DUHUN ZUCIYA

Page 6-10

by @phartybb

6-10

Da gudu ya tashi daga zaunen da yake ya taho wajen Radiyya cikin murna. Ta yi farin cikin ganinsa, hakan yasa ta buɗe masa hannuwanta ya shiga ta mayar ta rufe ta rumgumesa, ta yi kewarsa sosai, shi ɗin na musamman ne a gareta, sun yi sabo sun shaƙu, tun zuwansa duniya ya buɗe ido ya ganta, ta ya zai iya kwana ya wuni bai sa ta a idanuwansa ba.


"Kin ga ni ko Umma?"

Faɗin Mimi tana kai ƙosai bakinta. Idanuwan su gaba ɗaya akan Radiyya da Walid da suke rumgume da juna cike da farin ciki.


Umma da ta miƙewa don gabatar da sallah ta ce.

"Ban san me akan yarinyar nan ba? Ba dan Baban ku da ya ce in barta zuwa nan da azumi ba ko za ta canza ra'ayi, da babu abin da zai hana na sa ta dolenta ta koma."


"Yanzu ma Umma ta yi haƙuri ta koma don Allah."

Mimi ta ce har lokacin tana kallon Radiyya da Walid.


"Ga ki ga ita."


Daga haka Umma ta wuce ɗaki ta bar Mimi zaune. Tun karfe huɗu da rabi da ta gama haɗa kayan shan ruwa ta ɗauka ta taho gida, akan idan sun sha ruwa ta roƙi Radiyya su koma tare.

Zuwanta ta samu labari ta fita talla a bakin Umma, tun da ta ji ba ta nan take roƙar Umma, ta bi hanyar da duk za ta bi Radiyya ta koma gidanta. A fili ta nuna sun yi tsantsar kewarta da rashinta, cikin zuciyarta kuma ta gaji da wahalar aikin gida da hidimar Walid, ga Uncle ya fara canza mata motsi kaɗan faɗa, sai faɗin Radiyya ta fiki ka za, ta iya abu ka za. Dole yau ta yi tattaki ta zo roƙar Radiyya su koma, ko rayuwar aurenta zai gyaru.


Radiyya da suka saki juna ita da Walid ta ja shi suka yi alwala, har ƙasa ta durƙusa ta gaishe da Aunti Mimi, abin mamaki da fara'a ta amsa mata, ruwa kawai Radiyya ta sha ta shiga ɗaki don gabatar da sallah, ganin haka Aunti Mimi bin bayan su ciki.

Umma ta idar tana lazimi, Radiyya da Walid tare suka gabatar da na su, Aunti Mimi ce ƙarshe, bayan ta idar ta dubi Radiyya.


"Yanzu ke haka bai fi miki ba. Ko ba ki yi kewar yaronki ba?"


Radiyya da tasan da ita Aunti Mimi take, murmushin ƙarfin hali ta yi ta ce.

"Na yi Aunti."


"Ki bi ni mu koma mu ci gaba da rayuwar mu Radiyya. Ni ban san me muka miki ba lokaci ɗaya ki ka bijire mana? Ko kin manta tun tasowarki ki ke gabana, shekarunki goma sha biyu da haihuwa ki ke gurina, tun da na yi aure. Haifarki ne kawai ban yi ba Radiyya, amma alheri na miki daidai gwargwado."


Shuru Radiyya ta yi tana sauraran maganar Aunti Mimi, gefe ɗaya kuma tana tuna irin rayuwar da ta gudanar a gidan. Tun da ta fara mallakar hankalin kanta ita ce shara, wanke wanke, lokacin da ta haihu kuwa kula da yaron su tamkar ƴar raino ta zama, hatta ga mai gidan ita take kula da cin sa da wasu abubuwa. Tun da take a rayuwa ba ta taɓa jin inda Yaya ta mayar da ƙanwarta tamkar ƴar aiki ba sai a kanta. Duk abubuwan da take yi bai tsaya nan ba, bai gode ba mata ba sai lokaci ɗaya ta fara fuskantar mummunar farmaƙi daga wajensa, a matsayinsa na mijin yayarta.

Abu mai ɗumi ta ji yana bin kumatunta tasa hannu da sauri don tabbatar da menene, ruwa ta ji, ta ciro hannunta ta duba, nan tasan da hawaye ne ya zubo daga idanunta, ba ta san lokacin taruwar su ba balle zubar su, jin zuciyarta take yana zafi, wani tsanar su na shiga kowane ƙofa na jinin jikinta. Kallon Aunti Mimi ta yi da har lokacin haƙuri take bata me cike da gorin alherin da ta yi wa rayuwarta da mahaifiyar su, hatta da Baba Ƙarami da yake riƙe da su.


"Me ki ka ce Radiyya? Baba zai amince amma sai da yardar ki. Kin fi so kina fita layi kina talla da girmanki, kina rayuwa a gidan da cin yau da gobe sai an nema."


Kai Radiyya ta mayar ƙasa kamar ba za ta ce komai ba, ko abin da za ta faɗa ba zai fito a bakinta ba ta ce.

"Aunti ki yi hakuri amma na fi son zaman nan, kuma sana'a ta ba talla bane duk da ba shi da maraba da tallar, amma ina so a hakan, domin ina samu daidai gwargwado, nafi sauran mata da suke zaune sai dai a ba su."


"Kina nufin ba za ki koma ba?"

Faɗin Aunti Mimi da mamakin furucin Radiyya.


Kai Radiyya ta ɗaga ta kasa ɗagowa. Cikin jin haushi Aunti Mimi ta yi kan Radiyya za ta daka, da sauri Umma ta hanata.

"Ki rabu da ita Mimi, tafi son ganinta a wannan rayuwar, barta tun da ta zaɓawa kanta haka."


"Amma Umma...?


"Rabu da ita, kina zaune za ta zo ta sameki."


A fusace Aunti Mimi ta miƙe ta fizge Walid a jikin Radiyya ta fice, ko jin Umma ba ta yi ba. Radiyya kuka ta ci gaba da yi tuna irin mummunar hatsarin da ta kuɓuta da rayuwarta, abin da zai mayar da ita gidan nan babu shi sai dai gawarta za a kai, za ta rufa masa asiri ko ta ce ta rufa masa ma, amma suna ƙoƙarin ganin sun tona komai shi da ita. 

Haka daren Radiyya ta kasa gane kan Umma, duk da dama ba magana suke ba sosai. Radiyya da ciwon kai ta kwana don kuka da damuwa.

Kamar yanzu da take kwance, hawaye take zubarwa lokaci zuwa lokaci tana share su, tunanin nata rayuwar take, kullum da abin da zai ɓullo, lamarin Aunti Mimi da Uncle Nasir ya fara isarta, sun bi sun juya mata duniya da rayuwa, gaba ɗaya ji take ta tsane su, Uncle Nasir da Aunti Mimi sun cika mata zuciya da duhu, sun saka mata DUHUN ZUCIYA. Tana wannan tunanin barci ya kwasheta.


Washegarin ba ta fita kasuwa da wuri ba sai kusan sha biyu, shi ma da ƙyar don dole ne, haka ta dawo ta iya abin da za ta yi ƙarfe biyar ta fita da kayanta. Yau hatta Sahabi ya lura ba ta da walwala, kaɗan ne. Shida da mintuna komai ya kusa karewa tana faɗin idan ba a siya ba idan da rabi ya yi za ta tafi, nan taga shigowar wasu motoci masu shegen kyau guda biyu gidan man. Da kallo ta bi motar har suka samu guri suka faka, ganin za a fito ya sa ta ɗauke kai babu shiri, ta san dai ba za su saya abin naira ɗari ba, balle ma gani ta yi tamkar ba mai suka zo sha ba.


Sahabi gaba ɗaya ya rikici ganin Ogansa, mutumin da ya sanar da shi sai bayan sallah zai dawo kamar yadda yake kowacce shekara, gaba ɗaya ya rasa sukuni, burinsa ya samu Radiyya ya sanar da ita ta tafi, kafin ya rasa aikinsa ta rasa kayan sana'arta. 

Alhaji Shaheed kai tsaye bayan sun gaisa da Sahabi ya nemi ruwan alwala ganin magriba ta yi. Babu musu Sahabi ya ɗauko masa pure water biyu cikin wanda zai sha ruwa, ya ba shi da abokinsa da suka shigo tare. Bayan sun gama Sahabi ya yi nasa alwalar.


"Sahabi babu wani abin sawa a baki kafin mu ƙarasa gida? Sai da na sanar da shi magriba zai mana a hanya amma ya ƙi yarda."

Faɗin abokin Alhaji Shaheed yana gyara agogonsa.


Sahabi da duk ya rikice ya girgiza kai.

"Iya abun da nake da shi, sai dai idan zan karɓo muku abin sha a shagon big son."


"Wannan zoɓo ne?"

Alhaji Shaheed ya yi tambayar da Sahabi ya ji cikinsa ya murɗa gudawa zai zubo, da ƙyar ya ɗaga kai ya haɗiye iska mai zafi domin yawun bakinsa ya kafe.


"A ina ka siya? Ka karɓo mini ɗaya. Fatan hannu mai kyau ne ya yi?"


Kai kawai Sahabi ya girgiza, ji yake kamar ya ɗaura hannu a kai ya kurma ihu, kashinsa ya bushe, yau ya kaɗe har ganyensa.


"Yi sauri Sahabi kar a ƙira salkah don na fara ji kamar ma wasu masallatai sun fara kira."

Faɗin Kabir ganin Sahabi ya kasa tashi.


