11-15 Last Free Page
by @phartybb
Da mamaki Radiyya ta kalli Alhaji Shaheed, ganin shi ma ita yake kallo ya sa ta kawar da kanta ta ce.
"Na gode sosai wallahi, zan hau adaidaita."
"Ba godiyarki nake buƙata ba, ki shigo mu wuce. Ki na ɓata mini lokaci."
Ta ji ya faɗa mata. Fuskar tausayi Radiyya ta yi ta kalleshi ta rasa ma me za ta ce. Kansa ya kawar gefe yana cire lock ɗin motar.
"Zagayo ki shigo."
Ƙafafunta har rawa suke haka ta zagaya tana buɗe motar ta shiga. Ƙamshi da sanyi ne suka fara tararta. Idanuwanta ta lumshe ta buɗe tana sake buɗe ƙofofin hancinta don ci gaba da shaƙar daddɗan ƙamshin.
Tafe suke babu wanda ya yi magana cikin su, kowanne da abin da yake wassafawa a ransa. Alhaji Shaheed ne ya katse shurun ta hanyar tambayar Radiyya.
"Sunanki fa?"
Dum Radiyya ta ji maganar don ba ta tsammaci maganarsa ba. Ƙasa ƙasa ta ba shi amsa.
"Radiyyatun Mardiyya."
Kai ya jinjina alamar ya yi, bai ƙara magana ba har suka shiga kasuwar. Radiyya na son sanar da shi za ta sauƙa amma ta kasa, don tsoronsa take ji da girma, kuma tasan yasan da zamanta tun da shi ya ɗauketa. Duk ƙananun shagunan da tasan za ta samu abin da take so ya riga ya wuce. A babban shago ya tsayar da motar, bayan ya kashe ta fito da sauri. Shi ma fitowar ya yi yana yin gaba ya ce.
"Biyo ni."
Saman shagon idanuwanta ya kai ta ga sunansa ɓaro-ɓaro a jiki da manyan baƙi. Guri ne da ake saida kayan kitchen da duk abin buƙata na mace, babban guri ne sosai. Jiki a sanyaye ta ja ƙafafunta tabi bayansa. A can gurin masu karɓan kuɗin ta hangosa, ganinta ya sa shi yafitota da hannu, babu musu ta ƙarasa, gurin zama ya nuna mata ta zauna a ɗarɗar. Bai mata magana ba yajuya ga mutumin da yake kula da shagon.
"Me kike buƙata?"
Faɗin mutumin da yake gurin ganin Alhaji Shaheed ya kallesa.
"Firiji ƙarami nake so."
Radiyya ta ba shi amsa.
Juyawa ya yi ya kalli Alhaji Shaheed da yake danna wayarsa ya ce.
"Alhaji akwai Hisense akwai LG, su ake ya yi yanzu."
"A biyo bayanmu da guda ɗaya mai kyau."
Yana faɗar ya miƙe yana mayar da wayarsa aljihu, sai lokacin ya kalli Radiyya.
"Ta shi muje."
"Ban siya ba."
Ta ce a sanyaye cike da mamakinsa.
"Ta shi mu je kawai."
Ya faɗa yana yin gaba. Miƙewa ta yi ita ma tabi bayansa da sauri, dama tasan sunfi ƙarfinta na wajen nan. A wajen motarsa ta samesa tsaye yana kallon fitowarta. Gurinsa ta ƙarasa ta tsaye gefe.
"Na gode sai gobe."
"Kayankin ni zan kai miki gida? Ko wa ki ka barwa? Zan taimaka miki ne albarkacin abu ɗaya."
Bai saurari me za ta faɗa ba ya buɗe motar ya shiga bayan ya gama maganarsa. Sam Radiyya ba ta fahimci maganarsa ba, ta tafi duniyar tunani da neman gane maganarsa ta ji an danna mata horn. A razane ta kallesa.
"Za ki shigo mu wuce ko kuwa."
"Ka je kawai na gode."
Ta samu kanta da fada. Wani kallo ya watsa mata ya hanata ƙarasa maganar. Nauyinsa da Radiyya take ji ya sa ta zagayawa ta buɗe ƙofar ta shiga. Fizgar motar ya yi suka bar wajen. Ba wanda ya ƙara magana har suka iso ƙofar gidan su Radiyya, tana ƙoƙarin fita ya dakatar da ita ta hanyar ajiye mata leda saman cinyarta.
"Zan yi tafiya gobe, may be in kai sati biyu zuwa sama. Wannan kuma ki ƙara jari"
Kallon ledan ta yi tana ɗauka ta jujjuya, jin abin da ya faɗa ya sa ta kallesa, murya a ƙasa ta ce.
"Allah ya kiyaye hanya, ya bada Sa'a. Amma da ka bari."
"Ameen na gode. Ki gaishe da mutanen gida."
Kai ta girgiza ta fita, tana fita ya ja motarsa ya bar gurin. Radiyya na ƙoƙarin shiga gida ta ji tamkar ana mata magana. Juyawa ta yi taga masu jega da kwali firiji tare da su. Tamkar idanuwanta za su faɗo ta kalle su tana tambaya.
"Menene?"
"Saƙon da Alhaji ya ce a biyosa da shi."
"To ai shi za ku bi!"
Ta faɗa a tsorace, firgicinta ɗaya kar abin da take tsoron ji ta jisa a bakin mai isar da saƙon, sai dai abin da ta ji ya haifar mata da rawar jiki.
"Naki ne."
Ya mayar mata da amsa. Firijin suka cicciɓa tare da taimakon na sama suka nufeta. Radiyya ta rasa me za ta ce haka ta ga sun nufota. Amma Alhaji ya shammaceta, to duk zaman su a shagon ba ta ji an yi maganar da ya wuce biyar ba balle ta ji ya ce ya siya. Tsoronta ɗaya Baba da Umma su kasa fahimtarta.
"Ina zamu kai? Ciki?"
Masu riƙe da firijin suka tambayi Radiyya. Ita gaba ɗaya a tsorace ma take, amma haka dole ta girgiza kai ta nufi cikin gidan, a soro ta tsaya tana cewa.
"Bari in sanar da mutanen gidan sai ku shigo."
Sun yi na'am da hakan don ta nuna musu gidan da tarbiyya. Ciki ta shiga ta samu yarane kowacce tana cikin ɗakinta hatta Umma. Komawa ta yi sanar musu suka ɗauka suka shiga dashi, a saman barandar Umma suka ajiye ta musu godiya. Ɗaki ta shiga ta samu Umma tana zaune. Gefe ta samu ta zauna, tana son sanar da ita tana tsoro, amma ya za ta yi ita ce mahaifiyarta, dole ta sanar mata, duk hukuncin da ta yanke daidai ne, mayarwa ko riƙewa ko ba shi kuɗinsa. A hankali kamar mai ciwon baki ta ƙira sunan Umma tana miƙa mata ledar hannunta. Umma barin abin da take ta yi ta kalleta tana amsawa ta karɓi ledan, bayan ta kawar idonta daga kallon fuskarta.
Tiryan tiryan Radiyya ta sanar mata wanene Alhaji Shaheed da farkon zuwanta gidan mansa da duk abin da ya shafesa, har zuwa yau da yanzu da wannan lokaci. A tsorace Radiyya ta gama sanar da Umma ganin irin kallon da take bin ta da shi, ta lura Umma ba ta cika kallonta ba, amma yanzu yadda ta zuba mata ido abin ya tsoratata. Ga mamakin Radiyya gani ta yi Umma ta murmusa har tana buɗe hakwara tace.
"Ashe gaskiyan Malam da ya ce sana'arki shi ne hanyar arziƙinki. Ikon Allah! Ke kuma Allah da ya tashi lokaci ɗaya ya haɗaki da Alhaji. Alhaji Shaheed dai wanda gidan man sa yake farkon kwalta? Ko dai ƙarya ki ke mini Radiyya?"
Da sauri Radiyya ta girgiza kai duk da ba ta fahimci maganar Umma ba. Murmushi Umma ta sake ta matsa kusa da ƴartan.
"Abin da zan faɗa miki ki riƙe wannan maganar daga ni sai ke sai kuma Malam, zan sanar masa da kaina ba sai kin faɗa masa ba. Maganar siyan firijin kuma a barshi a matsayin ke ki ka siya abun ki saboda ƴan baƙin ciki. Kowa sai dai ya gani muna fafatawa da yardar Allah."
Idan Radiyya ta fahimci maganganun Umma to kaɗan ne a ciki, sam ba ta fahimci ina ta dosa ba da kalamanta. Ita da take tsammanin faɗa ko hani daga gareta, ko ta ce ta mayar da firijin ko kuɗin, amma sam hakan bai dameta ba ta lura.
'To ya zan yi?
Ta tambayi kanta tana zuba tagumi, Umma sai kirga kuɗaɗe cikin ledan take ganin uban yawan su.
Da matan gidan suka ga girman firijin da Radiyya ta buɗe kowa sai da ya tsorata, wasu tuni ƙishi ya turneƙe su sam sun kasa yarda da cewa da kuɗin zoɓo da Kunun Aya Radiyya ta siya babban firijin nan, ban da Amrah babu wanda ya mata murna. Amarya Zulaiha ranar wuni ta yi tsokanar Umma ta biye mata su yi cacar baki ta samu amayar mata na cikinta, sai dai Umma farin cikin ranta ya hanata biye musu, sai nannan take da Radiyya.
Da Baba ya dawo da daren ya gani ya ƙira Radiyya. Tare suka je da Umma har cikin ɗakinsa. Kai tsaye tambayar da ya mata shi ne.
"Firiji ki ka siya Radiyya babu sanarwa? Wannan ai sai ya janye ƙarfin wutar gidan. Ko kin manta kwan lantarki guda takwas ne a gidan sai soket a kowanne ɗaki."
Radiyya za ta yi magana Umma ta hanata da sauri ta ce.
"Ta shi ki je Radiyya zan masa bayani."
