BABI NA BIYU
“TARIHIN FATIMA IBRAHIM WACCE TA KASHE XAN MIJINTA NASIR” hakan aka rubuta da manyan baqi a farkon saqon, na xan tsagaita ina kallon fuskokinsu cikin nazari xaya bayan xaya, kowacce a zaqe take da son jin cigaban saqon, don haka na xora daga inda na tsaya.
“Marainiya ce gaba da baya, iyayanta Allah ya xauki rayuwar su tun tana ‘yar shekaru uku a duniya, hatsarin mota sukai a hanyar su ta dawowa da ga Abuja zuwa Kaduna marigayi Alhaji Ibrahim mahaifin Fatima shahararren mai arziqi ne. Fatima ita kaxai ce xiyar shi a duniya, mahaifiyar Fatima ‘yar Zindar ce a jamhuriyar Nijar, yawon kasuwanci ya kai mahaifinta can qasar har Allah ya haxa fuskokin su sannan ya sanya soyayya mai tsanani a tsakanin su har sukai aure, bayan kai ruwa ranar da akai da mahaifin Aisha (Kakannin Fatima na wajen Uwa) kan cewa ‘yarsu baza ta yi aure a wata qasa ba.
Lokacin da kakannin Fatima na wajen Uwa su ka samu labarin rasuwar ‘Yar su da mijinta sunyi kuka sosai, kuma sunzo har akai bakwai sun buqaci tafiya da Fatima amma Alhaji Musa qanin mahaifinta yace, sam! Hakan bazai tava yuwuwa ba.
Sunyi rabuwar dutse da hannun riga wanda hakan ya yi matuqar tunzura su har suka sha alwashin yanda su ka rasa ‘yarsu Aisha mahaifiyar Fatima suka haqura itama Fatima sun haqura da ita har abada, indai ita jinin su ce zata neme su amma su kam baza su tava nemanta ba har gaban abada idan akwai.
Bayan komai ya lafa riqon ta ya koma hannun qanin mahaifinta ya zama mahaifin ta kuma mahaifin dukiyar ta. Babu wata rayuwa ta jin daxi da Fati za ta karar wanda tayi a gidan qanin mahaifin nata.
makarantar gwamnati ya sanya ta savanin ‘ya’yan shi da suke makarantar kuxi, duk waxanda ya kamata su tsawatar mishi ya gama siyesu daman kuma mahaifansu (Kakan nin Fatima na wajen Uba tun ta na ‘yar jaririya suka rasu) Da daxi ba daxi har ta kammala Secondary School inda ta fito da sakamako mai matuqar kyau, babban burinta ta ci gaba da karatu amma sam Alhaji Musa yaqi bata damar hakan, amma ‘ya’yan shi da mazan da matan duk babu wanda yake karatu a qasar nan.
Alhaji Muhammad aminin kawunta ne don duk wani qulle qulle na kawun nata Alhaji Muhammad ya sani, tun tana aji uku a Secondary School yake damunta da maganar soyayya, nauyin shi ta ke ji sosai dan ta xauke shiu tamkar qanin mahaifinta, batare da saurarar amincewa ko ra’ayinta ba. Alhaji Musa ya xaura mata aure da Alhaji Muhammad.
Hannu bibbyu tasa ta rungume shi duk da ba ta son shi ko kaxan, gidanta da ban da na uwar gidan shi kuma uwar yaranshi, ya na nuna mata kulawa dai – dai gwargwado saboda ya na sonta, kuma tana daga cikin jerin matan Allah ya kyautata surar jikin su, da na fuskar su.
qarin armashin kuma shi ne yarinya ce qarama dan ita sa’ar xan autan shi ce, ita da Hajiya Kumatu uwar gidan shi suna zaman amana dan kuwa ba ko da yaushe suke ganin juna ba.
Idan bada wani qwaqwqwaran dalili ba sukan dauki tsawon lokaci ba su haxu ba.