Jiki a saɓule ya miƙe ya juya zuwa ga Radiyya, ta miƙe kenan jin kamar ana ƙiraye ƙirayen sallahr magriba, kayanta ta tattare ta nufi gurin Sahabi da ya nufeta da sauri ganin ta taso. A tsakiyar wajen suka haɗu, murmushi ta ƙirƙiro tana faɗin.

"Sai gobe, zan tafi kawai duk da akwai kusan biyar bai sayu ba, dare ya yi."


Kai ya girgiza zai yi magana ya ji Alhaji Kabir da ƙarfi ya ce.

"Yi sauri Sahabi."


Jin maganar su Radiyya ta kalli gurin, ido biyu suka haɗa da Alhaji Shaheed, ta ɗauke kanta da sauri jin zuciyarta ya buga ganin irin kallon da yake aika musu. Tana ƙoƙarin bin gefe ta wuce Sahabi ya tare hanyar.


"Radiyya ba ni zoɓo uku."


Babu musu ta ajiye kular ta buɗe ta miƙa masa, yana karɓa ya ce.

"Alhaji Shaheed ne da kansa yake nema."


Jin abin da ya faɗa babu shiri Radiyya ta sake goran, ba dan ya riƙe ba da ya zuɓe ƙasa. Tsoro ne ya bayyana saman fuskarta ta ce.

"Wanene shi a ciki? Ko dai wancan me farin kaya? Ko wanda ya ƙira ka?"


"Ki nutsu ƙanwata ni kai na a rikice nake, sai abinda ya zartar, zan ƙiraki ga kuɗinki."


"Ka bar shi kawai."

Ta ce tana mayar da hawayen idanuwanta. Daga haka ta ɗauki kulolin ta yi gaba da sauri, tasan ma ba zai amince ta ci gaba da zuwa ba, tsoronta kar abu ya samu Sahabi dalilinta, ko ya rasa aikinsa.


Bayan Sahabi ya karɓa ya koma gurin su ya miƙa musu, babu musu suka karɓa daidai lokacin an ƙira sallah a masallacin jikin gidan man.

Da bismillahi ya buɗe ya kurɓi zoɓon, wani sanyi da ƙamshi ne ya shige sa, ji ya yi ya kasa haƙura da shi ya ƙara kaiwa baki, wannan karon bai cire ba sai da ya shanye tas. Bai taɓa jin daɗin zoɓo irin wannan ba, ko don ya kasance ma'abocin son ne kuma da ƙishirwa a tare da shi.

Bayan ya ajiye goran ya ɗauki ɗayan yana ƙoƙarin buɗewa, da sauri abokinsa Kabir ya hanasa.


"Kai don ka ga abokinka shi he har da ƙari? To ni zan ƙara da wannan, don gaskiya na ji daɗin zoɓon."


Murmushi Alhaji Shaheed ya yi ya miƙe riƙe da goran.

"Sai ka jira na gobe, kasan babu me raba ni da zoɓo idan na gani."


"Shikenan amma don babu yadda na iya ne."


Kabir ya ce daga haka shi ma ya miƙe, bayan Alhaji Shaheed ya ajiye zoɓon a mota suka nufi masallaci don gabatar da sallah, ana idar da sallah suka fito anan ya samu keɓewa da Sahabi. Bayan sun tattauna akan ci gaba da ake samu har Sahabi na ƙara da cewa.

"Alhaji a sayi ɗayan, nan an samu ci gaba da kasuwa sosai."


"Haka ake so. Sai dai Sahabi ka karya mini doka, ko kasan da haka?"


Sani laifinsa ya sa shi yin ƙasa da kai yana cewa.

"Na sani Alhaji a gafarce ni, na kula tana da tsafta ne da bin dokoki."


"Hakan ya sa nasha abin hannunta. Wacece ita?"


"Ƴar uwata ce Alhaji."


Kai Alhaji Shaheed ya jinjina yana faɗin.

"Ta ci albarkacinka, sannan ta shayar da ni da abin da nake so a rayuwata bayan na wuni da ƙishirwa, ta ci gaba da tallarta amma tabi dokoki, bana son kazanta a guri. Kamar ma bata karɓi kuɗinta ba."


"Eh ta ce ta yafe."


Kai kawai ya girgiza ya yi gaba inda Kabir yake jiransa. Sahabi tsabar daɗi bayan wucewar su har da ihunsa na murna, bayan Alhaji bai masa faɗa ba ya bar Radiyya ta yi sana'arta a wajen, yasan duk dalilin zoɓonta ne da ya ji daɗinsa. Kasancewar yana da layin wayarta a take ya ƙira ya sanar mata. Radiyya ta yi murna sosai.


....


A hanya ya shanye ɗayan goran zoɓon, Kabir tun a gidan mai kowanne ya kama hanyae gidansa suka yi sallama. Bayan ya isa gidansa da ya amsa suna gida. Da fara'a Hajiya Fauzy ta tari mijinta tana masa ya hanya. Murmushi ya mata ya zauna, nan ta kawo masa abincin da ta girka masa na shan ruwa, bayan ta zuba masa ya hau ci suna hira sama sama, abinci kawai ya ci, ya kasa shan komai na gwangwani, har lokacin tunanin zoɓon yake, ji yake daɗinsa da garɗi ya ƙi barin ƙwaƙwalwarsa. Yana gamawa ya wuce masallaci don sallar Taraweeh.


Gurin Hajiya Fauzy ta sa mai aikinta ta tattarewa ta kimtsa wajen, ita kuma ta haye sama don shiryawa taran mai gida.


...


Washegarin da ƙarfin guiwa Radiyya ta tashi, da wuri ta gama ayyukanta, wanki ta haɗa nata da na Umma ta siya sabulu da kuɗinta ta fara yi, har sha biyu Umma da ta ga ba ta da niyar zuwa kasuwa ko fara aikinta ta kwala mata ƙira. Hannunta ta ɗauraye bayan ta amsa ta nufi ɗakin.


"Yau ba za ki je kasuwa ba ne?"

Umma ta tambayeta bayan shigowarta.


"Ina da sauran kaya zai ishe ni na yau, yanzu idan na gama wankin zan fara haɗawa."

Faɗin Radiyya da mamaki.


"Ya yi kyau. Ki je ci gaba da aikin ki."

Umma ta ba ta amsa. Miƙewa ta yi ta fita.


Ƙarfe biyar da rabi Radiyya ta fita a gida don ba ta samu ta gama da wuri ba, ga Sahabi sai doka mata ƙira yake.

Bayan ta isa ta samu ana jiranta mutane dayawa, ɗaya bayan ɗaya ta samu ta sallame su, abin da ya rage kaɗan ne ta zauna hutawa don yau ƙishirwa take ji don aikin da ta sha.

Tana zaune mutane biyu suka siya, ta ba su ta zauna kenan motar jiya ya shigo, kallo ɗaya Radiyya ta yi wa motar ta sunkuyar kai.


Yau bai fito ba, daga ciki ya ƙira Sahabi, bayan sun yi magana ya taho wajen Radiyya, har ya iso kanta a ƙasa sai da ya mata magana.


"Ƙanwata ki kawo gora biyu."


Jin muryar Sahabi ta ɗago kai, to tace ta buɗe kular ta ciro ta ba shi ya miƙa mata kuɗin, kai ta girgiza.

"Ka bar shi idan dai na Alhaji ne."


"Haƙƙin ne fa."


"Allah ka bar shi na yafe."


Duk yadda Sahabi ya so ta karɓa ƙi Radiyya ta yi, dole ya koma wajen Alhaji Shaheed a cikin mota ya ba shi aikensa ya sanar masa Radiyya ta ƙi karɓar kuɗin. Bai ce komai ba yaja motar sa ya bar gurin.

Ƙarfe shida da kwata Radiyya ta yi wa Sahabi sallama ta tafi gida, yau kayanta ya ƙare tas babu abin da ya rage. 


....


Haka Radiyya ta ci gaba da sana'arta tsawon azumi yana da kwana goma sha biyar, sosai take samun riba da ci gaba a ciki, har ta fara asusun kullum duba ɗaya duk Umma ba ta sani ba, a ciki kullum take ajiyewa Umma ɗari biyar idan za ta fita. Kullum idan za ta dawo daga gurin sana'arta tana siyawa ƴan gidan lemo na shan ruwa. Umma ta yi faɗan ta rabu da ita don Radiyya ba ta da rowa sam, ba ta sam faɗa ba ko ƙiyayya. Aunti Mimi ba ta ƙara zuwa ba tun ranar.



#votes

#comments

#keeplove

DUHUN ZUCIYA


Babi Na Bakwai


Pharty BB

Wattpad PhartyBB


Yau Radiyya ba ta fita da wuri ba sai kusan shida saura na yammaci. Duk a firgice take sakamakon abin da ta ci karo dashi kafin fitowarta, hakan ya sa gaba ɗaya tunaninta ba ya tare da ita. Har suka isa ba ta san sun iso ba, har sai da mai adaidaitan ya sanar mata. Hankalinta gaba ɗaya ya tafi wani yanayin, har sai da ya sake maimaita maganarsa da ɗan ƙarfi kafin Radiyya ta dawo hankalinta a tsorace tana dubansa.


"Mun iso!"

Ya ƙara faɗa, hakan ya sa ta kalli wajen ta ga lallai sun iso, fita ta yi a ciki. Ganin haka mai adaidaita ya sauka ya taimaka mata ta kai wajen da take ajiyewa. Bayan ya ajiye ta biyasa kuɗinsa kafin ta nemi gurin zama. A kowanne daƙiƙa tsoro ne yake ziyartar zuciyarta yayin da fargaba yake biyo baya. Ta rasa wani irin tunani za ta yi wa wannan lamari.