Babu musu ta miƙe ta fita a ɗakin. Bayan fitarta Umma ta nutsu don so take ya yiwa maganarta kyakkyawar fahimta.
"Mallam ina ba da haƙuri a bisa abin da ya faru jiya akan na ce Radiyya ta koma gidan Mimi. Kamar yadda ka faɗa ko wannan sana'ar shi ne arzikinta? Ashe tabbas shi ne. Domin yau Allah ya nuna mini. Kasan Alhaji Shaheed me gidan mai da manyan shaguna?"
"Na san shi Zuhra. Me ya faru?"
Ya tambayeta da mamakin da yake cikin ransa ya bayyana a fuskarsa.
"Ina zargin neman Radiyya yake da aure. Wannan firijin da ka gani shi ya siya mata yau."
"Shi Alhaji Shaheed ɗin! Yaushe? Babban mutum ne fa."
Baba ya ce da mamaki ƙarara a fuskarsa da wannan karon ya bayyana.
"Shi dai idan ba ƙarya ta min ba, kuma kasan Radiyya ba za ta min ƙarya ba."
Faɗaɗa fara'arsa Baba ya yi ya ce.
"Kin ga ikon Allah ko Zuhra? Tashi ɗaya Allah ya haɗata da rabonta mai tsoka. Ina musu fatan alheri."
"Ameen Ya Allah."
Ta furta ta kirga dubu goma cikin kuɗin Radiyya da ta bata ta miƙa masa. Karba ya yi ya kirga ya ce.
"Wannan fa?"
"Shi ya bata, ta ce kasa albarka."
"Ki ce abu ya yi nisa."
Ya ce yana sake kirga kuɗin, abin da tun safiya da ya fita yake neman bai samu ko rabi ba. Ranar sun yi kwanan farin ciki, musamman Umma ko a tunani da mafarki bai taɓa zuwa mata Radiyya za ta samu mai kuɗi haka ba kai tsaye, ga shi a ƙaramin sana'ar da take yi ya jawo mata farin Sa'a.
....
Radiyya tana jira ta ji Baba ya yi faɗa amma shuru har safiya da zai fita ya sameta a ɗaki. Bayan ta gaishesa ya ke faɗa mata cewa.
"Radiyya maganar kuɗin wuta, kin san firijin nan zai janye ƙarfin wutan ko."
Kan Radiyya a ƙasa ta ce.
"Baba da safe za ina kunnawa, sai kuma da yamma. Amma za ina bayar da wani abu duk ƙarshen wata."
Murmushi ya yi ya ce.
"Yawwa Radiyya, daɗina da ke akwai fahimta. Allah ya ƙara buɗi."
Da murnarta ta amsa kafin ya wuce. Tana jin daɗin addu'ar Baba gareta a kullum.
...
Tun daga lokacin sana'ar Radiyya ya ƙara bunƙasa, da sassafe za ta haɗa komai ta zuba a firiji ta kunna ya yi sanyi har da ƙanƙara. Mutane tuni sun saba da sha da siya, kafin yamma ya ƙare, wani lokaci sai ta sake haɗa zoɓo don masu siya da yamma. Masu raina sana'ar Radiyya sun fara ganin lalle abin ba daga nan yake ba, domin ta musu fintinkau. Yanzu tsakaninta da Umma lafiya lau suke zaune, babu faɗa ko hantara. Tun ranar Alhaji Shaheed bai ƙiranta ba, ita ma ba ta ƙira ba sanin baya nan.
Farin cikin Radiyya ya dawo, DUHUN ZUCIYARTA ya yaye, DUHUN da yake lulluɓe da rayuwarta ya zamo haske, hankalinta ya kwanta, ba ta da wani matsala ko damuwa a rayuwarta. Kullum a zuciyarta gani take tamkar Alhaji Shaheed shi ne mafarin yaye DUHUN ZUCIYARTA, kuma tana fata duhun ya yaye kenan.
***
"Ashe ke ƙazama ce? Me ya sa ta fiki tsafta? Dubi gidan nan dubi jikinki Mimi? Tamkar ba ke ba? Me ya sa Radiyya ta fiki tsafta da komai?"
Cikin faɗa ta buɗe murya tana faɗin.
"Komai ka ta shi Radiyya! Komai Radiyya!! To ka je ka dawo da ita mana. Kana gani dai ina iyakar ƙoƙarina."
Wani kallo ya watsa mata yana faɗin.
"A hakan? Dube ki. Tashi ki ba ni guri don Allah."
Tashi ta yi fuuu ta fice a ɗakin tana banko ƙofar. Sun fi sati biyu kullum cikin faɗa akan rashin kula da kanta da gidan. A ganinta tana iyakar ƙoƙarinta, amma sam ba ya gani, kuma ya hanata ɗaukar ƴar aiki. Radiyya yake so ta dawo don babu me iya kula da gidan sai ita a faɗinsa, ita ta ƙi sai dai ƴar aiki, shi ma kuma ya ƙi. Walid tun yana tambayar Radiyya har ya haƙura ya daina.
Da gaskiyar Radiyya da ta ce Alhaji Shaheed shi ne mafarin yaye DUHUN ZUCIYARTA?
#vote
#comments
#keeplove
DUHUN ZUCIYA
Babi Na Sha Biyu
Pharty BB
Wattpad PhartyBB.
Satin Alhaji Shaheed biyu a ƙasar Austaraliya kafin ya gama yin abin da ya kaishi. Tsawon kwanakin daurewa kawai yake, a daddafe ya tsaya aka gama abin da ya kai su. Ranar da za su dawo bai jira Kabir ba ko waɗanda suka haɗa tafiya tare ba, ƙarfe shida ya samesa a airport, jirgin ƙarfe bakwai ya tashi da shi zuwa Nigeria.
Sai da ya ganshi a cikin jirgi ya ɗaga da shi kafin hankalinsa ya kwanta. Murmushi ya sake tare da hamdala lokacin da jirgi ya sanar sun kusa sauƙa. Bayan saukar jirgin ya samu driver nasa ya iso ɗaukarsa. Driver yana kallon fitowar Alhaji Shaheed da sauri ya ƙarasa ya karɓi jakan hannunsa zuwa mota. Bayan ya saka ya zagaya ya shiga yana jan motar suka bar filin jirgin.
Tafe suke ya duba agogon hannunsa, yana da sauran lokaci da zai ishesa ya je gida kafin ya fita. Bayan isar su gidan sauka kawai ya yi ta wuce, driver shi ya fito da akwatinsa zuwa falo. Ya samu Hajiya Fauzy a falon ta yi kwalliyarta tana jiransa, murmushi ya akai mata ta mayar masa da amsa tana miƙewa.
Ganin ta taso kuma za ta ɓata masa lokaci ya sa ya nufi sama yana faɗin.
"Fauzy bari na watsa ruwa."
Da mugun mamaki ta bisa da kallo, mutum da koyaushe ya yi tafiya ya dawo ita yake fara son gani, ita take taimaka masa ya yi komai, idan ba ta yi ba har fushi yake.
Har ya haura da sauri ya dawo baya tunawa da akwatinsa, hakan yasa ya sauƙo, lokacin kuwa driver ya shigo da shi, karɓa ya yi kafin ya wuce. Mamaki iya mamaki Hajiya Fauzy ta shiga, tamkar wacce ta ga abin almara haka ta bisa da kallo har ya ɓacewa ganinta.
Ruwa kawai Alhaji Shaheed ya watsa ya fito, ƙananan kaya ya saka masu fitar masa da siffan yarinta, masu ƙara masa kyau da kwarjini. Mayuka masu ƙamshi ya shafa da turare kafin ya fita zuwa falo, a nan ya sake samunta zaune. Tana kallonsa ta sake miƙewa, kafin ta ce wani abu ya rigata faɗin.
"Just 5mins Fauzy, yanzu zan dawo ba zan jima ba."
Yana faɗar haka ya wuce zuwa ƙofar falon. Tana kallo ya fita ya barta tsaye, ba ta san yaushe ta zube dirshan saman kujera ba. Duk rashin zama da yake yi don yanayin sana'arsa bai taɓa mata haka ba a gida, yana bata dukkan kulawa na musamman.
...
Tafe yake yana murmushi shi ɗaya a cikin motar. Duk arziƙinsa abin da bai yarda ba da shi ne yawo da driver, a faɗinsa duk inda zai je sirrinsa ne, driver na aiken gida kawai ya ɗauka don Hajiya Fauzy wani lokaci, duk da ita ma ta iya motar.
Murmushin nan bai gushe a fuskarsa ba har sai da ya gansa ƙofar gidan su Radiyya. Agogon hannunsa ya kalla ya ga ƙarfe biyu da rabi, sai ya ga ya yi saurin zuwa, addu'arsa Allah ya sa ta yi. Tsawon sati biyu ji yake ya yi kewar zoɓonta, amma ƙasan ransa na hasaso masa ba zoɓon kaɗai ba hatta ita ɗin ya yi kewar gani. Nutsuwarta da shuru shurunta yana burgesa, sam ba ta da hayaniya daga yanayinta. Gani yake sam ba za ta yarda da buƙatarsa ba, sai dai ba daga nan take ba, domin shi ma Allah ne ya ɗaura masa don ya jarabci imaninsa.
Ganin yana ɓatawa kansa lokaci akan tunanin da ya fara damunsa kwana biyu akanta ya sa ya ciro wayarsa ya ƙira lambarta.
...
Radiyya na tsakiyar wanki ta samu ƙiran, ɗauraye hannunta ta yi ta nufi ɗaki, a ƙofa suka yi kiciɓus da Umma ta ɗauko wayar. Karɓa ta yi ta shiga ɗakin Umma kuma ta fita.
Sai da ta nutsu ta amsa ganin mai ƙiran. Duk da yana yawan faɗo mata rai har cikin ranta ta manta da shi yau. Bayan ta amsa da sallama ya sanar mata yana ƙofar gida, babu ɓata lokaci ta ce tana fitowa. Bayan ta kashe wayar ta miƙe, hijabi babba ta saka har ƙasa ta fita. Leda babba ta ɗauka ta buɗe firigi ta zuba masa zoɓo da kunan Aya da ardeb da ta fara, a faɗinta wannan hanyar kawai za tabi ta gode masa kyautar da ya mata.