Ba su fara samun matsala ba sai da Xan Alhajin mai suna Nasir ya dawo gida daga inda ya ke karatu acan qasar Malesia, tunda suka je air port da niyyar xauko shi ita da Alhaji da Hajiya ta lura da irin kallon da yake binta da shi, Nasir bunsuru ne gurin bin mata tun kafin ya tafi karatu qasar Malesia da ya je can kuma sai idonshi ya qara buxewa duk yarinyar da ya qyalla ido a kanta sai ya bi duk hanyar da yasan zai samu biyan buqatar shi.
Tun yana can ya ji labarin Dadyn shi ya yi aure amma bai tava tunanin daqwalwa irin wannan ya aura ba, ganin farko da ya yi mata gabanshi ya yanke ya faxi daqyar yayi qarfin halin daidaita nutsuwarshi don karya bada kanshi a gaban iyayan shi.
Suna tafe a mota zuciyar shi tana saqa mishi hanyar da zai bi dan cimma mummunan manufarshi a kanta, a zuciyar ta take ta addu’a Allah ya daidaita zaman su dashi dan sam bata fahimci wane irin kallo yake yi mata ba, a zaton ta kallon tsana ne da tunani yana taya mahaifiyar shi kishi ne, a minti biyar ya mantar da ita wannan tunani ta hanyar fara janta da hira yana kiran ta “Aunty Fati” duk iyayan ransu cike yake da farin cikin dawowar xan nasu dan haka sam hankalin su ba shi a kan Fatima, idan ya tsomata a hirar shi a xarare ta ke amsawa muryarta a sanyaye.
Hakan ba qaramin burgeshi yake ba, shauqin sha’awarta yayi ta xibar shi, har su ka isa gida, ba ta bar babban gidanshi ba zuwa gidanta sai bayan magariba gab da isha’I da yake Alhajin a gidan yake da kwana sai ya haxa ta da Driver ya kai ta gida da sauri Nasir ya miqe ya na kallon iyayan shi fuska a sake ya ce, “Ba ri in raka aunty Fati gida sai mu dawo ta re da Drivern”
jikinta sanyi qalau ta ke kallon shi don rashin ga ne manufar wannan cusa kai da ya ke mata. Izinin tafiyar daya samu daga gurinsu ya hanata tankwavar da shisshigin shi , sai ta qara yi musu sallama ta nufi harabar gidan.
Dukkansu suna zaune a bayan motar ba mai cewa wani uffan, amma idon shi ya na kanta tamkar zai cinyeta xanye, ba qaramin takurata yayi da idanun shi ba don haka ta takure acan jikin motar, a zuciyarta ta ke addu’ar Allah yasa su isa gidanta lafiya ko zata samu sa’ida da ga mayataccen kallon da yake bin ta da shi.
Suna isa ta dakatar da Driven a qofar gida, ta valle murfin motar ta fita sannan ta leqa kanta ta saqon glashi ta ce, “Nasir Allah ya huta gajiyan tafiya mu kwana lafiya” ta qarasa da sauri ta ciro key a jaka ta na buxe get xin gidan ba taga fitowar shi daga mota ba balle lokacin da ya nufota kawai muryarshi ta ji a kusa da ita ya na faxin “Haba aunty na rowar ruwan gidan ki za ki yimin?”
a firgice ta sa ki key xin ya faxi qasa muryar ta na rawa ta ce, “Ba… ba… ba haka ba ne, na… naga su Alhaji suna can suna jiranka ne.” bai ce komai ba ya ya tsuguna ya xauki makullin ya buxe get xin ya shige ciki ya bar ta nan a tsaye. Ganin da ta yi ba sarki sai Allah ga idanun Driver tun xazu ya na kanta ya sa ta yi shahadar bin bayan shi, har ya samu nasarar buxe qofar falonta ya shige ciki don haka ta haxa da sassarfa zuwa cikin falon.
Yana kwance akan kujera mazaunin mutum uku idanun shi alumshe, jakarta ta aje akan kushin ta nufi kiching ta jero mishi lemuka da ruwa ma su matuqar sanyi a cikin faranti ta xora Cofi guda biyu ta kawo mishi.