"Kar fa ya zamto gaskiya."

Radiyya ta faɗa a ranta tana haɗa kai da gwuiwa, kuka take son yi ko za ta ji sauƙi daga raɗaɗin da take ji a ranta. Ta tafi duniyar tunani ba ta san Sahabi ya zo saman kanta ba har sai da ya tsugunna da ƙarfi ya ce.

"Radiyya!"


Ta tsorata sosai ta ɗago a firgice, ganin wanene ya sa ta sauƙe mugun ajiyar zuciya, sai dai hakan bai hana jikinta yin rawa ba.


"Lafiyarki ƙalau?"

Shi ne tambayar da ya mata yana bin ta da kallo. Ya hango tsantsar damuwa a fuskarta, hatta ƙwayar idanuwanta sun kasa tsayuwa waje ɗaya.


Kai ta girgiza alamar eh, sai kuma ta yi saurin gyada kai tana faɗin.

"Lafiya lau. Azumi ne."


Bai yarda ba sai dai baya son shiga hurumin da ba nasa ba, ko wuce gona da iri, hakan yasa ya miƙe, bai ce mata komai ba ya bar gurin. Har ya koma wajen aikinsa ya fara sallamar mutanen gurin sannan Radiyya ta ɗauke kanta daga gareshi. Ji ta yi tamkar ba ta kyauta ba da ta kasa sanar masa da matsalarta, sai dai can ƙasan zuciyarta ta kasa hakan don tana ganin hakan sirrinta ne. 

Haka Radiyya ta yi cinikin ranar babu walwala a tare da ita, ga azumi ga tunanin da ya sa ta gaba ya haifar mata jin zazzaɓi. 

Shida da mintuna talatin da ɗaya ta masa sallama ta nufi gida, tana shiga gidan ta samu kowa na aikin gabansa. A dadafe ta watsa ruwa ta ɗauro alwala ta shiga ɗaki, kwanciya ta yi jin zazzaɓi yana neman rufeta, ta kasa fita wajen Umma su sha ruwa.

Umma ganin har an fara ƙiraye ƙirayen sallahr magriba babu Radiyya kuma babu motsinta a ɗaki ya sa ta miƙewa da sauri ta shiga ɗakin, can ta hangota kwance, da sauri ta nufi gurin tana yaye hijabin da ta rufe fuskarta da shi.


"Radiyyatu lafiyarki?"


"Umma zazzaɓi nake ji."


Tsakanin uwa da ƴa sai Allah, wani tausayin Radiyya ne ya ratsa zuciyar Umma ta tallafota ta zaunar, ba ta ce mata komai ba ta miƙe ta fita. Ɗauke da kofi cike da koko ta shigo ɗakin da kuma ruwa, gefen Radiyya ta duƙa ta ajiye sannan ta miƙe.

"Ki daure ki sha na aika miki magani."


Kai kawai Radiyya ta gyada ta ɗauki kunun ta fara sha, Umma kuma hijab ta ɗauka ta fara sallah. Rabin kofi Radiyya ta sha ta kurɓi ruwa kaɗan, ta miƙe don gabatar da sallah kenan yaron da Umma ta aika siyo maganin ya yi sallama ya shigo.


"Ga shi Umma ta aike ni magani."


"To an gode."

Radiyya ta faɗa tana karɓa ya fice, maganin ta sha ta tayar da kabbara ta hau yin sallah.

Umma tana gamawa fita ta yi ta nemowa Radiyya abinci ta dawo ɗakin, ajiye mata ta yi gefenta inda take sallah sannan ta fita a ɗakin. Bayan Radiyya ta idar ta yi addu'o'i ta shafa kafin ta gyara zama tana jawo filet ɗin gefenta, faten wake ne bai fi ci goma ba, tasan wannan shi ne rabonta da na Umma gaba ɗaya. Hawaye ta ji ya taru a idanuwanta ganin yau Umma ta damu da ita da lafiyarta, har ta iya sadaukar mata da cin ta ita ta ci duk da ta wuni da azumi, bayan hannunta ta sa ta share hawayenta da ta ji ya zubo sannan ta fara ci, kaɗan ta ci ta ragewa Umma sauran, da ta gama ta ajiye gefe gudun kar ta fitar wani ya gani ya cinye, sallar isha'i ta yi ta koma shimfiɗa ta kwanta.


Umma bayan ta gama komai ta shiga ɗakin, kwance ta hangota alamar ta yi barci. Zama ta yi ta cinye ta shanye sauran kokon kafin ta haɗa ta fitar waje, sai da ta ɗaura alwala ta koma ɗakin, tana sallah ita ma ta kwanta wajen ƙarfe taran dare.


...


Washegarin Radiyya ta farka da sauki jikinta sosai tamkar ba ita ba, tun asubani take jin yau ba za ta iya fita ba tana buƙatar hutu ƙaɗan, bayan haka ga sallah ya gabato kowa yana hidimar sallar idi ban da ita da Umma. Har ƙarfe biyu Umma ta ga Radiyya ba ta da niyyar fita, hakan ya sa ta sameta har ɗaki. Radiyya ganin Umma ta miƙe zaune tana binta da kallo.


"Yau ba za ki fita ba ne ban ga kin fara shiri ba?"


Jin tambayar Umma ya sa Radiyya jiki a sanyaye ta ce.

"Umma zan huta ne zuwa gobe. Kuma ga sallah yana gabatowa."


"Ke wacece da hidimar sallah zai hanaki yin uzurin gabanki? Ba kin zaɓi tallah ba, to tashi ki tafi."


"To Umma."

Abin da Radiyya ta faɗa tana miƙewa ta fita, kayan sana'arta ta fara haɗawa maganganun Umma na mata yawo akai, tana faɗawa zuciyarta cewa

'Lallai ni ɗin ba kowa ba ce balle hidimar sallah ya hanani neman gumina, sai dai shi sallah ba babba ba yaro ba mai kuɗi ba talaka, kowa farin cikin zuwansa yake.'


***


Kwanaki yana tafiya har ya rage sallah saura kwana biyar cib. Radiyya abubuwa da dama sun cunkushe mata akai, ta rasa wanne za ta fara fuskanta. Barin gurin sana'arta bayan sallah bai dameta ba kamar sauran, dama tabsan bayan sallah barin gurin za ta yi kamar yadda Alhaji Shaheed ya faɗa, dole ya sa cikin kwanakin biyun duk wanda ya zo siya take sanar masa da adireshin gidan su, akan bayan sallah za ta fara yi a gida duk mai buƙata ya je can za ta dai na fitowa nan, ba ta sanar da Sahabi ba don tasan yasan da haka.


Kwanakin da ya wuce Umma da Baba sun zuba ido suna jiran Uncle Nasir ya kawo. Baba ko abincin da za a dafa a ci bayan sallar idi bai siya ba cewarsa Uncle Nasir zai kawo. Matan gidan kowacce ta yi abin da za ta yi suka siyawa ƙananan yaran su ƙananun atamfa masu ƙaramin kuɗi, nan aka bar Umma da Radiyya da kallo.


Da magriban wani Alhamis ana shan ruwa Baba ya sanar da Umma idan ya dawo daga sallah yana nemanta za su yi magana, da to ta amsa zuciyarta na addu'ar Allah ya sa maganar da take son masa zai yi. Bayan dawowar Baba Ƙarami ya aika ƙiran Umma ba ta ɓata lokaci ba ta amsa ƙiran.


Zamansa Baba ya gyara yana cewa.

"Zuhra da ma akan wannan yaran ne Nasir da Mimi. Ki na sane tun zuwan Nasir na ƙarshe shi da matarsa ba su ƙara tako ƙafar su ba, sannan ga sallah yana gabatowa shuru babu ɗan abin arziƙin da yake mana. Ko ku na waya da su?"


Kai Umma ta girgiza ta ce.

"Ban yi waya da su ba kuma ban ji Radiyyatu na waya da su ba, sai dai idan zan turata ta duba ko lafiya."


"Hakan ya yi shawara mai kyau, gobe idan Allah ya kai mu ta shirya ta je."

Faɗin Baba Ƙarami, ya yi na'am da shawarar da ta bayar.

Daga haka Umma ta miƙe ta fita ta koma ɗaki, ganin Radiyya ta yi zaune ta zubawa fuskar wayarta ido tamkar za ta hango wani abu a ciki. Umma ta jima tsaye ko za ta ankara da zuwanta amma gani take Radiyyar tamkar an kafarta, ban da numfashi babu abu mai aiki a jikinta.


"Radiyyatu! Radiyyatu!!"

Ta ce a tsawa ce tana buga yatsun hannunta biyu ya yi ƙara.

Ƙarar sunanta da ta ji ya sa ta jin tamkar tsawan kwarankwasa ne ya ratsa dodon kunnuwanta, a mugun tsorace ta ɗago lokaci ɗaya ta yi wulli da wayar hannunta gefe.


"Hauka ki ke ne? Ko shafar aljanu gareki?"

Faɗin Umma tana fizgota cikin ɓacin rai, abu ɗaya ya hanata zuba mata mari shi ne jin yadda jikin Radiyya yake rawa. Tsawar Umma shi ne yasa Radiyya dawowa hankalinta ta kalleta, duk da jikinta mugun rawa yake haka ta samu kanta da girzawa alamar lafiyarta lau. 

Suna haka tsawon sakanni Umma ta sake Radiyya ta gyara zamanta.

