Waye Shi?Free

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

Waye Shi?

  • 1views
  • 2chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

Sample · Farko.

(☆_☆)"Nanne! nanne! nanne!!...ki tashi nace koh?"Yarinyar da aka kira da nanne ta motsa sannan ta cigaba da baccinta,"Zaki bude ido ko sai na tashe ki da ruwa..."Inna ta fada tana dad'a girgizata, jin haka yasa ta zumb'ura baki sannan ta mike tana murza ido ta cikin dogon gashin kanta daya hargitse ya rufe fuskarta."Ki tashi ki wanke ido ki fita tun kan salisun ya tafi, kin san tun jiya muka yi haka dake."Nanne ta dago ta kalli agogon dake kafe a dakin, k'arfe takwas da kwata na safe, gabadaya baccin da tayi bayan sallar asuba ma bai kai fi na awa biyu ba. Kwata-kwata ta manta sunyi da inna cewar yau zata je da safe ta gayawa salisu irin audugar da zai d'ebo mata a gonar baffansu wajen daza'a fitar da auduga yau kafin masu siyen kamfani su d'ebe masu kyan ciki, wai da ita zata yi sak'ar mayafan da amare zasu yafa ranar wankan amarya (Hakan wata al'adarsu ce ta wata kabila daga nijer)"Allah inna da kin san gajiyar da na kwanta da ita da kin hakura wani daga cikin su yaya umar kawai ya fad'a masa."Kema kin san ba ganinsu zanyi kafin su fita ba don haka ki tashi ki d'auraye ido kije tun kan salisun ya tafi na san zasu fara yin gaba, don tun dazu nake jin dirin motoci zasu fara tafiya."Nanne tasa hannu ta tattara gashinta baya sannan ta tufke shi, ta shiga band'akin dake jikin d'akin ta zuba ruwa a buta ta wanke bakinta da fuska sannan ta fito, inna ta miko mata hijabi daga inda take zaune."Haba dai, wannan ya cukurkude, bari in duba wani."Ta bud'e wardrobe ta janyo wani mai d'an tsaho ta zura sannan ta karbi k'atuwar ledar da innan ke nuno ta dashi."ki masa bayani kamar yadda na fad'a miki jiya dan Allah."Yadda ta marairaice murya yaso ya bata dariya sanda ta fita daga dakin, da yake a hawan farko suke tana iya hango k'aton tsakar gidan da ba mutane sosai saboda safiya sai daidaikun 'yan aikin dake wucewa akai akai.Ginin gidan nasu dake cikin wata unguwa a katsina, dad'ad'd'e ne da akayi shi da dakakken gini da ko k'usa ba kasafai take huda shi ba, sannan gabadayansa hawa uku ne, daga bakin gingimemen gate din dake jikin zungereriya katangar data zagaye gidan, faffad'ar haraba ce da tsaf zata d'auke bikin masu dangi, akwai manyan rumfuna na ajiyar motoci da kuma shukar fulawowi data zagaye filin gabadaya.Daga can jikin ginin gidan kuma doguwar baranda ce data bi tsawon fad'in wajen inda d'akunna ne a jere guda shida na yayyansu maza, a tsakiyar su kuma k'atuwar kofa ce data shigo ciki zuwa bangaren baffansu dake daga dama, inda ya had'a da k'aton falo na saukar bak'insa da kuma d'akuna biyu a ciki da bandaki, daya gefen hagu kuma k'aton kicin din gidan ne wanda shi kansa waje biyu ne dashi, da b'angaren da aka kafe da durowoyin ajiya, sai madafi inda ake jibge tarin itace da kuma manya-manyan tukwanen girki.Bayan shi babu komai a k'asan sai manyan...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters2
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play