Waye Shi?

Biyu.

by @ayshashafiee1


(☆_☆)

Nanne na sauka k'asa taci karo da Baba Azumi shugaban ma'aikatan dake kula da girke girke. Mace daya a cikin kalilan d'in 'yan aikin gidan dake nuna mata kauna.

"A'ah uwata ce da sassafen nan?"

Ta sake turo bakin daya zame mata jiki.

"Wallahi ba yadda na iya ne inna ce ta taso ni, ya akayi Kema kika fito da sassafen, wani abun za'ayi yau?"

"Yo, mu ai fitar safe yanzu ta ganmu, kin san masu kawo lefen jamila da safe suka taso, kuma kila wajen azahar zasu iso tunda a gobe zasu koma, ga aikin tarbar tasu da yawa."

Nanne ta d'an zare idonta tace.

"kice yanzu gabad'aya gidan zai tashi."

Don lefen jamila shine na karshe da za'a kawo kuma wanda kowa yafi d'okin gani a cikin na yayyen nata hud'u da za'a aurar, kasancewar wanda zata aura din a can nijar yake, d'an wata yayar baffan nasu ne da suke kamar cousins ita da baffan, kuma k'anin mahaifin baffan ne ma ya had'a auren, a cewarsa sunyi nisa da danginsu hakan zai dad'a kusanci tsakaninsu ya kuma sa zumunci ya d'ore.

Shine da akace baffan ya bada 'yarsa ya had'a da jamila 'yar gidan mama rabi, wanda zuwan yaron d'aya wajenta, aka tsaida maganar auren tare da nasu Aisha d'iyar hajiya babba da zata auri cousin d'inta, da Nafisa da maryam 'ya'yan mama halime.

Dama kusan duk sa'anni ne su hud'un, har ana zasu tafi su bar ita jamilan kasancewar ta dorawa kanta akidar sai mai kudi zata aura, don kowa shaida ne a gidan bata saurayi sai d'an wani babba ko mai nauyin aljihu, to sai abin yazo a daidai, don wanda zata aura d'in mai suna Al'ameen, mahaifinsa shahararren mai kudi ne a nijar d'in, shi kansa baffan ma bai sanshi sosai ba saboda gabadaya karatunsa a k'asashen waje yayi, shi yasa ma da akayi had'in babu wanda yaji bakin jamilan ko ita mama rabi akan basa so.

Wanda da ace bashi da kudi, kowa a dangi sai yaji masifar da zasu yi wadda zata sa a fasa auren. Amma yanzu mama rabin bata da magana sai habaicin cewa ana yiwa 'yarta kishi.

Kuma kusan hakane, don hajiya babba ce kawai bata sa ido akan auren ba, saboda ita irin k'ananan abubuwan nan wani bata ma sanin anyi, danginta na uwa da uba kaf! masu arziki ne, shi d'an wan nata ma da Aisha zata aura in bai fi su Al'ameen d'in kudi ba zasu iya karawa.

Amma mama halime ba wanda ya kaita kishi, ganin ita har 'ya'ya biyu zata aurar, amma duk cikin mazajensu ba wani mai shahararren arziki sai dai rufin asiri, duk da cewar kuwa 'ya'yanta sunfi kowa gayu a gidan.

Don a lokacin da taji zancen ma cewa tayi kamata yayi tunda itace mai 'ya'ya mata baffa yayi had'in da zainab, wai ai jamilan tana da tarin samarin dake sonta. Sai dai sanin kanta ne baffa ba zai taba yin hakan ba, tunda jamilan itace gaba da zainab.

Ita kuwa Aunty amarya bak'in cikinta bai wuce na cewa 'ya'yanta sune k'anana a gidan ba basu kai minzalin da za'a fara damawa dasu ba, tunda 'yan biyunta manya sai yanzu suke jarabawar fita daga sakandire, Kuma ko a cikin mazan sune k'anana, don muhammad da nasir ma 'ya'yan hajiya babba aiki suke yi banda Ahmad ma da yayi aure, ishaq ne kawai ya koma k'aro karatun masters, suma 'ya'yan mama rabi bayan ibrahim da yayi aure, sulaiman da umar duk aikin suke yi.

****

"ke don uw**ki ina zaki da sassafen nan?"

Muryar sulaiman ta katseta a daidai barandar waje, d'a na biyu a wajen mama rabi, yana tsaye daga jikin 'yar karamar katangar data raba k'ofofin d'akunansu da hanyar shiga gidan yana danne-danne a wayarsa, har tayi tunanin me yasa bai tafi aiki ba ta tuna cewa duk ranar da za'a fitar da kaya a gonar baffa tare da mazan gabadaya yake zuwa, har da masu auren ma kuwa, ita ko kadan bata kula ta wuce shi bama, a ranta tace.

