ƙyar na kimtsa wajen a wahalce na dawo na kwanta, hawaye kawai na ke zubarwa, saboda ni ɗaya na san irin azabar ciwon da na ke ji a jikina.
Ina cikin wannan halin aka turo ƙofar ɗakin, Rumana na ji tana cewa,"Anty mun gama shiryawa".
Fito da fuskata na yi ta cikin bargon kaɗan, bana iya ko ganinsu da kyau, murya a wahalce na ce da su.
"Wayata na kan mudubi, ƙarfe nawa?".
Atika ta duba tana cewa,"Bakwai da minti ashirin".
Na rufe idona, har ga Allah ban da wani ƙarfi da ƙwarin da zan tashi in dafa musu abinci.
A hankali nace da su,"Rumana ban da lafiya, ku yi haƙuri ku je kitchen, akwai sauran abincin dare a flask ɗin Abbanku ku ci kun ji. Abincin makaranta kuma zan bayar a kawo muku".
Suka yi shiru ba su ce da ni komai ba, su ka yi cirko cirko.
Tsoron abin da zai biyo baya yasa na miƙe zaune cikin tsananin azabar ciwo, cikin dauriya na yunƙura zan sauko Rumana tace.
"Anty ki koma ki kwanta, a bamu kuɗin makaranta idan muka je sai mu siya snacks kafin a shiga class. Ba zamu iya cin sauran abincin jiya ba".
Na san yanzu Hubbi bai tashi ba, don haka nace da ita,"Duba ƙasan littafin can, akwai ɗari biyar ku ɗauka".
Ɗari biyar ɗin kenan na ke ta riritawa, ko da ace wata buƙatar ta ujila zata taso min.
Ta ɗauko tana faɗin babu canji, nace su je da ita tunda ba su yi breakfast ba.
Nasa ta miƙo min magani, ta fita ta ɗauko ruwa ta kawo min. Na yi musu addu'a tare da a dawo lafiya sannan suka fita.
Rumana ɗin ce mai ɗan sauƙi sauƙin kai, ko yanzu ita ce ta yi min sannu tana Allah ya bani lafiya, amma Atika har suka tafi fuska a murtuke tana ta ƙunƙuni.
Cikin awa guda na kusa shanye sacet ɗin paracetamol, amma duk da haka babu wani sauƙi da nake ji a tare da ni, ciwon ma tamkar ƙara shi ake yi.
Hawaye masu zafi ne ke sauka kan kuncina, idan na yunƙura zan ɗau waya in kira Hubbi, sai in tuna kashedin da ya yi min. Ba kuma na so in kira gidanmu in ɗaga musu hankali, har su san ma halin da na ke ciki, haka dole na haƙura.
Addu'a dai na ke ta yi, da kaɗan kaɗan kuma na ji ciwon na raguwa, tunda har ina iya buɗe idona yanzu.
Cikin baccin da ke son kwashe ni, na ji muryar Hubbi daga can nesa, yana kiran sunana da amon sautin da ya gigita ni ya firgita ni.
Zan iya cewa ban taɓa jin tsoro da firgici irin na kiran da ya yi min a yanzu ba, take kuwa na ambaci Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, domin na san kiran bana lafiya ba ne.
Kafin na kai ga buɗe idanuwana ya banko ƙofar ɗakin, kana jin yadda ƙofar ta bada garam, kasan a hasale yake.
"Sa'idaaa".
Ya ƙara kiran sunan nawa a tsawace, hakan ya daɗa gigita ni, musamman da na ke jiyo hucinsa kamar mayunwacin zaki.
Ta cikin bargon da na ke ƙudundune na amsa, sai dai bai jini ba, ya ƙaraso ciki ya yaye bargon yana sa hannu ya yi min wata muguwar fincika. Sai ganina na yi tsaye akan ƙafafuna a gabansa, da sauri kuwa na rumtse ido, tare da dafe bango jin ina neman faɗuwa.
Na buɗe ido da ƙyar, a ɗan runtse na dube shi nace,"Lafiya? Bana jin...".
Ban ƙarasa furucina ba ya wanka min zazzafan marin da yasa ni zama daɓas babu shiri. A ruɗe na shiga girgiza kai ina kiran sunan Allah, tun da na ke da shi, tun da muke rayuwa, gefen rigarsa bai taɓa sakawa ya duke ni da ita ba, amma yau mari, marin ma a mawuyacin halin da nake ciki. Wato kenan har an kawo matakin da zai fara dukana? Mari fa!
Ban wartsake daga jin zafin ba ya shiga ce min.
"Wacce irin muguwa ce ke mara imani da tausayi, wannan ai tsagoron zalunci ne, banda rashin hankali da tunani irin naki, ki bar yara su fita da sanyin safiya ba tare da kin basu abinci sun ci ba. Haka babu abincin makaranta, Sa'ida haka aka yi miki shi ne za ki rama akan yarana? Wai me yaran nan suka yi miki kika ɗora musu karan tsana? Me yasa ba kya son jinina? Yunwa Sa'ida, kisa fa take yi, ko ke aka bari da yunwa ai an zalunceki balle ƙananan yara, idan Yaran da kika da cikinki ne, za ki iya barinsu su fita makaranta ba ki ba su abinci ba? Ba kya tunanin haƙƙin yaran nan ya biki ya hanaki sukunin rayuwa."