"Me ki ka gani a wayar da ya tsorataki haka?"


"Babu komai."

Radiyya ta samu kanta da furta haka tamkar yadda zuciyarta ya ba ta umarni, ganin mugun kallon da Umma ta aika mata ya sa ta sunkuyar kanta. Kafaɗa Umma ta ɗaga tana cewa.

"Idan ya yi tsami zan ji ai. Da ma mun yi magana da Baba gobe ki shirya ki je gidan Mimi ki duba su."


"Gidan Aunti Mimi!"

Radiyya da faɗa da sauri tana dafe kirjinta, bugun zuciyarta ya ƙaru, za ta iya aikata komai amma ban da kai kanta in da ajalinta yake, in da ta gwammace a kai gawarta da ta taka ƙafarta.

Maganar Umma ya sa ta dubanta in da take cewa.

"Eh gidan Mimi, akwai wata bayan ita."


"Umma zan ƙirata a waya."

Radiyya ta faɗa tamkar ta ɗaura hannu a kai ta fashe da kuka.


"Saboda me ya sa? Gidan ne ba za ki je ba?"


Kai Radiyya ta ɗaga a tsorace tana tsoron me kuma Umma za ta nemi sani game da ƙin zuwan ta gidan, tamkar kuwa Umma ta karanci zuciyar Radiyya ta watsa mata tambaya.

"Me ya sa ki ka bar gidan Mimi lokaci ɗaya? Sannan me zai hanaki zuwa?"


Tambiyoyi biyu da Radiyya tana da amsar su tana tsoron faɗa, tana tsoron ta ƙi yarda da ita, tana tsoron abin da zai je ya dawo.


"Ke nake saurara Radiyyatu."

Umma ta ce a tsarenta ta yi ƙoƙarin kallon Radiyya. Ba ta cika son su jima tare ba, duk da wani lokacin tana ƙoƙarin mance komai.


Hawaye fal idanuwan Radiyya ta kalli Umma, da ƙyar bakinta yana rawa ta furta.

"Umma...."


#vote

#comment

#keeplove

DUHUN ZUCIYA


Babi NA Takwas


Pharty BB

Wattpad PhartyBB


Har ta tsaya a ƙofar gidan ba ta ga alamun abin da ta faɗa mata ba ko kaɗan, hasalima unguwar shuru yau ko don azumi ne. Ƙoƙonto ne ya fara ziyartar zuciyarta akan ba ƙarya ta mata ba kuwa. Buɗewar ƙaramin ƙofar jikin get ɗin ne ya sa ta juyawa ta ga Mai Gadi ne.


"Mama sannu da zuwa bismillah."

Ya faɗa mata yana ba ta hanya ta shiga tana amsa masa. Kai tsaye falon gidan ta nufa, nan ma sai da ta ƙwanƙwass sannan aka buɗe. Aunti Mimi ce daga ita sai doguwar riga na barci, da alama farkawarta daga barci kenan. 


"Umma ke ce da sassafe haka?"

Mimi ta ce cike da mamakin ganin mahaifiyarta a wannan lokaci.


"Zan iya shiga ko na juya?"

Ta ce tana bin ta da kallon mamaki.


"Shigo ciki."

Ta faɗa tana matsawa Umma ta shige cikin falon. Turus ta yi ganin falon sama da ƙasa tamkar matsugunnin taɓeɓɓiya. Juyawa ta yi ta kalli Mimi da take susan kai lokaci ɗaya hamma ya taho mata ta buɗe baki, babu shiri Umma ta kawar kanta tamkar ta yi amai. Guri ta samu ta zauna saman kujerun falon da duk sun koɗe a ƙanƙanin lokaci. Ganin haka Mimi ta zauna ita ma.


"Mimi me zan gani! Ƙazanta?"

Shi ne abin da Umma ta fara faɗa mata kenan. Rai Mimi ta haɗa don ta tsani faɗar Umman su, sam ba ta da daɗin sha'ani.


"Magana nake miki Mimi. Yanzu ba wannan ba, babu labari shuru?"


"Labarin me kuma Umma?"

Mimi ta tambayeta tamkar ba ta fahimci inda maganar ya dosa ba.


Sake zama Umma ta gyara tana sassauta murya.

"Kayan arziƙi da yaron nan yake mana duk ƙarshen wata, ga kuma sallah sai gabatowa yake."


"Umma kenan, ku ƙara ba shi lokaci, akwai wasu ayyuka da ya sa a gaba ne."


"Amma Mimi shi ne har yanzu shuru? Ko dai ba shi da niyar ne bana?"


Ɓata rai Mimi ta ɓata ta ce.


"Umma na sha masa maganar ya ƙi wallahi, ƙarshe da na dame sa ya ce ba zai yi komai ba, dalilin haka har bama magana."


A razane Umma ta ce.

"Kul! Hauka ki ke!! Idan ki ka ɓata masa rai ya zamto aurenki ya samu matsala ina za ki je? Kin san mu ma ƙarƙashin ku muke ci, albarkacin ki. To a hir, ki sasanta da mijinki ko hakan zai sa ya fasa niyar ƙin yi."


"To Umma."

Mimi ta ce tana tuna rigimar su da Uncle Nasir.

T


un da sallah ya rage saura kwana goma sun kasa jituwa da juna. Faɗar yau daban gobe daban, ban da wanda suka gama kwanakin baya kan ƙazanta da take yi. Ba ta girki kullum sai ansha ruwa ya sayo, ba ta abincin sahur sai dai su sha shayi da biredi, gyaran gidan kuwa sai ta bushi iska.


Yau musamman ta samesa akan maganar kayan sallar iyayenta da yake siya musu kowanne sallah, da kayan abinci da yake siya kowacce ƙarshen wata. Kai tsaye buɗar bakinsa ba shi da kuɗi ya ce, da ta damesa ya ce ba zai siya ba. Hakan ya sa ta ɗauke masa wuta a gidan tun safe har dare tsammaninta idan ta yi fushi zai siya, ba ta san ta hutar da shi ba ne. Kyautatawar da yake don ya samu abin da yake muradi ne, yanzu kuma babu wa zai kyautata.


...


Gumi ne ya sassafo masa saman goshinsa. Gefen rigarsa ya sa ya share yana ci gaba da sauroronta har ta gama bayanin ya ka sa furta komai. Bayan ta gama shuru ne ya rasa wajen kusan dakiƙa, jin shurunsa ya sa ta miƙewa ta fita. Har ta fita ya kasa cewa komai, tagumi ya zuba jin wannan sabon lamarin da yake ɓullo musu, ya rasa wani irin tunani zai yi akan lamarin ma.

'Ko me ya sa ya yi haka lokaci ɗaya?'

Ya tambaya tamkar za a ba shi amsa.


...


Kowanne mahaluki idan ka duba za ka ga yana murnar washegari hawan sallar Idi. Rana mafi girma da Allah yake nuna wanda ya so a cikin shekara. 

Kwanaki biyar baya da suka rage na azumin Baba ya yi ƙoƙarin yin jakakkuna da takalma na fata da yake yi a sana'arsa na Dukanci wanda yake yi a kasuwa, ganin sun yi ƙyau ya sa mutane ire-irensa siyawa yaran su har da su kan su. Wannan abin ba ƙaramin daɗi ya yi wa Baba ba, bayan ya biya bashin da ake binsa ya wuce kasuwa, kayan abinci ya auno musu da za a dafa ranar sallah da kaji guda biyu.


Gidan kamar ba sallah ake ba, babu wani hayaniya balle dafe dafe ko soye soyen washegari sallah, kowanne yana ɗakinsa tare da yaransa. Cikin ɗakin Inna Saudatu ita da yaranta mata ne uku, babbar ƴar shekaru ashirin da shida Aadabiyya tana yi wa ta ukun kitso ƴar shekaru ashirin Sabira, ta biyun ƴar shekaru ashirin da huɗu Rabi'atu tana gwada kayan da ta karɓo a gurin tela. Inna Saudatu ce ta yi cuku cuku ta ɗinka ƙananan su hudu kala ɗaya ɗaya mai arahar kuɗi, saura huɗu mata ƙananan sun lalle. Manyan samarin su suka musu.

Ɗakin Amarya kuwa yaranta da taimakon dangi ta musu, wasu sun ba su atamfa wasu kuɗin ɗinki ita ma ta ƙara abin da za ta ƙara ta musu. A cikin ɗakin babbar ƴarta ƴar shekaru ashirin Amrah ta sa ƙannenta a gaba tana musu lalle, duk yadda taso ta yi wa su Aadabiyya su biyata Amarya Zulaiha ta hanata.

Umman Radiyya ta kasa tabuƙa komai. Ba haka suka saba sallar idi ba. Uncle Nasir yana wadata su da komai, ya riga ya sabar musu da wadatar kayan abinci, musamman a sallah. Haushi ne ya cika zuciyarta ganin kowa yana ciki da yaransa suna shiri ban da ita da wannan wawiyar ƴarta cewarta.


Baba Ƙarami yana shigowa gidan kai tsaye madafa ya wuce ya ajiye abubuwan da ya siyo, gidan shuru hakan yasa ya leƙa ɗakin Amarya, daga bakin ƙofa ya tsaya. Bayan sun masa sannu da zuwa ya sanar musu ya kawo kayan abinci su fito su gyara na gobe ne. Daga haka ya bar ƙofar ya fita a gidan.


...