A zaune ta tarar da shi hannun shi riqe da remot xin T.V ya na canza tashoshi, a gefe xaya ta aje ta xauko xan qaramin table ta xora sannan ta kalle shi ta saki fuskarta ta ce “Bisimillah.” Maqe ka faxar shi ya yi tamkar wani qaramin yaro sannan ya fara kashe ma ta ido irinna gogaggun ‘yan duniya. Muryar ta da mamaki ta ce
“Me ya sa? Bayan ruwa ka buqaci sha”
“Ni ba irin wannan ruwan nake so ba”
Ya faxa yana tura baki, ya fara kwarkwance mata tunanin ta don kuwa ya girme mata nesa ba ku sa ba, a qalla zai girmeta da shekaru goma sha huxu, wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi. Sam bata fahimci inda ya dosa ba don haka ta ce,
“dare yana qara yi fa kar su Hajiya su ji shirun ya yi yawa"
“Bikin Magaji ya na hana na Magajiya ne?" ya jefa mata tambayar yana qara qura mata ido. Kallo kawai ta bishi dashi ba tareda ta amsa mishi ba. Tashi ya yi ya matso dab da ita sannan ya ce,
“Gaskiya Fatima bazan voye miki ba sam baki dace da irin su Dady ba, da irin mu ki ka dace, kina da kyau matuqa, kina da dirin da duk wata qasaitacciyar mace za ta so ta mallaki irinshi, ganin farko da nai miki sha’awarki ta mamaye zuciya ta “Ina sonki” zanso ace kin rabu da mahaifina ki dawo gareni, idan kuma hakan bazai samu ba to gaskiya sai dai mu raba shi daidai da Daddy, don wallahi tunda na xora qwayar idanuna a kanki to tabbas sai na biya buqatata.
Gobe Daddy zai dawo gidan nan donhaka kwana biyu na baki ki yanke hukunci a ranar da Daddy ya koma gidan Momy zanzo danjin shawarar da kika yanke”
ba tare da ya qara kallota ya fice da ga falon.
Tofa! In ka ji qi gudu sa gudu ne bai zo ba, tsawon minti arba’in batasan a wace duniyar ta ke ciki ba dawowa hayyacinta ta yi ta ganta zaune dirshan a kan kafet xin da ya malale tsakiyar falon. A ranar idan ta ce tayi barci to tabbas ta yi qarya, duk qwarewar sarkin varayin gurin satar mutane a ranar bai yi nasarar satarta ba, daga qarshe ta xauro Alwala ta fara jera nafilfili tana kai kukanta da Ubangijin talikai.
Har Alhaji Muhammad ya bar gidan ta rasa mafitar da tafi dacewa a tsakanin zavin da Nasir ya bata, Alhajin da kanshi ya fahimci bata cikin walwala kuma ya tambaye ta amma ta kasa sanar dashi gaskiyar abinda yake damunta.
Tun qarfe shida da yamma ta kulle get xin gidan da qofar falonta, a tsammaninta ta kuvuta daga zuwan Nasir, don ko yazo zai koma tunda gidan yana rufe ne. fitowarta kenan daga wanka misalin qarfe takwas da rabi na dare, taji kamar hayaniyar T.V take jiyowa daga falonta, don haka ta xora hijabi akan towel xin da take xaure dashi ta fito zuwa falon. Yana hakimce akan kujeara yana karkaxa makullin motar mahaifinshi wanda ya ke haxe dana qofar get xin gidanta dana qofar falonta, hakan shi ya ba ta tabbacin inda ya samu makullin cak ta tsaya tana kallonshi ta kasa furta ko kalma xaya. “Babyna…” shiya katse mata tunanin da take yana mata kallon qurilla tamkar zai cinyeta.
“Me ya kawo ka gidannan?”