Ya bani damar yin magana ma yaƙi. Kumfar baki kawai yake. Yana ta huci alamun ma ba zai saurare ni ba. Kuma ba zai karɓi uzurina ba.
Sai na ƙara tsorata saboda yana yi kamar zai rufe ni da duka. Ina ta mamakin maganganun nasa.
"Yaran nan fa yanzu ni ne mahaifinsu, ko darajata ai saci ki sassauta musu, amma saboda dai zuciyarki ta yi maƙil da baƙin ciki da zalunci, shi ne za ki dinga azabtar da su, to Allah ya isansu, kuma ni ba zan yafe miki ba...".
Tun marin da ya yi min na nemi ciwon jikina na rasa, kallonsa nake da maɗaukakin mamaki. Idona tamkar an buɗe famfo haka hawaye ke sunturi saman fuskata. Jujjuya kaina kawai na ke na rasa bakin magana.
Cikin kyarmar jiki na kamo hannunsa, na san zafin jikina da ya ratsa shi ne yasa shi ware ido sosai akaina, ina hawaye na shiga ce masa.
"Don Allah ka yi haƙuri, wallahi ko kaɗan ba da gayya ko mugunta na bari su ka fita ba abinci ba. Hubbi ba ni da lafiya, ba ni da ƙarfin da zan iya tashi, ka tambayesu ka ji, har dauriyar tashi na yi na ji ba zan iya ba."
Wahala tasa na yi shiru, anya kuwa ina da lafiya? Kamar fa zuciyata tana buƙatar dubawar likita. Sai da na danne ƙirjina saboda yadda na ke jin yana min zafi sosai, tukunna na ci gaba da ce masa.
"Kai da kanka ka sani, in ba lalura ba babu abin da zai kwantar da ni a ɗaki har wa yanzu. Amma na rantse da Allah ban hana su abinci ba saboda bana Son su, Hubbi ban tsani yaranka ba, ban taɓa jin ina ƙin su ba, balle har in ƙuduri aniyar cutar da su. Allah shahidi shi ne shaidata, yadda zan so ɗan cikina haka na ke sonsu. Hubbi Ƴaƴan ƴan uwanka ne fa, kai kuma ɗin nan Mijina ne da ke matuƙar so da ƙauna. To don me zan ƙi abin da yake naka Hubby? Don Allah ka sassauta fushinka, ka daina faɗin duk abin da ya zo bakinka...".
Buge hannuna ya yi daga jikinsa yana ƙara faɗin,"Shashasha kawai, bagidajiya wadda bata san hakkin yaro ba. Sai ki yi laifi, kuma da an miki faɗa ki fashe da kuka, a hakan kike sona? Idan kina sona ai ba za ki wulaƙanta ƴan uwana ba, ba zaki ƙi yarana ba. Kuma ki sani wallahi tallahi yadda kika azabtar da su da yunwa, haka kema zan hukuntaki daidai da abin da kika yi musu. Sa'ida sai kin yi matuƙar danasanin abin da kika aikata a yau, wawiya kawai. Ƙila ma wannan baƙin halin na ki ya jaza min ban samu haihuwa ba".
Fita ya yi daga ɗakin yana ta surfa masifa, na daskare wuri ɗaya ina bin bayansa da ido, ƙirjina na ji ya matuƙar yin nauyi.
Me na yiwa Hubbi a wannan rayuwar ne? Wanne kuskure na aikata masa da na cancanci irin wannan wulaƙancin da gare shi?
Mijina fa mai kyan hali da nagarta ne, ta ko'ina amfani da yake da tarin ilimin addininsa, amma me ya sauya shi? Sauyi ma mai muni da yake cin zarafin iyalinsa?
Ban san lokacin da na zamo daga gefen gadon ba, gwiwoyina su ka dire a ƙasa, na fashe da matsanancin kuka.
Me yasa aurena zai tashi daga rayuwar farinciki ya juye zuwa rayuwar baƙin ciki?
Mun fuskanci ƙalubale da yawa tun daga haɗuwarmu har auren mu, duk tarin ƙalubalen da muka fuskanta bamu taɓa ji a ran mu cewa zamu haƙura da juna ba, haka har muka yi nasara, amma me ya kawo wannan canjin na muzguna min?
Lokacin da ya kamata ace mun ji daɗin rayuwar mu, mun dulmiya cikin kwanciyar hankali da natsuwa, amma sai tashin hankali da rashin kwanciyar hankali su iske mu.
Haihuwa! Kalmar ta motsa zuciyata, kenan yau da zan haihu shikenan komai zai sauya?
Kowa zai koma sona tamkar a baya? Dangin Miji zasu daina tsangwamata, mijina zai daina muzguna min?