Ba dai uwata ba sai dai taka.

"Nace ina zaki?"

"Inna ce take son auduga, shine zanje in yiwa salisu bayanin irin wadda za'a kawo mata."

Ya d'ago ya kalleta.

"Duk mutanen da zasu je ba wanda zai iya fad'a masa sai ke?"

"Ni ta yiwa bayani ne don zai fi saurarata."

Ya kalleta da mamaki.

"Saboda ke k'anwar babbarsa ce?"

Tayi kamar tace wani abu amma sanin hakan zai iya zama kamar ta zage shi ne yasa ta had'e rai ta juyar da kanta gefe.

"Koma ciki kafin in take ki."

Dama abinda take jira kenan, saboda haka tun kafin ya rufe baki ta taho fuuu! ta wuce shi.

"Yo, daya dawo min dake shi ya san irin wadda nake so ne koko ma zai fad'awa salisun ne?"

Inna ta tambaya tana kallon nanne dake cin d'umamen da mama Azumi ta kawo bayan fitarta.

Hankali a kwance ta daga kafad'unta.

"Nima ban sani ba...tunda har ya iya zaginki ina ruwansa da wata audugar da kike so."

"Wai ni ya zaga b'aro-b'aro?"

Ta saki lomar data d'auko cikin hannunta.

"Toh inna uwata fa yace, a duniyar nan ina da wata uwar ne bayan ke..."

Inna ta sake kwafa tana kokarin tashi.

"Rabu dashi dani yake zancen, Allah zai kawo shi har nan wajen ina zaune, daga shi har tasa uwar kuwa da yake tak'ama da ita."

Awanni hud'u bayan haka, Sadiq d'an wajen Aunty amarya dake sa'an Nannen ya shigo rik'e da wata k'atuwar leda cike taf! da farar audugar. Ya dire ta a gaban inna wadda ta hau dubawa tana sababinta, sannan ya matsa kusa da nanne dake yankan farcenta ya d'an sunkuyo yace.

"'Yan mata..!"

Taja wani dogon tsaki ba tare da ta d'ago ba, tun lokacin da ya samu labarin cewa in tana yarinya aka tambayeta ita mace ce ko namiji sai ta fara kuka tana cewa ita 'yanmata ce shikenan ya addabe ta, dama k'iris yake jira ya samu wani abin da ya san bata so, tunda a duniya burinsa kawai yaga ya tsokane ta.

"ke kika d'aukewa ya suraj kayansa da aka shanya a baranda? tun jiya yake nemansu."

Jin haka yasa ta d'ago da dara-daran idanunta ta kalle shi.

"Shi yace maka ni na d'auka, a ina zanga wasu kayansa ma balle in d'auka."

"Na san zaki iya daukar ne shi yasa na tambaya, in ma kece gwara tun wuri ki mayar masa, don wallahi ransa ya b'aci kuma yanzu zasu dawo, nima don yaya sulaiman yace in biyo su Aminu ne da tare zaki ganmu."

Caraf! kuwa inna ta karbe zancen.

"Kaga ni bana son neman tashi hankali da safiyar nan, daga aiko ka kuma sai ka soma bin ta da sharri, ina nanne ina wasu kayan surajo?"

"Rabu dashi inna, in ma na d'ebo ai dole nan zan kawo kuma zaki gani."

Sadiq yayi dariya kafin ya juya yana fad'in.

"Ni dai na fada miki, don wallahi kin san halinsa."

Ta sake jan tsaki sannan ta mike ta shiga bandaki don d'auraye hannunta. sai dai wani b'arin na zuciyarta tsoron kar da gaske sadiq yaje ya fadawa suraj cewa ita ta dauki kayansa ne, don ta tabbata ko muryar inna zata dushe wajen fad'a sai ya jibgeta kamar yadda ya saba, shi yasa ko kad'an basa shiri da inna.

Tana fitowa ta nufi can kasan kayan wankinsu inda ta cusa kayan nasa, kala biyu na shaddar gezna, wadda baffa ya bayar akayi musu aiki tun daga maiduguri, ta sake duk'unk'une su a ranta tana fad'in.

Ba dai ni zaka yiwa tsawa a gaban abokanka ba, wallahi haka zanyi ta kwashe duk wani abun da kake so.

Ta fada a zuciyarta.

●﹏●