Ba tambayeshi fuskarta ba walwala ko kaxan, saida ya xan ja fasali kamar bazai yi magana ba sannnan ya ce,
"Amsar buqatata nazo ji”
“Ni ba irin ‘yan iskan matan daka saba hulxa da su bane, ka je can ka samu dai dai dakai ni matar mahaifinkace ko mun rabu dashi aure ya haramta a tsakaninmu kuma ba zan tava yin zina da aure na ba, don haka karka qara zuwa min da zancen banza.”
Ta fadi hakan muryanta cike da masifa, idanunta a kankance.
“Kin manta abinda na faxa miki rannan koh? To wallahi bazan tava haqura dake ba, ko da tsiya ko da arziqi sai na cimma burina a kanki kinsan irin azabtarwar da nayi a kwana biyun nan kuwa? To wallahi sai kin haxa jikinki da nawa a gobe goben nan.”
Ya fadi haka cikin nuna rashin damuwa da masifa da take mishi.
“Qarya kake Nasir Allah bazai tava barinka ka cimma qazantacciyar manufarka a kaina ba, kuma idan baka janye wannan maganar ba zan kira mahaifinka in sanar da shi duk abinda kace.”
“Wannan shine babban kuskuren da zaki tabka a rayuwar ki kin manta irin son da iyayena suke min ne? ko kin faxa musu wallahi bazasu tava yarda ba, a qarshe sai dai ma ki janyowa kanki wani bala’in don zan tabbatar musu da cewar tunda na dawo qasar nan kike bibiyata, don naqi amincewa buqatarki ne kikai niyyar shiga tsakanina dasu.”
Ya qara matsawa dab da ita, ita kuwa ta fara ja da baya har sai da ta qure da jikin bango yana kusantar ta. Hannu biyu yasa ya dafa bango ya tare ta a tsakiya, fuskarshi ya matsar dab da ta ta sannan yace, “Kinsan kuma tsab zasu yarda da abinda nace, don ana canza mata amma ba’a canza da, kiyi tunani ki samu nutsuwar yau gobe zan dawo in kashe qishirwata.”
Daga haka bai qara furta komai ba ya fice ya barta tsaye a gurin kamar mutum-mutumi.
yau kam kasa yin sallar ta yi kawai sai ta rushe da kuka mai tsananin qarfi tsawon awa biyu tana kuka wa wannan mummunan al'amari da ke tunkarar ta, daga qarshe sarkin varayi ya yi awon gaba da ita a tsakar falon.
Washe gari ba abinda ta iya hassalawa a gidan jikinta sanyi qalau tana kwance akan kujera tana jan carbi, lokaci zuwa lokaci gabanta yana faxuwa tanajan “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un” har Alhaji ya shigo ya dubata kamar yadda ya saba idan ba’a gidan ya kwana ba.
“Bana jin daxi ne” amsar da ta bashi kenan lokacin daya matsa da tambayar abinda ke damunta.
“Zan turo Nasir ya kaiki asibiti” ya faxi hakan yana ficewa da sassarfa don karya makara zuwa Office.
Ganin zaman bazayyi mata ba yasa ta miqe ta nufi banxaki da niyyar watsa ruwa ko zata ji qarfin jikinta. Heater bayinta ya lalace kuma ta manta ba sanar da Alhaji ba don haka ta ciko bokiti da ruwa ta jona a jikin soket abayan kujera a falon, tana zama Nasir ya shigo ba tare da sallama ba, kallonshi tayi sama da qasa yana sanye da qananan kaya jeans da T.shet.
“Oh My God! Babyna wai baki da lafiya inji Daddy?” ya faxi hakan yana kusantar ta nufinshi don jin yanayin jikinta.
“Dakata Nasir, karka kuskura ka matso kusa dani.” Ta yi mishi gargaxin hakan muryarta tangaran babu alamar rashin lafiya a tare da ita cak ya tsaya tamkar an riqe shi, shi bai qarasa kusa da ita ba kuma bai koma baya ba.
“Kina tunanin akwai abinda zai hanani biyan buqata ta dake a yanzu?”
“Qwarai kuwa” ta faxa muryarta babu alamun tsoro ko kaxan.