Tana gamawa ta fita zuwa ƙofar gidan, cikin motarsa na farko da ta fara ganinsa cikin gidan mai da shi ya zo. Tun da ta fito ya zuba mata idanunsa da sun yi kewar ganinta, yayin da kunnuwansa suka yi begen sauraron daddaɗan muryarta, bakinsa ya yi rashin jin garɗin zoɓonta, zuciyarsa kuwa ita kanta ta yi kewa.
Isowarta ya ankarar da shi, a hankali ya zuge gilashin motar yana ci gaba da kallonta. Kallo ɗaya Radiyya ta masa ta sunkuyr tana gaishesa da masa ya hanya.
Murmushi mai kyau ya yi tamkar tana gani ya ce.
"Allahamdulillahi. Sai kewa."
"Ga shi wannan kyauta ne daga gurina. Ina sake godiya."
Ta faɗa tana miƙa masa ledar hannunta.
Karɓa ya yi ganin da nauyi kuma dayawa ya ce.
"Duk ni ɗaya Radiyyatu."
Karo na farko da ya ƙira sunanta, hakan ya sa ta ɗago ido suka haɗa ido, dole ta ɗauke nata, yana cika mata ido yana mata kwarjini.
"Eh, ka kaiwa yara."
"To muna godiya."
Ya faɗa yanayin muryarsa yana canzawa. Dole ya sa ta sake kallonsa jin maganarsa ya canza, ɗauke kai ya yi ya rufe gilashi. Hakan ya sa ta ja baya ya yi ribas ya bar gurin.
Cikin gida ta koma ta ci gaba da aikinta, cikin ranta tana tunanin me ya sa daga faɗin haka ya canza.
....
Alhaji Shaheed yana isa gida bayan ya yi fakin motarsa ya ƙira mai gadi ya ba shi kunu aya da ardeb shi ya riƙe zoɓo. Cikin falon ya nufa daga haka, a zaune ya samu Hajiya Fauzy da har lokacin tunani bai bar ranta ba. Tana ganinsa ta nufesa, a dinning ya zauna ita ma ta isa wajen tana zama.
"Daga ina haka daga zuwa babu tsayawa ka tafi?"
Tambayar da ta masa kenan.
Zoɓo ya jawo ya nuna mata da ido ya ce.
"Zoɓo na siyo."
"Amma Alhaji akan wannan zoɓon za ka wuce ka barni, ko damar sannu da zuwa ban maka ba. Wani irin zoɓo ne wannan? Me ne a ciki?"
"Ba za ki gane ba sai kin taɓa, idan za ki sha ɗauki ɗaya."
Ya faɗa yana kafa baki ya hau shan na hannunsa ko a kofi baya tsiyaya.
Tsaki ciki ciki ta yi tana hararan zoɓon ta ce.
"Allah ya kiyaye, nasan me aka zuba ciki, wannan kayan ƙazanta."
"Kuma idan ki ka yi ba ya daɗinsa ba. Zuba mini abinci."
Ya ƙarasa maganar yana bata umarni ya haɗa rai, idan ta ci gaba da kushe abin Radiyya ji yake zai tanka, zuciyarsa ba zai iya ɗaukar duk mai cin zarafinta ba.
Babu yanda ta iya ganin ya basar da zancen dole ta miƙe ta zuba masa abin da mai aiki ta girka musu. Suna ci babu wanda ya yi wa juna magana, yana ƙoshi ya ta shi ya bar wajen. Da kallo ta bisa tana ajiye cokalin hannunta, hannayenta ta kai ƙasar haɓarta ta tallafo.
"Dole na yi bincike."
Ta faɗa a ranta tana miƙewa ta bar wajen. Ji ta yi abincin ya fita a ranta gaba ɗaya.
....
Washegari Alhaji Shaheed bai fita da wuri ba barcinsa ya sha sosai sai gurin sha ɗaya ya farka. Wanka ya yi ya fita zuwa ɗakin Hajiya Fauzy da tun daren jiya take masa fushi. Ɗakin fes ita ma ta yi kwalliyarta cikin doguwar riga mai kyau. Abu ɗaya da take burgesa kenan. Bayan son da yake mata tana da son ƙamshi da kwalliya, kullum fes fes take.
Ganinsa ya sa ta haɗa rai tana miƙewa, ƙoƙarin barin ɗakin take ya hanata ta hanyar tsayuwa gabanta. Hannayenta ya kamo da suka sha jan lalle.
"Afuwan Uwargidana."
Kallonsa ta yi ya ɗaga mata kai yana murmushi. Son da take masa da yadda yake mata ya sa ta saki ranta ta rungumesa ta ce.
"Na haƙura."
Cikin nutsuwa suka gabatar da breakfast cikin plate ɗaya. Yana gamawa ya kwashi mukullin motarsa da wayarsa ya mata sallama ya fita. Da kallo ta bisa tana sakin murmushi a ranta tana faɗin.
"Duk daɗin bakinka da son da nake maka ba zai hanani bincike ba."
....
Alhaji Shaheed yana fita wajen da ake kula masa da dukiyarsa ya bi ya duba kowanne. Ƙarshe ya yada zango a gidan gonarsa, ya ɓata lokaci yana abu ɗaya a wajen kafin ya samu abin da yake so ya tafi, a kasuwa ya tsaya ya ƙara da wani abu sannan ya kama hanyar gidan su Radiyya. Karfe ɗaya da mintuna lokacin. Bai ƙirata ba yau shi da kansa ya fita a motar, rana na farko da ya fito kenan. Matasa da manyan mazan unguwar ganin wanene tuni an fara tsayawa kallonsa.
Alhaji Shaheed dauriya kawai yake ganin kallo ya koma kansa duk da dayawa basu san fuskarsa ba, ƙiran ƙananan yara ya yi ya buɗe but ɗin motarsa tare da nuna musu kwai na Zabi da za su ɗauka zuwa cikin gidan su Radiyya.
...
Amarya ce da girki, tana bakin madafa tana kwashe tuwo aka fara shigowa da kwalaye. Inna Saudatu na zaune tare da yaranta. Umma tana cikin ɗaki yayin da Radiyya tana aikin ɗura zoɓo Amrah na tayata da rufe goruna.
Bayan sun ajiye kwalayen Amarya Zulaiha ta musu magana.
"Kai daga ina?"
"Wani Alhaji ne ya ce a kawo, yana waje."
"To! ikon Allah, shi Alhaji ba shi da suna. Ko wannan mijin yarinyar ne Maimuna?"
Yara dai basu san wanene ba, hakan ya sa basu tsaya bata amsa ba suka fita. Tuni gidan duk an iso bakin kwalayen ana ganin menene.
"Kwai ne wallahi! Kamar na Zabi?"
Amarya Zulaiha ta ce da ƙarfi tana ɗaukan ɗaya ta fara jujjuyawa.
Radiyya tana saurin ta gama na hannunta ta isa gurin ta gani ta ji ƙarar wayarta. Tsaki ta buga ta jawo, ganin me ƙiran ya sa ta nutsuwa ta amsa da sauri.
"Ina ƙofar gida."
Ya sanar mata ta ɓangarensa.
"Ina zuwa."
Ta ce ta kashe. Hijabi tasa ta fita da sauri bayan ta ɗauka masa abunsa, babu wanda ya lura da fitarta sai Umma, hakan yasa tabi bayanta a sanɗa.
Ta yi mamakin ganinsa tsaye yau a waje, manyan wajen tsofi duk sun zagayesa suna gaisawa. Fitowar Radiyya ya sa ya sallame su bayan ya ciro damin kuɗi ya miƙa mutum ɗaya su raba, dama abin da ya kawo su take suka ja gefe.
Da sallama ta iso tana gaishe sa, cikin fara'a ya amsa domin yanzu burinsa ya yi yaƙi a kanta sai inda ƙarfinsa ya ƙare. Abun da take miƙa masa ya karɓa, ya leƙa kansa cikin mota ya ɗauki ledar ciki da hannunsa ya kallota yana miƙa mata.
"Tsarabarki ne."
"Ni kuma?"
Ta ce da mamaki tana kallon ledar.
Kai ya ɗaga mata har lokacin yana miƙa mata. Dole ta karɓa don ganin girmansa take, haka kawai kuma ba ta iya musa shi.
"Kai ka yi ake cikin gida?"
Ta tambayesa da sauri ganin zai shiga mota. Kai ya daga yana faɗin.
"Wancan na su ne, idan sun soya idan suna so su ba ki kaɗan."
Dariya da kunya Radiyya ta ji ta rufe fuskarta. Ta yi mutuƙar masa kyau hakan yasa ya shagala da kallonta har sai da ta tsargu ta kalli gefenta. Ganin haka ya sa ya yi murmushi ya shige motar yana ja ya bar gurin. Komawa cikin gida Radiyya ta yi, a soro suka yi kiciɓus da Umma. Radiyya ta tsorata da ganinta. Umma ko murmushi ta yi ta ce.
"Shi ya aiko ko? Wannan ma shi ya ba ki ba?"
Kai Radiyya ta ɗaga tana miƙa mata ledar, karɓa Umma ta yi ta wuce ta barta nan tsaye. Da sauri kuma Radiyya ta bi bayanta jin abin da take faɗawa mutanen gidan.
Samun Umma ta yi ta ɗauke dukka kwalayen ta kai saman baranda tana faɗin.
"Wannan sakon na Radiyya ne. Don haka kowa ya kama aikin gabansa."
Inna Saudatu daga bakin ƙofarta ta ce.
"Ta ya za ki faɗi haka? Bayan ke kan ki ba ki san waya aiko ba."
Ledan hannunta ta nuna mata ta ce.
"Wanda ya bayar wannan shi ya bada wannan, a ciki muka ga ni."
"To wanene? A faɗa mana mu sani."
"Dole ne?"