Radiyya a ranar bayan ta gama sayar da abubuwanta ta samu Sahabi da maganar barinta gurin don masa sallama, sannan za ta fara yi a gida. Sun yi rabuwar mutunci, ya jaddada mata zai sanar da Alhaji ko zai haƙura ya barta ta ci gaba da zuwa albarkacin shi ma yana aikowa kullum. Anan ya ciro kuɗinta da yake tara mata na gurinsa ya bata, dubu biyar da ɗari takwas. Ta yi godiya sosai da hidima da ya yi da ita sannan ta tafi.

Tana shiga gidan ana ƙiran sallar magriba, da sauri ta ajiye kulolin ta ɗaura alwala, bayan ta gama ta zauna kusa da Umma suka sha ruwa, kamar ance ta ɗago a lokacin ta lura duk yaran sun yi lalle baƙi a hannun su, take ta ji ya burgeta tana son yi.

Bayan ta gama shan kunun hannunta ta wuce ɗaki, sallah ta gabatar ta fito ta zauna a barandar su tana korawa cikinta ruwa don yau ta ji ƙishi.


Washegari ranar sallah, rana mafi girma, kowa ka duba yana hidimar zuwa sallar Idi. Haka ya kasance a gidan Baba Ƙarami, kowa ya yi wanka ya hau ado. Baba Ƙarami ba shi da yara maza manya, duk yaransa mata ne guda goma sha uku, maza biyu ne ƙanana yaran Amarya.

Radiyya cikin kayanta ta saka sabo wanda ba ta taɓa sawa, tana da sabin kaya sosai domin Uncle Nasir yana ƙoƙarin kyautata mata da yi mata duk abin da budurwa za ta buƙata, halin da ya ɓullo mata da shi yasa ta daina karɓar komai daga gurin sa, amma duk da haka bai dakata ba sai ma ƙari da yake yi ko hakan zai ja ra'ayinta.

Cikin kayan ta samu leshi ruwan hoda ta saka hakan ya sa tayi amfani da hijabi ruwan hoda, ta yi mutuƙar yin ƙyau, fuskarta daga hoda sai kwalli da man baki, ta yi fiyau da ita. Bayan ta gama shiryawa ta fito don yin jam'i da ƴan matan su tafi tare, nan fa kowacce ta raina kanta ganin shigar Radiyya, haka ya sa duk suka yi gaba sai Amrah ce ta jirata suka jera tare.


A filin Idi, fili ya cika da ɗimbin mutane ana ta huɗu ba. Filin ba shi ne Radiyya suka saba zuwa ba, dalilin haka wajen shiga ta rasa Amrah don jama'a. Da kokuwa ta samu ta shiga gurin, duban duniya ta yi ba ta ga ƴan gidan su ba, haka ya sa ta samu gefen wata mata ta zauna. Kallo ɗaya ta mata ta hango arziƙi a jikinta, take ta ji ta raina kanta. Da sauri ta miƙe ta ƙara gaba ta zauna gefen wasu yara. Matar duk tana kallonta bayan zaman Radiyya wajen yaran ta ja siririn tsaki.

Mintuna arba'in da zuwan su aka gabatar da sallah, wasu sun yi jinkiri zuwa yasa da kyar suka samu, wasu kuwa basu samu ba. Bayan an idar Radiyya ta yi wa yaran godiya ta tafi. Har za ta wuce ta gefen wacce ta fara zama gurinta kamar wani abu ya sa ta kallonta, ta kallota

sau ɗaya. Tsaye take sai dai wanda yake tsaye a gabanta ya hanata kallon fuskarta. Juyawa ta yi ta duba ta ga gurin babu namiji ko ɗaya sai shi ɗaya. Girgiza kai ta yi ta wuce abinta.


Bayan Radiyya ta isa gida ta samu duk an dawo sai ɗaiɗaiku, ɗaki ta shiga ta cire hijabinta ta kwanta. Amrah ce ta shigo da sallama hannunta ɗauke da kula. Zaune Radiyya ta miƙe tana amsawa. Guri Amrah ta samu ta zauna tana ajiye kular, kallon Radiyya ta yi tana cewa.

"Ki ka ɓace mini."


Murmushi Radiyya ta yi ita ma ta ce.

"Kin san wani ikon Allah? Babu wanda na haɗu da shi har na dawo, kai akwai mutane a duniya."


"Sosai ma. Ga abincin sallah in ji Mama."


"Muna godiya. Umma shuru."

Faɗin Radiyya.


Miƙewa Amrah ta yi tana faɗin.

"Ta dawo ai, tana waje."


"Oho sai yanzu na ji wasai."


Dariya Amrah ta saka ta fita. Bayan fitarta Radiyya ta jawo kular ta buɗe. Shinkafa ne sai miyar ja duk kabewa da kaza a sama, shi ma cinya ɗaya da kirji ɗaya. Abincin ta kurawa ido tunanin gidan Aunti Mimi ya faɗo mata. Yau sallah idan a gidan Aunti Mimi ne abinci sai ta ture, kayan ci irin du meatpie, samosa, spring rolls da soyayyen kaji har dambu sai ta yi, gefe ɗaya kuma ruwan lemon gwangwani kala kala Uncle Nasir zai siyo, su Umma kan su tana aiko musu balle ita da take gidan sai ta ture. Amma yau har karfe goma sha ɗaya shuru. Kewar gidan ne ya kamata lokaci ɗaya, sai dai tana jin har mutuwarta ta bar gidan kenan, ba za ta iya komawa gidan da yake cike da duhun da suka dasa mata DUHUN ZUCIYA ba ita ma.

A sanyaye ta miƙe ta fita ta ɗauko cokali da plate a madafa ta dawo ɗakin, abinci ta zuba daidai wanda za ta iya ci ta rufe sauran ta ajiyewa Umma a gefe. Da bismillah ta ɗauki cokali ta kai bakinta, tana ƙoƙarin kai na biyu wayarta da yake gefenta ya yi ƙara alamar shigowar saƙo. Da murna ta jawo duk tsammaninta Sahabi ne da ta turawa sakon barka da sallah da safe ya turo mata da amsa. Lambar da ta gani rubuce shi ya sa ta kwarewa ta hau yin tari, sosai ta yi tarin kamar za ta shiɗe ta samu ta dawo daidai, idanunta har sun kaɗa. Bayan samuwar nutsuwa ta ɗauki wayar ta buɗe sakon ta zuba masa ido.

Ba na ɗaya ba, na biyu ba kenan wannan layin yake turo mata sako, sako ne me tattare da irin kalaman da ta saba jin su, duk lokacin da ta ci karo da shi sai ya haifar mata da tsoro.


"Radiyya! Radiyya!!"


Ƙira na biyu kenan Amrah ta mata sannan ta dawo hankalinta ta kalli Amrah a tsorace.


"Za muje gidan Kawun mu ne ko za ki bi mu."


Girgiza kai Radiyya ta yi har lokacin ba ta dawo dai-dai ba. Hakan ya sa Amrah wucewa ta barta. Bayan barin Amrah gurin Umma ta shigo ta kalli Radiyya a wannan halin.


"Wa ki ka barwa guntun abincin?"


Kallon abincin Radiyya ta yi ta kalli Umma sai kuma ta sa hannu ta ɗauki cokali ta hau ci. Ganin haka Umma ta ɗauki na kular ta fita da shi don ci.

Radiyya tana ci tana tunanin sakon da ya risketa har ta gama, yunwar da take ji ya sa ta ci sosai.

Bayan ta gama ta fitar ta dawo ɗakin ta kwanta don hutawa tun da babu inda za ta je. Sallah azahar ya tasha ta gabatar ta sake kwanciya. Haka Radiyya ta yi wunin sallanta da kwanakin biyun da suka gabata, har lokacin ba ta ƙara cin karo da wani saƙo ba.


#vote

#coments

#keeplove

DUHUN ZUCIYA


Babi Na Tara


Pharty BB

Wattpad PhartyBB


Tsawon sati ɗaya kenan Radiyya tana hutu, ba wai don ta gaji ba ne sai don ganin tamkar tsoro take ta yi ta rasa masu saya, sai dai abin mamaki tun sallah da ya wuce da sati biyu da kwana uku aka fara nema, an turo yara kusan sau biyar zuwa shida babu, hakan ya sa yau ta tashi da niyar yi.


...


Tun kwanakin sallah hidima da fama da jama'a ya hanasa zama, har yau da ana neman cinye sati biyu ya samu hutu. Tun safen bai fita ba yana kwance a gida don hutu, barci yake tun da ya yi sallar azahar. Sai misalin ƙarfe huɗu da rabi ya farka, babu kowa a ɗakin kamar yadda ya buƙata da zai shiga don kwanciya, hakan ma kuma yanzu babu wanda ya shigo. Kai tsaye banɗakin dake cikin ɗakinsa ya shiga, haɗuwa iya haɗuwa ya yi tamkar ba za a mutu ba. Ruwa ya watsa ya ɗaura alwala sannan ya fito, kayan shan iska ya saka ya tada kabbara, sallah ya gabatar lokacin ƙarfe biyar saura. Bayan ya idar ya isa gaban mirror nasa da yake cike da kayan shafe-shafe da turaruka tamkar na mace, mai ya shafa lotion mai ƙamshi kafin ya bi jikinsa da turare ya feshe kusan kala uku, tuni ɗakin ya ɗauki ƙamshi, bayan ya gama ya fito zuwa falon gidan. A hankali yake taka matakalar benen, kallo ɗaya ba za ka iya wassafa shekarunsa ba saboda jin daɗi da kuɗi da ya zauna masa. 

Tana zaune ta ji alamar motsi daga sama, kallonta ta kai gurin, ganin mijinta ya sa ta miƙewa da sauri ta nufesa fuskarta ɗauke da murmushi.