“Meye shi?” ya tambaya da tsananin mamaki a fuskarshi.
“Allah bazai baka nasara a kaina ba.”
Dariya ya qyalqyale da shi tamkar sabon hauka sannan ya qara kusantar ta da niyyar haxa jikinta da nashi ko ta halin qaqa.
“Dakata” ta sake bashi umarnin haka a karo na biyu lokacin baifi saura taku biyu ya isa gareta ba, bayyi niyyar tsayawa ba amma ga mamakinshi sai ya tsaya.
“Bani minti biyar inyi wanka…” ta faxa sannan ta rava ta gefenshi ta wuce zuwa bayan kujera inda ta jona heater.
“Fatima shure shure ba ya hana mutuwa duk abinda zakiyi yau sai na biya buqata ta a kanki, don haka jeki dawo ina jiranki” yana gama faxin haka ya zauna akan kujerar da ta tashi yana qyalqyala dariya.
Idanun shi kaxai ta kalla ya tabbatar mata da cewa tabbas yau da gaske yake don haka gara ta nemi mafitar qarshe tun kafin wankin hula ya kaita dare, ruwan yana tafarfasa don ya haura minti talatin da jonawa, tana xaukar ruwan a bayan kujerar da yake zaune ta xaga bokotin ta sheqa mishi tun daga tsakiyar kanshi ba tare da ya ankara ba.
Raxaxin da ya ji tun da ga tsakiya kanshi zuwa sassan jikinsa yasa ya qwallah gifitaccen qara saboda azaba, second goma tsakani ya sume akan kujerar sai a lokacin ta ji dana sani mai tsanani ya mamaye zuciyarta jikinta ba inda ba ya rawa saboda tsabar tsoro.
Tsawon minti biyar ta rasa waqar farawa sai kuka take tana safa da marwa a tsakiyar falon, daga qarshe ta yanke shawarar kiran number wayar Alhajin, kuka kawai take a wayar tana faxin Alhaji Nasir ne…..”
“Me ya faru da Nasir din…..?” Ya tambaye ta hankalinshi a tashe.
Ta kasa furta komai bayan sai kuka daga bisani ta jefar da wayar ta ruga cikin xaki ta kulle kanta.
Duk inda aka tava a jikinshi savewa yake yi, gaba xaya likitocin sun taru akanshi don qoqarin ceto rayuwarshi.
Alhaji Muhammad yana jikin qofar hankalinshi a matuqar tashe, Nasir kawai ya samu a sume akan kushin duk jikinshi a jiqe da ruwa ba Fatima a gidan ba alamar ta, sai da ya kama hannun Nasir yaga ya saluve fatarshi sannan hankalishi ya qara mummunan tashi da taimakon Allah dana Drivern da ya kawo shi daga Office suka kama Nasir duk jikinshi a qone zuwa asibiti tswon minti talatin kenan likitoci suna cikin xakin da aka kaishi amma har yanzu ba wanda ya fito.
“Kaine mahaifinshi ko?” wani siririn likita daya fito daga xakin ya katsewa Alhaji Muhammad tunanin da yake yi. “Qwarai kuwa" ya amsa yana gyaxa kai don qara tabbatar da abinda ya faxa.
“Biyoni ciki don tunda ya farfaxo yake roqon a kira mishi Daddy”
Duniya ba komai ba ce, duk wanda bai ji tsoron Allah ba ya shiga uku cikin lokacin da bai wuce awa xaya ba Ubangiji ya canzawa Nasir halittan jikinshi yana kwance tamkar gawa. Daqyar ya yi qarfin halin faxawa mahaifinshi cewa:-
"Fatima … Fati ce … tamin haka!!! Saboda… saboda …” Allah bai bashi ikon qara faxin koda kalma guda ba bayan haka Mala’ikan zare rai ya zare mishi ranshi.