Umma ta mayar wa da Amarya Zulaiha amsa tana buga mata uban harara. Radiyya tana jin su tana aikinta, taƙaici kamar ya kasheta.
Ƙarshe dai Umma dukka kwalayen ta jide zuwa ɗakinta ta hana kowa taɓawa. Da yammaci da Baba ya dawo har rige-rigen sanar masa aka yi, da ya ƙira Umma jin ba'asin ta faɗa masa Alhaji Shaheed ne ya aiko wa Radiyya. Da fara'arsa ya ƙira Radiyya ya ce ta isar da godiyarsa zuwa gareshi. To kawai ta ce ta fice.
Bayan fitarta ya roƙi Umma ta basu kwali ɗaya a ƴan gidan, babu yadda ta iya dole ta bayar. A daren aka soya kusan rabi kowa ya ci, har Amarya da taƙaici ya kusa kasheta.
#vote
#comments
#keeplove
DUHUN ZUCIYA
Babi NA Sha Uku
Pharty BB
Wattpad PhartyBB
Tin daga ranar Alhaji Shaheed ya fara kyautata Radiyya da iyayenta, burinsa ya samu gurbi a zuƙatan su musamman ita Radiyyar da ya lura tana ganin girmansa. Tabbas haƙarsa ta cimma ruwa, domin duk girmansa hakan bai hana Radiyya sa shi cikin ranta ba, wani matsayi ta ba shi don dalilinsa ta fara ganin haske a rayuwarta, shi ne ya yaye mata duhun da zuciyarta yake ciki, ya haskaka mata rayuwa. Idan dai yana gari to kamar faɗin Allah kullum sai ya zo, a baya idan ya zo baya jimawa amma yanzu zai tsaya su gaisa, ba zai bar gurin ba sai ya sa ta dariya.
Ƴan gidan su Radiyya tuni suka fara janta a jiki. Umma duk abin da Radiyya ta samu sai ta ƙwace. A ɓoye Radiyya ta ci gaba da yin asusunta ba da sanin Umma ba.
Baba ɓangarensa shi ma yana jin daɗin sauyi da ya fara samu dalilin Radiyya, yunwar gidansa ya fara tafiya.
Sakwannin da ake turowa Radiyya an daina sai dai a ƙirata, idan ta ɗauka ba a magana sai dai ta gaji da sallama ta kashe wayar.
...
Aunti Mimi da Uncle Nasir har ya kai ya kawo sun fi sati basa magana, kullum yana cikin faɗa da zagi. Faɗar su na ƙarshe da ya shigo ya samu inda ta ci abinci ta bari ta shiga ɗaki ta kwanta, daga nan barci ya kwasheta. A hasale ya bankaɗa ƙofar ɗakinta ya shiga, wani baƙin ciki ne ya turnuƙesa ganinta kwance tana barci.
A tsawace ya tasheta ta hanyar ƙiran sunanta.
"Maimuna! Maimuna!!"
Cikin daddaɗan barcinta ta ji ƙiran. A firgice ta miƙe zaune, murza ido ta yi ganin waye a tsaye. Cikin muryar barci ta ce.
"Lafiya?"
"Au tambayana ki ke? Wani rin ƙazanta ne wannan? Me ya sa ke ƙazama ce? Radiyya ta fiki tsafta."
Jin sunan da ya ƙira ta hargitse ta miƙe tsaye.
"Wallahi ka fara ishena da sunan yarinyar nan. Me ya sa komai sai ita?"
"Saboda..."
Sai kuma ya yi shuru ya fasa faɗar abin da zai faɗa ya nufi ƙofa. Da sauri ta tare hanyar tana masa wani kallo.
"Saboda me ya sa? Ka bani amsa."
"Ba zan bayar ba. Bani hanya na wuce."
Yana faɗin haka ya fizgeta gefe ɗaya ya yi wucewarsa. Durƙushewa Mimi ta yi jin ƙafafunta sun kasa ɗaukarta, Allah ya sa dai ba abin da take tunani ba kenan.
...
Ɓangaren Hajiya Fauziyya yanzu lamuran mijinta ya fara wuce tunaninta, duk hanyar da za ta yi bincike ta kasa. Wannan jarababben zoɓon da yake sha ya fara isharta, kullum ba ya rabuwa da shi, duk juice ɗin zamani idan ta gani za ta yi amma wani lokacin ko kallo ba ya yi. Dalilin haka ya sa yau ta zage ta shirya masa zoɓo da kanta, ƙamshinsa da daɗinsa tasan dole ne ma yau ya yaba, kuma ya haƙura da shan wanda yake siya.
Da yamma ƙarfe huɗu bayan ya dawo daga wajen Radiyya ya shigo falon. Da ledar hannunsa ta ci karo idanuwanta suka sauka akai. Miƙewa ta yi zuwa gareshi bayan ta katse wayar da take yi. Gurinsa ta nufa tana masa sannu da zuwa. Da fara'a kamar koyaushe ya amsa, daga haka suka wuce teburin cin abinci.
A babban plate ta zuba musu ta saka musu cokali, ba ta zauna ba ta wuce ta buɗe fridge ta ciro jug ɗin da zoɓon yake ciki, ya yi sanyi sosai sai gumi yake. Komawa ta yi gurin teburin ɗauke da shi, kofi ta ɗauka da yake saman teburin a jere ta zuba ta ajiye gefen mijinta, sai lokacin ta zauna ita ma tana faɗin.
"Yau dai ni ma nayi wannan zoɓon, sai ka hakura da na kasuwa."
Murmushi ya yi yana ci gaba da cin abincinsa, kamar ba zai ce komai ba can ya dakata bayan ya haɗiye abincin bakinsa ya ce.
"Wannan daɗinsa daban ne, ba na kasuwa ba ne."
"Dagaske Alhaji?"
Ta tambaya cikin mamakin da ta ɗaura bisa fuskarta.
Kai ya ɗaga mata ya na ɗaukan cokali ya ce.
"Eh ko za ki taɓa."
Cikin sauri kamar jira take ta ce.
"Eh idan ka bani ba, in ji da me ya fi nawa. Amma fa sai ka faɗa min ina kake siya, don ba zan sha abin da ban san ina ka samu ba."
Bai kawo komai a ransa ba ya miƙa mata yana faɗin.
"A gida ne ake yi. Yarinya ce ƙarama."
Babu musu Hajiya Fauziyya ta karɓa goran ta miƙe, ba ta ba shi amsa ba ta wuce kitchen. Tas ta juye a sink ta jefa gorar a dusting ta dawo tuburin. Dafa tuburin ta yi tana yi wa Alhaji Shaheed wani kallo da ya gama cin abincinsa yana goge baki da tissue.
"Ka ce karuwa ce take ba ka? Ashe dole ka maƙalewa abin da bai kai ya kawo ba, abin da idan kana so yau za ka iya sarrafa na kamfaninsa, amma ka tsaya kana layin zuwan siyan zoɓo. Da kuɗinka da darajarka da girmanka Alhaji ka dinga zuwa layin sayan zoɓo. Menene karuwar nan ta maka haka ni Fauziyya? Tun zaman mu ba ka taɓa kawo min sunan wata ba sai a kanta. Me ya ke faruwa? Ko dai tana ba ka kanta ne?"
Ransa a haɗe tamkar hadarin da ya haɗo yake kallonta, cikin tsawa ya dakatar da ita.
"Shut up Fauzy! Kar ki kuskura ki ƙara ƙiran Radiyya karuwa!! Tana da hankali da nutsuwar da ba kowacce ƴa mace take da shi ba."
Tuburin ta buga da ƙarfi tana faɗin.
"Na faɗa karuwa! Karuwa ce mana. Idan ba haka ba me zai sa ka din ga bibiyarta akan abin da bai kai ya kawo ba."
Miƙewa Alhaji Shaheed ya yi ya buga teburin wanda ya fi nata ƙarfi har plate ɗin sama suna canza mazauni, kafin ya nuna ta da yatsa.
"Ki shirya kishi da karuwa Fauziyya."
Daga haka ya kwashi mukullinsa ya bar mata gurin, a gidan ya fice gaba ɗaya.
Mutuwar tsaye Hajiya Fauziyya ta yi jin furucinsa, ƙafafunta sun yi laushi tamkar yaron da ya fara takawa, hakan ya sa suka kasa ɗaukarta dole ta kai ƙasa daɓas. Mamaki da al'ajabi sun dabaibayeta akan maganganunsa. A kan wata mace har mutumin da su ɗauki tsawon shekaru talatin da aure zai mata wannan maganar. Zumbur ta miƙe ta bar gurin, sama ta haye zuwa ɗakinta.
...
Alhaji Shaheed gidan gonarsa ya wuce don hutawa. Maganganun Hajiya Fauziyya na masa yawo, babu abin da ya fi cin ransa kamar yadda ta ƙira Radiyya da karuwa. Girgiza kai ya yi yana cije leɓbensa, ya yanke hukuncin da yake ganin shi ne daidai ga dukkan su uku.
Sai ƙarfe goman dare ya bar wajen, daga can gida ya nufa. Falon wutar a kunne, bai kawo hakan komai ba ya wuce sama. Shirin barci ya yi ya kwanta ko duba Hajiya Fauziyya bai tsaya yi ba.
Washegarin Alhaji Shaheed ƙarfe goma ya sauƙo ƙasa don yin breakfast. Mamaki ne ya kamasa ganin tuburin yadda ya bari jiya haka ya samu. Abin da ya jima bai yi shi ne shiga kitchen, dole ya leƙa don ƙiran ƴar aiki ta gyara wajen. Wayam ya tarar da kitchen din, hakan ya sa ya nufi sama ɗakin Hajiya Fauziyya. Abin mamaki babu kowa ciki, ɗakin a hargitse. Duk inda zai ganta a gidan ba ta ciki, ƙarshe ya ciro wayarsa ya ƙirata, yana ta ringing ba ta ɗauka ba, dole ya fita don nemanta in da ya san zai sameta.
...