Idan kuma ban haihu ba shikenan haka za'a ci gaba da tafiya?.
Zuciyata ce ta fara jujjuya tunanika, wa ya kamata in kira in shaida masa halin da na ke ciki ne?
Wa zan sanarwa da cewa rayuwar aurena ta juya cikin tsananin baƙin ciki da ƙuncin da ban taɓa tsammani ba, wa zan kira ya lallashe ni ya bani haƙuri da shawara?.
Mahaifiyata ce ta zo cikin kaina, sai dai ba zan taɓa iya kiranta in sanar mata da matsalar nan ba, ba zan iya faɗa mata matsalar gidan aurena ba. Na ƙwammaci in zauna a haka ko zan mutu, har kullum farin cikin iyayena da kwanciyar hankalinsu na ke so, saboda haka ba zan taɓa bari su san halin da na ke ciki ba, komai mai wucewa ne, ina da yaƙinin Allah na tare da ni, kuma hakan duk da ke faruwa da ni jarabawa ce yake yi min. Kuma in sha Allahu zan yi ƙoƙarin ganin na cinyeta.
Na kifa kaina a gefen gadon, idona a rumtse, kalaman cin mutuncin Hubbi nata yawo cikin kaina.
Lokaci guda kuma wani lokaci can baya ya haska a cikin idanuna, yayin da wasu kalamai na lokacin suka haska tarr a cikin kaina, jinsu na ke suna amsawa a ƙoƙon kaina tamkar yanzu yake faɗa min su.
"Na yi miki alƙawarin zan tsaya a tare da ke a kowanne irin yanayi, na yi miki alƙawari cewa duk wata matsala ta hanyarki ni zata fara fuskanta, na yi miki alƙawari zan ba ki kariya ta kowanne gefe. Na yi miki alƙawari ba zan taɓa bari idanunki su yi hawaye ba, na yi miki alƙawari a kowacce rana zan yi ƙoƙarin dacewa da ke, ba zan juya miki baya ba, ba zan taɓa canja miki ba. Na yi miki alƙawarin cire ki daga duk wani baƙin ciki, na yi miki alƙawari Sa'ida! Daga yau da kika zamto Matata, dukkan soyayyata, amanata da rayuwata naki ne ke ɗaya, Ina sonki Sa'ida, alƙawarin dawwamammen farin ciki Habibty".
Waɗannan su ne kalaman da ya furta min a ranar da aurenmu ya tabbata. Bayan ɗaurin aure da suka zo gidanmu gaisuwar surukai, na same shi a ɗakin Yashaik kafin a gama kimtsa cikin gidan su shiga.
Lokacin da na shiga ɗakin, na tsaya na kasa zama wurin da yake min nuni saboda kunya.
Hakan yasa shi tasowa ya tsaya gabana, tare da kamo hannayena duka biyun ya saka cikin nasa ya haɗe. Kaina na ƙasa a wannan lokacin, amma haka ya ɗago fuskata da dogon hancinsa, ya tilasta min saka ƙwayar idona a tasa, kafin ya shiga karanta min waɗancan kalaman, kalaman da ya faɗe su fuskarsa na washewa da murmushin farin ciki da jin daɗi, gami da alfahari.
Sabbin hawaye masu zafi suka shiga zubo min, a raina ina tambayar duk ina wannan tarin alƙawarin da ya yi min?
Shin mantawa ya yi? Ko kuma yasa ƙafa ya yi fatali da su ne? Wacca gazawa na yi da na fita a ransa?
Doguwar ajiyar zuciya na sauke, ina tunawa da farkon rayuwar aurenmu. Kawai na saki murmushi mai ciwo, ko ba komai, na yi farin ciki tare da shi ko ya ya ne, kuma ina alfahari da iyaka wannan ma.
Na tsayar da kukana, na miƙe na shiga banɗaki na wanko fuskata, na gyara jikina sannan na fita jiki a saɓule.
Tunanin me zan dafawa yaran cikin ƙanƙanen lokaci kawai na ke yi, don bana so ya ƙara zuwa ya ci zarafina, gwara na yi gaggawar dafawa a kai musu makaranta.
Wannan tashin hankalin bana son sa, abu kaɗan ya tunzura shi ya hau sama. Koma dai menene ya shiga tsakanina da shi Allah ya yi min maganinsa.
Ina ta tunanin ma abinci mai daɗi da zan dafa musu, wanda zai gusar da rashin jin daɗin da na haifar musu su da Babansu.
Gwara in wanke kaina daga zargin da yake min na bana son Yaran.
Cikin karsashi na sauka daga benen, tunawa da abincin da suke matuƙar so. Sai dai da zuwana ƙofar kitchen, na murɗa handle na ji ƙofar a rufe. To ai bana rufe kitchen, ko kuma lock ne ya shiga mistakely. Ɗakin ƙasa na shiga duba maƙulli sai na tarar duk basa nan, sai na zaga ta ɗaya ƙofar, itama na ji ta a rufe.