Rayuwar Amal

Rayuwar Amal 1&2 Na Aisha Abdullahi Yabo

by @fulani2

Kyakyawar matashiyar yarinya ce da ba za ta haura shekara sha huɗu ba ta shigo cikin gidan tana mai yin sallama cikin sassanyar nuryarta, Umma da take zaune a tsakar gidan nasu da aka kawata da inter lok tana tankaɗe ta amsa sallamar fuskarta a yalwace da murmushi, tana faɗin "Amal kin dawo"?

cikin ladabi ta ce; "eh Umma na dawo, sannu da aiki"

   "yauwa 'yar albarka je ki ajiye littafan kizo kici abinci"

   

   Ta wuce zuwa ɗakinta tana faɗin "kin manta Umma yau ina azumin Litinin"

   Umma ta ce; "oh hakane Sam na manta kin sanni da mantuwa".

    bayan ta ajiye littafanta ta dawo gurin Umma ta ɗauko kujerar tayani gulma ta ce; "Umma Kawo na ƙarasa maki aikin"

   "Aa je ki huta ke da kika dawo yanzu, ga azumi barshi kawai na ma kusa ƙarasawa"

   

    Cikin ladabi tace "haba Umma karki hanani, akwai lada matuƙ da albarka ga 'ya'yan da suke taimakawa iyayensu, ki barni nima nasamu wannan albarkar"

ganin tadage ya sa Umma tabar mata gyaran alayyahun, zuciyarta ciki da kaunar 'yarta, yarinya mai hankali da natsuwa.

*******************************

da dare bayan sallah isha, tana ɗakinta zaune a kan darduma tana karatu Alƙur'ani mai girma, ƙanwarta Maryam ta yi sallama, sai da takai aya ta amsa sallamar "ya akayi Maryam"?

   "Aunty Amal Malam Ali ni yazo yana ɗakin baƙi yana jiranki"

wani abu marar daɗi taji ya daki zuciyarta, sai dai bata bari hakan ya bayyana afuskarta ba, cikin murmushi ta ce; "je kice ina zuwa" bayan fitar Maryam ta ajiye Ƙur'anin a ma'ajiyarsa ta fito, dama da hijabi ajikinta.

sai da taje ɗakin Umma ta faɗa mata, kafin daga bisani ta nufi ɗakin baƙi, zaune ta tarar da shi kan ɗai daga cikin kujerun da aka ƙiyamarkikin da su, ɗan nesa da shi ta samu waje ta zauna, cikin ladabi da kunya ta gaishe shi, cya amsa cikin fara'a "Malama Amal ya gida ya karatu"?

  

  "Alhamdulillah"

  ta bashi amsa kanta a sunkuyi, haka yayita magana amsar daga eh Aa, haka zancan nasu ya ki aduk lokacin da zai zo, hakan bai taɓa damunsa ba, kasanciwar halintani rashin magana, bai wani jima ba yayi mata sallama.

waceci Amal? iyayen Amal 'yan a salin Gusau ne acikin jahar Zamfara suna zaune a tudunwada bayan gidan yari tsoho, babban gidani na ilimi mahaifinta Shek Abubakar babban malamini Wanda akeji dashi bama a jaharba har kewayan ƙasar nan, yana da matan aure biyu, Mama Bintu wacci itace mahaifiyar su Zainab wacci ake kira da (Amal) kasanciwar sunan mahaifiyar shek Abubakar akasa mata, sai ƙanwarta Ruƙayya sai auta maryam,

Umma Maimuna, yaranta biyar Muhammad, Abubakar (Baba Ƙarami), Umar, Usman, Ali Haidar. Amal nada shekara goma Allah yayiwa mahaifiyarsu rasuwa sakamakon ciwon cikin dare ɗaya, rasuwarta ta girgiza Al'ummar Annabi (S.A.W) ba iyalanta kaɗai sukai rashi ba kasanciwarta kamilar mace mai haƙuri da kyan hali, Umma ta cigaba da riƙi yaranta cikin gaskiya da amana bata barsu sunyi maraicin uwa ba sai dai kukan sabo.