Cikin kuka Daddy ya ke xaukarwa kanshi alqawarin ko zai yi yawo tsirara sayya xaukar mishi fansa, bai iya haqurin ankai Nasir ma kwancinsa na gaskiya ba sai da ya danqa Fatima a hannun ‘yan sanda. Bayan angama addu’ar bakwai aka turasu kotu, Alhaji Musa qanin mahaifinta ya bita har gidan Prison ya yi mata “Allah ya isa rainon da ya yi mata ya qi bata dama kokaxan tayi mishi bayanin yanda abin ya faru, kuma ya qara tabbatar mata da cewa bashi ba ita har abada.
A wannan ranar ne Fatima ta yanke qauna da rayuwar duniya, shi ya sa ko da aka shiga kotu bayan amsa laifinta babu wani qarin bayanin da ta yi har zuwa yau da aka yanke mata hukunci.
***
Na xago idanuna daga kan wayar ina kallon fuskokin ‘yan matan da dukkansu hawaye suke saboda tsananin tausayawa Fatima, Idanuna abushe suke qamas, babu ko alamar hawaye amma zuciyata suya kawai ta ke saboda tsananin takaicin halin maza da mugunta irin tasu.
“Wannan labarin ka xan kenan daga cikin rashin adalci irinna maza, kunga dai A DALILIN XA NAMIJI ta shiga cikin uqubar daya janyo za ta qare rayuwarta a gidan yari, shi yasa a kullum nake qara fada muku maza azzalumai ne! Tsakanin mu da maza ba sani ba sabo, duk wacce takeso rayuwarta yazo qarshe ta qulla dangantaka da Xa namiji, zamu gudanar da kyakykyawar rayuwa ba tare da Namiji ba, kuma ko a gurin Allah ba laifi bane.”
“Qwarai kuwa ‘yar uwa Aysha”
Dukkan su suka haxa baki gurin faxin haka cikin nuna gamsuwa da maganganu na.
Dayar wayar tawa na janyo na buxe saqon da aka turo min daga 7777.
“ZAKU KAI HARI GA GIDAN YARIN DA AKA AJIYE FATIMA”
Abinda aka rubuta kenan da manyan baqi a saman saqon, da qarfi na karanta don sauran ‘yan matan suji abinda ya qunsa.
"Gidan yari ne da ake ajiye mata a hanyar da mutane da suke bi idan zasu je Abuja daga Kaduna, akwai masu gadi da makami a hannunsu su biyu daga qofar get xin gidan yarin, katangar gidan yana da matuqar tsawo ya wuce ace za’a haura ko kuma a dira, koda da tsani ne za’a xauki tsawon lokaci don haka ta get xin zaku shiga bayan kun janye hankalin masu gadin ko da ta hanyar sumar dasu ne. Xakuna ne a jere sama da guda xari cikin gidan, ako wani xaki ana zuba mata su goma sha biyar duk da qanqantar xakin, akwai jami’an tsaro guda goma sha biyar daga gaban xakunan, duk wani shige da fice na masu laifin akan idonsu suke yi, babu wata hanya da zaku iya fitar da Fatima face sai kun fafata da jami’an tsaron, idan kukai amfani da hikima zaku ya xauke hankalinsu har ku cimma burinku. Xaki mai lamba 87 anan aka ajiye Fatima abayan rigar ta an rubuta lamba 268, da farko zata yi muku gardama kan cewa ba zata biyoku ba tunda ba ta san ku ba.
To dukkanku ku juya mata bayan rigar ku taga tambarinku, ku da ita daga yau ta zama ‘yar uwarku, duk matsalarku iri xaya ne A DALILIN XA NAMIJI kuka tsinci kanku a halin da kuke ciki.
zaku fita da misalin qarfe goma sha biyu da rabi na dare, ku lazimci karanta “HAZBUNALLAHU WA NI’AIMAL WAKEEL” don samun nasara kamar yanda ku ka saba."
Iyakar abinda na saqon ya qunsa kenan don haka ban tsaya vata lokaci ba na janyo dayar wayar na buxe saqon da aka turomin a cikinta daga Number 7777.
“GAREKI AYSHA AZZAHRA’U”