"Ka farka? Na leƙa sau biyu ka na barci."


Kallonta ya ci gaba da yi kamar yadda yake tun sauƙowarsa, ta yi kyau cikin shigar jikinta, jin abin da ta faɗa sai lokacin ya buɗe ba ki ya ce.

"Amma Fauzy kin san na hana hakan ko?"


"Na sani ka yi haƙuri. Gani na yi lokacin sallah zai wuce ne."

Matar da ya ƙira da Fauzy ta faɗa a ɗan sanyaye.


Bai ƙara cewa komai ba ya nufi hanyar ƙofa, ganin haka ta bi bayansa.

"Abinci fa Alhaji."


"Ba zan jima ba."

Haka kawai ya faɗa mata ya fice daga falon. A sanyaye ta dawo ta zauna, tun ɗazu take jiran farkawarsa domin su ci abincin rana tare. Tana son mijinta tamkar yadda yake sonta, tana kishinsa.


...


Kai tsaye wajen sana'arsa da ake masa ya biya ya dudduba da bai samu ya yi ba yau, komai daidai ƙarshe ya tsaya a gidan mai nasa da Sahabi yake aiki. Burinsa da muradinsa yau yasha daddaɗan zoɓon nan, ya yi kewa kwana da kwanaki, tun bayan sallah haƙuri yake kuma rashin zama ya hanasa zuwa. Tun da ya shigo yana raba idanu ta ina zai hangota, sai dai abin mamaki iya juye juyensa bai kalli ko kulolin ba balle ita. Ba shi da niyar sauƙa amma haka dole ya buɗe motar ya fito, da Sahabi ya fara cin karo da yake jiran saukowar ogansa. Da girmawa Sahabi ya gaishesa, bayan ya amsa ya yi shuru don rasa ta ina zai fara tambayarta, amma da ya tuna Sahabi nada masaniyar ƙaunarsa ga zoɓo, musamman nata da yake aikowa ya sa ya daure ya ce.

"Sahabi ina yarinyar nan mai siyar da zoɓo?"


Sahabi jin Alhaji Shaheed da kansa ya kawo maganar da yake son masa ya sa shi da sauri faɗin.

"Ai Oga ta dai na fitowa."


"Saboda me? Me ya faru?"

Alhaji Shaheed ya faɗa da saurinsa.


Sahabi da mamaki ya kusa kashesa, mutumin da ya ce ana gama azumi ta tattara ta bar gurin baya son ƙazanta, amma tunawa da Alhaji ya zama shaƙiƙi ga son zoɓonta ya ce.

"Oga kai fa ka ce ka bata nan da bayan azumi, shi ne ta dai na zuwa. Amma ta ce za ta yi a gida, mai so ya je can ya siya. Idan kana so in karɓo maka."


Alhaji Shaheed kallon Sahabi yake yana sauraran bayaninsa, tabbas an yi haka a lokacin bai bai san zai zamto abin so ga zoɓonta ba. Bayan Sahabi ya gama bayanin Alhaji Shaheed ya sa hannu a aljihun wandon jikinsa ya zaro haɗaɗɗiyar wayarsa ya miƙa masa.

"Saka min lambarta ka faɗa min adireshinta. Idan ka tafi wa zai kula da gurin."


A mamakince Sahabi ya karɓi wayar ubangidansa, nasa wayar ya zaro a aljihu gaban rigarsa ya buɗe ya kwafi lambar Radiyya zuwa wayar Alhaji Shaheed, bayan ya gama ya miƙa masa tare da fara masa kwatancan gidan su Radiyya. Yana gamawa Alhaji Shaheed ya yi gurin motarsa yana faɗin.

"Thank you."


Bai jira me Sahabi zai faɗa ba ya shiga cikin motarsa ya kunna yana barin guri. Tafiya yake yana bin kwatancen da Sahabi ya masa, gefe ɗaya yana mamakin kansa da yau shi ne ya biyo abu, abun ma zoɓo. Allah ne ya jarabce shi da son abun tun yana yaro, amma kuma jarabawar Ubangiji sai matarsa idan ta yi baya daɗin da yake so. Tun daga farkon layi ya fara bin wajen da kallo, unguwar talakawa ne da za a ƙira su masu rufin asiri, majalisa da ƙananan yara sun fi yawa a unguwar. Duk in da ya wulga da motarsa sai an bi da kallo, har ya tsaya a babban bishiyar da yake gefen gidan su Radiyya kamar yadda Sahabi ya masa kwatance. Gidan su Radiyya ya zubawa ido, mamaki yake yanzu a wannan gidan ake dafa abu yasha.

Kai ya girgiza yana ɗaukar wayarsa ya lalibo lambarta, babu ɓata lokaci ya ƙira. Har ya tsinke ba a ɗauka ba, sake ƙira ya yi.


... 


Radiyya tin da wayar ya fara ƙara ta ɗauka ta zubawa fuskar wayar ido, ganin lamba mai sauƙi ya hanata ƙin ɗauka. Umma tana madafa tana girki, sauran jama'ar gidan kowa hidimarsa yake. Radiyya da Amrah suna zaune a barandar su Radiyya suna taɓa hira, kasancewar ana shigowa a siya kunun Aya da zoɓo ya sa ba ta tashi a gurin ba, hatta samarin unguwa sun gano daga shigowa siya mutum ɗaya biyu, su ma suka fara aikowa. Ƙarar wayar ne ya damu Amrah ga Radiyya ta sa wayar a gaba ta ƙi ɗauka.


"Radiyya ki ɗauki mana, sau biyu ana ƙira."


Girgiza kai Radiyya ta yi, ta ɗauki wayar ta nunawa Amrah tana cewa.

"Kalli fa ki ga lamba mai sauƙi. Ni tsoron ɗauka nake."


"Kawo ki ga."

Amrah ta ce ta warce wayar, da bismillahi ta ɗauka ta kafa a kunne.

Diff wayar ya katse bayan gama bayanin ciki. Zaro wayar Amrah ta yi ta kalli Radiyya da ta zuba mata idanuwanta, wayar ta ajiye mata a cinye ta kwashe da dariya ta ce.


"Ke zoɓo ake so gora biyu, mai buƙata yana waje yana jira."


Ajiyar zuciya Radiyya ta sauƙe ta miƙe.

"Amma ko waye wannan ya tsorata ni, ya ɗauki alhakina.


"Ki yi dai sauri kar ya yi fushi ya tafi."


Hijabi Radiyya ta canza zuwa babba, leda ta ɗauka ta buɗe kular zoɓo ta ɗauki gora biyu masu sanyi ta zuba ta rufe kular.

"Bari in kai."


Daga haka ta fita, duk tunaninta a tsaye za ta hango mutum tsaye jikin gidan sai ta ga babu, juye juye ta fara ta ji ƙarar wayarta da yake hannunta, dubawa ta yi taga lambar ne, a sanyaye ta ɗauka duk tsammaninta ko zai ce ya tafi ta ji akasin haka.


"Ki ƙaraso ina cikin motar nan na bakin bishiya."


Yana gama faɗar haka ya kashe wayar. Tun fitowarta ya hangota da dube duben da take. Galala Radiyya ta bi motar da kallo kafin a sanyaye ta ja ƙafafunta zuwa gurin, ta gefen driver ta tsaya. Sauƙe gilashin motar ya yi ido biyu suka haɗa da juna, kaɗan ya rage Radiyya ta sake ledan hannunta ya fadi, ita kanta sai da ta ja baya don ta tsorata. Ba ta tsammaci ganin shi ba, sam tunanin bai zo mata shi ɗin ne ba. Bayan ta samu ta daidaita nutsuwarta murya ƙasa ƙasa ta ce.

"Ina wuni."


"Lafiya lau. Miƙo ledar ga kuɗinki."

Ya amsa yana miƙa mata ɗari biyu sabo gal. Sai lokacin ta tuna me ta ke yi, da sauri ta miƙa masa, ba ta karɓi kuɗin ba ta ɗauke hannunta bayan ya karɓa. Idan a baya ta bar masa tana zama a wajensa yanzu kam ba zai danne mata haƙƙi ba.


"Karɓi kuɗinki!"

Ya faɗa yana ƙara haɗa rai.


"Wallahi ka bar shi na yafe."

Ta ce tana ƙoƙarin barin gurin.


Ganin da gaske tafiya za ta yi ya sa ya ce.

"Kin ga dawo ki karɓi abunki na fasa siya."


Cak Radiyya ta tsaya kafin ta juyo a sanyaye, babban mutum kamarsa bai kamata ta masa haka ba ta ji, don son da yake yi wa abunta ya biyo har gida. A hankali ta koma gurin motar ta tsaya.

"Kawo kuɗin. Amma sai na shiga gida na ɗauko canji."


"Babu matsala."

Ya faɗa ya miƙa mata tasa hannu ta karɓa tana barin gurin. Yana ganin ta matsa ya yi ribas ya ja motarsa yana barin gurin. Da hanzari Radiyya ta juya taga har ya yi nisa, rasa ma me za ta yi tai, ƙafafunta ta ja ta koma gida. Babu wanda ta sanar abin da ya faru hatta Amrah da take jiran dawowarta.


...


A inda ya barta anan ya dawo ya sameta, da sallama ya ƙarasa kusa da ita. Amsawa ta yi ta miƙe tsaye.

"Ka jima."


"Sorry Uwargidana, mu je mu ci abincin."