Amal kyakyawaci ajin farko tkana da kyan diri da kyan fuska gata da sanyin hali haƙuri ladabi Uwa uba kunya ba inda tabar mahaifiyarta kyau da kyan hali, tana da sekara sha ɗaya ta yi saukar Alƙur'ni mai girma tare da wasu littafai, daganan ta fara harda yariya ce mai shiga rai tanada matukar farin jini tana da tarin masoya sai dai tsoro baya barinsu bayyana kansu kasancewarta babban gida.

*******************************

Malam Ali ya kasance aboki ga mahaifin Amal tun suna yara,   akwai aminci mai ƙarfi a tsakanin su, ranarda aka haifita yazo ganin jaririya yana ɗaukarta ya ce; "barakallah Masha Allahu, akarmakallahu wanan 'ya kamar ita tayi kanta dan kyau, ai akarmakallah nifa nayi mata kuzama shida Malam hadi, gabaki ɗaya akayi dariya.

tundaga wannan lokacin kumai Malam Ali ya samu Amal, dukan kyautatawarsa yanaga Amal, haka Jama'a suke kiranta Amal amaryar Malam Ali tun bata fahimta harta ganu abunda hakan ke nufi, bata taɓa jin son sa aranta ba, sai dai ba wanda zai Fahimci hakan kasan cewarta mai haƙuri da zurfin ciki. Malam Ali D'an asalin sokoto ne karatun almajiranci ya kawo mahaifinsa zamfara har yayi aure anan yana zaune da iyalansa azamfara da mahaifin Malam Ali da shek sudais mahaifi shek Abubakar aminan juna ne da har amince ya rikiɗe zuwa 'yan uwan juna.

Malam Ali matarsa ɗaya Hajiya Hauwa da yaransa biyu Asma'u Halima, Amal tana gaban Asma'u a shekaru, kasanciwar matarsa ta jima bata haihu ba.

*******************************

    *Cigaban labari*

Da safe Amal ta shiga ɗakin mahafinta ta gaishi shi kamar yanda ta saba, mahaifinta ya kalleta cikin ƙauna, itace 'ya mafi soyuwa azuciyar sa, cikin kulawa ya kira sunanta "Amal"

  "Na'am Abba" gyara zamansa yayi kafin daga bisani yaci gaba da magana,

"kamar ko yaushi ba zan gaji da yi maki nasiha ba, ina mai horanki da ki bi duniya asannu, wannan duniya da kike gani tamkar kasuwaci, ko kin gama sayayya ko baki gama ba da zarar  lokacin tashinta yayi za ta tashi, to haka duniya koda shiri ko babu shiri idan lokacinka yayi ba makawa zaka karɓi kiran Ubangiji, daga ranar anyi tashin ƙiyamarki,

dan haka ko wani ɗan Adam ya na da kyau ya tanadarwa kansa kyakyawar rayuwa wacce zata amfanishi duniya da Kuma lahirarsa, ina mai horanki da kiji tsoron Ubangijinki aduk inda zaki samu kanki, salatin Annabi ya zamu abokin firarki, wannan zai sa ki samu haske arayuwarki, kiriƙi haƙuri domin shini gishirin zamn duniya kinji Mamana"?.

cikin natsuwa ta ce; "eh Abba nagode zan kiyayi Insha Allahu"

"yawwa Allah yayi maku albarka, ki kula da 'yan-uwanki, ke ce babba ki janyosu jikinki, kinuna masu abu mai kyau da Kuma marar kyau kinji"?

"to Abba" ta amsa cikin natsuwa, "yawwa maza aje ayi shirin makaranta karku makara", dama ashirye take bayan tayiwa Umma sallama taja ƙannanta suka wuce makaranta.