Tana ganin ƙiran ta ƙi ɗauka, har ya katse ya sake ƙira ta ƙi. Wacce suke zaune tare ne ta kai hannunta ta ɗauka. Ganin me ƙiran ta miƙa mata.
"Ɗauki ki ji me zai faɗa mu ji."
Dole ta amsa tana kafawa a kunne. Ya jima yana magana tana basarwa har ya zamto ta amsa kafin ta kashe. Kallon ƙawarta ta yi tana faɗin.
"Yana ƙofar gida ya ce na je mu koma. Me ki ka ce Sopiyya."
"Ki je Fauzy. Zamu san abin yi da izinin Allah."
Faɗin ƙawarta tana karfafa mata gwuiwa.
Tashi Hajiya Fauzy ta yi ta ɗauki handbag nata da yake saman gado. Daga nan suka fita zuwa ƙofar gidan. Zaune cikin motarsa suka samesa. Bayan Sopiyya ta gaishe da shi Hajiya Fauziyya ta buɗe motar ta shiga. Daga nan suka yi wa juna sallama ya ja motar.
Suna tafe babu wanda ya yi magana shuru, kowa da abin da yake wassafawa a ransa. Ita jira yake ya buɗe baki ya ba ta haƙuri kamar kullum sannan ya sanar da ita ya daina zuwa wajen wannan yarinyar. Shi kuma hukuncin da ya yanke yake son sanar mata.
Haka suka isa gidan, bayan ya shiga a fusace ta buɗe motar ta fito ta nufi ciki. Hakan shi ma ya fito ya rufe ya bi bayanta. Ba ta falo hakan ya sa ya hau sama. Har cikin ɗakinta ya sameta ta kwanta bisa gadonta. Takawa ya yi ya zauna gefenta. Tana ƙoƙarin juya masa baya ya ce.
"Ta shi mu yi magana Fauziyya."
"Me za ka faɗa min kuma?"
Ta tambayesa tana fasa juyawa gefe ɗayan. Hannu ya sa ya tallafota ta miƙe. A nutse ya fara magana.
"Fauziyya ni ban yi fushi ba kin yaɓa mini magana sai ke. Duk zaman mu na taɓa kallon wata mace da sunan so bayan ke? Ke shaida ce. Abin da na faɗa cikin ɓacin rai ne, hakan ba zai ƙara faruwa ba."
Jin maganganunsa cikin nutsuwa har da lallashi ya sa Hajiya Fauziyya sassauta murya ita ma ta ce.
"Ka bani mamaki ne Alhaji, duk arziƙinka ka dinga abu tamkar talaka. Ni dai kawai wannan zoɓon za ka daina zuwa siya, ka daina sha."
Shuru Alhaji Shaheed ya yi. Idan ya ce zai daina ya yi ƙarya. To Radiyya fa? Amma ji ya yi zai yi ƙoƙarin ganin ya kauce duk abin da zai ƙara haɗasu da Hajiya Fauziyya ta dalilinta.
"Ba za ka iya ba ko?"
Maganarta ya dawo da shi hankalinsa. Kallonta ya yi ya girgiza kai.
"Ba ki tambaye ni dalilin zuwana ba. Ni kaina bansan zan zamto ma'abocin shan zoɓonta haka ba duk da ina son zoɓo a rayuwata. Sai dai tun cikin azumi da na sha sau ɗaya na kasa hakura, shi ya sa ya zamto kullum sai na aika an siyo mini. Barinta gurin sana'arta bayan azumi ya sa na nemi gidan su na fara zuwa da kaina. Amma yanzu shikenan ba zan sake zuwa ba na haƙura."
Kai ta ɗaga tana rumgumesa, dole ya karɓeta suka canza salon. Ranar sai ƙarfe sha biyu da rabi suka samu yin breakfast. Bayan samun nutsuwa ya wuce ɗakinsa don kimtsa jikinsa.
Tana ganin fitarsa ta miƙe ta ciro wayarta. Ƙira ta yi ringing ɗaya aka ɗauka.
"Sopiyya a ci gaba da bincike."
Daga haka ta kashe wayar ta faɗa bathroom. Ranar Alhaji Shaheed bai fita ko'ina ba don gudun ɓacin ranta har dare.
...
Radiyya ranar har ƙarfe shida tana zuba ido don jiran ƙiran Alhaji Shaheed. Bai ƙirata ba kuma ta kasa ƙiransa don bai saba mata hakan ba. Dole ta dangana hakan da ya yi tafiyar gaggawa ko wani uzurin.
Har washegari Radiyya ba ta ƙiransa ba ,dole ya sa ta amince cewa ya yi tafiyar ne. Haka ta mayar hankalinta ga sana'arta kamar kullum.
***
A kwanakin ukun da ya wuce Alhaji Shaheed iya dauriya ya daure ba ya fita ko'ina. Duk wani harkar business nasa ta waya yake yi. Sai dai zuciyarsa da idanuwansa sun yi kewarta. Duk ƙoƙarin ganin ya danne kasawa ya yi domin shi da kansa ya nemi gurbi a rayuwarta kuma ya samu.
Hajiya Fauziyya ta ji daɗin haka dama tasan mijinta nata ne ita ɗaya sai yadda ta yi da shi. Kishi ya sa ta aikata haka gareshi, ga shi yanzu ta hanasa aikata komai.
Ƙiran gaggawa da Alhaji Shaheed ya samu akan kayan da suka yi order sun iso dole ya sa shi shiryawa ya fita yau. Fitar da ya samu da ƙyar a wajen Hajiya Fauziyya. Bayan ya isa Plaza ya gani, ya yaba da kayan ya musu sallama don komawa gida. A hanyarsa na tafiya kasa jurewa ya yi da abin da zuciyarsa ta haska masa, dole ya karkata kan motarsa zuwa wajen.
#vote
#comment
#keeplove
DUHUN ZUCIYA
Babi Na Sha Huɗu
Pharty BB
Wattpad PhartyBB
Da sauri ta ɗauki wayar tana amsawa ganin me ƙiran. Sallama ta yi tana sauraron abin da aka faɗa. Kashe wayar ta yi ta miƙe, hijabi ta saka ta fita a ɗakin. Ɗauke da zoɓon da ta saka a leda ta fita waje.
A ƙofar gida ta samesa zaune cikin motarsa. Kanta sunkuye ta ƙarasa wajen.
Har ta tsaya kafin ya sauƙe numfashi yana sauƙe gilashin. Buɗewar gilashin ta ɗago kai suka haɗa ido. Dole ta sunkuyar kanta tana gaishesa. Amsawa ya yi yana buɗe murfin motar, bai fito ba yana zaune a ciki ya miƙa hannun ya karɓa ledar hannunta tare da faɗin.
"Kin ga kwana biyu shuru ko?"
Kai Radiyya ta ɗaga da sauri, tambayar da take son masa kenan ta kasa. Murmushi ya faɗaɗa ganin ta fara jin abin da yake ji akanta.
"Na yi tafiya ne."
Ya samu kansa da furta haka.
"Ka dawo lafiya?"
"Lafiya lau sai kewa. Amma..."
Bai ƙarasa ba wayarsa ya katsetsa da ƙara. Da sauri ya ɗauka yana duba wa ya ga Hajiya Fauziyya ce. Bai ɗauka ba ya ajiye yana kallon Radiyya ya ce.
"Zan wuce sai gobe."
"Allah ya kaimu."
Faɗin Radiyya ta juya zuwa gida. Har ta shige yana binta da kallo kafin ya ja motar yana barin wajen.
...
Haka ya zamana tun ranar, duk zuwan da Alhaji Shaheed zai yi wajen Radiyya a ɓoye yake zuwa. Idan ya karɓo zoɓo tun a hanya yake shayewa. Tsakaninsa da Hajiya Fauziyya suna zaune tamkar babu abin da ya faru. Kowanne na ciki na ciki.
Ɓangaren Hajiya Fauziyya sun bazama binkice ita da Sopiyya akan Radiyya. A ranta take jin har yanzu Alhaji Shaheed yana zuwa wajen Radiyya.
Yayinda a hankali hankali Alhaji Shaheed ya din ga cusawa Radiyya son sa a ranta. Yana sake mata fuska tamkar ba shi ba. Radiyya tana girmamasa da ba shi matsayi sosai a ranta, duk kunyarsa take ji idan yana mata hira.
Bayan sati biyu da faruwar haka ya samu ƙiran gaggawa daga ƙasar Canada. A ranar da zai tafi ya sanar Hajiya Fauziyya, ta dage ta ce za ta masa rakiya zuwa airport. Sam ya ce ya ƙi don yana son yi wa Radiyya sallama. Fahimtar tamkar yana da wani abin da yake ɓoyewa ta nuna masa ta hakura.
Shiryawa ya yi ya mata sallama ya fita a gidan tare da driver. Tana ganin fitarsa ta miƙe ta zari wayarta da gyale ta fita. Bin bayansa ta fara a hankali yayin da take ƙiran Sopiyya.
"Sopiyya ina zuwa."
Daga haka ta kashe wayar ta ci gaba da tuƙi duk inda suka shiga. Har cikin unguwar da ya shiga ta shiga ta samu gefe da nisa ta yi fakin. Tana kallo ya fito tare da wayarsa a hannu.
Bayan tsayuwarsa ya fito ya ƙira Radiyya. Ba ta jima ba ta fito kamar kullum cikin hijab. Sallama ta masa ya amsa ta gaishesa. Kallonta yake ya ce.
"Zan yi tafiya ne Radiyya. Tafiyar gaggawa ya same ni, shi ne na zo miki sallama."
"Allah ya kiyaye hanya ya bada sa'a."
Ta masa addu'a kamar kullum.
"Ameen. Ga wannan ki riƙe."
Ya amsa yana miƙa mata kuɗi.
Girgiza kai ta yi ta ce.
"A a na gode sosai wallahi. Hidimar da ka ke mini ya yi yawa wallahi."
"Karɓi na ce, ai ba roƙana ki ka yi ba."