Agogon jikin bango Hajiya Fauziyya ta kalla, biyar da minti goma. Ba ta ce komai ba tabi bayan mijinta zuwa dinning, abincin ta buɗe har yanzu da zafinsa don kwalitin filas ɗin, zuba musu ta yi cikin filet ɗaya babba ta saka musu cokali. Murmushi ya yi ya ce.

"Na gode Fauzy."


Fari ta yi da idanuwanta tana faɗaɗa murmushinta. Cokali ta ɗauka ta ɗebe abincin ta kai bakinsa, buɗewa ya yi ta saka masa ya rufe yana taunawa, haka ita ma ta fara ci. Hira suke suna ci ganin ya kusa ƙoshi ya sa ya jawo ledan da ya shigo da shi yana ƙoƙarin ciro abin da yake ciki.


"Menene wannan?"

Ta tambayesa don tunaninta bai kawo nan ba.


"Zoɓo ne."

Ya sanar mata da amsa.


Baki ta taɓe don wannan zoɓon ta rasa na menene, tsammaninta idan azumi ya wuce zai daina sha. Daga lokacin babu wanda ya ƙara magana. Alhaji Shaheed da ya gama a take ya shanye zoɓon dukka biyu don ƙananan goruna ne. Hajiya Fauzy bayan sun gama ta tattare gurin ta kai kitchen, anan ta samu mai aikinta na tambayar abinci dare fa. Girgiza kai ta yi tana sanar da ita ba sai ta yi girki ba.

Alhaji Shaheed yana gamawa ya bar gurin ya koma falo, kallo ya kunna wanda bai samu gani ba dalilin ƙira da ya shigo wayarsa. Miƙewa ya yi yana ɗauka ya haye sama don amsawa. Hajiya Fauzy da ta ga hakan fitowarta daga kitchen ba ta bi bayansa ba, don ta lura sautari baya son amsa wasu wayoyin a gabanta.


...


Radiyya har dare abin da ya faru yana ranta, har Umma na tambayarta lafiya ta sanar da ita lafiya lau. Washegari da safe bayan ta gama ayyukanta ta kama hanyar kasuwa, kaya ta siyo na zoɓo masu kyau da sa ƙamshi, goruna ma sabi dal ta siya. Bayan dawowarta ta samu Umma a ɗaki, asusunta ta ɗauko ta fasa kuɗaɗen ciki suka zubo, da kallo Umma ta bi ta tana tattarewa. Bayan ta gama ta zauna kusa da Umma ta miƙa mata.


"Me zan yi da shi?"

Faɗin Umma na bin kuɗin da kallo.


"Umma ki riƙe tukunna."


Girgiza kai Umma ta yi. Jiki a sanyaye Radiyya ta kirga kuɗin, da ta gama ta kalli Umma ta ce.

"Dubu talatin da huɗu da ɗari takwas ne Umma. Ina son sayan firiji ko ƙarami, kullum sayan ƙanƙara ba shi da riba."


Wani kallo Umma ta mata tana faɗin.


"Wai ke kina ganin dawwama za ki yi da sana'ar nan? Aure za ki yi Radiyya daga miji ya fito miki. Ko kin fi so ki yi ta zama a wannan baƙin gidan?"


Girgiza kai Radiyya ta yi ta ce.

"Umma komai da lokacinsa. Maganar sana'a kuma ina jin daɗin abuna, kuma ina fatan ko a gidan da zan shiga in ci gaba da yi. Duk wanda ki ka ga baya son sana'a ko baya son iyalinsa ta yi sana'a to tabbas ba masoyi ba ne, ko kuma bai san daɗinsa ba. Sana'a ga mace yana da daɗi, sai wanda ya fara zai san haka. Komai kuɗinka idan kana sana'a kafi jin daɗinsa..."


"Ya isa ba nasiha na ce ki min ba. Allah ya ba ki ikon duk abin da ki ka ga damar yi Radiyya."

Umma ta katse Radiyya da sauri jin dogon sharhin da ta ɗauko mata akan marasa yin sana'a, musamman mata.


Dubu biyar Radiyya ta cire cikin kuɗin ta ajiyewa Umma kafin ta miƙe.

"Umma ki sa albarka."


Da kallo Umma ta bi Radiyya har ta fice sai kuma ta kalli kuɗin, a sanyaye ta sa hannu ta ɗauka ta kirga, a ƙarancin kuɗin amma ta zare wani abu ta bata don faranta mata. Tunawa da kwanakin baya ne da Uncle Nasir ya ba ta ukunsa ya ta taɓe baki tana ɗaure kuɗin bakin zaninta.


Radiyya tana fita aikin sana'arta ta fara, gefe ɗaya tana tunanin Allah ya sa ta samu ƙaramin fridge daidai kuɗinta, ko da na hannun ne idan zai mata sanyi.


#vote

#comments

#keeplove

DUHUN ZUCIYA


Babi Na Goma


Pharty BB

Wattpad PhartyBB.


Kamar jiya haka yau ma ta samu ƙiran Alhaji Shaheed. Da farko kamar ba za ta fita ba, sai dai rashin ɗan aike yasa dolenta ta ɗauki hijabi, tare da sa gora uku a leda masu sanyi sosai kafin ta fita. A gurin da jiya ya yi parking anan ta sameshi, kallo ɗaya ta yi wa gurin ta sunkuyar kai tana ƙarasawa. Isowarta ya sa shi buɗe gilashin motar, tun fitowarta ya zuba mata idanuwansa yana ƙare mata kallo, anan ya hango ƙarancin shekarunta. Bayan ya buɗe gilashin Radiyya ta ɗago kai ta kalli gurinsa tana gaishesa. Amsawa ya yi yana miƙa hannayensa duka biyu, ɗaya kuɗinta ɗaya kuma alamar ta miƙo masa ledar hannunta. Babu musu ta miƙa suka yi musanye.


"Sai dai babu canji, kuma akwai sauran canjin jiya."

Ta faɗa ƙasa ƙasa kanta sunkuye.


"Don't worry. Keep it with you."

Ya faɗa yana zuge gilashin motar tare da ƙoƙarin barin gurin. Radiyya ta ɗan fahimci abin da ya faɗa saboda tana da sanin turanci kaɗan. Tana kallo ya bar gurin kafin ita ma ta koma cikin gida a sanyaya.


...


Cikin satin tana samun ƴan ciniki sosai, unguwar duk an gano Radiyya mai kunun Aya da zoɓo, musamman har bukin ake take ajiyewa mutane. Kamar yau abin tamkar a mafarki aka kawowa Radiyya kuɗin kunun Aya da zoɓo da za ta yi na suna. Ba ta karɓa ba sai da ta sanar da Umma. Da ƙyar ta samu yardarta don Umma ba wannan bane a gabanta. Burinta ta koma gidan Aunti Mimi tin da sallah ya wuce, amma daga Baban har Mimi babu wanda ya ƙara tayar da maganar, kuma dole ta tayar, don haka suka yi da Radiyya azumi za ta yi kaɗai ta koma. 


Radiyya bayan ta karɓa aikin da aka bata ta wuce kasuwa, tare da Amrah suka je don taimaka mata, bayan sun gama siyayyar suka dawo. Suna dawowa sun huta wajen bayan azahar ta fara nata aikin don na sunan sai gobe. Ƙarfe huɗu da mintuna ta gama don tun ɗazu ana ta shigowa tambaya. 

Kamar koyaushe haka yau ma Alhaji Shaheed ya yi tattaki ya taho zuwa ga Radiyya, gaisuwar mutunci suka yi kafin ta ba shi ya amsa ya biyata. Bai jira ta ƙara faɗin komai ba kamar kullum ya ja motarsa ya bar gurin.


Washegari Radiyya tun safe ta fara aikin kunun Aya da zoɓo na sunan da aka kawo mata, da taimakon Amrah take yi, Amarya Zulaiha ta hana Amrah ƙiri-ƙiri amma yarinyar ta ƙi bari. Ba su gama ba har ƙarfe biyu kafin nan, a cikin manyan kulolin da suka kawo ta zuba musu ta jera. Ƙarfe biyu da rabi suka zo suka ɗauka sai godiya suke mata, ita ma ta yi murna don sun mata sallama mai tsoka.

Gajiyar da ta yi yau ya hanata yin nata sana'ar, tun wuri masu turo a musu bukin take sanar da su yau babu sai gobe, sam ta manta da oga kwata-kwata da shi ne ruwan shansa idan ya ci abinci, wani lokaci a firiji yake sawa ya kwana da safe ya yi breakfast da shi.

Ƙarfe uku ya masa a ƙofar gidan su saboda rashin zama da bai samu ba yau, tasowarsa zai wuce gida don hutawa ya ga gwara ya tsaya ya siya kafin ya wucen. Ƙiranta ya yi a waya kamar kullum.


Radiyya na kwance ta yi ɗaiɗaiya a ɗakin Umma tana huta gajiya ta samu ƙiran wayar, sam ta manta da shi, jin ƙarar wayar ya haifar mata da fargaba, babu me ƙiranta sai shi a daidai wannan lokacin. A sanyaye ta miƙe ta ɗauki wayar, shi ɗin ne kuwa. Kasa ɗauka ta yi kawai ta zurma hijab ta fita. A gurin da ya saba tsayawa ta hango sabuwar motar da ya tsaya, canjin mota na uku kenan. 

Bayan tsayuwarta ya sauƙe gilashin, murya ƙasa ƙasa Radiyya ta gaishesa, bayan ya amsa ya ƙara da faɗin.

"Da alama yau kin mini rowa."


"Wallahi ban samu zama ba ne, ka yi haƙuri."

Ta samu kanta da furta haka.