*******************************

ta fito cikin shiri tana sanyi da riga da siket na atamfa, ta sa Hijab ya sauko mata har ƙasa, ta je wajan Umma ta samu tana zaune a ƙofar ɗakinta tana shan iska, kasan cewar lokacin zafe ne, "Umma na shirya" 

 "Yawwa Amal ki cewa Hajiya Jummai ta bayar da cikun kuɗin jibi za atafi ɗauko mun wasu kayan"

"to Umma ina Maryam tazo Ta rakani"?

"Ita da Ruƙayya suna babban gida (gidab iyayen Shek Abubakar) Baba ƙarami na ɗaki, kira shi ya rakaki"

  "Baba Ƙarami"! 

   "Na'am Yaya" ya fito ɗaki yana faɗin "gani Yaya"

  "Sa takalmi ka zo ka rakani".

*******************************

Bayan sun karbu saƙon a hanyarsu ta dawowa wani kyakyawan saurayi yazo gabansu yana mata sallama, murya ƙasa-ƙasa ta amsa masa sallamar, tariƙo hannun Baba ƙarami rin tana ƙoƙarin wucewa ganin hakan ya sa ya sa ya sha gabanta cikin karyar da kai da taushin muryarsa ya ce; "haba malama daga ganin yanayinki nasan ba kiyi yanayi da 'yan matan da ke wulaƙanta masoyansu ba, na roƙeki dan girman Allah da Ma'aikin sa da ki taimaka ki saurare ni"

"Kayi haƙuri ni ban saba tsayuwa kan hanya nayi magana da maza ba" tana gama faɗa ta ja Baba Ƙarami su kai wucewarsu, ya bi bayansu, Amal su ka samu daidaita su ka hau yana ƙara sawa suna tafiya, ya zubawa hanyar da su ka bi idanu yana murmushi.

Amir ya zo ya tsaya gabansa ya na harararsa ya ce; "to ɗan wahala, ai sai k zo mu tafi dama na faɗama wannan da ganinta za tayi jin kai" cikin ajiyar zuciya Ahmad ya ce; "ba girman kai bane ta san kanta ne, hakan kuma ya sa ta ƙara shiga raina" yana murmushi ya ɗora hannunsa saitin zuciyarsa "ita ce mace ta farko da ta buɗe wannan zuciyar da ƙaunarta In Sha Allah za mu sake haɗuwa, ina ji a jikina ita ce uwar 'ya'yana In Sha Allah"

 Amir ya ƙyalƙyace da dariya  Ahmad ya zuba masa lumsasshin idanunsa ya na faɗin "dariya na baka ko"? Amir ya ɗan tsagaita dariyar ya na faɗin "ba dole ba wannan irin a zaɓaɓɓen oh na manta farin shiga ne a she, ka ga duk ka ɓata mana lokaci akan yarinyar da ko sunanta baka sani ba, dan Allah ka zo mu je" murmushi Ahmad ya yi yana mai jan numfashi ya furzar cikin natsuwa da shauƙi ya ce; "duk wannan ma su sauƙi ne, zan gano ko wace ce fatana ka tayani addu'a Allah ya sa ita ɗin rabo a ce"

"Allah ya tabbatar da hakan idan har ita ɗin Alkhairi ce a rayuwar abokina"

 "In Sha Allah ita ɗin Alkhairi ce".

*******************************

Tun haɗuwarsu da saurayin da bata san sunansa ba ya tsaya mata arai ta rasa dalilin hakan, ƙoƙarin yaƙinci tunaninsa take daga zuciyarta sai dai ta kasa yin hakan, baƙon yanayin za ta iya kiransa yanayi mai matuƙar wahala, yanayi ne da bata taɓa tsintar kanta a ciki ba yanayi ne da ya wuce fahimtarta, tana kwance a kan gado ta lulluɓe da bargo duk da lokacin zafi ne amma ita sanyi take ji yana ratsa dukan ƙafofi na jikinta, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, jikinta karkarwa ya ke, ta lumshi idanunta tana maganar zuci 'ni me ya ke shirin faruwa dani ne'?.

*Fulani*