Dole Radiyya ta sa hannu ta karɓa tana godiya ganin ya haɗa rai. Daga nan ya mata sallama ta koma gida, shi kuma ya shige mota suna barin gurin.
...
Yana barin gurin da ƙyar ta iya jan motar tana barin wajen. Tsananin tashin hankali har rufewa idanuwanta suke, zuciyarta ya bushe. Dishi dishi take kallo Allah kaɗai ya kaita gidan Sopiyya. A karkace ta yi parking ta faɗa cikin gidan, jikinta har rawa yake yayinda maƙoshinta ya bushe.
Da sauri Sopiyya ta tashi zuwa ga Hajiya Fauziyya ta rikota.
"Lafiya Fauziyya! Me ya faru?"
Kasa cewa komai ta yi ta zauna daɓas saman kujera. Sopiyya duk ta rikice ganin ƙawarta ba ta cikin nutsuwa.
Hajiya Fauziyya da ƙyar ta jawo numfashi ta ce.
"Sopiyya ba ni ruwa."
Da sauri ta miƙe ta shiga kitchen ta tsiyayo ruwa ta dawo ta miƙa mata. Karɓa ta yi ta shanye tas tana wulli da kofin. Sai lokacin ta samu damar magana.
"Idan kin ga na bar yarinyar nan ta ji daɗin rayuwarta bana numfashi! Ba zan taɓa kishi da yarinyar da a haife na haifi na sama da ita!!"
"Ki nutsu Fauziyya! Me ya faru?"
Sopiyya ta ce tana zama gefen Hajiya Fauziyya. Kusan mintuna uku ya shuɗe tsakanin su shuru, Sopiyya ta katse shurun ta ce.
"Ki mini bayani Fauziyya."
Gwauron numfashi Hajiya Fauziyya ta sauƙe tana labarta mata tun fitowarta biyo bayan Alhaji Shaheed har zuwa ƙofar gidan su Radiyya da yanzu, ƙarshe ta rufe maganar tana faɗin.
"Me abin yi Sopiyya?"
Sopiyya da abin ya ba ta mamaki cikin al'ajabi ta ce.
"To me hakan yake nufi? Sonta yake kuma da ma bai rabu da ita ba."
"Ga alamu nan. Akan Alhaji Shaheed zan iya komai, idan na ce komai ina nufin komai."
Hajiya Fauziyya ta ce tana cize yatsa.
Da sauri Sopiyya ta girgiza kai tana riƙo hannun ƙawarta.
"Fauziyya in ba ki shawara?"
"Ina sauraronki Sopiyya."
Ta faɗa tana kallon Sopiyya.
"Yin maganarki zai sa ka Alhaji Shaheed fito da zancen auren yarinyar nan yanzu idan ma ba shi da niyya. Mu yi shuru mu zuba musu ido zuwa wani lokaci."
Kafin ta ƙarasa da sauri Hajiya Fauziyya ta ce.
"Idan ya kasance haka, ni na san ta ina zan ɓullo masa."
Murmushi Sopiyya ta yi tana faɗin.
"Yawwa kafin nan mun samu mafita ma. Babu wata bayan ke a gidan Alhaji, shi ko duba da rayuwar da aka gudanar a baya ba ya yi."
Tsaki Hajiya Fauziyya ta yi ta girgiza kai.
"Namiji kenan. Ƙaramar yarinyar da idan na ci gaba da haihu zan yi ƴa ta uku da ita."
Sun jima suna jaljaltawa akan wannan lamarin har Hajiya Fauziyya ta ji sauƙin kishin da ya turnuƙeta. Hajiya Fauziyya ta lissafa abubuwa iri-iri da za ta yi idan har Alhaji bai daina zuwa wajen Radiyya ba. Sai yamma lis kafin ta koma gida bayan sun gama tattaunawa da irin hukuncin da za su ɗauka.
Alhaji Shaheed da ya isa Canada ya ƙirata dole ta ɗauka. Da ƙyar ta kawar komai ta amsa masa tana tambayar ya hanya. Ba su jima suna wayar ba ta ce za ta kwanta kanta yana ciwo. Dole ya kashe ya mata sai da safe tare da addu'ar neman sauƙi.
....
Satin Alhaji Shaheed ɗaya ya dawo Nigeria. Bayan sauƙarsa bai nufi gida ba don gudun fitina ko Hajiya Fauziyya ta zargi wani abun kai tsaye gidan su Radiyya ya nufa. Ita kanta ta yi mamakin ganinsa a lokacin. Bayan sun gaisa ya ba ta tsaraba, da ƙyar ta karɓa ya mata sallama zuwa gobe zai dawo.
Bayan barinsa wajen ya nufi gida. Duk ƙoƙarin Hajiya Fauziyya ta nuna masa kulawa ta kasa, har sai da ya lura kamar akwai ɓacin rai tattare da ita. Dole ya tambayeta bayan zamansa wajen cin abinci.
"Lafiya Fauzy? Ko kan naki ne?"
Girgiza kai ta yi tana miƙewa ta bar wajen. Bai ce komai ba ya ci gaba da cin abincinsa. Dare ma ɗaki ta shige ta bar shi kamar ba ita ce take zumuɗi idan ya yi tafiya ya dawo ba. Abin tun bai damesa ba har ya ji ya damu, kuma dama dole ya damu da damuwarta.
Washegarin har ya fita zuwa duba business nasa ba ta sake masa ba kamar kodayaushe. Bayan ya bar wajen business ɗin gidan su Radiyya ya nufa. Fitowarta ya sa ya buɗe motar bayan ta zagayo gefensa. Kallonta ya yi karo na biyu bayan sun gaisa ya ce.
"Radiyyatu!"
"Na'am."
Ta amsa a sanyaye haka kawai ta ji bugun zuciyarta ya ƙaru. Kanta a ƙasa har lokacin da ya fara bayani.
"Radiyya, rufa rufar nan ya isa, ni ba ƙaramin mutum ba ne. Ba na son wannan tsayuwar da muke yi a ƙofar gidanku tsawon watanni, ba mutunci ba ne a gare ni da ke. Ina son iyayenki su san da zamana a wajenki duk da nasan sun san ni waye, kuma mun haɗu da Baba sau ɗaya mun gaisa. Na san ba ki fahimci me nake nufi ba, amma ina da yaƙinin ki na jin abin da nake ji akan ki. Ma'ana ina son aurenki idan har kin amince."
Tamkar sauƙar aradu haka Radiyya ta din ga jin maganganunsa, na ƙarshen yafi tsorata ta, gaba ɗaya ya haddasa mata bugun zuciya. Ba ta taɓa kawo maganar so tsakanin su ba balle aure. Duk tunaninta tausayinta yake don irin rayuwar da take yi ita da halinta, da irin matsin da take ciki ita da ƴan gidan su. Kuma shi ne mutum na farko da ya haskaka mata zuciyarta. Shi yasa take ba shi girma sosai da matsayi babba a ranta.
Alhaji Shaheed ganin Radiyya ta tafi duniyar tunani ya mata magana. Dama yasan hakan zai faru, amma yana sa ran lokaci kaɗan za ta fahimci hakan. Haka ya sa ya ce.
"Ki yi tunani Radiyya, zuwa gobe zan dawo don jin amsata."
Yana faɗin haka ya shiga motar ya kulle ya barta tsaye kamar gunki. Ta kasa kowanne irin tunani, dole ta ja ƙafafunta zuwa gida. Kai tsaye ɗaki ta wuce ta nemi lungu ta zauna tana zuba tagumi. Umma da ta lura da yanayin da ta shiga ɗaki ta miƙe ta bi bayanta. Zama ta yi kusa da ita tana ƙiran sunanta. Radiyya kasa amsawa ta yi sai kallon Umma da ta yi da ido.
"Me ya faru ne? Alhaji Shaheed ne ya zo?"
Ta tambayeta ganin yanayinta ya canza. Sanin Umma da kowa idan har ta fita a gidan to shi ne ya zo ya sa ta ɗaga kanta a hankali. Har lokacin ta ka sa magana.
"To me ya faru? Ki sanar min. Idan ba ki sanar min ba wa za ki faɗawa damuwarki Radiyya?"
Sai lokacin Radiyya ta samu bakinta ya buɗe, kamar me tsoron magana ta ce.
"Umma aure na yake son yi..."
Abin mamaki fara'a Radiyya ta gani ya bayyana saman fuskar Umma. Baki buɗe Radiyya ta bita da kallo. Umma cikin farin cikin da ta ji ya ratsa ranta ta ce.
"To sai me Radiyya. Me abin damuwa? Da ma ba soyayya ku ke ba."
Girgiza kai Radiyya ta yi idanuwanta na cika da hawaye.
"Umma ni babu komai tsakaninmu. Yana kyautata mini saboda halin da nake ciki, sai kuma yana son zoɓo. Ni ba zan iya aurensa ba."
"Me ya sa?"
Umma ta faɗa tana haɗa rai fara'ar fuskarta ya fara gushewa.
Radiyya hawayen da ya zubo mata ta share tana faɗin.
"Umma babban mutum ne fa. Kuma wallahi na san ba zai rasa mata ɗaya ko biyu ba."
"Matan a kan su za ki zauna? Ko kuwa shi babban mutum ɗin ba a aurensa don kina ƙarama? Wa ye zai faɗa babba ne idan ba faɗa aka yi ba. Kuɗi da jin daɗin rayuwa ya mayar da shi yaro." numfashi Ummu ta sauƙe tana cigaba da maganarta,"Radiyya ki godewa Allah da ya aiko miki shi lokacin da ki ke tsananin buƙatar taimako. Ya nuna yana son ki zai aureki. Kin ga idan kin auresa kin huta na huta, sannan shi kan sa Babanku ya huta. Ki rufa mana asiri ki amince da aurensa Radiyya."
Kai da gwuiwa Radiyya ta haɗa tana fashewa da kuka. Duk girma da matsayin da take ba Alhaji Shaheed, da kulawa da kyautatawar da ya mata ji ta yi ba za ta iya karɓan buƙatarsa ba. A zuciyarta ji take idan ta amincen wani abin zai faru. Gani take zai aureta ne don buƙatarsa kawai don ya ga tana buƙatar taimako.
