2
by @sadikgg26
Sadik Abubakar
Lafazi Writers
Wattpad @sadikgg
Shafi Na 2
Tun lokacin da wan mahaifiyar Sahura ya dauko ta gidansa, Umma ta kafa mata kahon tsana, take gallaza mata da ukuba iri-iri. Dukkan aikace-aikacen gidan nan ita ce ke yin su kama daga wanki, wanke-wanke, shara, girki da sauran su. Sam ba ta bukatar ganin Sahura ta samu hutu ko kadan, aiki har da marar amfani ma Sahura yin sa take.
Komai tsananin sanyi ko ruwan sama ba sa hanawa Umma ta aiki Sahura kuma koda a cikin dare ne. Duk lokacin da aka samu akasi, Sahura ta yi kuskure, to babu shakka za ta fada wa aya zakinta a hannun Umma, za ta sha duka ba kadan ba.
Hafsat ta dauki halin uwarta, ita ma haka take muzguna wa Sahura, wulankanci da gori tana fada mata ita 'yar kauye ce kuma 'yar talakawa. A gaban Unman takan fada mata hakan amma ba ta kwabar ta balle ma ta hana ta.
A gidan nan dai Sahura ba ta samun sauki ko tausayawa a wajen kowa sai mutum biyu, Faruk da kuma shi wan mahaifiyar nata. Salim ma fitinannen kansa ne, ba shi da mutunci. Shi kam abin nasa ma ya fi muni. Yakan rika yi mata wasu abubuwa da ba su dace ba, musamman a wajen da ya ga babu kowa daga shi sai ita. Tun ba ta kai haka ba sai ya rika kokarin kai hannunsa kan kirjinta.
Lokuta da dama idan ya kintaci ta shiga toilet sai ya je da niyyar zai shiga, ya bude kofar, haka yake yi mata. Wannan kuma shi ne abin da ya fi tayar mata da hanakali, shi yasa ba ta bari su kasance ita da shi kawai a guri, domin ba ta san abin da yake zuciyarsa ba.
Shi kuwa Faruk halinsa daban ne da na mahaifiyarsa da 'yan uwansa. Mutumin kirki ne, duk abin da Umma ke yi wa Sahura a gidan nan ba ya so, ransa baci yake sosai, don haka duk lokacin da ya ga Salim da Hafsat na yi mata gori da rashin mutumci sai ya yi musu kaca-kaca.
To sai dai duk lokacin da Umma ta ga yana tsawatar musu, shi ma ya shiga uku duk da kasancewar sa babba, haka za ta rika masa fada a gaban yaran tana cewa kar ya sake shiga harkarsu. Wannan daurin gindin da suka samu, ya sa Salim yin abin da ya gadama, sannan kuma Umma ta fi son sa akan sauran 'ya'yan. Wannan ke nan.
Sahura na can kitchen tana sharar aiki tun sanyin safiyar nan, ita kuwa Hafsat na can tana sharar barcinta ko niyyar tashi ma ba ta yi ba. Haka shi ma Salim, Faruk shi kadai ne kan tashi da Asuba ya je Masallaci.
Sahura ta gama hada abincin breakfast ta shirya komai ta je ta sanar da Umma. Allah Sarki maraici! Duk wannan wahala da ta sha ba ta isa ta ci wannan abincin ba, sai dai ragowar abincin daren da suka ci suka rage, shi Umman take tura mata kuma a haka za ta ci shi da sanyi ba ta isa ta dumama shi ba.
Idan ka ga Sahura ta samu abincin da aka yi a lokacin, to dayan biyu ne, walau Faruk ne ya ba ta nasa ko kuma ya raba biyu ya ci rabi ya ba ta rabi ko kuma dai sauran da Hafsat ta ci ta rage, sai a tura mata kamar wata karya.
Wan mahaifin Sahura mutum ne da bai cika lura da abubuwan dake faruwa a gidansa ba, harkokin siyasarsa kawai yasa a gabansa, yau meeting a Abuja gobe meeting a Kaduna aikin ke nan. Don haka bai san wace wainar ake toyawa ba a gidan.
Faruk na da burin sanar da shi halin da Sahura ke ciki da irin yadda aka mayar da ta baiwa, to sai dai yana shakkar Umman tasu, matukar ta san cewa ya kai karar ta wajen mahaifin nasu to lallai sai ta saba masa fiye da tunanin duk wani mai tunani, domin a kan haka za ta iya yi masa baki ta tsine masa.
Wata rana Umma ba ta nan, sai Hafsat da Sahura kawai a gidan. Sahura na zaune a falo, Hafsat ta debo kayan wankinta har da breziya da pants, ta watso wa Sahura a kanta tare da cewa, "Tashi ki je ki wanke mini su sosai."
Shiru Sahura ta yi ba ta tanka mata ba. "Ba magana nake miki ba, yar renin hankali, ko ba za ki tashi ba ne? Me ye amfanin ki a gidan nan?"
Dago kai Sahura ta yi ta dubi Hafsat ta ce, "E, ba zan tashi din ba, kin haife ni ne? Ko don kin samu daurin gindi wajen mahaifiyarki, kyale ki nake albarkacin mahaifinki, ba na son na yi wani abin da zai ba ta masa rai, shi yasa nake rabuwa dake ba don tsoro ba."
A fusace Hafsat ta kalli Sahura tare da mayar da mata martani, "Ke! Ni kike fadawa wannan banzar maganar?"
Sai ta daga hannu ta kai wa Sahura mari, tuni Sahurar ta kama hannun ta rike gam ko matsi ba ta iyawa. "Duk ranar da kika sake hannunki ya taba jikina da sunan duka, za ki ga abin da zan miki, a ranar za ki tantance tsakanin aya da tsakuwa."
Suna cikin wannan cacar bakin ne sai ga Salim ya shigo, yana tangadi idanuwansa jajir tamkar gautan da ya shekara a rana, aiko da ganin sa sai Hafsat ta saka kuka tare da dafe ciki tana fadin, "Wayyo Allah cikina! Ta naushe ni a ciki."
Zubewa ta yi kasa a kan carpet ta ci gaba da kukan, "Wayyo cikina zan mutu! Yaya Salim za ta kashe ni."
Cikin murya irin ta makakku Salim ya ce, "Keee ba ki da mutumci dan ubanki, ke 'yar daba ce za ki ki kii kashe ta, me me mee ta yi miki?"
Bai tsaya jin amsar da Sahurar za ta bashi ba sai kawai ya cire belt dinsa ya yi ta dukan ko ina a jikinta. Ita kuwa Hafsat da ta ga haka sai ta mike daga faduwar karyar da ta yi, suka hadu suka yi wa Sahura lilis da jiki, tun tana kuka har ta kasa, har goshinta ya fashe.
Ta yunkura za ta tashi sai Salim ya sa kafa ya yi tamaula da ita, sai jini ta baki, ya fasa mata bakin. A daidai wannan lokacin ne Umma ta dawo ta shigo. Ganinsu su biyu a kan Sahura da kuma jinin da ke zuba daga goshin Sahura da bakinta bai sa hankalinta ya tashi ba, ba ma Sahura ta tambaya ba sai ta mayar da dubanta ga su Salim din tare da cewa, "Me ya faru?"
Whatsapp: ***