Murmushi ya yi da shi ne karo na farko da Radiyya ta gani a fuskarsa, sai ta ga ya mata kwarjini duk girmansa, dole ta sunkuyar kanta ƙasa.


"Kar ki damu, kowanne ɗan Adam yana son hutu. Jini da jiki."

Radiyya ta tsinci muryarsa, dole ta mayar masa da amsa ta ce

"Na gode da fahimta."


Bai ƙara wani abin ba ya zuge gilashin ya bar wajen. Radiyya ji ta yi ba ta kyauta masa ba, ta ji sam babu daɗi. Haka ta koma gida.


...


Kaɗan ya ci abincin ya ture na gabansa, hatta abincin ba ya masa daɗi duk da yana cikin abin da yake son ci. Hajiya Fauziyya da mamaki ta kalleshi ganin ko kaɗan bai ci ba.


"Lafiya dai? Ko abincin bai yi maka ba ne, yanzu ina shiga kitchen na girka maka."


'Da hakan take min da nafi jin daɗi.'

Ya faɗa a ransa a fili kuma fuska ya yamutsa yana miƙewa, ruwan gora ya ɗauka cikin jerin lemukan gwangwani da ta tara masa ganin babu kayan jarabarsa cewarta. Ganin ta bisa da kallo tana buƙatar amsa ya girgiza kai ya ce.

"Babu komai kar ki da mu."


Daga haka ya bar gurin yana hayewa sama. Da kallo ta bisa har ya ɓacewa ganinta, ji ta yi ita ma abincin ya fita a ranta, ƙasan ranta kuma ya sosu akan wani zoɓo ya hana mijinta cin abinci. Miƙewa ta yi tana kwalawa mai aikinta ƙira, a gaggauce yarinyar ta fito.


"Kwashe abincin nan."


"To Hajiya."

Ta faɗa ta hau tattare wajen. Sama Hajiya Fauziyya ta wuce wajen mijinta.


....


Da dare misalin ƙarfe tara kowacce mace tana ƙofar ɗakinta da yaranta suna cin abincin dare, wasu hira suke. Radiyya a ƙofar ɗakin su ta yi shimfiɗa ta kwanta, har lokacin abin da ya faru tsakaninta da Alhaji Shaheed yana ranta. Cikin ɗakin Baba da shi da Umma ne, yana cin abinci da ta zuba masa yana fifita don zafi.


"Idan ka gama ina son maka magana Malam."

Ta faɗa masa don tun safe take jiran koda dawowarsa ne.


"Ina sauraronki Zuhra."

Ya faɗa don ya san bai fi wani ƙorafi ba ne ta kawo. Zama ta gyara ta karɓi maficin hannunsa tana tayasa.

"Da ma akan maganar Radiyya ne. Ya kamata ta koma haka nan ya isa."


"Ita ta nemi hakan?"

Ya ce yana kora ruwa a bakinsa.

Girgiza kai ta yi ta ce.


"A'a ni naga dacewar hakan."


"Sai ta amince, bazan mata dole ba."


A hasale Umma ta ce.

"Ko ta ƙi ko ta so sai ta koma, azumi kaɗai ta buƙaci ta yi a gidan nan muka barta, don haka dole ta koma. Ba zan zuba mata ido ina kallo tana sana'ar da babu ci gaba ba, kullum a wahale take. Ga can inda tana kwance za a bata, ta ci mai kyau ta sha mai kyau, sai taga damar cin abin da take so."


"Koma me za ki faɗa ki faɗa Zuhra amma Radiyya ba za ta koma ba, fakat. Ki na kallo ta tsaya da kafafunta, ta samu sana'ar da Allah ya buɗa mata, abin da take samu ko ni da na shekaru ina sana'ar Dukanci ban tara irinsa ba. Zuhra ba a tunkaho da abun wani, kar ki zama Hankaka mai da ɗan wani naka."


"Na ga ƴata ce?"


"Ni kuma ke nake aure ba. Ki sa Radiyya ta koma Zuhra a ranar za ki ga ɓacin rai na."


A fusace Umma ta dangwarar da maficin ta miƙe, ficewa ta yi a ɗakin. Girgiza kai ya yi halin Zuhra sam ba zai canza ba, ba dan ƙaddarar Allah ba da ina shi ina aurenta.

Umma ta ji haushin furucin Baba sosai, har ita Radiyyar haushinta ya lulluɓeta. Har ya manta alherin Uncle Nasir da yake masa, mutumin da tun da ya auri Mimi yake taimaka masa da hidimar gida, musamman idan sallah ya zo ko azumi.


....


Washegari ranar Lahadi aikin girkin gidan duk Radiyya ce ta yi, Umma ƙin yin komai ta yi, ita ta girka na safe ta raba, ta girka na rana ta raba, kasancewar Umma za ta bar girki ya sa Radiyya ta samu hutu. Ƙarfe biyu ta fara shirin haɗa zoɓo da kunun Aya, Amrah ta fita yin lalle maƙota babu mai taimaka mata. Wajen la'asar ta gama komai ta kimtsa. Wanka ta yi ta wuce ɗaki, kaya ta saka ta kimtsa jikinta kasancewar ba sallah take ba. Zama ta yi ta jawo wayarta, ita da kanta za ta ƙirasa yau ta sanar masa akwai zoɓo, a tunaninta kar ya ce yau ma babu ya ƙi zuwa. Sai dai saƙon da ta tarar a wayar ya sa tabi daki daki tana karantawa. Sako ne da ta tsani ganinsa, tun kwanakin baya ta fara cin karo da irinsa, sai dai ta banzartar da kashin me shi, tun tana jin tsoro idan ta gani har ta cire hakan a ranta ganin babu abin da ya faru, tasan duk barazana ne.


"Ina begenki, ina muradin kallonki. Na yi kewarki."


Daga haka babu abin da aka ƙara a saƙon. Ta rasa wa yake mata hakan, duk tunaninta ta kasa gano wanene, hakan yasa da zaran ta gani take karantawa ta goge. Yanzu ma gogewan ta yi ta shiga sahun ƙira, lambarsa ta lalibo ta ƙira, tasan wayar ba zai rasa kuɗi ba kuma haka ne don ya shiga.


....


Yana kwance yana waya da aboki ko aminsa za a faɗa, don yana ba hiran da suke muhimmancin da ya sa ko Hajiya Fauzy ba ya bari ta ji idan suna waya. Ƙara ne ya damesa ta cikin wayar da yake katse musu hiran, dole ya sanar da abokinsa zai amsa ƙiran zai ƙirasa. Bayan sun kashe ya duba lambar ya ga lambar Radiyya ne, a ransa ya shirya tsawatarwar wanda ya ƙirasa a wannan lokaci amma ganin Radiyya ne ya sa murmushi bayyana a fuskarsa, duk ɓacin ransa ya kawar. Ƙira ne ya sake shigowa da sauri ya ɗauka yana sallama.

...


Ta ɓangaren Radiyya jin an ɗauka tare da sallama ta amsa cikin sanyin muryarta. Gaishesa ta fara yi tana haɗawa da faɗin.

"Akwai zoɓo yau."


"Ina godiya, ina tafe yanzu."

Ya faɗa ta ɓangarensa farin ciki na lulluɓesa. Daga haka ya kashe wayar. Ƙiran abokinsa ya yi suka gama wayar su kusan mintuna talatin domin ta mayar musu da aiki baya. Bayan sun gama ya lallaɓa ya shiga bathroom, kansa ya sakarwa shawa ya yi wanka ya haɗa da alwala, bayan ya gama ya fito ya canza kaya, iya gama saka kayan ya shimfida sallaya ya tayar da kabbarar sallah. Da ya idar ya isa gaban mirror ya shafa mayukansa masu ƙamshi da daɗi, ya feshe jikinsa da turare kafin ya fita.

Hajiya Fauzy ba ta falon sama, ƙasa ya sauka nan ma ba ta nan, bai tsaya nemanta ba ya sa kai ya fice.

A ƙofar gidan su Radiyya ya faka motarsa, ƙiranta ya yi ya sanar mata ya iso. 


...


A shirye take tsaf, fos nata da kuɗaɗenta da yake ciki ta ɗauka ta, flat shoe ɗinta ta saka ta fito waje, leda ta ɗauka ta zuba masa goruna uku. Amrah da take bakin baranda tana cin tuwo dawowarta kenan ta isa wajenta.


"Amrah ki kula don Allah ko za a nema ya kusa karewa. Idan na miƙa saƙo zan wuce kasuwa."


"To sai kin dawo. Ba dan zan taya Yaya girki ba da na miki rakiya."


"Kar ki damu."

Radiyya ta ce tana murmushi ta fita. 


Kai tsaye da fara'a ta isa wajensa, yana ganinta ya buɗe gilashin motar. Miƙa masa ta yi ya karɓa yana faɗin.

"Thank you so much."


Murmushi ta yi tasa hannu ta karɓi kuɗin da ya miƙa mata. Yau ba ta jira ya bar gurin ba ta wuce abinta ta nufi titi inda za ta samu adaidaita sahu. Motar ya yi ribas ya bar gurin, har ya wuceta ya dawo baya daidai wajenta, sauƙe gilashin ya yi yana faɗin.

"Ina zuwa?"


"Kasuwa zan shiga."

Ta ba shi amsa tana ƙoƙarin yin gaba, a tsammaninta zai wuce sai ta ji akasin haka daga gareshi.


"Shigo in rage miki hanya, ni ma can na nufa."

....


Ya ku ke ganin tafiyar Alhaji Shaheed da Radiyya zai kasance?


#vote

#comment

#keeplove