#vote
#comment
#keeplove
DUHUN ZUCIYA
Babi Na Sha Biyar
Pharty BB
Wattpad PhartyBB
Last free page.
"Hakan shi ne dai-dai!"
Ya faɗa a fili yayinda yake kwance saman doguwar kujeran ɗakinsa. Tun barinsa gurin Radiyya abin da ya faru yake masa yawo. A nasa ra'ayin hukuncin da ya yanke musu shi ne daidai gaba ɗayan su. Addu'arsa Allah ya sa ta amince, balle ma ya san tana jin abin da yake ji.
A haife yana ganin zai haifeta har ya yi ƴa ta uku da ita. Sai dai kuma shi ma ba daga garesa ba ne, daga zuciyarsa ne Allah ya ɗaura masa ƙaunarta cikin lokaci ƙanƙani. Bai taɓasawa a rai ba cewa zamani zai yi kwatance da shi ba, auren ƙananan yara da manya maza suke yi yanzu.
...
Radiyya daren ranar ta kasa barci sai juyi take, duk yadda ta so runtsawa idanuwanta Alhaji Shaheed yake gani yayinda yake faɗa mata waɗannan maganganun. Bayan haka takanas yau Uncle Nasir ya zo don su gaisa, ta san duk neman hanyar ace ta koma ne. Sai dai babu wanda ya mata maganar, haka ya sa ta ji sanyi. Gefe ɗaya kuma Umma ta hanata faɗar nata ra'ayin, burinta ta amince masa ko ya ya ne. Shi ɗin babu abin bincike akan sa domin kowa ya san shi, lokaci ɗaya Allah ya azurtasa da arziƙi ya zamto sunansa ya zaga gari.
Gabanin asuba barci ya kwasheta. Umma sai da ta idar da sallah sannan ta tashi Radiyya. Da ƙyar ta miƙe ta fita ta ɗaura alwala ta dawo ta tayar da kabbara ta hau yin sallah. Ta jima tana addu'a da neman zaɓin Allah kafin ta shafa.
"Ki je Baba yana ƙiranki."
Umma da ta leƙo kanta ɗakin ta faɗawa Radiyya. To ta ce ta miƙe ta fita. A ƙofar ɗakin ta yi sallama ya ba ta izinin shiga. Gefe ta samu ta zauna tana gaishesa ya amsa, daga nan ya ci gaba da faɗin.
"Na ji bayani daga wajen Umman ku Radiyya, ta sanar da ni komai, sai dai ta sanar da ni kin fara kawo wasu maganganu. Me ya sa za ki guji ni'imar da Allah ya miki Radiyya?"
Radiyya da jikinta ya yi mugun sanyi ta girgiza kai, ta kasa cewa komai. Haka ya sa Baba ci gaba da maganarsa.
"Shi bai ji nauyin sanar miki da kudurinsa ba, sai ke za ki ce ba kya so. Ko da ma ba soyayya tsakanin ku?"
Da sauri Radiyya ta ɗaga kai tana kai hannu ta share hawayenta. Baba ji ya yi jikinsa ya yi sanyi ganin hawayenta.
"Ki dai na kuka Radiyya, Allah ne ya zaɓa miki shi. Ba ki ga irin rayuwar da ake a gidan ba, ba dan zuwansa ba da yanzu abinci ma sai ya fara gagararmu na kullum. Ki godewa Allah ki karɓi zabinsa hannu biyu. Ki huta muma mu huta."
Hawayen idanuwanta bai tsaya ba da ƙyar ta gyaɗa kai murya yana rawa ta ce.
"Na amince Baba."
"Yawwa Allah ya miki albarka. Idan ya zo yau ki sanar masa kin amince, sannan ina nemansa."
Kai ta ɗaga tana miƙewa ta fita, ɗaki ta shiga ta kwanta jin tamkar zazzaɓi yana neman rufeta. Hawayenta bai tsaya ba har lokacin. Idan aka ce za ta yi aure kwana kusa ba za ta yarda ba. Bayan haka auren ma da wanda ya haifeta, babban mutum. Amincewa da aurenshi shi ne kufcewarta ga Uncle Nasir, kuma ba ta da tsayayyen saurayi. Tunanin haka ya sa ta amince.
Haka ranar ta wuni sukuku babu walwala tare da ita. Har Amrah sai da ta tambayeta lafiya ta sanar da ita lafiya ƙalau. Ranar kayan sana'arta kaɗan ta yi don ba ta da ƙarfin yin aiki sosai.
Tun da azahar ya yi bugun zuciyarta ya ƙaru dalilin zuwan Alhaji Shaheed don jin amsarta. Ji take tamkar ta ce ta fasa ta ci gaba da tserar da mutuncinta da kula da sana'arta. Amma ya ta iya? Ta riga ta sadaƙar za ta amince ko don iyayenta.
...
Yau kai tsaye wajenta ya nufa bai nufi wajen business nasa ba, kwana ya yi yana tunanin irin amsar da za ta ba shi. Shi ma ɓangarensa da ƙoƙonto ya kwana. Baya fargaban sanar da Hajiya Fauziyya kamar zai ji rashin daɗi idan Radiyya ta sanar da shi a'a. Haka ya ƙarasa gidan su zuciyarsa yana bugawa.
Bayan tsayuwarsa ya laliɓo wayarsa ya ƙirata. Ba ta ɗauka ba sai da ya sake ƙira ya ji ta ɗauka tana masa sallama a hankali. Sanar mata ya yi yana ƙofar gidan kafin ya kashe.
...
Kamar kullum hijabinta babba ta saka, babu wani kwalliya a fuskarta ko jikinta kamar kodayaushe haka ta fita. Da ƙyar ta ja ƙafafunta har ta isa wajen daidai inda take tsayawa kullum. Murfin motar a buɗe ya sauko da ƙafafunsa.
Cikin daƙiƙa biyu ta ƙarewa shigarsa kallo. Sanye yake cikin shadda yau ruwan kasa, hannunsa ɗaure da agogo, saman kansa da hula. Ya yi kyau shigar ya fito da dattakunsa. Shigar ƙananan kaya yafi fito masa da yarinta sosai.
Shurun da ya ji daga ɓangaren Radiyya ya sa ya ji zuciyarsa ya buga ya kalleta. Kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.
"Radiyya!"
Ya ƙira sunanta yana ci gaba da kallonta. Wannan nutsuwar nata shi yake ƙara burgeshi a kanta. A hankali ta amsa tana gaishesa. Amsawa ya yi yana ƙara faɗin.
"Yau kuma babu magana? Ko dai akan maganar jiya ne?"
Girgiza kai ta yi da sauri hawayen da ya taru a idanuwanta ba ta bari ya zubo ba, cikin muryar da ya fallasa rauninta ta ce.
"Na amince. Allah ya sa haka shi ne alherin mu."
"Da gaske Radiyya!"
Ya faɗa cikin mamaki da ya bayyana a fuskarsa. Kai ta ɗaga. Numfashi ya sauƙe yana faɗin.
"Allahamdulillahi! ni kuma za ki same ni masoyin gaskiya. Iyayenki sun yarda na zo?"
Nan ma kai ta ɗaga tana faɗin.
"Baba yana son magana da kai."
Cikin farin ciki ya ce.
"MashaAllah! Kin ga ikon Allah ko? Zuwa yaushe Baba yake gida?"
"Da safe ko dare."
Ta sanar masa jikinta duk ya yi sanyi.
"Gobe zan zo da dare mu yi magana, ki sanar masa."
To ta amsa da shi ganin tsayuwar su ya jima ta ce.
"Zan shiga gida."
"Babu zoɓo yau?"
Kai ta ɗaga tsaf ta manta ba ta fito da shi ba.
"Bari in kawo."
"Ki bari kawai Radiyyatu."
Kai ta ɗago ta kalleshi jin abin da ya faɗa. Gira ya ɗaga mata da sauri ta ɗauke kanta. Daga nan ta masa sallama ta wuce gida.
Tana shiga cikin gidan ta wuce ɗaki kai tsaye, guri ta samu ta zauna. Kukan da take dannewa ta fara. Ji take tamkar ba ta yi wa rayuwarta adalci ba.
...
Alhaji Shaheed da farin ciki ya koma gida. Hatta Hajiya Fauziyya da take masa fushi fushi sai da ta sauƙe gefe ta tambayesa.
Murmushi ya yi yana dubanta lokacin da suke zaune a falo.
"Alheri ne Fauzy. Ki taya ni addu'a."
"Ba za a faɗa mini ba?"
Ta tambaya tana gyara zamanta jin alheri zai samu mijinta. Kuma idan ya faɗi haka to tasan na kuɗi ne.
Murmushi ya faɗaɗa ya ce.
"Zan sanar da ke gobe ko zuwa jibi. Sai komai ya yi tukunna."
"To Allah ya nuna mana."
Ta amsa da ɗan fara'a.
...
Washegari Radiyya da asuba ta sanar da Umma yadda suka yi da Alhaji Shaheed. Daga nan ita kuma ta sanar da Baba. Hukunci da suka yanke suka sanar da Radiyya akan ya zo da dare. Hakan ya sa a ranar da ya zo ta sanar masa.
Ƙarfe takwas na dare Alhaji Shaheed ya zo, har soro aka masa jagoranci, rana na farko da ya taka ƙafarsa zuwa gidan. Bayan gaisuwa Alhaji Shaheed ya gabatar da kudurinsa akan Radiyya.
Bayan Baba ya gama sauraron bayaninsa sannan ya ce.
"Idan dai Radiyya ce na ba ka, ka ci gaba da shiri. Ka turo manya mu yi magana a gama komai."
"Ina godiya sosai."
Faɗin Alhaji Shaheed ya ciro damin kuɗi a aljihunsa ya ajiye masa.
"Baba ga wannan."
Cikin fara'a Baba ya kalli kuɗin ya ce.
"Har da wahala haka?"
"Babu komai ni ne da godiya."
Ya faɗa ya miƙe don tafiya, nan ya masa sallama ya fita. Bayan fitarsa Baba ya jawo kuɗin, ko kirgawa bai yi ba ya zura a aljihunsa ya miƙe ya bar soron.
....
Tun lokacin tsawon sati ɗaya Alhaji Shaheed ya ci gaba da cusawa Radiyya soyyayarsa a ranta, kullum sai ya zo da yamma ko dare. Radiyya tana ƙoƙarin ganin ta sa yarda a ranta ta saki rai sun yi hira. Umma da Baba sun fi kowa murna.
Ɓangaren Hajiya Fauziyya kullum suna waya da Sopiyya don tattaunawa. Hakurin Hajiya Fauziyya ya ƙare. Duk da tana ganin kamar Alhaji Shaheed ya bi maganarta, amma hakan bai hana kokonta a ranta ba cewa yana zuwa wajen Radiyya.
Yau safiyar Alhamis an yi sanyi saboda yanayi na sanyi ya fara shiga. Garin ya yi daɗin barci don ni'imar da ya sauƙa. Wanda ba shi da aikin yi duk yana cikin ɗaki yana barci, hakan ya kasancewa Alhaji Shaheed da Hajiya Fauziyya. Da ma ba farkawar wuri suke ba yau kuma ya kasance garin ya sake yin daɗi.
Sai ƙarfe sha biyu saura suka farka, shi ma Alhaji Shaheed ne ya farka sannan ya tasheta. Dole ta miƙe ganin rana ya yi. Wanka suka yi kowanne su ya shirya cikin kwalliya kafin su sauko ƙasa don yin breakfast. Mai akin su ta gama jera musu komai tun ƙarfe goma da wani abu.
Kai tsaye nan suka nufa tare. Hajiya Fauziyya ba ta zauna ba ta hau zuba musu. Bayan ta gama ta zauna suka hau ci, babu wanda ya yi wa juna magana. Ganin shurun ya yi yawa ya katse ta hanyar faɗin.
"Fauzy akwai maganar da za mu yi idan mun gama. Ko kin tuna na taɓa sanar miki akwai wani abin alherin da nake sa ran samu."
Sai lokacin ta kalleshi tana sakin fuska jin abin da ya faɗa, da fara'a ta ce.
"Haka ne mun yi maganar, ka ce za ka sanar da ni."
"Eh mu gama tukunna."
Cokalin hannunta ta ajiye ta ɗauki cup ta tsiyaya ruwa ta kora, ajiye cup ɗin ta yi ta ce.
"Na gama."
Ta san idan ya samu wani alherin ita ma za ta samu nata kason.
Murmushi ya yi ya ci gaba da cin abincinsa. Sai da ya gama ya ɗauki cup din black tea ya hau sha, rabi ya sha ya ajiye ya miƙe tsaye.
"Mu je sama."
Da murna ta miƙe ta bi bayansa har zuwa ɗakinsa. Bakin gado ya zauna hakan ya sa ta zauna kusa da shi. A nutse ya dubeta sannan ya fara magana.
"Fauzy kin san dai ina sonki ko? Tun ban kai haka ba muke tare, kuma don na zama wani abu bazan wulaƙantaki ba ko daina sonki."
"Haka ne."
Ta faɗa zuciyarta na hasaso mata abubuwa iri-iri. Ba ta kawo abin da zai faɗa ba ta ji ya ci gaba da cewa.
"Ina son ƙara aure Fauzy, zan auri Radiyya. Don har na yi magana da iyayenta, nawa iyayen zan tura ayi maganar aure."
"Aure dai! Auren ma da wannan karuwar yarinyar!!"
Ta ce tana buɗe idanuwanta don tabbatar da gaskiyar maganar da ya ke faɗa. Ga ni ta yi ya ɗaga mata kai. Hakan ya haddasa mata fasa ihu ta ɗaura hannu a kai. Da sauri ya rikota ganin ta rikice, dama yasan hakan zai iya faruwa don kishin Hajiya Fauziyya.
"Ki nutsu Fauzy! Ba don na tozartaki ba ko bana sonki zan yi wani auren ba. Ji nake kamar da rabona a tare da ita."
"Shi ɗin fa? Ko shi ba ɗanka ba ne?"
"Sanin kan ki ne babu wannan tsakaninmu."
Ya faɗa fara'ar fuskarsa yana ɗaukewa.
Jikinta ta fizge daga riƙon da ya mata ta miƙe, da yatsarta da yake karkarwa cike da masifa ta nunasa.
"Ka sani idan ina raye babu kai babu auren wannan yarinyar. Kai babu kai babu auren kowacce irin mace ma, balle har na yi zaman kishi da ƙaramar yarinya. Alƙawari na maka Shaheed."
Tana faɗar haka ta fice a ɗakin tare da banko masa ƙofar. Bai yi mamakinta ba don ya santa da kishi, kuma yasan nan da ayi auren ne za ta haƙura kamar kowace mace. Miƙewa ya yi ya nufi gaban wardrobe nasa. Mukullin mota ya ɗauka ya fito don yin magana da manyansa, maganganun Hajiya Fauziyya ba zai sa ya fasa niyarsa ba.
A ranar ya sanar da ƙanin mahaifinsa da babban abokinsa Kabir. Bayan sun yanke lokaci da rana suka bar maganar ya sanar da Radiyya ranar zuwan su, ita kuma ta sanar a gida. Daga nan ya musu sallama ya nufi gidan su Radiyya. Bayan ya ƙirata ta fito ta masa jagoranci zuwa soron gidan su. Sallaya ta shimfiɗa masa ta zauna a gefe tana gaishesa. Amsawa ya yi yana faɗin.
"Mun yi magana da Baffana da aboki na. Amma zan yi tafiya nan da kwana biyu, ba zan kai kwana uku ba zan dawo. Da zaran na dawo a ranar za su zo a yi magana, ki sanar da Baba yasan da zuwanmu."
Kai ta ɗaga masa ta ce.
"Allah ya kiyaye, Allah ya kaimu lokacin."
"Ameen Radiyyatu."
Ya amsa da shi ya ajiye mata abu a envelope ya miƙe ya mata sallama bayan ya ɗauki zoɓon da ta ajiye masa ya fita. Jiki a sanyaye ta ɗauka ta ɗauki sallayar ta yi cikin gida.
A daren Radiyya ba ta sanar da Umma maganar ba, a ranta ta bari akan idan ya dawo daga tafiyar a ranar ta sanar da ita sai ta faɗawa Baba. Haka kawai ta ji ta kasa faɗa mata.
....
Bayan tafiyar Alhaji Shaheed ƙasar Austaraliya, bayan ya sauka ya huta, abin da bai taɓa yi ba shi ne ƙiran Radiyya da lambar wani ƙasa. Haka yau ya laliɓo lambarta ya ƙira.
Radiyya tana cin abincin rana ta samu ƙiran. Katsewa ta yi ta tashi ta ɗauki wayar, ganin wanene sai da zuciyarta ya buga. Ɗauka ta yi tana sa wa a kunne yayinda ta koma gaban abincinta ta zauna.
Amsawa ya yi yana amsa gaisuwarta. Cikin taushin murya ya ce.
"Radiyya ina ƙaunarki sosai. Tarbiyyarki da nutsuwarki ya sa ni faɗawa kogin sonki, ban yarda da hakan ba sai da na ji na yi kewarki da rashinki. Ina addu'ar Allah ya bani ikon riƙeki, Allah ya sa sauran rabona yana tare da ke."
Shuru Radiyya ta kasa ba shi amsa. Maganganunsa duk sun kashe mata jiki. Sai lokacin tunanin zaman auren da za su gudanar da shi da ita ya fado ranta. Zaman aure da mutumin da ya haifeta. Ba don abubuwan da ta lissafa a baya ba, da tana jin akwai sake a lamarin.
'Anya ina jin na zaɓawa rayuwata abu mai kyau?"
Ta tambayi kanta tana juya lamarin a zuciyarta.
Maganarsa ya dawo da hankalinta in da yake cewa.
"Ba ki ce komai ba Radiyya."
A hankali ta ce.
"Na amsa a zuci. Ina godiya da dukkan kulawa da hidima."
Hira ya din ga janta da shi don yana so ta fara sakewa da shi sosai. Duk ƙoƙarinta kamar kullum kasawa ta yi tana jin nauyi. Kusan minti goma kafin ya rabu da ita ya kashe wayar. Radiyya wayar ta zubawa ido tamkar za ta hango hasken da zai haskaka mata hanya cikin duhun da zuciyarta yake ciki.
Tuwon da ba ta ci kenan ta ɗauka ta fitar waje ta koma ɗakin. Ranar ba abin da yake fito da ita sai sallamar mutane idan sun zo siyar abu. Magriba yana yi ta yi alwala ta shige ɗaki, da ta idar da sallah ta kwanta kamar koyaushe ta fara tunani. Ba ta jima da kwanciya ba ta ji an ɗaga labulen ƙofar. Umma ce tsaye hakan ya sa ta miƙe ta zauna.
"Babanku yana ƙiranki."
Miƙewa Radiyya ta yi ta bi bayan Umma da tana faɗar haka ta juya. Bayan isarta ƙofar ɗakin ta yi sallama Baba ya amsa yana ba ta izinin shiga. Guri ta samu ta zauna bayan shigarta. Ba ita ɗaya ba ce a ɗakin har Umma.
Kuɗi ya ciro a aljhunsa masu ɗan dama ya ajiye a gabanta. Da kallo Radiyya ta bi kuɗin sai dai maganar da ya biyo baya ya kusa fasa zuciyarta don tsoro.
"Sadakin aurenki ne kamar yadda ku ka roƙi alfarma a ɗaura auren. Wanda ki ka turo ya zo wajena ɗazu da mutanensa, daga tambaya ya nemi a ɗaura aure, kuma an ɗaura ga sadakinki da kuɗin sauran abubuwa. Za ki tare nan da sati uku."
...
#Keeplove
#comment
#vote